Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   31 / 67

90K to 93K   out of 199.9K words

ta yi tana tunanin tabbas ta taSa ganin wannan abun a mafarki, ko kuma ya taSa faruwa.

"Wallahi sai na gaya wa mama, tun da kasheni zai yi, sai na gudu na bar gidan nan"

Can kuma sai wata zuciyar ta tunatar da ita, muddin mama ta ji a kan meye, ya yi mata abun da yayi mata, ba zata goya mata baya ba, faWa za su yi, a bata rashin gaskiya, kuma a kirsheta ace sai ta faWi abun da ta sani, bayan ta riga ta ce ita ba ta san komai ba.

'Subhanallah, na fasa faWa, bari na yafe masa, wataran ya na da kirki, amma wallahi ko zai kasheni ba zan faWa masa komai ba, sai lokacin da na ga dama, bari na lallaSa na san yanzu ji yake kamar ya kashe ni' sai kuma ta Wan yi shiru ta ce "To da ya sha?e ni kuma sai na yi bacci, oho dai? Ta gama abun da Allah ya nufe ta da yi, ta yi salla ta fito dan yunwa take ji.

Adam ya tashi ya nufi Wakinta, domin ya duba ko ta na lafiya ta gama wartsakewa, sai dai ya jiyo motsi a kitchen.

Ya le?a kitchen Win, ya hango ta taka kujera, tana saka Wan wake, kamar babu abun da ya sameta.
Abun har mamaki ya bashi, kamar ya yi mata magana, sai kuma ya fasa ya fita.

Baba Uwani na ganin fitar Adam, ta lallaSo ta hawo benen.

"Sannu ?ar nan, ina fatan bai yi miki komai ba?"

Rumaisa ta waiwayo ta kalli baba uwani ta ce "Yayi mini me?".

"Ai ganin yadda ya janyo ki Win nan, abun ya tsoratani, ke ma da ko me yake bu?ata kin bashi kin wuce wurin, idan ransa ya Saci hankalinsa gushewa yake wasu lokutan, zai iya yi miki illa. Ko dai hakkinsa ki ka hana shi ne?"

Rumaisa ta juyo gaba Waya ta kalli baba uwani ta ce "Wane irin ha??i kuma?".

"A'a ha??in aure mana".

"Meye ha??in aure kuma?"

Baba uwani ta ce "Ahh shikenan, bari maganar kawai".

Har baba uwani za ta fita ta ce "Kenan papa da gaske maye ne?"

A razane baba uwani ta waiwayo ta ce "Me ki ka ce?"

"Kin ji me na ce ai".

"Ke waye ya gaya miki?"

Rumaisa ta ce "Ke ce ki ka gaya mini yanzu"

Baba uwani ta ce "Ke, yaushe na gaya miki? Ki ji tsoron Allah"

"Ke ki ka faWa, wannan ne karo na biyu ki na gaya mini, zan kuma tambaye shi".

"Dan girman Allah ki rufa mini asiri, da wasa nake yi ma fa, dan Allah kar ki gaya masa"

Rumaisa ta juya ta cigaba da saka Wan wakenta, baba uwani kuwa ta toshe baki ta na fatan, Allah ya sa kar garin neman gulma, ta janyo kwaSarta ta yi ruwa, domin kuwa ta lura bayan ?uriciya, har da wauta ke damun rumaisa.


***
"Hajiya Lubabatu, ki na free gobe in Allah ya kaimu". Mummy ta yi maganar da waya a kunneta.

"Ya aka yi ne?".

Mummy ta ce "wurin malam na gidan dutse, zaki rakani, akwai case ne".

Hajiya Lubabatu ta ce "Wane irin case kuma?".

"?an maje ne ya turo mini sa?o, wai ya ji mai martaba zai wakilta turaki, zuwa taron bun?asa al'adu da harsunan afrika, rainon burtaniya, wai ya Wauki mutum biyu a matasan yaran nan ya tafi da su, kuma da alama za a samu cigaba, wai ya ji turaki ya ce har da Adam za ayi tafiyar".

Hajiya Lubabatu ta ce "To ba sai su yi ta yi ba"

"Ina ba fa zai yiwu ba, wai ke meyasa ki ke Waukar al'amuran nan da sau?i, komai sai dai shi, duk wannan miyagun fentin da suke tare da shi, komai sai dai a saka shi, ke me zai hana a tafi da Jabir, ga mahmud, ga Jamil nan, ina su yarima jikokin mai marataba, duk ba a Wau kowa ba sai shi? A dalilin me?".

"Kuma fa da gaskiyarki Jamila"

"Dan Allah ki shirya, na ga da yadda zai tafi ai".

"Ke dole ma, zan shigo da wuri ma yi maganar, ni Jabir ne yadda ki ka san an yi masa asiri,gaba Waya hankalinsa ba ya kan harkar sarautar nan, mussman idan abu da adam a ciki, sai ka ce ya yi masa asiri".

"Ni ma na fuskanci kamar aikin da ake yi wa Mahmud ba kamar da ba, zamu haWu kawai".

***
Ko da Adam ya dawo da yamma, ya iske ruma, tana kwance a doguwar kujera, tana kallon cartoon.

Ya kalleta ya na jiran ya ji ko za ta ce wani abu, suna haWa ido ta galla masa harara, bai dai tanka mata ba, ya wuce Wakinsa.

Adam dai hatta abincin sa bai iya ci ba, yadda aka kawo su, haka ruma ta Wauka ta mayar musu.
bacci sai Sarawo, kwana ya yi ya na juyi, kuma yau sai ya kasa tashi ya yi sallar dare kamar yadda ya saba, tasbihi ma sai ya kasa saSanin da, sai ajiyar zuciya da istigfari, ji yake komai ya yi masa zafi, ba ya jin daWin komai, ko abinci ya kasa ci, ya rasa ta ina zai fara.
Sai gefin asuba barcci ya Wauke shi, ana kiran salla shi ma ya tashi.

Ko da ya dawo daga sallar asuba, neman wuri ya yi ya zauna, ya cigaba da Adduoi, sai da rana ta Waga, sannan ya tashi ya shiga wanka.

Har ya kammala shirinsa, bai ji motsin ruma ba, gashi yau Monday.
Gaba Waya ba shi da kuzari, balle karsashi, ya nufi Wakinta.

Ta na tsaye a gaban mudubi, yau ta fara saka uniform Win ta, ta saka skirt Win ya zauna a jikinta cif, da taimakon jigidar da ke Waure a ?ugun na ta.

Ta saka ?ar cikin, ta Waga kai tana ?arewa wuyanta kallo, ta na shafa wurin da ya yi mata rauni. Uniform Win sun yi mata kyau sosai.

?an gyaran murya ya yi ya ce "Haryanzu ba ki shirya ba, balle ki karya yau monday fa"

"Na gama shiryawa, uniform nake ?arasa sakawa".

Ya juya ya tafi dining ya zauna, da niyyar ko yaya ya ci wani abu, dan ya na jin yunwa, amma ya ji bakinsa babu WanWano.

Ta fito ta ajiye jakarta a kan kujera, ta nufo dining Win.

Ta buWe food flask Win abincin, soyayyiyar doya ce da miyar ?wai.

Ta ce "Bari na yi bisimillah, na ci abincinka, yau ban yi girki ba, ko sallar asuba ba ka tashe ni ba, da safe na yi salla kuma alhaki a kan ka".

Ta kama kujera, ta haye saman dining ta zauna.

Kallon ta yake, yana jiran ta yi maganar abun da ya faru jiya, amma ya ga ba ta yi ba, ta haWa shayi ta tura masa kofin gabansa, ta Wau na ta.

Jujjuya cokali ya din ga yi, amma ya gaza kai wa bakinsa ya sha.

"Wai da zafi ne shayin?" Bai ce mata komai ba, ya cigaba da kallon shayin.

"To in ?ara maka madara?" Sai a wannan karon ya girgiza mata kai alamar a'a.

"To ka sha mana, ka ci abincin"

A hankali ya kai kofin bakinsa, sai dai zu?a Wayan da ya yi, sai da yayi ta fama sannan ya haWiye shi, ?arshe ya tashi ya ce mata, ta same shi a mota.

Kasancewar rumaisa tana son shayi, haka ta haWe nasa da nata ta shanye abun ta, ta Wauki jakarta, ta ga tasa jakar ma ya bar ta a wurin, ta Wauki jakarta da tasa, ta fita.

Ta tarar da shi, ya kifa kansa a sitiyarin motar, sai da ta buWe motar, sannan ya Wago. Idanunsa sun yi ja, kamar am zuba masa abu a cikin su, har sai da ta fara fargabar ko haya?in ne zai fara fitowa, amma ta ga idon ya tsaya a haka, ya fara jan motar a hankali.

"Wai zazzaSi ka ke yi ne?" Bai amsa ba, sai lumshe ido da yake ya na buWewa.

"Yauwwa papa ka san me? Na san ba zaka amsa ba, haka mai sunan baba yake yi, shiyasa bakomai ka ke yi mini na ji haushi ba, na san ka na ji na. Dan Allah ka sai mini lunch box mana, in din ga zuba abinci ina tafiya da shi makaranta".

"Lunchbox na ?an primary ne"ya faWa a hankali.

"Eh, ni shi nake so, ?arami mai kyau" tana cikin maganar traffic ta tsayar da su, sai ga mai alawar madara, rumaisa ta tsayar da shi ta kalli Adam ta ce "Papa Wan sai mini". Ya kawar da kansa gefe, yana kallon wajen window.

Ta saka hannu ta zuge jakarsa da ke hannunta, ta ga kuWi a ciki, ta ?yal?yale da dariya ta ce "Allah ya kama ka, ga jakarka a hannuna ai, na ranci dubu Waya, idan na gama makaranta, na samu aiki, salaryna na farko zan biyaka" sai da Adam ya kalleta jin abun da ta ce, ta bawa mai alwar madara, ta ce ya bata ta duka.

Gaba Waya ba shi da kuzarin da zai biye mata, dan haka bai ce mata uffan ba.
Ita kanta ta lura shirun nasa ya yi yawa, shi kuma mamaki yake yadda duk surutunta, da mitar tsiya amma ta yi shiru, ba ta ce masa komai ba, a kan abun da ya faru.

Suna tafe ta cika masa kunne da wa?o?in indiya, ga abun da yake damunsa, ga wa?arta da ta addabe shi, kuma ya san da ya kuskura ya ce ba ya so, za ta tsiri wani abun.

Sai kuma ta koma wa?e-wa?e, masu kama da habaici "Idan mutum ma bashi da lafiya, shan kunu ba magani bane ba. Idan kuma wani abu ne yake damunsa, rashin cin abinci ba maganin matsala bane ba. Cikin mutum ne zai gaya masa, ulcer ta kama shi na ruwan rumaisa, lalaaalallaaa, alawar madara da daWi".

Duk ta yi ta gama ya na jin ta, ya kaita ?ofar makarantarsu, ta sauka ta Wau jakarta, ta shiga.

***
Ya na tsaye ya na saka lense Win rigarsa, sai kokowa yake ya saka, amma ya kasa sakawa saboda hankalinsa ba a kan abun da yake yi, yake ba, jin zuciyarsa yake tamkar a kan wuta, wata ?ishirwar baWini ce ke addabar ruhinsa, abun da yake ji a jikinsa, zai iya rantsuwa da abun da zai kashe shi, tun da Allah ya sa mama ta kawo shi duniya, bai taSa jin irin sa ba, duk yawon zuwa makaranta da yake yi, da yadda ?an mata, ke kaiwa suna komowa a gabansa, bai taSa damunsa ba, amma yau ba gaira ba dalili ?ar mutane ta tsaye masa a tunaninsa.
Mussman jiya da ya ga status Win ta, ta yi video ita da sabir, ta Wora, ya kalli status Win nan, bai san adadi ba, sai da ya fara bawa kansa haushi. Kuma ya kwanta bacci ya din ga mafarkinta, mafarkin da sai ya kai shi ga danganawa ya tsarkake jikinsa kan ya yi salla.

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ya mayar da hankali, ya gama abun da yake yi, ya fita ya yi wa mama sallama ya tafi.

Sai dai a ?asan zuciyarsa ya na jin, da zai samu dama ya ganta, wata?ila atleast, zai rage abun da yake ji a tsakanin ?irjinsa zuwa zuciyarsa, amma ta yaya?.

***
Sanin halin rumaisa na rashin isasshen saiti, ya sanya ba ya wasa da abun da ya shafeta, duk da halin da yake ciki, da lokacin tashi ya yi, haka ya tafi Waukota.

Sai dai ya shafe mituna goma sha biyar, a tsaye, bai ganta ba bai ga alamarta ba.

Sai da ya Wan tsorata, ya fara addu'a Allah ya sa ba tafiyarta ta yi gida ba, saboda abun da ya faru.

Har zai shiga mota, ya shiga cikin makarantar yana duddubawa, can ya hangota, a cikin liluka, ta ajiye Wan ?aramin hijjabinta, sai fama take yi kai ka ce wata ?ar primary 2.

Sai da ta hango shi, sannan ta saukko, ta Wauko jakarta da hijjabinta, ta zo ta wuce shi, ta tafi mota, ba tare da ta ce masa uffan ba.

"Wallahi idan ka kuma daWewa ba ka zo da wuri ba, sai na tafi gida, idan na Sata a hanya shikenan"

Ganin ya zame mata tamkar kurma, ya sanya ta Wan fara tsorata, shirun na sa yayi yawa, dan kafin su yi aure ne yake da yawan shiru, da suka yi aure ta fuskanci yana da baki, amma daga jiya zuwa yau, shirun ya wuce hankali.

Ta yi shiru ta zuba masa ido, damuwa kwance a fuskarsa. Duk sai jikinta ya yi sanyi, ta daina yi masa surutun, da neman magana.

Har suka je gida, tana tunanin, ko dai wani abun ta yi masa, yake jin haushinta, har ya daina cin abincin?.


A karo na farko tun da ya kaita makaranta, ya tarar da ita a falo, ta du?ufa ta na rubutu, bai san me take rubutawa ba, ya nufi in da take ya tsaya a kanta, takardar kifi ce, da wani math a jiki, da gani question paper ce, take ta fama sai ta yi soloving, ko a ina ta samo takardar oho mata.

?afarsa ya saka ya daki ?ashin bayanta, take ta ban?are tare da Wan yin ihu, dan ta ji zafi.

Ya zauna a kan kujera, ya ce "Samo mini abun da zan ci".

Sai da ta Wan tura baki, a ranta kuma ta ji daWi da ya kulata, har ya nemi cin wani abu.

Bayan ta tashi ya zauna ya na duba litatafan ta, maths dai gashi nan, ta na cin abun ta, daga assignment har classwork.
Sauran subjects kuwa, har 2/10 ruma ci take.
Assignment Win ma ba yi take yi ba, babu wanda ya fi kunna shi, har haushi ya saka shi dariya, irin subject Win basic technology, an basu assignment a kan cewa, a matsayin ka na matashin Wan makaranta, wani abu ne zaka iya ?ir?ira, da ka ke ganin zai amfani al'umma da ?asa baki Waya.

Shafi guda ta ware, ta zana malamin nasu, ri?e da maka a hannunsa, yana bayani, sai dai a real portrait of him, kai ba ka ce ita ta yi zanen ba, very accurate, a matsayin amsar tambayar.
Ya yi shiru yana shafa haSarsa, wasu lokutan yarinyar kamar bil'adama ba.

Ta dawo da plate a hannunta, ta ajiye masa a gabansa.

"Meye wannan?" Yayi maganar yana nuna mata litattafanta"

"Me na yi?"

"Karatun ne ba kya ganewa, ko kuma meyafaru ki ke cin wannan makin".

"Ni fa bana gane turancin da ake yi, kuma ba za ayi wa mutum bayani da hausa ba, wai ba a hausa a makarantar, yanzu haka kuWin vanacula ya kai dubu uku ake bi na, wai idan ka yi hausa Wari biyu, ina zan iya na ce idan ka zo a gaya maka zaka biya".

"Saboda ke ki ke nemo mini kuWin ko? Kin taSa ce mini ga abu baki gane ba, in koya miki?"

Ta yi shiru, ta kawar da kanta gefe, matsawa ya yi kusa da ita, yana kallon wuyanta, ciwon da ya ji mata, ya fara ba?i.

Ya kai hannunsa wurin, amma ta ri?e hannun ta ce "Meye haka?".

"Ciwon zan gani, haryanzu ban ji kin yi mini magana a kai ba".

Ta sunkuyar da kanta ba ta ce komai ba.

"Kin rantar mini dubu Waya, kuma kin ce zan biya kuWin vanacula da ki ka yi, amma yaushe zaki biyani??



Ayshercool
08081012143
Ban da kira please, what's app only =?O? masu jiran document, idan sai an kammala 1k ne document.
*Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?

Shiru ta yi masa, ta kasa magana, saboda yadda take jin wani iri a jikinta.

Ya janye hannunsa ya kalleta ya ce "Ba a bani abinci a plate".

Ta kwaSe fuska ta kalleshi, ta lura adam akwai saka aiki, ba gaira ba dalili.

Ta tashi ta Wau plate Win, sai da ta zubo a flask, da cokali, da ruwa ta kawo masa, ya ce mata ta kunna masa tv.
Sai da ta ji kamar ta yi tsaki amma ta fasa, ta kunna ta dawo ta zauna, sai dai ta lura da yanayin sa, abincin ba wai daWi yake yi masa ba, ci kawai yake yi.

"Papa maiyasa idonka yake haya?i, idan ka yi fushi?"

Yayi dariya ya ce "Sai ka ce generator, ko wani murhu, saboda gani jarababbe"

Ganin ya mayar da maganar shirme, ya sa ta yi shiri.

KaWan ya ci, ya rufe, a lokacin ta fara ?o?arin mayar da litatafan ta, ya ce "Ban gama da litattafan ba".

Ya karSa ya cigaba da duddubawa, a hankali ya din ga bi Waya bayan Waya, ya na sake yi mata bayanin darussan da aka koya mata, sai a lokacin ta ?ara ganewa ta kalleshi ta ce "Ai da za a din ga yi mini da hausa, da sai na fi ganewa".

"No, da turanci suke magana, ni ma da turancin zan din ga yi miki magana".

"Ashe za ayi zaman kurame, dan bai fi kalmomi, sha biyu na sani da turanci ba"

Bai bata amsa ba ya cigaba da cewa "Zan saka a ki islamiyya, ko ba na nan, sidi zai din ga kai ki yana Wauko ki, sannan wannan zanen da ki ka yi, ki goge shi, ki rubuta wani abun".

"Ba ka san ma'anar zanen nan ba, duk makin da na ci zan zo na nuna maka" ta ?arasa maganar tana tattare litattafan ta, a cikin jakarta, daga nan ta mayar da hankali kan abun da yake kallo.

Film ne na Hollywood, sai dai yadda ake nuno matan, bai yi wa rumaisa ba, ta din ga kawar da kanta gefe, ba ta yi aune ba ta ga ana kiss, da sauri ta saka?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? hannu ta rufe idanunta, ta sunkuyar da kai.
Sai dai ta Waga kanta, ta gefen ido, ta ga takawa ko a jikinsa, ya cigaba da kallo.

"Ka canza mana wannan tashar"

Ya ce "Saboda me?".

"Ba ka ga abun da ake yi ba?".

"A ina?".

Cikin ?ulewa ta ce "Ka na gani ana abun da bai kamata ba, amma ka ke kallo, mama ta ce ba kyau, a gida ba a bari mu kalli irin wannan film Win ma fa, ka daina gani za ka makance".

Ya kalli cikin ?wayar idonta, iya gaskiyarta take gaya masa, bai ga alamar wasa a abun da take faWa ba.

"Ko zamu gwada?" Yayi maganar yana tsareta da ido.

"Waro masa ido ta yi ta ce "Mu gwada me?".

"Kiss Win"

Mi?ewa tsaye

31 / 67