Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   63 / 67

186K to 189K   out of 199.9K words

?arya take yi, binciken su Jamil da kama shi da aka yi fa?.

Ammi kuwa ta wani fannin a iya cewa, rashin lafiyar Mahmud gaba ta kaita, domin kuwa sun fi ?arfe biyu suna hira.
Ta yi iya ?o?arin mantawa da abubuwan da suka faru a baya, ya bata labarin makaranta, da yadda ya samu kansa a wurin aiki, amma a cikin hirar ya din ga haWawa da abubuwan alkhairin Mummy.

Sai dai ga marasa gaskiya, ciki ya Wuri ruwa, Samha ta din ga kiran wayar baba uwani, dan tabattar da abun da rumaisa ta faWa a bakinta, amma wayarta ba ta shiga. Gashi ba tare da saninta ba, maman su, ta je ta sanarwa da turaki komai, cikin bala'i da tashin hankali, kuma ta kira wambai ta gaya masa, cewar takawa ya mari Samha, kuma ya ce a kan matarsa ba abun da ba zai yi ba, sai dai zumuncin ya watse.
Ga gefe guda, Hajiya Lubabatu ta kai ?arar Mahmud, wai Mummy ta saka shi, ya yi wa Jabir duka, ya saka an rufe shi, ba tare da ta san wani station Win aka kai shi ba.

Samha ta san muddin aka yi zaman nan, to fa kashin su ya bushe, domin wannan matar ta takawa, ba mutunci ne da ita ba.

Suna tsaka da wannan bala'in, maman ta lura da wuni guda, yau Jamil bai kira su ba, sun kira shi amma ba ta shiga, hakan ya ?ara dugunzuma hankalinsu.

Dan haka marasa gaskiya, bacci sai rabi da rabi.

***
Da safe ruma ko ta kan takawa ba ta bi ba, ta shiga sabgoginta, Asiya ta tayata gyara Waki, saboda yadda cikinta ya fara tsufa, duk da ba a gani, sai ta saka kaya ?anana.

"Rumaisa" ta ji ya kira sunanta.

"Ba zamu Asibiti ba?"

"Sai ka dawo, kar na je na kuma Sata muku zumunci"

"Kiyi ha?uri, na rasa yadda zan yi ne"

Ta ce "Ni ba zani ba"

"Dan Allah "

Ruma ta ce "Ba fa zani ba, idan an shirya zama a gaban Wamban, na je kuma ba zan yi magana ba, sai da ?an sanda a wurin".

Juyin duniya ruma ta ce ba in da za ta je.

Ya ?yaleta ya fita tafi.

Ya tarar da ammi, tana bawa Mahmud abinci a baki.

Takawa ya samu wuri ya zauna, yayi shiru bai ce komai ba.

Ammi ta ce "Takawa, ya dai?"

"Bakomai" zata sake magana Mummy ta shigo, Mahmud ya ce "Mummy sai yanzu ko?"

"Eh ai jiya korata aka yi, aka nuna bani na haifeka ba, ba dan kai ne ba ba abun da zai dawo da ni".

Ya ce "Allah ya baki ha?uri, a cewa likita ya zo ya sallame ni, saboda ayi ta ?are a yau"

Mummy ba wanda ta kula sai mahmud, suma ba su kulata ba.

"Mahmud ina ka kai Jamil ne? Kana a wannan yanayin zaka je wani wuri? Ka sa matar nan ta tayar wa da mutane hankali, sai bala'i take yi. Ta shafa mini kashin kaji, wai ni na saka ka dake shi ka kulle shi. Ga wani zancen ma wai ko an kama Jamil gaske ne ko ?arya oho"

Ammi ta ce "Kenan maganar ruma gaskiya ce"

"Ba da ke nake ba, da Wana nake malama" Mummy ta yi maganar gatse-gatse ga giwa.

Ammi ta ce "Allah ya baki ha?uri"

***
Katafaren falon ya cika ga Wambai, ga turaki da wasu manya daga masarautar kano.
Ammi ta hallara, ga Mahmud dan ko gama warwarewa bai yi ba. Aka jima sai ga rumaisa da takawa, Bashir jami'an tsaro da wasu daga cikin yayyen rumaisa, ga Samha a wurin da mahaifiyar ta, ga Hajiya Lubabatu da duk wanda yakamata su halarci zaman.

Gaban Samha sai dukan uku-uku yake yi, dan bata san mai rumaisan za ta kwatsa ba.

Wambai ya ce "Su kuma waWan nan lafiya?" Yayi maganar yana nuna jami'an tsaro, da suka shigo da jabir, a wahale.

Bashir ya ce "Ranka ya daWe, zuwanmu wannan zaman yana da matu?ar muhimmanci, zaka ji dalilin zuwanmu in sha Allah. Zuwanmu nan ayi tattaunawar da mu, sai ya fi sirri, saboda wasu abubuwan da za a bayyana, akwai kunya ace wasu laifukan daga gidan girma da daraja suka fito"

Adam ya ce "Allah ya taimake ka, wannan ita ce rumaisa matata kamar yadda ka sani, waWan nan kuma ?an uwanta ne, wannan kuma abokan aikina ne"

Wambai ya kalli rumaisa ya ce "Ke! Ke ce mai haddasa mana husuma da tashin hankali a cikin family ko? Kafin ki zo lafiya lau mu ke zaune, amma daga zuwanki kin hargitsa komai, ki ce wancan yana asiri, ki ce wannan baya son wannan saboda me?" Ya fara yi wa ruma faWa, tayi shiru ta sunkuyar da kai.

Turaki ya ce "Ina ganin, a fara bari mu ji ta bakinta tukuna ranka ya daWe, kar a yanke mata hukunci kai tsaye"

Wambai ya kalleta ya ce muna saurarenki.

Ruma ta ?ulu, basarwa kawai ta yi, ta haWiye wani abu mai Waci sannan ta ce "Kafin na ce komai, zan fara da bawa babana ha?uri a kan abubuwan da zasu fito daga bakina, duk da ya san wasu, na san bai san wasu ba. Ina neman afuwarka babana mai girma turakin kano"

Turaki yayi murmushi mai ciwo, sannan ya ce "Kar ki damu yarinyar kirki, kamar yadda na ri?e miki al?awari a baya, ina umartar ki da ki faWi komai, dan fita daga zargi.

Ayshercool.
08081012143
08081012143

Rumaisa ta ja numfashi, sannan ta fito da wata waya, duk ta sha jiki, screen Win ma duk ya tsage, ta ce "Wannan wayar, ita ta fara haWani da takawa, kafin ?addara ta sake haWa mu a karo na biyu.
Silar haWuwarmu na farko wannan abu ne da ya shafi rayuwarmu ni da shi, bai shafi abubuwan da suke faruwa a yanzu ba"

Ta Wan yi shiru sannan ta cigaba da cewa, "Kamar yadda wasu suka sani, yayyena maza ne, nice ?arama da duk wanda ya sanni, aka yi mini shaidar rashin ji.
Wannan wayar na Wauke da wasu abubuwa da ka iya taimakawa jami'an tsaro, saboda a rashin ji na, bani da tsoro, kuma cikin ikon Allah ranar da mu ka tafi kai ziyara dangin mahaifina, muka haWa mota da ?an bindiga. A cikin wayar akwai hotunan wurare da abubuwa da na yi ta Wauka, ciki har da jakar bullet mai Wauke da wasu lambobi, da sunan SMOKE.
A rashin ji na, na tattauna da ?an bindigar, har shugaban su yake ce mini, ?asa ta san da zaman su, dan kuwa akwai kason su, a kasafin kuWi da ake duk shekara.
Kasancewar a lokacin bakomai nake ganewa ba, amma na fuskanci wasu abubuwan.

Zuwana garin su babana, wanda ?an bindiga kusan suke mulkar garin, nan ma nayi wata tattaunawar da wani dattijo da aka ?ona rigar su, sai shi kaWai, wanda shima yana da ala?a da ?an ta'adda.

Daga nan har zuwa lokacin da aka yi garkuwa da ni, abubuwan dai tamkar a mafarki, duk yadda za a bawa mutum labarin yadda abun yake, sai ya je ya gani. Na sha ba?ar wahala saboda ina da taurin kai da rashin jin magana, na daku kamar ba mutum ba, saboda ban daina rashin kunya ba.

Kwatsam! Aka kawo matar da silarta abubuwa da dama suka faru, mace da tsohon ciki, ta din ga magiyar a bari ta tafi, ko dan cikin jikinta, aka ce a kula wannan ajiyar wakili ce".

?iff Wakin yayi, Wambai ya ce "waye wakili, wane waikilin tukuna".

Turaki ya ce "A daina katse ta, mu bari ta kammala tukuna".

Rumaisa ta Wora da cewa "Lokacin da ta zo ina tsaka da rashin lafiya, halin da take ciki bai dameta ba kamar ni, ta kula da ni sosai da sosai, sai dai wasu lokutan sai tayi ta kuka, idan na bata ha?uri sai ta ce; ba sace ta da aka yi ne dameta ba, mijinta, ba yadda bai yi da ita ta fasa tafiya ba amma ta?i, sai kuma sanya hannun Wan uwanta a wurin saceta.

Ta bani labarin mijinta, iyayensa, yadda suke rayuwarsu, da kuma irin rayuwar da tayi a nasu gidan.

Ta gaya mini mahaifinta ya saka sunanta a kadararsa, kuma wasu kuWinsa na shiga account Win ta, saboda ita bai taSa mallaka mata wata kadara ba, saSanin ?an uwanta, da kowa yana da wani muhimmin abu da ya bashi.

Ta gaya mini matar mahaifin ta da yayyenta, sun uzzura mata sosai a kan hakan, kuma babu wanda ya san da zuwanta Nigeria, sai yayanta da ta gayawa, ta sanar masa ga ranar da zata je dubiya....

"?arya ne, me ki ke nufi, Jamil ne ya sanya aka yi garkuwa da aisha, wallahi ?arya ki ke yi, ni za a yi wa sharri, a cuci Wa na a Sata mana suna"

Wambai ya Wagawa babar su Jamil hannu, ya dubi ruma ya ce "Wani tabbaci zaki bamu a kan haka, ta yaya zamu yarda da ke?".

"Na yi wa anty aisha al?warurruka, bayan ta ce mini ta bani amanar mijinta da Wan ta, duk da ?arancin shekaruna, na fahimci abubuwa da dama a labarin da ta gaya mini" rumaisa ta basu labarin komai, har kan mutuwar aisha.

Ta kalli Abdallah ta ce "Bismillah"

Abdallah ya dawo tsakiya, ya zauna da kayan zanensa.

Ruma ta ce "Wannan yayana ne, kuma ?wararre ne wurin iya zana abubuwa, da shi nake koyi, ya sanya nima na iya zane-zane, amma kasancewata ?ar koyo, zan ba shi damar ya zana wani abu, kar ace na yi son zuciya ko sharri nake son yi wa wani, yana daga in da yake zaune, zan siffanta masa abun da zai zana Win, Abdallah ba ya nan aka sace ni, nikaWai aka sace, dan haka you should be good in judgment"

Kowa yayi shiru ya zuba musu ido, sannu a hankali take siffanta masa abubuwa yana zanawa, bai ja lokaci ba ya kammala zanen ya mi?a musu takardar da yayi zanen a kan ta.

Ta siffanta masa Mutanen da suka je suka Wauki gawar aisha ne, da motarsu, da yanayin da suka Wauki gawar.

A yadda rumaisa ta suffanta masa ya zana, Jamil ne a gaba cikin kayan ppe, amma yanayin tsayuwar da sashin da aka iya gani na fuskar sa, zai tabbatar maka da shi ne, idan har ka san shi.

A lokacin takawa ya tuna a tsukin lokacin yayi ta fama da faWuwar gaba, da fita hayyaci, kuma Jamil yayi balagro a lokacin.

Mahaifiyarsa ta cigaba da bala'i, da i?irarin wannan shegantakar banza ce ba Jamil ba ne ba.

Mahmud ya ce "Allah ya baku yawan rai, muna da shaida ta gaba, ban sani ba kafin ni, ko ta gaya wa wani, amma ta same ni da maganar, kuma da ni da wasu daga cikin ?an uwanta maza muka yi aikin nan.
Akwai lambar waya da ta bani, lokacin tana magiyar a kai aisha asibiti kan ta rasu, ita ce lambar da aka kira, na bayar an yi tracking Win ta, haka zalika Wan uwanta Yasir yayi tracking Win ta, an daina amfani da layin, amma Jamil ne yayi register da layin, Yasir na da tracking result Win sa, ni ma ina da nawa da police suka yi"

Wani daga cikin ?an sandan ya ce "Amma wannan ai aikin police ne, mu yakamata ace mun yi shi, ko shi Adam tun da jami'in tsaro ne".

"Ban ji na yarda da kowa ba da zan iya Waukar shaidu, masu muhimmanci na bawa ?an sanda ba, dan a lokacin na ji takaicin ace ?asata da jami'an tsaro amma aka kasa kuSutar da ni, daga hannun ?an bindiga, kuma ?an bindiga da kansu, suka tabbatar mana da kun san da kune ku ke sau?a?a musu aiki, ku jami'an tsaro.
Takawa kuma ban gaya masa komai ba, saboda a wancan lokacin yana cikin damuwa da tashin hankali ne, da kuma fuskantar matsin lamba daga mutane, a yadda yake a zuciye zai iya Sata komai a wannan lokacin.

Maganar ina ?o?arin Sata zumunci ta hanyar haWa husuma kuma, ina da shaida babu wanda na yi wa sharri, ranka ya daWe wannan ledar ta gabana, cike take da kayan tsubbu da na sanya baba uwani tsohuwar hadimar ammi tonewa, kuma nayi amfani da wayar Waya daga cikin ma'aikatana, na naWi duk abubuwan da aka saka ta yi mini, suma suna cikin wannan wayar na tura a ciki".

Adam ya tashi jiki a matu?ar sanyaye, ya Wauki excuse ya fita amsa waya.

Tun da suka shiga ake kiran wayar, sai dai da ya duba ya ga private number na.

A yadda ruma suka tsara da Mahmud, shi ne zai faWi abubuwan da suka shafi Sangaren Mummy, kutungwilar da take shiryawa amma ya kasa.

Turaki ya sunkuyar da kai zuciyarsa na yi masa raWaWi, saboda abun duniya yana ciki Waya da aisha, ubansu Waya, ya sanya aka saceta, kuma yake ta ?o?arin sanyawa a Wora zargi a kan Adam, Adam Win da ya kasance abokinsa Wan uwansa da suka tashi tare.

Kuka matar turaki take yi, ta ce "Ita haryanzu ba ta yadda da cewa Jamil zai iya aikata mummunan abu irin haka ba sharri ake yi masa".

Bashir ya ce "Hajiya sai dai ki yi ha?uri, domin kuwa jami'anmu sun riga sun kama shi ma"

Mahmud kuwa ya dubi Jabir, sannan ya mayar da idonsa kan Hajiya Lubabatu ya ce "In faWi me Jabir yayi, ko kuma in bari ku faWa da kanku?"

Suka yi tsit babu wanda yayi magana, Mahmud ya ce "Dole ka cigaba da zama a hannun 'yan sanda su kammala bincike"

Wambai ya ce lallai a nemo masa baba uwani duk in da take, gaba Waya falon ya hargitse da hayaniya.

Rumaisa ta ce "Babban ro?on da zan yi muku shi ne, kar wanda yayi ?o?arin yin wani abu a kan wakili, saboda nikaWai ce shaida a kansa, sai dai in Jamil ne ya yi magana a kan sa, idan ba haka ba".

Bashir ya ce "Haka ne, amma ban taSa tsammanin wakili zai kai haka ba, saboda tsamar da ke tsakanin sa da Adam ba"



Adam ya Waga wayar tare da yin sallama "Na san ko ban yi magana ba, ka san da wanda ka ke magana, Senator mai wakili ne. Ina tayaka da ?an team Win ka murnar gano suwaye SMOKE. Sai dai nikaWai ka sani a SMOKE, amma ka sani gano smoke ba shi da wani amfani, saboda su kansu wanda ka ke tunanin zasu Waukar maka matakin suna cikin SMOKE.
ministan man fetur ke da shiyyar satar mai, ?angaren tsaro suna da kamasho a kasafin da ake yi, da wasu manyan mutane a ?asar nan.
Talakawan da ka ke yi domin su, basu isa su yi maka komai ba, duk wata shaida da kake tunanin kana da ita a kanmu, akwai gaSar da idan aka kai, kai ne zaka kwana a ciki, dan na san baka isa ka yi jayayya da shugabannin rundunar tsaro ba, ba ka da wata shaida a kan sa.
Dan haka kai zaka kwana a ciki, duk yaranmu da ku ka samu ku ka kama, babu wanda ya san suwaye SMOKE, kai kaWai ka yi nasarar gano suwaye, Wan uwanka Jamil yaron Khalifa ne, tare da shi suka yi aiki, sai dai shima bai san mune SMOKE ba, mun yi amfani da sace matarka, wurin Wauke hankalin ka daga kanmu, kuma cikin ikon Allah ta haihu ta rasa ranta. Abu Waya zuwa biyu nake son gaya maka. Ka bar al'amarin nan a iya haka, idan ba haka ba zaka yi ta ranka, ko kuma ran matarka da Wanka, dan kuwa? ita ce duk sanadin komai, dan kuwa duk motsin ku, da duk abun da take yi, muna samun labari ta Sangaren Jamil.
Dan haka sai ka zaSi Waya, fito na fito da masu ?asa, ko kuma ka rasa rayuwarka da na matarka, dan ka san ba abu ne mai wahala ba. Sai dai fa ka yi ha?uri, domin kuwa rayuwar matarka ta salwanta kamar ko wani karabutin Wan ?asa, duk da kasancewar ka mai kaki, kuma jinin babbar masarauta, ire-iren yaranmu ne kisan su baya tafiya a banza. Kuma duk wani abu da zai faru Jamil ba zai taSa furta sunana ko na Wa na ba. Dan haka gara ka watsar da duk wani yin?urinka, ka tattala abun da yayi saura a rayuwarka, kan mu gama WiaWaita ku" ya katse wayar.

Duk da hatsaniyar da ta kaure a falon, yanayin da takawa ya shigo, ya sanya kowa yin shiru, wani irin gumi yake yi, jikinsa yana tsuma, kuma aka rasa mai tambayarsa meyafaru, kowa ya zuba masa ido.

Ruma ce ta mi?e tsaye, ta ce "Papa lafiya kuwa?"

Gabanta ya ?arasa, jiki a matu?ar sanyaye ya zube a kan gwiwoyinsa ya furta "Na gaza, dama kin gaya mini, na gaza rumaisa ba laifina bane, na yi iya yina, abun ya fi ?arfin yadda nake tunani, na barwa Allah, tun da a cikin gidanmu ma aka kware mini baya, ba ni da saurin ?warin gwiwa. Da izzar da tawa da sarautar tawa da komai na zube su a kan gwiwoyina, na gode rumaisa, na gode. Ke alkhairi ce ga rayuwata da ahalina, wata?ila ba dan ke ba, ba zan gane bara gurbin da suke rayuwata ba" Hawaye yake zubarwa kamar ?aramin yaro, cike da ?unar zuciya. Lallai faWa da aljani ba daWi, shiya san bai isa cigaba da fito na fito da wannan mutanen ba, in dai a Nigeria ne, mutane sun san ta'addancin Smoke, sai dai basu san suwaye ba, kuma wani abun shaidar rumaisa kawai ba zata wadatar ba, hakazalika da rayuwar rumaisa ta salwanta gara ko menene ya ha?ura da shi, yarinyar tayi sacrificing alot".

Rumaisa ta dur?usa ta ce "Papa dan Allah ka tashi, ka sakani a duhu, ni ban gane me ka ke nufi ba, ka tashi dan Allah, a gaban mutane ne fa"

Mahmud ne ya tashi ya kama Adam, ya mi?ar da shi tsaye, ya ja hannunsa ya cewa rumaisa su tafi.

?an sanda suka tattara duk wasu bayanai da suka kamata, wanda rumaisa ta bayar, da zanen Abdallah da aikin da Yasir yayi, Bashir ya karSe ya ce sai sun kammala na su binciken tukuna, zasu gani idan da yiwuwar ba wa ?an sanda.

Wambai kansa ya girgiza da jin lamarin, tausayin Wan uwansa turaki ya kama shi.

Sosai babar Jamil ke kuka, tana cewa turaki ya saka baki, ya ?aryata abun da suka faWa, ya sanya a saki Jamil.

Wambai yayi mata tsawa, ya ce su tashi su tafi sai ya sake nemansu.

Mummy godiya ta yi wa Allah, da ba a faWi komai a kanta ba, Hajiya Lubabatu ta zube tana yi wa wambai

63 / 67