AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   91 / 95

270K to 273K   out of 283.8K words

murya suka sinkayo tana fad in  You should have thought about this a lokacin da kuka kashe nawa D an.!

Zuciyar Hisham Tai wani irin tsinkewa.. A hankali ta furta  DAREEN..!

Dareen taci gaba da tura wheelchair din da take zaune bisa har ta k araso yanda Hisham ke kwance tamkar Wanda yai paralyze.

Jikin Anisa Ya d auki rawa daga nan yanda take kwance shame shame.. Ta soma k ok arin jada baya cikin tsananin tsoro tana cije keb e sabida azaba. Har lokacin jikinta karkarwa yake tamkar wacce taga fatalwa.

Dareen ta dubeta sai ta shek e da dariya  Ina zakije Anisa..? Tsoro kike kinga fatalwa.? Kun zata Kun kashe Dareen koh..? Kun zata Dareen ta tafi bazata dawo ba ko.? Sabida Kun cika marassa kunya harda zuwa ku aure juna.?! Sai ta kuma darawa  But you two look perfect together..! Ku biyun Kun dace da juna.!

Cikin jin jiki Anisa ke tamke ido tana girgiza kai lokaci guda take furta  Dan girman Allah kiyi hakuri Dareen..! Wllhi ba abinda kike tunani bane.. Ban auri Hisham dan ina son kasancewa dashi ba..! Wllhi he tricked me too..! He betrayed me kaman yanda yaci amanarki.. Na amince da Aurensa ne dan na kawo k arshen yaudararsa da fuska bayinsa.. Cikin da kika gani jikina ma wllhi fyade Ya mun bada son raina bane..! Bata kai aya ba taji sauk an Mari maiji da lafiya a fuskarta Wanda Ya k ara had a mata jini da majina.

Dareen taci gaba da huci tana duban Anisa  Sa anki d aya Anisa ni mace ce da bata yarda aci zarafin wata mace ta hanyar fyade ba.! Because I believe babu macen da ta cancanci aci zarafinta ta hanyar fyade komin munin halinta.. Ba don haka ba da wad ann k artan zansa suyita sukuwa akanki sai tsinannen dake cikinki Ya fita fit.! Amma da nau ukan azaba sai na ciresa kafin Haidar ya iso nan.! Dareen ta kuma bud e murya tace  Kelly.! Take wann k aton Ya k araso gabanta yana risinawa. Nan tabasa umarni da Ya zana Anisa da murd add iyar bulalar dake hannunsa.
Kan kace me Kelly ya shiga nade bulalar dake hannunsa Ya shiga zuge Anisa dashi tana sakin k aran azaba dan ko motsawa bata iyayi.

Hisham Ya zaro ido waje daga nan yanda yake karb an nasa hukuncin. Cikin tsananin rawar murya Hisham ke fad in  Please don t Dareen.. Don t kill my child please..! Anisa is pregnant with my child.. She s three months pregnant.. Ina son cikin nan fiyeda komai a duniya Dareen.. Ki kasheni idan kina so.. Ni na miki laifi.. But please sapere my child..! Let the child live please.. Kiji tausayin jaririn dake ciki Wanda baida hakki..!

Wani kafurin dariya Dareen ta kece dashi tana duban Hisham  Unbelievable..! Ban iso kanka ba cikakken D aniska.! Ni zaka duba kace I should spare your child.?! Did you spare my own child Hisham..?! Ta kuma kecewa da dariya kafin taci gaba  Wai ni kake ce na tausaya ma jaririn cikinka da baida hakki..? Ka mance lokacin da kai da wann k aramar doluwar kuka murk ushe nawa jaririn da tayun mota.?! Ka gaya min Hisham nawa jaririn shi hakkin uban wa yaci cikinku.?! Taci gaba da jinjina Kai tana dubansa  Gwara ma wann shegen dake cikinta iyayensa tsinannu ne azzalumai Watak ila zunubinku Ya shafe shi.. Amma ni nawa jaririn fah.? Cikin innocent Haidar ne Hisham..! Haidar shine uban jariri na..! mutumin da ka tarwatsa masa rayuwa kai destroying d insa from the root..! Uban cikina is innocent..! shi aka zalunta cikin gaba d aya labarin.! Taci gaba da jinjin kai tana duban Hisham  Kamar yanda zan k araci rayuwata saman wheelchair sabida murkushe mun k afafu da kukai da mota, kaman haka zan tabbata ka zama paralyzed for the rest of your miserable life Hisham..! Kaman yanda kuka kashe D ana da Haidar yana watanni uku kacal a ciki..! Kaman haka zan kashe wann cikin naku mai watanni uku a ciki..! Haidar zai k araso nan Hisham.. Zaka bud e baki ka sanar dashi komai..! Ina nufin komai..! Duk abubuwan da kai masa a rayuwa..! Duk shiga rayuwarsa da kai..! Duk tarwatsa masa rayuwa da kai.. Zaka bud e baki ka karanto zunubanka gaban Haidar..! Ko d aya bazaka bari ba sai ka fad a taryan taryan..! Ta k arashe tana mai kiran d aya gardin tace Ya sake mana ma Hisham igiyan shocking.

**

Cikin zuban hawaye take duban Hajja, da kyar take furta  Dan Allah Hajja kice mun bai kai kansa ma  Yantadda kaman yanda suka nema ba.. Ta rintse idonta hawaye na gangaro mata  Yau Aurenmu yake cika watanni uku cif a karo na biyu.. Hajja dan Allah kice mun zai dawo gareni kice mun ba AUREN WATA UKU muka sakeyi ba..! Ya mun alk awari wann karon Aure mukai na Har abada.. Dan Allah kice zai dawo gareni.. Idan na rasashi nima mutuwa zanyi Hajja..! Ta k arashe tana kame k irjinta tana kuma rintse idonta dake ci gaba da zuban hawaye.!

Hajja Tai k ok arin maida nata hawayen tana jijjiga Ummul take fad in  Ki daina maganganu irin haka Ummul. Ba abinda zai samu Haidar.. Ba abinda zai samesu gaba d aya da izinin Allah. Haidar zai dawo gareki Babu zancen AUREN WATA UKU tsakaninku.. Zakuyi rayuwa mai tsawo tare in sha Allah kinji koh.. Kici gaba da ambaton Allah kinji koh. Da sannu zai kawo mana sauki cikin al amarin.! Ta k arashe hawayen da take ta k ok arin dannewa na zubo mata itama.

Mommy da Aunty Asshe ma an rasa mai bama wani baki Hilal na tsakiyansu Ya rungumesu dukansu biyu shima hawayen yake Ya kasa jurewa. Aunty Asshe fad i take  Ina yawan kiran Anisa shashasha kun sani..? Amma lokacin da akai Aurenta sanda zasu tafi SouthAfrica.. Kun san mai tace min da muka keb e a d aki.? Ce min Tai Ammi ki yafe min.. Nasan na sakaki bak in ciki da dama because of my stupidity..! Asshe yaci gaba da hawaye tana jinjina kai  Sai tace min I ll make it up to you Ammi..! You will be proud of me..! Ammi Ina sonki..! Kice ma Abba ya yafe min.. Kuma kice ma Hilal ina son shi.. And I thank him for always having my back.! Ta k arashe cikin kuka yayinda Hilal ma ta matse hawayen da suka gangaro masa.

Mommy kam bata iya cewa komai ba sai hawaye dake ci gaba da gangaro mata tana tuna randa ya dage sai an basa matarsa da D ansa Sun tafi.. Ta tuna irin draman da akai kafin ta amince Ya d auki iyalinsa su tafi.. Ta tuna saida ta aje masa mata na tsawon watanni uku kafin ta basa matarsa.. Ta tuna sanda ya shigo ya mata Sallama da kalamansa na soyayya a gareta. Ta tuna yanda yaita bata hakuri yana fadin bazai tafi ba sai ya daina fushi dashi kuma sai ta saka masa albarka. Sai Mommy ta rintse ido hawaye masu tsananin zafi suna gangaro mata  My prayers are with you Son.. Allah bazai basu dama akanka ba.! Ta k arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.


Daddy kuwa yana daga waje bakin parlorn shida Alhaji Gimba yanda Alhajin Gimban keta k ok arin kwantar ma abokin nasa hankali.

Duk k arfin hali na Daddy saiga hawaye na gangarowa daga idonsa. Ya kuma d agowa yana duban Alhaji Gimba. Cikin zuban hawaye Daddy yaci gaba  Gimba my two Sons.. Yarana guda biyu wanda nai failing dinsu tin suna yara ko ince Tun suna ciki basu zo duniya ba..! Wad anda Allah ya bani su cikin tausayinsa da jin k ansa da kuma rahamarsa amma sai nai masa butulci ban nuna godiya a gareshi ba.! Guda d aya na sheganta shi da harshena na koreshi tin yana ciki.. Ya girma babu mahaifi..! Guda d ayan kuma.. Ya girma gaba na amma banyi appreciating d insa ba. Ya girma tamkar Babu mahaifi sabida wofantar dashi da nai akan idona..! Yau gashi dukansu biyu suna hannun barayin Daji Gimba.. Su biyun sunyi abota tin basu san sud in  yanuwa bane. Amma abotan Ya koma k iyayya a lokacin da Ya kamata sufi son junansu bayan sun fahimci Sun had a mahaifi guda.. Gimba inaji kaman ni na haifar da conflict d in dake tsakanin yarana guda biyu.. I failed them both.. And now.. Ban sani ba.. Ko dai na sake ganinsu ko ba na sake ganinsu ba..! Gimba kana ganin Har yanzu Ubangijina hukunta ni yake akan laifuka na na baya.?! Ya k arashe yana girgiza cikin zuban hawaye.

Alhaji Gimba Ya girgiza kai  Kar kayi magana irin haka abokina. Duk abinda Ubangiji Yayi daidai ne. Ba a saka ayar tambaya. Tsarki ya tabbata gareshi mai mulkin sammai da k assai mai juya al amara yanda yake so. Idan yaso Yayi mana rahama idan yaso Ya azabtar damu duka iko nashi ne akan halittunsa. Sann duk halinda muka tsinci kanmu ciki rahamarsa ne. Ya dan numfasa kafin yaci gaba  Ka daina dawo da kurakuren da kai baya kana azabtar da kanka dasu. Mu dukanmu  yanadam ne kuma masu kuskure sann mafiya kyawun masu kuskure cikinmu sune masu tuba. Wanda mukai tuba na gaskiya dominsa Ya sani sann shi d in mai yawan gafara ne mai jin k ai. Ya dan dafa hannun Daddy  Tabbas idan Munyi imani za a jarabce mu.! Kai hakuri abokina kai tawakkali. Ka saka ma ranka wann rajabawa ce daga Allah.. Muyi addu an Allah Ya kub utar dasu Ya dawo mana dasu lafiya..

Daddy ya amsa da Ameen yana mai waigawa ko zaiga Sadis amma bai gansa nan wajen ba.

Alhaji Gimba Ya gyara zama yace  Kuma Haidar kawai suka nema yakai kansa.? Sann meyasa baayi gaggawan sanar da jami an tsaro ba dan a samu a shawo matsalar da wuri.

Daddy yai saurin girgiza kai  A a Gimba rayuwar yarana are at stake here.. Kaga ita Anisa ma cewa sukai juna gareta kaga dole abisu yanda suka buk ata kasan yanda wad ann azzaluman mutane suke gudanar da al amaransu sam babu Allah a ransu Gimba. Yanzu mistake kad an zaayi su hallak a min yara gaba d aya. Watak ila idan Haidar yaje su nemi Ransom mai tsoka.. Ni ko rayuwata suka nema ba Kampanina da abinda na mallaka ba zan basu dan su sako yaran nan Gimba.

Alhaji Gimba Ya tsare Daddy cikeda tausayawa. Sai yana tuna lokutan baya da Daddy ke cewa kampanin sa Ya fiye masa Haidar. Yau gashi yana ce zai sadaukar da komai nasa dan ya ceci Haidar ciki harda rayuwarsa. Ya dan numfasa sai kuma yace  Amma akwai alaman tambaya a nan Abokina.. Meyasa zasu buk aci Haidar Ya kai kansa..? Meyasa Kai tsaye basu nemi Ransom ba.? I m sorry to say this.. Abokina Anya baza a duba maganar Haidar ba.? Banso na saka maka zargi ko shakku akan D anka musamman da shike baku jima da kasancewa da juna ba.. Amma..

Daddy yai saurin dakatar da Alhaji Gimba yana girgiza Kai  Haba Gimba kar kace kaima ka yarda da shirmen Haidar. Haidar zafin kishi kawai ke d awainiya dashi amma d an uwansa bai nufinsa da komai face alkhairi. Masu garkuwa su suka sacesu. Kasan mutanen nan da salo salo na yaudara.. Kar ka mance sukan sace mutum su nemi kud in fansa Wanda yakai kudin ma suyi garkuwa dashi.. Sai ya d anyi shiru kaman Wanda Ya tuna wani abu  Haidar shine in charge na sabon kwangilan titi da mukeyi a jihar Lagos.. Kasan Kampani da dama sun nemi kwangilar basu samu ba.. Kanaga garkuwa da akai da yaran nan nada alak a da wann kwangilar tinda gashi basu nemi ransom ba sai Haidar..!

Alhaji Gimba yai shiru sai kuma ya jinjina kai kad an  Everything is possible here.. Amma Kai tsaye bazamuyi saurin yanke hukunci ba.. Saidai dole mu saka abinda kace into consideration. Allah dai ya bayyana mana su cikin aminci..

Daddy ya amsa da Ameen yana jinjina kai.

**

Kutsawa yake cikin dajin yayi tafiya da baida wani nisa daga bakin kwalta. Kasancewar ba daji bane sosai hakan yasa Sadis bai sha wahalan samun layin Haidar ba. Bakin kwalta Haidar ya bar motarsa Ya sauk a d Ya fara tafiyar k afa. Nan yake sanar da Sadis ya kunna tablet d in da sukai connecting spy camera din dake button din wuyar rigar Haidar d in dashi. Akwai app da sukai installing cikin tablet d in yanda kowa zaiga live streaming abinda ke faruwa. Spy Camera d in dake jikin button d in wuyar rigar Haidar zata dinga nade komai yanda su kuma zasuke gani cikin tablet d in.

Lokaci guda Sadis ke fad in an gama.

Daddy yana gefe nan cikin parlorn yana amsa waya bayan Alhaji Gimba Ya fice zuwaga majalisunsu zai sanar dan a tayasu da addu a. Ga security ya kuma zama very tied a gidan. Har lokacin su Mommy jigum jigum suke. A haka Sadis ya shigo parlorn rik eda tablet d in yace dasu gaba d aya Haidar yana so suga abinda zai kunna musu.

Take hankulansu ya dawo ga Sadis. Daddy ya katse wayan da yake ya k araso yana tambayar Sadis meke faruwa.? Mai Haidar yake so su gani.?
Take Sadis ya kunna tablet d in ya kam video na sirri da Haidar ke nad a Wanda ke mak ale gaban rigarsa kaman button.

A haka Haidar yaci gaba da kutsawa. A daidai jikin wata bishiya yaji alamun fito. Yaja Ya tsaya yana waige waige. Can ya hangi wasu k artai guda biyu Sun fito daga bayan wata k atuwar bishiya.

Daga nesa sukai masa umarni da  Hands in the air.

Haidar ya d aga hannayensa sama alamun surrender.


Kartan suka k araso guda d aya yai searching Haidar dan ya tabbatar bai d auke da makami. Yayinda guda d aya yake lek en bayan Haidar d in dan ya tabbata shi kad ai yake babu jami an tsaro.

Ya dubi Haidar yace  Are you sure you are alone.?

Haidar ya jinjina Kai  You can be sure I m alone.!

Suka amshi cell phone d insa kafin sukai blindfolding d insa.

Tafiya kad an sukai idanun Haidar suna rufe. Sai yaji alamun kaman ba mutanen wajen. Abinda kunnuwarsa suka soma sinkayowa shine gurnani da kuka kaman na mutanen dake cikin azaba.

Anisa wacce ita ta soma hangosa fad i take  Haidar..! Haidar please help.. Help me.. Zasu kashe ni& !

Cak Haidar yaja Ya tsaya ga idanunsa a rufe.. A hankali Ya furta  Anisa..! Cikin sauri Ya zame abinda suka rufe masa ido dashi. Ya nufo Anisa dake kwance jini na bin k afarta. Cikin tsananin shock yake furta  What happened to you..? Mai Hisham ya aikata Miki..? Ina Hisham yake..? Su waye wad ann..? Come.. I ll save you.. We need to leave this place.. Ya k arashe yana k ok arin d agota. Saidai bai rufe baki ba ya sinkayo muryar Hisham dake baje cikin chakwabi na laka. Sam bai ma zata mutum bane wajen Ya zata curin k asa ne ko wani abin. Da kyar Hisham Ya d ago hannu yana fadin  Brother please don t leave me here.. Dan Allah kar ka barni a nan.. Zasu kashe ni wllhi..!

Girgiza kai Haidar yake yana duban Hisham cikin rashin yarda  Wai meke faruwa ne haka a nan..? Meye kake shiryawa ne Hisham..? Meye ka aikata ma kanka.. Mai ka aikata muku.. Mai zakai gaining cikin duka wann wasan.?

Cikin murya irinta mai kuka Hisham ke fad in  Ka yafe mun Haidar..! Ka tausaya mun ka fitar Dani a nan.. Wllhi kasheni zatayi..?

 Zata kasheka..? Ita wa..?

Daga bayansa Ya sinkayo murya tana fad in  Banyi alk awarin kashe ka ba Hisham Har sai kayi confessing duk wasu abubuwa da kayi ma Haidar da ahalinsa.!

Cikin wane irin yanayi Haidar ke juyowa Har ya sauk e idanunsa tsaf akanta.  Dareen.! Ya furta cikin tsananin shock yana duban Dareen dake zaune bisa wheelchair.

 You.. you are alive.??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? Haidar ya kuma fad i yana dubanta.

Dareen ta saki murmushi  Im alive Haidar my love.. I am very much alive.. Burin wad ann azzaluman na ganin sun kashe ni sun rufe baki na bai cika ba.! Sunyi k ok arin takeni da mota dan kar na isa gareka na tona asirinsu wajenka.. Sunyi nasaran takeni da mota amma basuyi nasaran kasheni ba kaman yanda sukai nasaran kashe mana jaririnmu mai watanni uku a ciki..! Haidar I was carrying your child.. Our child.. The fruit of our love.. The only abu da zan dinga gani na tuna soyayyarmu.. Wad ann azzaluman Sun kashe min shi.. Kaman haka nayi alk awarin tatse tsinannen D ansu dake cikin Anisa dan su d in basu cancanci zama iyaye ba.!


Girgiza kai Haidar yake yana dubanta tashin hankali k arara saman fuskarsa. Lokaci guda Ya daga hannaye sama a hankali kaman mai surrender. Fad i yake  You don t need to do this Dareen..! You don t need to torture them like this.. You don t need to kill their child.. Just let them go please.. Let Anisa go.. She s bleeding..!

A fusace Dareen ta katsesa da fad in  No Haidar.! They killed our child..! These two monsters killed our child.. Na kiraka ne kaga fansar d aukan ran D anmu da sukayi sann wann Devil din yai confessing duk abubuwan da Ya maka. Wanda ya hana na sanar dakai ta hanyar amfani da Anisa ta bigeni da mota..! A yau shi da bakinsa zai fad i komai akan fuskarka Haidar. Zai fad i duk

91 / 95