AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   77 / 95

228K to 231K   out of 283.8K words

shigowa.

Wa zata gani.? Mama Tani ce da  yanuwanta guda biyu Azeema da Badia. Suka tafi a guje suka rungume Ummul suna kuka. Yayinda Haidar ke gaisawa da Mama Tani ya mik a mata jaririn yana musu sannu da hanya. Dan dama Tun a daren jiya ya tura Sadis ya tafi Kano d aukosu. Asuba Sun kamo hanya shisa sukayi isowan safiya.

Haidar ya fice wajen Sadis ya basu waje.

Sosai Ummul ke kuka tana tambayan sauran ahalinta. Ta dubi Azeema tace  Ina Khulsum..? Maiyasa bata biyoku ba..? Itama tana fushi dani ko.? Umma da Abba duk fushi suke dani ko.? Hawaye suka ci gaba da gangaro mata tana girgiza kai take fad in  Bazan iya dubansu cikin ido ba. Cikin tsananin rawar murya take maganar.

Azeema ta murmusa tana share ma Ummul d in hawayen da suka gangaro mata  Dukanmu muna fushi dake  yaruwa.. Shin wak e gudun danginsa a lokaci mai mahimmanci irin wann& ? Amma Kar ki damu zamu iya yafe Miki ko dan zuwan Sabon D anmu.! Ta k arada  Kinga d ago ki gani.. D ago kiga da wa muke tare. Ta k arashe da murmushi saman fuskarta.

D agowar da Ummul zatai sukai ido hud u da Khulsum. Rabon su da su saka juna a ido Tun lokacin Auren Ummul d in a gidan Hajiya Asshe ranan da mahaifiyarsu tai ma  yanuwan Farrak u a k ok arinta na ganin Auren Ummul Ya tabbata.

Hawaye suka ci gaba da kwaranya musu.. Khulsum tana k arasowa gaban Ummul kukan Ummul d in Ya k aru sosai. Murya na rawa Khulsum ta furta  Adda Ummul..! Sai sukai bursting cikin kuka sosai su duka biyun. Suka rungume juna suna yin mai isansu. Har saida Mama Tani tace zasu tasa mata sabon maigida da kukan da suke dan tuni bacci ya d auke jaririn cikin hannunta.

Ana haka su Mommy harma da Daddy sukai sallama tareda jagorancin Haidar.

Gaishe gaishe aka soma kan Ummul na kife k asa tin shigowar Mommy da Daddy. Mama Tani ta mik a ma Mommy yaron tana fad in ta rigata ganin angon nasu. Sukaita  yar bankwanci a tsakani Mommy tana fad in ma sha Allah ta sumbaci goshin yaron. Sak Haidar dinta sanda yake jariri. Su Azeema kaw ficewa sukai bayan Sun gaisar da iyayen Haidar.

Mommy ta mik a ma Daddy dake zaune saman farar kujera yaron. Ya amsa yaron kyakkyawan murmushi bisa fuskar Daddy. Haidar yana gani Daddy na ma yaron a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ddu a ya tofa masa. Ya mik a ma Mommy yaron bayan ya jero ma jaririn da mahaifyarsa add u o i. Har kawo wann lokacin Ummul bata iya d ago fuskarta ba.

Daddy ya dubi Haidar yace suje daga waje. Ba musu Haidar yabi bayan mahaifinsa.

Bayan ficewar su Mama Tani ma ta zame jiki ta fice tana ce da Mommy bari ta barta ta gana da sabon Angonta dan gashi da alama har ya kori Daddy.

Mommy ta murmusa tana jinjina barkwancin Mama Tani.


Mik ewa Mommy tai rungume da yaron cikin hannunta ta dawo kusan Ummul wacce tinda Mommy ta nufota k irjinta ya tsananta bugu. Ta kasa koda motsawa balle ta dubi Mommy tin bayan gaisuwa Wanda shima da kyar ta iya. Ta sani tana fara magana kuka ne zai biyo baya.

Mommy ta kwantar da jaririn cikin baby crib d insa dake gefe. Ta kuma matsowa sosai kusan Ummul. Sai Mommy ta d aura hannayenta saman na Ummul. Ummul na ganin hannun Mommy saman nata hawaye suka shiga gangaro mata.

Mommy ma kuka ne taji na zuwa mata. Sai kawai ta rungumo Ummul cikin jikinta tana fad in  Taho nan  Yata..! Mommy ta rungumeta sosai cikin jikinta yayinda Kukan Ummul ya k aru, Mommy na ci gaba da lallashinta.

**

A can waje kuwa taryan taryan Haidar ya karanto ma Daddy komai gameda Abokinsa Hisham da irin cin amanar da yai masa bayan ya aminta dashi. Sann ya sanar da Daddy baida haufin duk wani scandals da failures da Kampaninsu ta fuskanta da saka hannunsa ciki. Daddy yaita jinjina lamarin domin kuwa zai iya cewa bai tab a tsayawa ya tantance kamannin matashin ba cikin employees d insa dukda kuwa cewa suna tareda Haidar kusan ko Yaushe a company. Ya dubi Haidar yace ai sai su wuce police station din snn ya kuma ce da Haidar d in ya kirawo company lawyer d insu cikin gaggawa. Dole Hisham nada Ubannin gidan da suka turosa kampaninsu domin Ya musu zagon k asa.

Tuni Sadis ya jasu suka nufi station yanda Hisham ke gark ame.

*

Hajja na gaban Kanta tana magiya ma  yansanda da su saki D anta dan bata fata Aliyu Maitama ya tadda su a station d in. Alk awari tai ma kanta bazata tab a jingina ma D anta sunan Aliyu Maitama ba koda kuwa shine abu na k arshe da zatai a rayuwarta. Ba yanda batai su bata belin Hisham ba amma sunk i sunce sai Wanda yai filing complaint akansa yazo idan D anta nada lawyer yana iya kiransa.

Hajja ta kuma marairaice fuska  Rankaidade ka dubi girman Allah ka min alfarmar nan.. Ka dubi soyayyar dake tsakanin D a da mahaifiya ka bani belin D ana.. Ko nawa zan kokarta na biya in sha Allah.

Shi kaw Hisham addu a yake daga nan cikin cell yanda yake gark ame kar a bada belinsa har sai mahaifinsa Aliyu Maitama yazo station d in. Aiko kaman daga sama ya hango Haidar da Sadis ga Daddy na biye dasu. Hisham ya saki murmushi da gefen bakinsa. Cikin zuciyarsa yake furta  Bingo.! Daga k arshe dai, korarren D an zai had e da mahaifinsa. Bari dai mu gani Aliyu Maitama.. Ya zakai da wann D an naka da ka sheganta& The Son you never noticed dikda jimawansa yana aiki k ark ashinka.!


A haka suka k araso cikin station d in waya manne kunnen Daddy dake magana da company lawyer dinsu.

Cak Hajja ta had iyi kalamanta. Tai mutuwar tsaye nan wajen. Ta ina zata mance wann murya dukda muryar ta manyanta a halin yanzu.. Ta tuno muryar a lokacin da ya jajanta mata rashin mahaifinta kuma leburansa a Kampaninsa. Ta tuno muryar a lokacin da yai alk awarin Aurenta bayan rashin mahaifinta. Ta kuma tuno muryar a lokacin da ya furta mata kalman saki ya kuma sheganta jaririn cikinta. Ta tuna sanda ya turata kurkuku har ta haife D anta a gidan yari. Yau gashi nan zai kuma tura D an da yai sanadin haihuwarsa a gidan kasu zuwa gidan kasu. Ta lumshe idanunta tana jin zuciyarta na bugawa cikin sauri.

Cak Daddy ya ja ya tsaya, ya dakata da wayan da yake a daidai sanda ya shigo cikin ofishin yana jin bugun zuciyarsa na k aruwa ba tareda yasan dalili ba.



SameenaAleeyou=???*AUREN WATA UKU..!*



*55*





*??Sameena Aleeyou&
'


Officer yana hango su Haidar yace  Yauwa Hajiya.. Ki adana duk wann magiya da kike. Gasu nan sun iso su yafi cancanta ki roka ba mu ba. Ya k arada barkanku da isowa.

Zuciyar Hajja yaci gaba da harbawa daga nan yanda take tsaye gaban kanta.

A hankali Daddy ke takowa kusan matar yana jin bugun zuciyarsa na k aruwa. A b angaren Hajja ma hakan ce ta kasance. Ta kasa koda motsawa balle ta waigo. Addu a kawai take cikin zuciyarta Allah Ya kawo mata da sauk i. Ji take tamkar numfashinta zai bar gangan cikinta haka nan k afafunta tamkar bazasu iya d aukanta ba. Tana jin officer yana fad in  Ga mahaifyarsa nan tun safe take mana magiya a nan.. Tak i barinmu mu huta.. Cewa take lallai lallai sai mun bata belin D anta.

Haidar ne ya katse D ansandan da fad in  Idan D anki nada lauya kuna iya gabatar dashi k arshen gata da zaki masa kenan. Dan sai nayi sharia da D anki with every means and resources da nake dashi.! Ya k arashe yana aika ma Hisham dake tsare cikin cell mugun kallo kaman zai shak o sa.

Har lokacin jikin Daddy a matuk ar sanyaye yake dan matar tak i juyowa ta dubesu Har wann lokacin. Sai Ya d anyi gyaran murya yace  Sannu Baiwar Allah.!

Zuciyarta taci gaba da harbawa tana sanar da ita  Bakida sauran zab i da Ya wuce ki fuskanci baya Fannah. Komai yazo k arshe.. Yau dai gaki ga Aliyu Maitama.. Ki juya ki fuskance shi.. Dole ki juya koda zaki tuna masa bayansa da ya k yamata. Just turn and face the reality.! Lumshe idanunta Tai hawaye suka gangaro mata kafin ta soma k ok arin waigowa cikin wane irin yanayi.

Daddy ya daskare nan wajen. Ya kasa gaskgata abinda yake gani. It s her.. It s really her& Ta ya zai mance kamanninta bayan ya shafe tsawon shekaru yana nemanta.? Ta Ya zai mance wann fuskar nata koda ace sanin k uruciya yai mata. Fannah..! Fannah ce.. Fannah matarsa da ya d aukar ma Marigayin mahaifinta alk awarin rik eta bisa amana. Fannah da Ya datse igiyan Aurensu da jaririn cikinsa cikin jikinta. Cikin da Ya fidda shi daga cikin ahalinsa tun kafin ya shak i iskan duniya. Fannah da Ya tura fursuna da jaririn cikinsa. Cikin tsananin rawar murya Daddy ya furta  Fann.. Fannah..!

Sai tai bursting cikin kuka ba tareda ta iya furta komai ba.

Haidar ya dubi Daddy cikin tsananin shock sai ya kuma dubi matar. Ya sake duban Daddy da mamaki  Fannah kuma..?! Daddy& Fannah naji kace..?! Ya kuma girgiza kai kad an cikin rashin fahimta ko rashin aminta  Fannah.. Your exwife.. Matar da.. Matar da Mommy ta jima tana nema..? Daddy ita ce wann..?! Ya k arashe yana nuna Hajja cikin tsananin shock.

Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta. Har lokacin cikin tsananin shock shima yake  Eh Haidar..! Ita ce.. Ita ce Fannah.. Matata..! Matata da muka rabu tsawon shekaru na kuma nemeta ban sameta ba.!

Daga nan cikin cell Hisham ke girgiza kai fuskarsa na nuni da tsananin mamaki yake furta  Hajja.. Hajja meye nake ji haka..? Meye suke cewa haka..?! Ya dubi Haidar Har lokacin da mamaki samar fuskarsa tamkar gaske  Meye nake ji haka..? Ta Ya mahaifiyata ta zama matar mahaifinka..?!

Sai sann Daddy yakai dubansa ga Hisham zuciyarsa na tsananta bugu. Bai san sanda ta soma takawa ya isa har gaban k arafunan cell da Hisham ke rufe ciki. Daddy ya k ura masa ido without saying a word. Su duka biyu shida Hisham kallon juna suke cikin ido.. A hankali Daddy ke bin Hisham da kallo k walla tab idanunsa tin daga fuskarsa har izuwa k afafunsa yanda yaga k afafun Hisham d in Sun jeru da nasa k afafun suna kallon juna. Sai Daddy ya k ura ma yatsun k afafunsu kallo. Babu abinda ya raba k irar halittar k afafunsa da na matashin. K wallan dake kwance cikin idanun Daddy suka d igo suka sauk a saman k afan Hisham. Sai Daddy ya juyo yana duban Hajja dake kuka sosai shid in ma hawaye ke gangaro masa. Yana dubanta yake nuni da Hisham yatsarsa Har rawa take  Is.. Is he my son..? Shi ne D ana.. da kika tafi yana ciki..!

Sai Hajja ta kuma fashewa da kuka ba tareda tace komai ba.

Cikin wane irin yanayi Hisham ke girgiza kai yana duban Hajja. Ya tamke k arafan cell sosai yana kuma girgiza kai mai cikeda nuna rashin amincewa  Hajjah.. Mai nake ji haka..! Mai haka yake nufi..? Mai Mahaifin Haidar yake cewa..? Hajja mahaifin Haidar .. Shine mahaifina..?

Har lokacin ta kasa cewa komai sai kuka yayinda Daddy yaci gaba da duban Hisham hawaye naci gaba da gangaro masa.

Haidar da yai mutuwar tsaye yana duban abin al ajabi cikin wane irin yanayi yake girgiza kai  No.. No.. No way.. This can t be.. No this can t be happening..?

Hawaye suka ci gaba da gangaro ma Hisham. Cikin wane irin yanayi yake furta  Hajja please answer me.. Is he my father..? Da gaske shine mahaifina..? Hajja shekara da shekaru ina tambayarki ina mahaifina..? Ina danginsa.. Ce min kike ya mutu all these years.. Ce min kike baida kowa baida dangi.. Hajjah.. Ta Ya mahaifin Abokina Ya zama mahaifina..? Hajja ki sanar Dani dan Allah.. Hajja zuciyata tana nauyi.. Dan Allah Ki sanar Dani bazan iya d auka ba.!

Hawaye ne ke ci gaba da gangaro ma Daddy yai saurin shigar da hannunsa cikin k arafan cell d in Ya tallafi fuskar Hisham dake kuka sosai. Cikin rawar murya Daddy ke furta  My son.. My son.. You really are my son.. I m your father.. Your father is alive.. He s very much alive.. Mahaifinka na raye D anah.!

Sai Hisham yai bursting cikin kuka yayinda Haidar yaci gaba da dubansu cikin tsananin shock.

 Yansandan ma duk mamaki da al ajabi ne Ya cikasu. Kowa a wajen mamaki yake. Sai babba cikin  yansandan ya fito yana gyara d amararsa yace  Inaga an sami rashin fahimta a nan..! Da alama rikicin na cikin gida ne.. Inaga bai kamata mu bar wann k araffan su zama shamak i tsakanin D a da mahaifi da suka shafe shekaru basu tare. Ya k arashe yana mai bud e cell.

Kaman jira Daddy yake sai Ya shige Har cikin cell d in Ya rungume Hisham sosai cikin jikinsa.

Girgiza kai kurum Haidar yake yana duban Daddy da Hisham yana jin tamkar dai duniyar na juya masa. Ya kasa yarda da abinda idonsa ke gani.. Ta Ya mutumin da yaci amanarsa zai zama D an mahaifinsa.. Ta Ya zai soma kiran wann bak in k umurcin D anuwa. Just what is this.? Meye yake faruwa haka.? Bazai iya jure tsayuwa nan wajen ba. Bai san sanda Ya fice daga wajen cikin wane irin yanayi ba.

**

A can asibiti kuwa an rasa gwani wajen tarairayar sabon jariri da mahaifiyarsa tsakanin Mommy da Mama Tani. Dr ne Ya shigo ya duba jariri da mahaifiyarsa nan yake sanar dasu a ranar zaayi Sallama. Mommy ta kuma daukan jaririn ta mak ale shi cikin hannunta tana fad in zasu fice lambun dake bayan d akin Ya samu vitamin d in dake cikin hasken ranar hantsi a cewarta.

A wasa Mama Tani ke fad in su dai basu saba da jegon turawa ba. Jariri a d aki yake har yai kwanaki bakwai.

Mommy ta murmusa tace gwara dai su fice taji dumin mai gidanta koda na dan lokaci ne tinda gashi har zaayi Sallama.

Sai jikin Mama Tani Ya d anyi sanyi Har taji ba dadi dan ta kula sosai yaron ya shiga ran Kakar tasa gashi Haidar da Ummu basu tare balle ta Sami kusanci da yaron. Sauken ajiyan Zuciya Mama Tani tai tana addu an samun maslaha a al amarin ma auratan cikin zuciyarta. Musamman idan ta tuno wani rikicin da suka baro gida wato Abba. Ta maido da dubanta ga Ummul bayan Mommy ta fice tace  Yauwa Ke Ummu, nace ba.. Kinga dai a halin yanzu ke uwa ce.. Abinda aka sani ga uwa kuma shine sadaukarwa.. Ummul inaga tinda Allah yasa kin haihu lafiya sann yanzu rabo Ya tsaga tsakaninki da yaron nan Aliyu.. Bakiga yanda Ya shiga damuwa da tashin hankali ba sanda baki nan, yaro mai k aunarki ga dattaku da sanin yakamata ba irinsu mijin Badia Tasi u barawo da mijin Azeema Habibu gantalalle. Ni inaga zaifi kyau a maida aurenku tinda ga rabo a tsakani.. Yaro Ya girma tsakanin iyayensa biyu yafi.. rabuwar sai dole. Idan Har ke d in kika sauko daga dokin fushi kika amince a maida auren Abbanku mai sauki ne.. Bata Kai aya ba ta soma sinkayo kukan Ummul.

Taci gaba da girgiza kai  Ni dai a a dan Allah Mama. Wllhi bani son komawa gidan Haidar.. Ni ko ganinsa bani son yi.. Kuka ya hanata ci gaba da magana.

Mama Tani ta jinjina kai a hankali  Shikenan kiyi shiru Ya isa haka.. Kinji gashi ana Sallama a k ofa. Ta k arashe tana bada izinin shigowa.

Ga tsananin mamakinsu Asshe suka gani.

Mama Tani ta mik e tsaye tana gyara daurin zani tana huci  Toh gayyan tsiya gayyar Allah tsine.. Waye Ya gayyatoki.?

Ga mamakinsu cikin sanyi Asshe ta dubi Mama Tani tace  Kiyi hak uri mu gaisa kafin duk wani tashin hankali.. Hasalima no ban zo nan da wani tashin hankali ba.

Mama Tani ta rakata da harara  Yo ai ke ganinki babu alkhairi Sam Sam.

A hankali Asshe ta jinjina kai  Komai kika fad a akaina bazan mayar Miki ba. Wanda nayi tuba domin shi Ya sani. Ta dubi Ummul dake zaune saman gadon ta kuma duban Tani tace  Wajen Ummulkhair nazo idan kinmin izini.

Mama Tani ta kuma gyara daurin zani  Toh ban miki izini ba.. ki kwashe k afafunki ki fice tin muna mu biyu..

Ummul Tai saurin girgiza kai tana duban Mama Tani  Kiyi hak uri dan Allah Mama.. Kiyi hakuri ki kyale Aunty Asshe.

Shek ek e Mama Tani ke dubanta  Awho na fice na k yaleki da ita a d aki ta shak eki kaman yanda wancan muguwar  yar tata taso kashe ki.

Asshe ta share hawayen da suka gangaro tana mai zama gefen Ummul.

Harara Mama Tani ta rakata dashi Tai mata nuni da k ofa tace  Ba nisa zanyi ba.. Ina nan daga k ofa ina gadinki.! Tana ida fad in haka tasa kai ta fice tana aika ma Asshe mugun kallo.

Bayan Mama Tani ta fice Ummul ta bud e murya ta gaida Aunty Asshe. Saiga Asshe na hawaye. Ta kamo hannayen Ummul tana rok onta gafara. Taci gaba  Tabbas a wann ranar da za a Miki aure ni da kaina na baki zab

77 / 95