AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   89 / 95

264K to 267K   out of 283.8K words

Hilal masu Aunty Salima. Bata Ankara ba sai sinkayo muryarsa tai yana fad in  May I please.. see him..

Cak ta dakata da abinda take bugun zuciyarta na k aruwa. Ta ina zata mance muryarsa. Ta d ago a hankali tana dubansa. Shi d in ne dai.. Saidai wann karon ya k ara mata girma fiyeda sanin da tai masa a baya. Wann sumar tasa mai laushi da tsantsi irinta asalin k abilar shuwa arab ya tara shi wann karon. Harda jiki ya k ara saidai girman yasa ya k ara duhu kad an. Har Hilal ya amshi Baba Ali daga hannunta bata dawo daidai ba. Sam bama ta kula har su Azeema Sun wuce sashen Mommy ba. Gaba d aya sai ta daburce.. Ga Hilal kusan k ofa yake tsaye rik eda Baba Ali yana fad i ma Haidar yaron dashi yake kama ba da Haidar ba. Harda cewa za a basa yaron he s his Godfather.

Ai kawai sai Khulsum tabi bayan Ummul ta nufi kitchen.

Ummul ta dubeta da mamaki yanda ta shigo duk a daburce  Ke kuma fah.? Mai kikeyi a nan.. Na zata kun tafi sashen Mommy gaba d aya..

Kasa amsata Khulsum tai sai ma dibi dibi da take. Ummul dai d an tabe baki tai kadan Ta d auko carrots zata pilling Khulsum tai karaf ta amshe tana fad in zata fere mata.

Ummul ta tsareta da ido yanda take komai sauri sauri ba natsuwa. Ta aje chopping board din dake hannunta tana kuma tsare Khulsum da ido  Khulsum. Ta k ira sunanta cikeda kulawa.

Khulsum ta amsa tana dubanta.

 Fad a mun.. Meke faruwa ne.?

Khulsum ta d an girgiza Kai  Ba.. Ba komai.. Mai kika gani Adda Ummul.?

Ummul ta jinjina Kai  Idan zaki b oye ma wani nidai kinsan bazaki b oye min ba.. Ki fad a min meke faruwa.?

 Da gaske ba komai fah Adda Ummul..

Daidai lokacin suka soma sinkayo kukan Baba Ali daga parlor.

Ummul ta zame apron din dake jikinta tana nuna Khulsum  Ni dake bamu gama ba.. K arasa fere mun carrot d in ki yankasu k anana ina zuwa.

Daga haka Ummul ta fice sauri sauri.

Ta tadda Hilal ya mika yaron ma Babansa yana fad in ya kamata ya sanshi dan shine Godfather d insa. Ba maganan k iwa tsakaninsu.

Haidar ya amshe yaron yana fadin  Come to Paapa. Ya shiga jijjiga yaron yana fad in yai shiru Maama is here. Daidai sanda Ummul ta zauna gefen Haidar tana k ok arin amsar yaron.

Yanda gaba d aya attention d in iyayen ya koma kan yaron sosai hakan ya birge Hilal ya kuma basa sha awa. Sai ya dan murmusa yana k ok arin barin parlorn. Hanyar da yaga ta nufa yabi. Nan ya hangeta tsaye cikin kitchen din tana dicing carrots. Ya jima yana dubanta sihirtaccen murmushi saman fuskarsa kafin Ya soma takowa cikin kitchen din a tsanake.

Sam bataji alamun mutum ba sai taji gyaran murya daga bayanta yana fadin  Hello.. Excuse me..
Ta dan razana Wanda hakan ya sata saurin aje knife d in da take yanka carrots din dashi had ida rintse idanunta alamun ta razana.

Hilal ya dan leko yana duban fuskarta. Murya a hankali yace  Sorry..! I didn t mean to scare you.

Huci Khulsum keyi ba tareda ta dubesa ba. Lokaci guda tana dunk ule knife din cikin hannunta. A fusace ta waigo tana fad in ya kuwa bazataji tsoro ba mutum yana shiga waje ba Sallama kaman goyon yahudu. Tana maganar a fusace tana juya wuk ar dake cikin hannunta.

Kallon yanda take juya wukar kawai Hilal yake ya d ago hannayensa sama alamun surrender lokaci guda yake jada baya yana fadin  Easy.. Easy..! Yanda yake ja da baya kaman zai auna a guje sai ya kuma tsorata Khulsum. Ta soma waigawa baya tana duba mai ya gani yake shirin guduwa. Hilal bai daina jada baya ba ai kawai sai itama ta nufo k ofa a guje dan ta zata wuta ne ya gani a kitchen din ko wani abu mai Kama da haka.

Kafin tai aune Hilal ya tare k ofan kitchen d in wanda hakan ya hanata k arasawa. Bai daina nunata ba bai daina daukan saiti na gudu ba bai daina furta easy ba.

Ta kuma waigawa cikeda tsoro wann karon  Wai meye ne.. Meye ka gani.?

Ya nuna mata hannunta mai rik eda knife  Pleae keep that away.. Yai maganan yana rik eda k ofar kitchen din gam. K afarsa d aya na waje d aya na kitchen din.

Sai ta d ago wukar dake cikin hannunta tana kallo. Gajeren tsaki tai had ida sauk e ajiyan zuciya kafin ta koma bakin aikinta.

Hilal ya murmusa kad an kafin ya kuma takowa gareta. Wann karon Sallama yai. Kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa da kyar.

Hilal ya k arada  You haven t changed a bit. Ya fad i da murmushi saman fuskarsa. Bata ko dubesa ba balle ta kulasa. Saima ci gaba da tai da abinda take.

Ya dan langab e Kai yana dubanta  Wai ko darajan gaisuwa bazan samu ba balle sannu da zuwa.?

Ta dan dubesa a dak ile sai ta tabe baki had ida janye idonta  Wanda yai Sallama idan zai tafi shi ake ma sannu da zuwa.

Hilal ya dan murmusa dan ya tuna sanda zai tafi bai mata sallama ba. Dikda lokacin itama tana Jigawa gidan Inna Dije amma ko a waya bai kira ya sanar da ita tafiyarsa makaranta ba. Sann tinda ya tafi bai sake nemanta ba. Alk awari yai ma Kansa zai natsu yai abinda ya kaisa once and for all ya k arasa karatunsa ko dan ya share hawayen Amminsa ya kuma tabbatar ma Abbansa bazai sake asaran kudi Akan karatunsa ba. Above all, zaiyi ne ma Kansa ta yanda idan yazo ma Abbansa da batun Aure zai tsaya ya sauraresa.

Gyaran murya ya d anyi yace  Lallai ban kyauta ba amma kiyi hak uri. Ya d anyi shiru kafin ya ambaci sunanta cikin wane irin siga da ya haifar mata da sanyin jiki.

 Khulsum.

Ta d ago ta d an dubesa. Hilal yaci gaba  Tafiyar da nai ba Sallama yanada dalili wanda nasan idan muka samu time na miki bayani zaki fahimta.Ki yarda Dani nayi hakan ne for us.
Sai ta d an kuma dubansa. Yayinda Hilal yaci gaba da jinjina Kai  Believe me, Ban manceki ba daidai da dak ik a guda. A koda Yaushe kina nan a nan..! Ya k arashe yana nuni da b angaren k irjinsa yanda zuciyarsa take bugawa. Yayinda Khulsum taci gaba da dubansa jiki a sanyaye. Kyakkyawan murmushi saman fuskar Hilal yaci gaba  I never stopped loving you my cute cute miss grumpy.!

Daidai lokacin sukaji alamun ana shigowa kitchen d in.

Khulsum tai saurin juyawa tana ci gaba da yanka carrot din sanda Ummul ta shigo kitchen d in.

Shi kaw Hilal saurin daukan glass cup yai yana fadin  I.. I will have a glass of water.! Ya k arashe da murmushi yana daukan ruwan gora dake wajen. Ya dubi Khulsum ya kashe mata ido yayinda Khulsum d in ma ta bisa da wani kallo sihirtaccen murmushi saman fuskarta.

Ita dai Ummul dubansu kawai take. Ta dubi wann ta dubi wancan har Hilal ya fice sai waigowa yake yana duban Khulsum.

Bayan Hilal ya fice Ummul ta tsare Khulsum da ido wacce ke ta faman sakin murmushi a hankali.

Ummul tai gyaran murya tace  Toh ai ya fice sai ki daina wann murmushin da kike.

Khulsum ta dan zaro ido  Na am Adda Ummul..!

Tsareta Ummul tai da ido sai ta murmusa tana aje Kayan miyan dake hannunta cikin roba a sink  Zama kimin bayani ne dalla dalla yarinya. Bari dai mu k arasa da kitchen din nan.

Dan darawa Khusum tai tana fad in  Adda Ummul ba fah abinda kike tunani bane.

Ummul tace  Toh ni mai kikaji nace.. Kin Kama kanki tin baaje ko ina ba yarinya..

Khulsum ta sanne Kai tana dariya.

Bayan Sun gama girkin ne kuma suka soma shirin shagalin. Tuni masu kwalliya Sun iso sunyi mata light make-up da ya matuk ar mata kyau. Shima Haidar d in saida ya k ara shiryawa sabida pictures da zasuyi da jariri. Haka kowa ya dinga santinsu dan ba k aramin kyau sukai ba. Daga bisani Ummul da jaririnta sukaita hotuna da  yanuwa da abokan arziki.

**

Wasa wasa har rana ta kusa k arewa su Hisham basu iso ba. Har akaci taron shagalin suna aka watse basu Anisa ba dalilinsu.

Izuwa lokacin hankulansu ya soma tashi dan tuni anyi conforming jirginsu ta jima da landing.

Ana haka wayar Sadis ya shigo ma Daddy yanda yake sanar da Daddy sun kalla daga security footage na airport Hisham da Anisa Sun shiga wata mota mai d auke da fake plate number na Kampaninsu. Akwai possibility din kidnapping dinsu akai daga Airport.

Daddy yaci gaba da karanto Innalillahi wa inna ilaihi ilairaji un.

Daidai lokacin da su Hajja da Mommy harma da Aunty Asshe suka shigo parlorn a kid ime dan tare Sadis da Hilal suka tafi airport binciko abinda ke faruwa kuma tuni Hilal ya kira mahaifiyarsa yayi updating d inta.

Aunty Asshe kuka kawai take tana fad in anyi kidnapping su Anisa ne dan ance tun rana jirginsu ta sauk a ga kuma shaida wani mota da ba a tantance ba ya d auke su.

Kwantar musu hankali Daddy keyi da fad in in sha Allah ba komai dan idan ma kidnappers ne dole zasu kira su nemi ransom kuma ko nawa sukai demanding zai bayar dan ya ceto yaransa.

Girgiza Kai Haidar yake yana duban Daddy  Na tabbata this is one of his games Daddy.. There s nothing like kidnapping here.. Hisham shi ya shirya wann wasan kwaikwayon. And he used Anisa as a bait.!

A fusace Daddy ya daka masa tsawa da fad in  Ka rufe mun baki Haidar.! Cikin b acin rai Daddy yaci gaba  Your brother is kidnapped.. Ba shi kad ai ba harda iyalinsa wacce ta kasance Yaruwarka.! And you are here blabbing nonsense..! Yaci gaba da girgiza Kai yana duban Haidar cikin rashin yarda  For once in your life Aliyu, call a truce with your brother.! If you can t do anything to help. Then just shut your mouth and get hell out of my house.! Fitar mun a gida nace.! Ya k arashe yana nuna ma Haidar k ofa cikin tsananin b acin rai.

Idanun Haidar Sun kad a sunyi ja yake duban Daddy. Meyasa Daddy bazai yarda dashi ba.! Meyasa idonsa ya rufe Akan d aya D ansa.?! Ya soma girgiza Kai yana jada baya lokaci guda ya fice daga parlorn kaman zai kifa.

Mommy tabi bayansa da kallo tana kiransa amma inaa bai tsaya ba. Hajja kaw tashin hankalinta ne ya ninku. Duk yanda taso ta hana zuciyarta yarda da abinda Haidar ke fad i gameda D an nata meyasa taji yau d in kaman ta yarda da Haidar. Addu a take a cikin zuciyarta Allah yasa Haidar kuskuren fahimta kawai yake ma D anuwansa. Allah ya bayyana Hisham da Anisa cikin k oshin lafiya ya warware komai ya kuma kawo k arshen matsalolin Ahalinsu.

Haidar na fitowa sashen Mommy ya nufa kaman zai kifa. Ya shige su Salima a parlor Wanda tuni suma sunyi jigum jigum dan sunga ficewar su Mommy dasu Aunty Asshe hankali tashe.

A d aki ya iske Ummul tana bama Baba Ali nono.

 Tashi mu tafi.! Ya fad i babu walwala.

Ta dan dubesa da mamaki. Dan tin shigowarsa bata gane yanayinsa ba.

 Ban.. Ban gane ba.. Na tashi mu tafi kuma.? Amma meyasa zamu tafi yanzu.?

 Kar ki bata mun rai Khairy.! Ki tashi nace mu tafi.! Ya kuma fad i cikin tsananin b acin rai.

Itakam sai taji k walla na zuwa mata. Ga Baba Ali da tuni ya rigata fara kuka ciresa da tai yana tsaka da shan nono.

Haidar ya amshesa ya izasa bisa kafad a  Ki same mu a mota.. Kar ki bata lokaci.! Daga haka ficewa yai cikin sassarfa.

Mamaki da tsoro suka cikata. Haidar ya juye mata tashi daya. Tasan bai iya fushi ba amma mai ya bata masa rai irin haka. Toh kodai ta masa laifi ne.? Bata ida tunanin ba ta sinkayo sautin horn kaman zai daga gidan alamun ita yake jira.

Kuka ta fashe dashi tana mai zira mayafinta.

Koda ta nufo k asa hankulan su Khulsum bai ta b angaren da take. Hakan yasa ta nufi k ofa tana danne kukanta.

Khulsum da ta hangeta tai saurin mik ewa ta nufeta tana ambaton sunanta.

Bata iya amsa ta ba sai kawai tasa Kai ta shige cikin sauri wani kukan na kuma zuwa mata.

Hakan ya janyo hankulan sauran  yanuwan . Wann ta kalli wann wancan ta kalli wann gidan dai da alama ba lafiya. Aunty Asshe ta fice tana kuka.. Su Mommy sun fice hankula tashe yanzu ga Ummul ta fito tana kuka.

Badia ta rapka tagumi tana fad in  Oh ni Badi atu yau meke faruwa ne a gidan nan.?

Salima tace  Gaskiya ba lafiya.. Toh amma meke faruwa ne.?

Badia ta tsaida wata ma aikaciyar gidan tana tambayarta meke faruwa a gidan.

Matar ta girgiza kai tace  Naji securities da suke gate suna cewa yaron Alhaji da zai dawo daga SouthAfrica aka kidnapping together with his wife Anisa.

Azeema ta saki baki tace  Anisa dai.? Sai ta rangad a guda tana fad in Alhamdulillah an gama taro lafiya ba Anisa dan ta iso kafin a gama taron da ta wargaza komai.

Salima ta girgiza Kai tace  Kedai bazakiyi hankali ba Azeema. An ce Miki an sace mutane kina shewa. Toh gashi bata zo d in ba amma taro ya tashi ba dad i. Ki gaya min hankalin waye ke kwance.?

Azeema ta tabe baki tace  Wllhi Anty Salima dan dai baki zo bane lokacin bikin tariyar Ummul da ke kanki sai kin tsani wann anisar.

Salima ta girgiza Kai  Toh yanzu dai duk ba wann ba. Mu had a hannaye mu tayasu da addu a Ubangiji ya bayyanasu cikin aminci.

Suka amsa da Ameena gaba d aya.

**

Koda suka isa gida a d aki ta k ule tana share share hawayenta bata bi takansa ba. Har saida ta soma sinkayo kaman muryoyi daga parlorn.

Hilal yaci gaba da girgiza Kai yana duban Haidar  I just don t get you Haidar.. Kasan bazan iya abinda kake fad i ba. Anisa  Yaruwata ce and she s been kidnapped.. I can t just sit bac???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?k and do nothing.!

A zafafe Haidar ya katsesa  Well Anisa ita ta jefa kanta cikin mess d in nan.. I warned her not let that maniac use her.. but what did she do.?She went ahead and married him.. Now she s trapped. Dama na fad a amfani kawai zai da ita. Ni na tabbata ba kidnapping dinsu akai ba. Hisham zai iya shirya komai ta yanda Zai looking kaman sace su akai dan ya cimma wani manufa nasa.!


Hilal yaci gaba da girgiza Kai yana duban Haidar  Ya kake magana kaman ba Nigeria muke ba. Yanda satan mutum ya zama ruwan dare.? Mai zai faru idan real kidnappers ne suka d auke su.?

 Tell me akwai abinda zaka iya yi ne idan ma sacesu d in akai.? Ka fad a mun zaka iya tracking motar da suka shiga..? Tell me, Did the kidnappers call.? Did they ask for ransom.? Yaci gaba da girgiza Kai yana duban Hilal  Babu ko d aya Wanda hakan yake tabbatar da wasan Hisham ne kawai.! That imbecile is using Anisa as a bait.! I warned her from the very start amma tak i taji. She thought she could outsmart him.!

Hilal ya furzar da huci yana girgiza Kai  Kai hakuri brother, a wann b angaren Nima ban yarda da kai ba.! Yana ida fad in haka yasa kai ya fice cikin sauri.

Juyowan da Haidar zai ya hangi Ummul tsaye bayansa tana hawaye. Lokaci guda itama take girgiza kai  Da gaske ne.? Da gaske ne an sace Yaya na Hisham da Anisa.?

Cikin huci yake furta  Kar ki sake kiran wann D aniskan Yayanki. He s nothing to you.!

Taci gaba da zuban hawaye  Meyasa kake nuna masa k iyayya irin haka.? Meye ya maka da tsanani.? Shid in fah D anuwanka ne.. Kan wani dalili kake masa irin wann kiyayyar.?

Cikin huci ya juyo yana dubanta  Do you want to know the reason.? Kece Khairy.. That maniac is obsessed with you.! Do you know that.!

Ta soma girgiza Kai tana dubansa  Baka fahimta bane.. Na san shi tun kafin na aureka amma babu komai tsakaninmu.. Ya taimaka min a wajaje da dama taimakon da bazan tab a mancewa ba. Shi d in mutumin kirki ne bai kamata ka masa irin wann mummunar fahimtar ba.! Cikin kuka take maganar.

Yaci gaba da jinjina kai yana dubanta da idanunsa da suka rine  Ya aikata duka abinda ya aikata Miki ne for a reason. And that s to win your heart. And he s doing what he s doing now for a reason. To separate us.!

Taci gaba da zuban hawaye tana girgiza Kai  Meyasa kake fad in haka.?! Meyasa kake furta wani yana sona.! Of all people D anuwanka.! Ni fah matarka ce.!

 You too don t believe me. Do you.? Ya tambaya yana dubanta cikin sanyin jiki idanunsa na kuma rinewa.

K arasowa tai kusansa ta kamo hannayensa  My love.. Please don t misunderstand me.. You are being paranoid for no reason. You are being jealous for no reason.. Hisham

89 / 95