AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   30 / 95

87K to 90K   out of 283.8K words

afa kazo. naji sauk i Alhamdulillah.

Hisham Ya girgiza kai  Haba Hajjah. Har kiyi ciwo ban sani ba.. Hajja a duniyar nan sabida wa nake neman duk abinda nake nema. Hajja sabida kece.. Lafiyarki na gaba da komai da kuma kowa. You are my number one priority kin sani.. ya kuma girgiza kai  Da ace wani abu ya faru dake da bazan tab a yafe ma kaina ba. Ya k arashe fuskarsa fal damuwa.

Sai ta k ura ma d an nata ido ganin yanda hankalinsa ya matuk ar tashi a sabida ita. Koda duka duniya zasuyi rejecting d insa zata so shi ta k aunace shi domin kuwa Hisham d inta definition ne na d a na gari a idonta.

Ta d an dungureshi  Silly. Ba abinda zai sameni da izinin Allah sai naga  ya yanka.

Ya murmusa yana duban mahaifiyar tasa cikeda so da k auna  And very soon zaki gansu in sha Allah. Dan wann karon na d au d amaran neman aure da gaske. Bazan koma ba sai na tabbata an bani ita. Ya k arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.

Zuciyarta yai wani irin tsinkewa. Take annurin fuskarta ya d auke cak. Ta soma k ok arin kauda fuskarta dan bata so su had a ido. Hasalima bata san ta yanda zata soma sanar dashi labarin Auren Ummul ba. Shin da wanne zata fara.? Cewa Ummul tayi aure ko kuma D anuwansa da baisan yana dashi ba ta aura. Shin mahaifinsa tasowa yai daga kabari kokuwa dai yana raye tintinin.

Zata mik e Hisham yai saurin dakatar da ita ganin gaba d aya yanayinta Ya sauya tashi guda  Hajja na fad i wani abu ne da bai dace ba.?


Girgiza masa kai tai  Hisham kaje ka kwanta dare yayi. Tana fad in haka ta mik e ta shige d aki ta barsa nan wajen yana sak e sak e. Fatansa Allah sa dai lafiya ba wani abun bane ya faru. Jiki babu wani kuzari Ya mik e Ya nufi nasa d akin.

**

Washe gari Inna Dije bata Ida warwarewa ba sai a cikin mota bayan Sun d auki hanya sunyi nisa. Ita kad ai sai layi take dan baccin bai saketa ba. Haka Asshe da Anisa suka turata cikin mota. Ko zarafin Sallama da Ummul basu barta tayi ba.

Saida sukai nisa Abadan kafin Inna Dije ta ida warwarewa. Ta dubi Asshe dake gefenta da mamaki tana kuma duban cikin motar.

Asshe ta karyi goron dake hannunta dan galibi idan zatai tafiya mai tsawo da goronta cikin jaka. Ta murmusa tana duban Inna Dije  Barka da safiya K awalliya.

Inna Dije ta kuma dubanta da mamaki sai lokacin take tuno duk abubuwan da suka faru.

Asshe ta murmusa had ida mik a mata goro  Karb i ki karya kumallo.

Inna Dije kallon mamaki kurum take ma Asshe Har lokacin. Ta dubi goron da take mik a mata  Kin bani k waya cikin dare yanzu zaki had a min da goro ki k arasa kasheni. Makira algunguma.!

Asshe ta dara kad an  Haba K awalliya wasa fah ake bugawa. Da sauran lokaci ai ba a gama ba. Kika sani ko anjima ki lallasa ni.

Inna Dije tace  Ina muke..?

Asshe ta kuma karyar goronta  Kar ki damu mun kusa isa gida nasa a shirya Miki karin kumammalo mai kyau gudun kar kiyi mutuwar bakin al muru.

Inna Dije ta girgiza kanta Wanda Har lokacin nauyi Ya mata  Yanzu sabida rashin imani naki Asshe shine kika bugar dani ko sallan asuba banyi ba kika nad oni kika saka cikin mota.. Toh ina jakan kayana.?

Asshe ta tab e baki  Buhun tsummokaranki zakice. Wari suke min a mota nai watsi dasu. Kar ki damu sabbi suna jiranki idan mun isa. Yanzu bari a samu waje a tsaya kiyi sallah tinda kin dawo hayyacinki.

Inna Dije sai kallon mamaki take ma Asshe dan ta fara zarce tunaninta.


Koda suka iso Kano kai tsaye gidan Asshe suka nufa. Inna Dije ta samu ta saka abu cikinta sann tai wanka aka bata tufafi ta canza.

Asshe ta k araso tana dubanta lokaci guda tana tinda ransa Suwaiba ta soma zuwa gidan.

Murmushi ta sakar mata ganin ta shirya tsaf  Ko kefa K awalliya. Kin ganki kuwa..

Inna Dije ta d aga mata hannu alamun dakatarwa  Ke ni fah ba Suwaiba bace. Babu wani makircinki da zai bani tsoro. Bazan bari na sake fad awa tarkonki ba. Mijina baisan nayi tafiya ba a nasa tunanin ina tare ne da d a uwana. Ni ba ballagaza bace kaman Suwaiba.

Asshe ta murmusa  Ashe duk kanwar ja ce.

 Mai kika ce.? Inna Dije ta katseta.

Asshe ta kuma murmusawa  A a K awalliya cewa nai idan kin gama Hilal sai ya kaiki masaukin ki.

Zata fice kenan Inna Dije ta janyota. Saitin kunnenta take rad a mata  Kinyi kuskure tinda kika kaini naga gidan. Watak ila kin lashe wasan a wann karon. Amma ki kiyayi karawa na gaba. Abun bazai miki da kyau ba. K walliya. Ta k arashe harda kashe ma Asshe ido.

Sai Asshe ta murmusa su duka biyun suna k are ma juna kallo.

 Kar ki damu na Miki alkawarin babu had uwa na gaba. Dan kafin wann lokacin zan tabbata  yarku ta fice daga rayuwar D anmu. K awalliya. Asshe tace tana mai ficewa. Lokaci guda ta kira Hilal Tai masa umarni da yakai Inna Dije Asibitin koyarwa.


**

Cikin sand a Umma ke takowa ta nufi k ofan d akin Abba tana addu an Allah yasa kar ta tadda Dije.

Ai kaw tana tura k ofan a hankali taga Babu kowa sai Abba dake kwance shi kad ansa.

Tai k uri tana dubansa sai taji hawaye na neman ciko idonta. Rayuwarsu na baya taketa tunowa da yanda burin son ganin ta aurar da Ummul ko ta halin k ak a ya rufe mata ido. Ta share hawayen da suka zubo mata tana neman afuwan mahaliccinta cikin zuciyarta. Cikin sand a tamkar mai tsoron kar wani ya ganta ta shigo d akin. A d arare ta zaune gefe dashi. Tana hawaye take furta  Abban Ummul ka yafe mun. Na tapka kuskure mai girma. Kuma nasan ni ban cancanci yafiya ba.. Amma.. Kuka ya hanata ci gaba da magana. Saida tai mai isarta kukan da ba sauti kafin taci gaba  Bazan gushe ba Ina maka addu an samun lafiya mijina.. Hak ik a duniya makaranta ce kuma naga izna akan hakan. Duk abubuwan da na aikata Sun dawo gareni harda tukuici. Kaico na.. Kaicon irin wann rayuwa. Kaiconki Suwaiba.! Ta k arashe tana toshe bakinta dan kuka ne na gaske ke zuwa mata.

Shigowar Khulsum kenan ta hangi Umma zaune gaban gadon Abba tana shesshek ar kuka.

Khulsum Tai saurin k arasowa ta raba tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta.

Umma ta d ago jiki a sanyaye tana duban Khulsum wacce itama d in ita take duba saidai babu d igon annuri a fuskarta.

 Khulsum..! Umma tace cikin tsananin rawar murya.

Khulsum ta girgiza mata kai  Umma me kikeyi a nan.. Dan Allah ki tashi ki fita kafin Inna Dije ta shigo ta taddaki. Dan yau ta sanar Dani zasu dawo tareda  Yaruwata wacce kikai mata auren rashin galiho. Inna Dije tace bazata bari aci amanan mahaifinmu dake kwance ba. Tace bazata dawo ba sai tareda  Yaruwata wacce kika rabamu da ita sabida son zuciya irin naki Umma. Khulsum ta k arashe hawaye na gangaro mata yayinda Umma ma ke hawaye tana jinjina kai. Dan a halin yanzu ita dai kam tasan batada wani hujja ko kalamai da zatai amfani dasu dan ta wanke kanta. Ta kuma san sai yanda k arfin Dije ya k are wajen ganin ta rabata da ahalinta.


 Umma dan Allah ki tashi ki fice.. Bamu neman wani tashin hankali a nan.. Khulsum ta sake fad i cikin rawar murya.

Jiki a sanyaye Umma ta mik e sai ta ajiye  yar kular da ta shigo dashi na abinci Wanda ta kawo ne ma Khulsum d in.

Duban foodflask d in Khulsum Tai ganin Umma takai k ofa tai saurin dakatar da Umma kafin ta d auki kular ta mik a mata  Kin mance wann Umma. Idan dan Abba kika kawo baici.. Idan kuma sabida ni kika kawo kiyi hak uri nima bana buk ata. Ci na ko shana bai tab a damunki ba Umma. Abu d aya ne damuwarki a gidan duniyar nan shine ki aurar da  Yaruwata. Tai murmushi mai ciwo  Auren da kikai ikirarin kin rabu dani akan shi Umma.. Wacce Har zaki mata irin wann kalami bana tunanin akwai sauran damuwar da zakiyi da ita Umma.. Haka ne.? Ta k arashe tana duban mahaifiyar tata.

Har lokacin Umma bata iya cewa komai ba sai hawaye.

Khulsum ta share hawayen da suka zubo mata kafin ta kuma nuna ma Umma k ofa  Idan Inna Dije tazo nan ta sameki Umma kinsan abin bazai kyau ba. Ki dubi girman Allah ki duba jinyan da mahaifina ke ciki dan Allah ki fita ki tafi Umma..


Umma ta jinjina kai tana hawaye ta nufo waje. Khulsum tai saurin bin ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?bayanta rik eda kulan abincin tana k ok arin dakatar da ita.

Daidai lokacin motar Hilal tai parking..


Aiko Inna Dije tana hango Umma da Khulsum tai saurin fitowa ta nufosu.

Ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Saida tai ma Umma tas kafin ta janyo Khulsum tace maza su shige wajen Abba.


Khulsum ta kaikaito ta dubi Umma tana kuma sharan k walla.

Haka Umma taci gaba da tafiya kaman kazar da k wai ya fashe ma.


Hilal da akai komai gabansa bayan Umma yabi da mota dan sosai ta basa tausayi. Ya fito ya gaida Umma bayan yayi parking gefen kwalta. Umma ta ganesa d an wajen Hajiya Asshe ne da ba yau suka fara had uwa ba. Hilal Ya rok eta ta shiga mota ya kaita gida. Da fari k in amincewa Umma tai saida Hilal yai da gaske dan ta kula idan har bata shigan ba bazai k yaleta ba.

Yai saurin bud e mata backseat ta shige kafin ya dawo mazauninsa Ya shige had ida tada motar.

Har k ofan gida yakai Umma kafin Ya juya. Maimakon ya koma gida sai ya koma asibitin.


Room number d in Abba ya tambaya a reception suka sanar dashi. Ya isa yai knocking. Har lokacin Khulsum kuka take bayan Inna Dije ta sanar da ita sab anin halinda ta baro Ummul ciki. Cewa da gaske Suwaiba ta saida ta ne ma wasu irin mutane marassa imani balle mutunci. Ba yanda bataiba ganin k ok arin ta dawo da Ummul amma mutanen sunce kudi suka sa sukai sayi Ummul. Ko Kotu za aje bazasu iya kashe auren Ummul ba tinda tak ama suke da kudi . Yacce kasan zamanin cinikin bayi haka aka saida  yaruwarta a wulak ance.

Knocking d in ne Ya d auki hankalinsu. Inna Dije ta mik e tana tambayan wanene. Ga mamakinta Hilal ta kuma gani.

Ya sakar mata murmushi yana gaisheta had ida tambayarta mai jiki. Ta amsa tana tambayarsa lafiya. Ko wani mantuwa ne Asshen Tai.


Hilal Ya girgiza kai alamun a a. Sai ya k ara da  Em.. Da Allah dama nace.. Emm yarinyar nan da na gani d azu.. Dan shi dik had uwar da suke da Khulsum kusan sau uku bazaice ga sunanta ba.

Inna Dije ta katsesa  Wace kenan..?

Hilal yace  Emm.. K anwar Matar Haidar. Dan ya tabbata ta haka kawai za a ganeta.

Jin haka yasa Khulsum lek owa tana dubansa dan taso d ago muryar. Ai kuwa shi d in ne dai.

Ta galla masa harara cikeda takaici musamman da Inna Dije ta sanar da ita yanda sukai da danginsa akan  yaruwarta Ummul.

Hangota da Hilal yai sai ta sakar mata murmushi Ya d ago mata hannu alamun gaisuwa.

Inna Dije da Tai k ebebe bakin k ofa tace  Toooh mai kake nema wajenta.?

Hilal Ya rasa abun fad i. Sai ya soma  yan kame kame  Em.. Dama akwai wani sak o ne da zan bata.. Idan hakan na matsala.


Ta dubeshi a dak ile, sai Ta juyo ta dubi Khulsum, ta kuma duban Hilal  Minti goma. Minti goma na baka. Kuma kar kuyi nisa Ku tsaya bayan lambun d akin nan yanda zanke hango ku ta window ehe.. Ta dubi Khulsum tace  Zo kije ina kallonku ta window.

Har lokacin hararsa kurum Khulsum take. Kaf danginsu ta tsanesu.

Suka jera suna tafiya har suka isa zuwa wajen wani dogon kujera na shak atawa. Hilal Ya nuna mata kujeran  Bismillah..

 Kaga Malam ba zuwa nan nai dan na saurareka ba. Zuwa nai na baka sak o ka fad a ma azzaluman danginka. Ni UmmuKhulsum  yaruwarta sai na raba wann auren k etar da sukai ma d ansu da ita. Ka fahimta.!

Hilal ta girgiza kai kad an dan sai yanzu yake jin sunan nata  Ki rik e sak on ki dan bazan isar ba. Kinsan dalili.? Ya tsareta da ido yanda take huci kafin yaci gaba  Ni ba maras kunya bane. Kuma Ina daraja iyayena.

Ganin irin duban da Khulsum ke masa ya sanya shi saurin d aga hannayensa biyu alamun surrender  Look, I m not implying anything here. Kar ki dauka da wani manufa. Quite the contrary. Ya jinjina kai kafin yaci gaba  But honestly, abinda kikaima mahaifiyarki d azu ba daidai bane. Ko meye mahaifiya tayi ta cancanci a saurareta& . Ko dan girman hakkin da take dashi akan D anta. Nasan kin sani amma tunasarwa yanada kyau.

 Malam kai baka san komai ba. Kar ka bada shaida kan abinda Bakada masaniya. Ta fad a hawaye na gangaro mata dan ita kanta tana jin ciwon abun cikin ranta.

Hilal Ya jinjina kai  Matsayin iyaye musamman mahaifiya Ya wuce a k ullacesu. Barin baki wani labari gajere. Ya d an kuma takowa ya zauna saman kujerar. Lokaci guda yaci gaba  A lokutan baya inada kusanci sosai da Abba na. Baya iya bacci ba tareda ya ganni ba.. Ko baya gidan mahaifiyata idan yazo Ya tadda ban dawo makaranta ba sai ya jira na dawo kafin ya tafi. Gidan stepmom d ina da gidanmu isn t that far. So takai ta kawo ko sallan asuba Ya fito sai ya biyo har gidanmu Ya tadani mun tafi tare. Toh wann tashi na da asuba da Abba yake sai yasa gaba d aya naji bana son kusancina dashi a ganina tak ura min yake yana yanke min bacci na. Ya d an murmusa yana girgiza kai  Back in the day, Haidar cousin d ina yakan zo gidanmu yai kwanaki . Abin sosai yake birge Haidar yanda yake ganina tareda Abba na. What he s been denied his whole life. Ya girgiza kai  I know I shouldn t be telling you all this amma ta kama ne shiyasa nake sanar dake. Hilal yaci gaba  Bama son fita sallan asuba but Haidar yana mun sha awan wann opportunity d in na kasancewa da Abba na. Ko naji Abba yazo tada mu tafiya masallaci bana tashi sai na barsa yai knocking har ya hak ura ya tafi. Amma sai Haidar Ya tadani dole yace mubi Abba masallaci ba tareda munyi alwala ba tinda shine bama sonyi wai mu gudun kar baccinmu Ya tafi. A haka za ayi sallah damu idonmu a rufe muna bacci, idan mun dawo gida sai muci gaba da baccinmu.

Ya d an dubeta ganin ta zuba masa ido  Hey ba wai fah bama yin sallah bane idan mun dawo gida. Quite alright zamuci gaba da baccinmu ne bayan mun dawo masallacin. idan mun tashi da safe sai muyi alwala muyi sallah mai alwala. Wai mu munyi dabara baccinmu bai gudu ba.. Crazy right. Ya fad i murmushi saman fuskarsa yana jinina kai.  That was then nake fad a Miki. Lokacin k uruciya.. Idan ban mance ba Babban Yayana Haidar kanshi bai rufa ashirin ba balle ni. Ya fad I haka tamkar wacce ta tsile shi.

Hilal ya murmusa yana jinjna kai  I Guess a halin yanzu k anan k annena yaran third wife d in Abba sun k wace Fada na wajen Abba. Na daina ganinsa often musamman a gidanmu. And ya daina zuwa tadani sallan asuba. Ya zama everyday idan zan tashi sallan asuba sai na tuna Abba da yanda yake zuwa ya tadani koda baya gidanmu. Ya d ago ya dubeta  Moral of the story kar kayi wasa da damar da ka samu. Sometimes we don t know the value of what we have in hand until we lose it. So please ki saurari mahaifiyarki tin kinada daman hakan. Ya k arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Lokaci guda ta mik e yana fad in  Barin tafi before you attack me da irin wann kallon da kike mun.

Khulsum ko janye k afarta ta kasa jikinta yayi mugun sanyi da maganganun Hilal.

Har ya soma tafiya ya juyo ya dubeta nan yanda ya barta tsaye  Kar fah wataran kiyi Haidar yaji labarin nan a bakin ki since he s married to your sister now. My cousin will definitely kill me idan yaji na bada labarin k uruciyarsa ma k anwar matarsa. sallan da muka dingayi babu alwala. Ya k arashe yana murmushi. Har ya soma tafiya ya kuma juyowa  And.. kar ki damu zaki jima baki ganni ba daga yau. Cos I ll be flying back to school in a couple of days. I hope zakiyi tunani kan abinda na fad a Miki.. Goodbye. Ya k arashe yana d ago mata hannunsa mai rik eda mabud in mota.

Jiki

30 / 95