AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   85 / 95

252K to 255K   out of 283.8K words

ta suka so bama Mama Tani dariya amma sai ta gimtse tace  Toh ke ba haka kike so ba. Inji a nan kike kumfan bakin ke ba don kina sonsa kika amince da komen gidansa ba. Ke bari kiji na fad a Miki maza irin Aliyu ba a ja musu aji dama kad an k adangarun nan na bariki masu d ingilallun buje ke jira akansu. Ahtoh.!

Badia dake daga parlor ta dage labule ta lek o tace  Ahtoh Mama fad a mata dai. Tana nan tana wauwauta taji ana shafe Fatiha a Abuja.!

Ummul ta kuma tunzura da kalaman Badia. Sai ta kuma fashewa da kuka.

Mama Tani ta aika ma Badia dak uwa  Kinci gidanku Badia. Ke bakinki bazai fad i alkhairi ba. Kiji da naki matsalan wann gantalallen mijin naki ya gudu Ya barki ba tsuntsu balle tarko. Ke ba mai aure ba ke ba sakakkiya ba.

 Haba Mama Aure ni da Tasi u kuma ai ko a k iyama.! Cewar Badia.

Mayafi Mama Tani da dauka tana fad in zata dubiya layin bayansu. Badia tace da ita a dawo lafiya.

Mama Tani na tafe can k asan babban kwalta ta hango ana ihun b arawo sai jibgan mutumin ake ana masa ihun b arawo mutane kaw sai tururuwa suke.

Kaman Wanda aka ce Mama Tani ta kutsa nan ta hangi Wanda ake ma ihun b arawo ba kowa bane face Tasi u mijin Badia. Tasi u dai da Ya gudu da kudin Bakauye da takardun bogi na shagon Abba ya kuma jefata a uku. Mama Tani ta dafe k irji tana salallami  Na shiga uku mai zan gani ni Tani.?! Tasu u.!

Tasi yaji muryar da Ya sani yana tunanin samun rahama daga jibgan da yake sha sai Ya soma k ok arin rarrafowa ga Mama Tani yana fadin  Mamana Mamana takaina kimin rai wllhi akasi aka samu ba ni ne b arawon ba.!

Samarin dake wajen suka dubi Mama Tani sukace  Baaba D anki ne.?

Mama Tani ta zaro ido waje tana dafe k irji  Ni Tani haramiya.! Allah shaida ban haifi b arawo ba. Wllhi ba D ana bane nima nan a sanadiyan wann kafuri na tafi gidan kasu bada hakki ba.! Kucimin uwarsa da kyau amma kafin nan ku dakata.!

Ta waiga gefe ta dubi yaran da aka tasosu daga makaranta ta amshi paper da pencil hannunsu ta mik a ma Tasi u tace  Rubuta.! Rubuta ma  yatsa rasidi dan ubanka!.

Tasi yana haki yake girgiza kai  Mama kimin rai wllhi ina son Matata hasalima abinda Ya shigo dani layin nan kenan dan na maida matata kawai tsautsayi Ya hau kaina aka soma ihun b arawo ni kuma na karyo kwana kenan na taka sawun b arawon amma wllhi bani ne b arawon ba.!

Mama Tani ta jinjina kai  Sanin gaskiyanka sai Allah Tasu u. Amma ko hakan d in ne ba abinda zance sai Alhamdulillahi.! kaji yanda akeji. Kaman yanda ka gudu da kud i ka barni a tsaka mai wuya banci nanin ba nanin ta cini. Ba kunya ba tsoron Allah ina Uwar matarka. Da tsufa na geme geme na tafi kurkuku k anun yara suka shassahata ma wann fuska tawa Mari sabida Kai. Toh kaman haka kaima yau ka taka sawun b arawo. Wann sai Ya zama wa azi gareka damu baki d aya Tasu u.!

Samarin sukaci gaba da girgiza kai suna fad in  Karya yake bakinsu d aya da b arawon wllhi sai munyi ajalinsa a nan ehe.!

Mama Tani tace ku dakata kar kuyi ajalinsa.  Yata ta shafe shekara da watanni tana zaman gaibu da aurensa ba tareda ansan yanda yake ba. Bazata kuma yin takabansa ba bayan tsawon lokacin da ta diba babu sanin makomar aurensa. Tasu u wllhi sai ka sakar min  ya.! Ta k arashe tana dangwala masa paper.

Bai rubuta ba hakan yasa samarin nan sukaci gaba da dukansa. Tasi u da yaji bugu kaman zai Mutu sai yace su dakata su daina dukansa zai rubuta ma  yar Mama Tani Badia takardan saki da sharad in samarin zasu mik asa ga hukuma bazasu kashesa ba. Ya gwammaci su kira  yansanda su mik a shi ga  yansanda da dai su masa dukan kisa wajen.

Samarin sukace yaci darajan Mama Tani Ya rubuta takardan sakin su kuma zasu basa kariya bazasu bari a illatasa da bugu ba har  yansanda su iso. Haka kuwa akai Tasi Ya rubuta takardan sakin Badia Wanda Ya zame masa kariya daga dukan da yake kwasa.

Mama Tani ta amshi takardan sakin tai hamdala kana tai godiya ma samarin tasa kai ta shige tana fad in ta gode Allah da Ya kawo k arshen auren  yarta Badia da miji irin Tasi u.

**
Kwanci tashi babu wuya wajen mai duka. A ranar da Ummul ta cika kwanaki arba in da haihuwa Abba yace Ya cika alkawarinsa yau zata tafi ga mijinta. A zaton Ummul Haidar zai zo amma sai taga baizo ba. Aunty Asshe ce kawai tazo sann Abba bai bari wani daga gida Ya mata rakiya zuwa Abuja ba. A Cewar Abban tinda ba sabon aure bane kome ne ba sai an Tara mutane an mata rakiya ba. Daga ita sai Aunty Asshe da jaririnta suka nufi Abuja. Ummul taci kuka har ta gode Allah.

Tarba mai kyau suka samu daga wajen iyayen Haidar baga Mommy ba baga Hajja ba an rasa waye yafi d okin zuwan Ummul da jaririnta. Tuni an gyare musu masauk i a b angaren Mommy amma sai Hajja ta rok i alfarmar Ummul ta zauna a nata b angaren ta k arashi bik inta dan dama Mommy tace bazata tare gidan Haidar ba sai ta cika watanni uku da haihuwa. Koda Hajja ta buk aci Ummul da ta zauna a b angarenta Mommy cewa Tai hakan yayi dama  yarta ce.

A b angaren Haidar kaw da mugun mamaki yake duban Aunty Asshe yana jin wani sabon turanci wai Khairy bazata tare gidansa yanzu ba.

Ya girgiza Kai kad an still yana duban Aunty Asshe  Aunty, wai kina nufin akwai wani watanni biyu nan gaba da zan sake jira.?

Aunty Asshe tace  K warai kuwa. Zancen kake so muyi Haidar. Mommy tace  yarta bazata tare da d anyen jego ba sai ta cika watanni uku da haihuwa.

Girgiza kai yake disbelievingly  Unbelievable.! Ya furta a hankali yana jinjina kai kafin ya gyara zamansa kad an ya bud e murya yace  Aunty ni kuma sai na zauna Har tsawon watannin nan ba mata.? Tsakani da Allah an min adalci kenan.? Seriously this is unfair fah.! Yai maganar duk a gajiye.

Ya dan fito daga cikin kujerar yana dubanta  Aunty you need to talk to Mommy. Knowing Mommy tinda tace sai Khairy sai ta cika watannin nan bazata bari ta tare d in ba. Please Aunty do something.. Ki rarrashi sister dinki ta amince ta bani matata mu tafi. Aunty wllhi hakuri na gab yake da k arewa.! Ya k arashe kaman wani maraya.

Aunty Asshe dai tausayinsa taji kai har kunya saida Haidar yasa taji. Tinda Ya iya budan baki yace mata hakurinsa ya kusa k arewa tasan an kusa wajen. cikin zuciyarta cewa take  Gata ake maka Haidar dan Mommy so take a gyara maka matarka sosai kafin akai maka ita. Ta yanda bama zakai tunanin ta haihu ba. A fili kuwa cewa Tai  Kai hakurin shekara sanda bata nan balle yanzu da watanni biyu ne jal bai cika wata biyu ba tinda Anci kwanaki arba in already.

Girgiza kai yake yana furta  Aunty wancan lokacin daban. Nasan babu auren a wancan lokacin amma yanzu da aure. Thank goodness wann karon ba Mommy ce ta biya sadakin nan ba balle ta hanani Matata... Mommy Sam ta daina tausayi na Aunty. Kawai gwara na nemar ma kaina mafita.

 Ban gane ka nemar ma kanka mafita ba mai kake nufi Haidar.? Aunty Asshe ta tambaya tana duban Haidar dake k ok arin mik ewa.

 Mommy taita ajiye  yarta amma Aure zanyi Aunty. Ki shirya zaki had a mun lefe ko Mommy bata sani ba.

Ummul dake mak ale jikin k ofa tana sauraron su zuciyarta yai wani irin tsinkewa taga wani irin duhu ya gifta k wayan idonta. Wani hajijiya Ya kusan aikata k asa. Bata san sanda ta k unshe bakinta ba cikin kokarinta na hana kukan dake zuwa mata. Muryar Aunty Asshe ta sinkayo tana ceda Haidar.

 Dakata dakata.. Wane irin aure kuma Haidar.? Mai yai zafi.?

 Khairy da Mommy bakinsu d aya Aunty.. Idan kuma kema zakiyi joining team din nasu ne fine. I m used to fighting my battles alone.

Ummul bata ida k arashe sauraron hirar Haidar da Aunty Asshe ba ta janye jiki da kyar ta fad a kan gado tana rera kuka mai dalili. Shikenan itakam da gaske Haidar baya sonta. Badia tayi gaskiya da tace tana nan tana wauwauta zataji an shafa fatihan Aurensa a Abuja. Ashe dama aurensa yake nema Shiyasa Ya wofantar da ita bai kuma bi takanta ba. Kuka ya kuma b alle mata. A haka Mommy ta shigo ta isketa.

Da mamaki Mommy ke dubanta. Ta girgiza kai kad an  Ahah.! Ummulkhair, kuka kuma.. meke faruwa.?

Tai saurin gyara zamanta tana k ok arin Had iye kukan nata.

Mommy ta zauna gefenta tana karantar ta sai tace  Lafiya kike kuka Ummulkhair.?

Shiru bata iya amsa Mommy ba tanata k ok arin danne kukanta.

Ganin haka yasa Mommy yin shiru tana nazarinta. Sai ta tuna Haidar bai jima da ficewa daga gidan ba cikin yanayi na rashin walwala???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? da fushi. Sann koda ta tambayesa abinda ke damunsa bai sanar da ita komai ba. Koda Mommy ta tambayesa bazai kwana nan gida ba sai ce ma Mommy yai no kawai zai tafi can gidansa Ya kwana da safe zai shigo.

Ta tsare Ummul d in sosai da ido kafin tace  Kunyi Sallama da Haidar d in ne.?


Ambato sunansa da Mommy tai yasa ta kasa danne kukan kawai sai ta fashe da sabon kuka.

Ganin haka yasa Mommy tsareta da ido tace  Fad a min Haidar Ya Miki wani abun ne.?

Tai saurin girgiza kai  A a Mommy.. Kawai.. Kawai ina kewan gida ne.

Mommy ta d anyi still dan tasan bata fad a bane kawai amma kukanta nada alak a da Haidar. sai Mommy ta soma lallashinta ta k arashe da fad in  Gobe in sha Allahu Y?Gumsu zata taho daga Maiduguri.. Zata tayaki da kula da Baba Ali& Barin duba Hajjan taku. Ta k arashe tana mik ewa.

Da kai kawai Ummul ke iya amsa mata dan ita bama tace ta fahimci maganganun Mommy ba tsananin tashin hankalin da ta tsinci kanta ciki.

Mommy ta fito tana sababin Haidar zaizo gidan Ya sameta dan ita bata yarda baima Ummul komai ba. Ta kula a yan kwanakin  yan halin nasa ne suka motsa. Tai k wafa tana fad in  Ai shi dama mai haki baya fasawa.

Aunty Asshe ta dubeta  Wai lafiya Aunty Kwaise keda waye haka.?

Mommy ta kuma yin k wafa  Banda Haidar& Na rasa mai Ke yawo akansa cikin kwanakin nan.. Jibi dai yau Ummulkhair tazo gidan nan ya d age kafafunsa yayi tafiyarsa. Allah kad ai yasan wani bak in cikin Ya tura mata Ya fita yai tafiyarsa. Kuka sosai na shiga na tadda tanayi..

Murmushi Aunty Asshe Tai ba tareda tace komai ba.

Mommy ta dubeta baki sake  Aw dariya ma abin ya baki?

Aunty Asshe ta kuma murmusawa  Toh idan ba memanmu kukeda fitina ba Aunty Kwaise Kun dakemu kuma kukan ma so kuke ku hanamu.

Mommy tace  Ban fahimceki ba. Haidar d in yace an masa wani abin.?

 Eh mana mun d auko matar mu Kun k wace a nan.. Ni yanzu duk laifina ma yake gani yace da na d auko masa matasa da straight can gidansa na wuce da ita da ba a masa fin k arfi ba a nan.

Mommy tace  Aw wai duk wann fushi da kumburi da yake akan ba a kai masa ita bace.? Ai kaw saidai ya fashe dan kumburi, ba ta yanda za ayi akai masa yarinya da d anyen jego. Kema dai Asshe so kawai kike ki biye ma rigimar Haidar amma ina aka tab a haka. Yoh idan acan gida Maiduguri ne ai sai ta kwashe watanni ma bai sakata ko a ido ba.

Aunty Asshe ta murmusa  An rage al adun nan fah yanzu Aunty Kwaise a duba al amarin yarona kar azo ana cewa bamu kyauta ba. Iyaka hakuri fah munyi kar kuma a k ure mana hakuri. Dan takaiga mun fara maganar k arin aure.

Galala Mmmy ke duban Aunty Asshe  Haidar d in ne ke maganar karin aure.?

 K warai kuwa. Aunty Asshe tace tana karanto ma Mommy yanda sukai da Haidar d in.

Girgiza Mommy tai had ida tab e baki  Rigima ce kawai irinta Haidar.. Kuje can kuyita auren naku  Yata tana nan sai na tabbata Martabanta Ya inganta.

Daga haka Mommy bata kuma bi takan Aunty Asshe da rigimar Haidar ba.

**

A b angaren Ummul kuwa sosai ta damu da zancen Auren Haidar gashi ta kasa sanar da kowa damuwarta. Ga Haidar kaman ya k ara janye jiki da gidan. Ko ya shigo gaisuwa kawai ke kawosa saiko duba D ansa sam baya bi takan Ummul har kawo wann lokacin. Iyaka damuwa da tashin hankali Ummul ta shigesa. Da kyar ta iya sanar da Hajja halinda take cik. Hajja ta lallasheta da fad in ta cire damuwar Auren da Haidar yace zaiyi a ranta. Ta maida hankalinta ga karan kanta. Ta natsu ta kwantar da hankalinta. Dan ita tama fi so lokacin da Haidar zai ganta ya kasa ganeta. Ga gyara mai aminci da take samu daga Hajja harma da Y?Gumsu wacce da alama ba don kula da Baba Ali kawai Mommy ta kawota gidan ba harda kula da Uwar Baba Alin. Y?Gumsu sunada dangantaka da Daddy dan mazaunin Kaka take ga Haidar.

Gyara na kankaro mutunci da dawo da martabar d iya mace bayan haihuwa Y?Gumsu ke mata. Gyara tin daga ciki Har kawo fatarta daga waje. Kan kace mai Ummul tayi kyau ta k ara haiba. Ga wani haske da shek i na musamman da take ba a maganan wani musulmi k amshi da tuni yabi jikinta Har zuwa suman kanta. Ita da kanta jinta take ta canza kama daga matantakanta har zuwa gangar jikinta. Wasu lokutan sai ta d auki wayarta tana duban layin Haidar kaman zatai dialing sai kuma ta tuno kashedin Hajja na cewa ta maida hankalinta ga karan kanta ta mance da zancen Auren Haidar. Cikin zuciyarta take furta  Toh ma ni ina ruwana.. Ba sai yaje Yata auren nasa ba. Dama ni sabida Abba da Mommy na amince da aurensa. Ta Kai dubanta ga YGumsu da shigowarta kenan rik eda Baba Ali yaron ya girma yayi wayau ga kyau da ya k ara kaman D an turawa bazaka ce d an wata biyu bane. Ga shiga rai wajen duk Wanda ya d ora ido kansa.

A haka suka doshi watanni uku suna samun kula da tarairaya daga ita har jaririnta. Tayi k ok arin kauda tinanin Haidar cikin zuciyarta kaman yanda Hajja ta shawarceta. Ita zama ta iya cewa ta mance da Haidar d in balle wani zancen aurensa. Sosai ta natsu ta kwantar da hankalinta. Idan tana tareda Baba Ali ba k aramin d ebe mata kewa yaron yake ba. Ya shiga ranta yanda baka tsammani. A sama ranan ta stinci hirar Y?Gumsu da Mommy. Y? Gumsun na shirya Baba Ali bayan ta masa wanka take jajen uban Babagana kaman yanda take kiran Baba Alin.

Mommy tace  Ai zaman Lagos ya auresa yanzu yana can kudu bai Faye zaman nan d in ba. Abinda Ummul ta sinkaya kenan taji kanta na juyawa. Wai zaman Lagos ya auresa.. Innalillahi wa inna ilaihi raji un.! Toh kodai Haidar aure yai ya aje matar a Lagos ba tareda saninta ba. Toh kodai ya b oye ma Mommy zancen Auren nasa ne kaman yanda yace da Aunty Asshe zata had a masa lefe ko babu sanin Mommy.. Idan ba haka ba maiyasa zai tare garin Lagos.? Sam bama ta kawo tunanin aiki ko wani abu zai iya kaisa Lagos ba. Haka ta yini d aki tana faman sak e sak e. Duk yanda taso ta yakice tunanin ta kasa. Haka ta shige band aki taci kukanta ita kad ai tana mai tausayin kanta.
**
Kwance take da hantsi d akin Mommy. Idanunta a lumshe irin na mai bacci.. Baba Ali na cikin cradle d insa dake nan d akin Mommy shima baccin yake. Haidar da shigowarsa gidan kenan Kai tsaye d akin Mommy ya nufo yana nemanta. Cak yai tsaye yana dubanta zuciyarsa na wane irin fuzga.. Ta masa kyau har ta gaji ga wani k yalli na musamman da fuskarta keyi. Shi zai iya cewa rabon sa da ita ya mance..

A hankali yake takowa cikin d akin kaman mai tsoron kada ya tadasu daga baccinsu.

Yai tsaye akanta yana dubanta sihirtaccen murmushi saman fuskarsa. Ya furta  sleeping beauty a hankali kafin ya zauna nan gefenta yana kuma k are mata kallo tin daga fuskarta har zuwa d an yatsarta. Ga wani musulmin k amshi mai sauk ar da nitsuwa da yai ma k ofofin hancinsa Sallama tinda ya zauna kusanta. Bai san sanda ya rank wafo sosai yana shak an k amshin nata. Idanunsa a lumshe yake shak an dadd an k amshinta Wanda ya sauk ar masa da natsuwar da ya mance yaushe rabonsa da yaji irin haka.

Kaman a mafarki Ummul ke Jin hucin numfashin

85 / 95