AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   62 / 95

183K to 186K   out of 283.8K words

batazo ba dole ya tambayi Mommy Ina take mai take gida.?

Mommy ta dubesa a dan tsare  Hutawa take gida, ka kyale nurse room dinka ya kula dakai. After all, aikinsa ne. An biyasa domin yayi hakan.

 But Mommy he doesn t do anything right.. And I don t want him touching my things. Ya k arashe fuskarsa duk a dame.

 Oh kasan da haka kai mata mugun hali.? Mommy tace a dake.

Sai Ya d ago a d an firgice  Mommy mugun hali kuma.? ita tace Miki na mata wani abin.?

Yanda yai tambayar ya tabbatar ma Mommy D anta Ya fara nitso a tekun soyayya bai sani ba. Ta kifa kai ta murmusa kafin ta kuma d agowa a tsare ta dubesa  Nasan ka mata wani abin ne amma wann ji da kan naka bazai bari ka amince kayi ba.

Ya lumshe idonsa kadan had ida furzar da huci  Mommy I didn t mean to hurt her feelings.. Believe me.

Dakatar dashi tai  Ba ba asi na nema ba. Sai ta kuma dubansa wann karon a d an sanyaye  Haidar, ni na haifeka nasan halinka tun k uruciya. Nasan abubuwan da kai going through a rayuwa. Tin kana yaro baka bari a gane lagonka dukda tarin k alubale da ka fuskanta. Jarumtarka baya bari a gane raunin ka. Amma ka sani even the strong people need help sometimes.

Sai ya dubi Mommy a d an sanyaye wann karon.


Mommy taci gaba da jinjina kai  I know your psychological wounds are much deeper.. But I believe they ll heel in time with Ummulkhair by your side. Haidar ya kuma duban Mommy without saying a word.

Mommy taci gaba  Ba gazawa bane to Own up to your mistakes and apologies when necessary. Even if it hurts.. Ta murmusa tana dubansa  Kana so matarka ta dawo wajenka.?

Sai ya dubi Mommy har lokacin baice komai ba. Saima kaikaitar da fuskarsa da yai.

 Shikenan zan sa driver ya kawota. But I have my conditions.

Yai saurin duban Mommy  Mommy conditions kuma.? You.. just call her my wife fah.

Dariya Ya kusa kufce ma Mommy tai k ok arin gimtsewa  Toh so kake na kawo maka ita ka wulak anta ta. Ai dai naga ni na biya sadakin ba Kai ba.

Ta kuma gyara zamanta  Conditions dina sune Bazaka sakata fushi ba. And you must kill that prideful behaviour of yours. Kayi alkawari.?

Ya marairaice fuska  Mommy do I have to promise.?

 Aw! Toh kaga ni saida safe.. Room nurse d inka na jira. Ta mik e tana k ok arin d aukar jaka.

Saurin kamo hannunta yai  Ok, fine. I promise. Ya fad i kaman Wanda aka masa dole.

Mommy ta k unshe dariyarta dan sosai draman Haidar d in Ya bata dariya. Ga abu kana so amma ka kasa fitowa kai tsaye ka furta. Wani abun sai Aliyunta. Ta tuna da fari da kyar Ya amince Ummul ta zauna wajensa sai gashi yanzu da kanshi yake nemanta.  Sannu a hankali ma zaka kawo kanka wajen Ummul d ita Haidar. Mommy tace a zuciyarta.

Ba Mommy ce ta maida ma Haidar matarsa ba sai ana gobe sallamarsa. Dan so take ta wana Haidar kad an yanda idan ta mayarsa da Ummul zai shiga taitayinsa. Sa arsa d aya ma dan jinya yake.

*
Yana nan kishingid e saman gado yana duban yanda taketa fito da kayayyakin daga hospital wardrobe d in tana shiryawa cikin suitcase. Fuskarta babu yabo babu fallasa. Dan tinda ta dawo bata yarda sun koma kaman da ba musamman idan ta tuna maganganun Anisa. Ta k udiri niyyan gano koma menene ke b oye da izinin Allah tinda tasan a shashanci irin na Anisa haka kawai bazata shirya zance irin haka ba face tanada k wakk waran hujja.

Ta dan saci kallonsa tana linke Kayan. Nan taga ya kafe ta da ido. Tai saurin janye idonta.

Mik ewa yai Ya soma takowa a hankali. Ta bayanta ya tsaya had ida rungumota, Ya rik e hannunta da kayan cikin nasa. Ummul ta lumshe idonta a hankali jin hannunta saman nasa. A hankali yake k ok arin linke kayan ba tareda ya saki hannunta ba. Har lokacin idanun Ummul a lumshe suke tana jin kwalla na k ok arin ciko idonta. A hankali Ya d aura hab arsa saman wuyarta had ida lumshe idanunsa. Wasu abubuwa yake mata Wanda k afafuwansu ke barazanar gaza d aukarsu. Rigar dake cikin hannunsu Ya silale Ya fad i k asa& Ta soma k ok arin cire jikinta daga nasa amma saiji tai ya rik eta tsam. Murya can k asa yake furta  I wanted to hate you.. I tried to hate you.. But I couldn t..! Ya d anyi fasali yana mai ci gaba da sinsina wuyarta. K amshinta da yai missing. Har lokacin idanun Haidar a lumshe suke. Yayinda hawayen da Ummul ke k ok arin makalewa suka shiga zarya.
 I can t get you out of my mind Khairy& Please stay.. right here..And don t let go.!

Hawaye shar suka soma ambaliya a fuskarta. Ta shiga cikin rud ani matuk a. Ta rasa da waye zata yarda cikin ukun. Mommy ce, ko Anisa ce ko kuwa Haidar ne.



SameenaAleeyou=???*AUREN WATA UKU..!*




*45*






*??Sameena Aleeyou&
'





Zame jikinta tai daga nasa tana mai goge fuskarta. Lokaci guda ta k arasa saman sofa ta zaune tana mai ci gaba da goge hawayen da ya wanke mata fuska.

Ya d anyi still a wajen yana dubanta kaman bazaice komai ba sai kuma ya zira hannayensa cikin aljihun wandonsa. Ya soma takowa a hankali zuwa yanda take. Har lokacin babu walwala a fuskar Ummul.

Haidar ya zauna daga gefenta ba tareda ya dubeta ba. Dak ik ai suka gifta. Ya soma tuno kalaman Mommy da tace he should own up to his mistakes. Ya dan lumshe idonsa kadan. Har Ta cire ran bazai ce komai ba ta sinkayo muryarsa  Are you.. Still mad..?

Ta dan dube shi. Sai taji yace  Do you want me to apologise.?

Nan ma batace komai ba sai d an dubansa da tai.

Haidar ya dan furzar da huci wann karon yana janye idanunsa daga barin dubata  Oh no Khairy. You are not going to give me that silent treatment.

Nan ma bata ce komai ba.

Sai ya mik e a dan fusace  Ok fine.. Dama kawai baki dawo ba idan b??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????azaki ce komai ba.!

Mik ewa tai itama cikin fushi  Da gaske, haka kace& ? Sai ta nufi k ofa da zummar ficewa. Haidar yai saurin dawo da ita.

Ta d an kalleshi  Ni ka sakar mun hannu.

 Idan ank i fah.?! Ya fad i yana tsareta da ido sosai. Sai ya dan sassauta rik on da yai mata  Wai duk mema genesis na fushin nan ne .? Kan project d in nan ne right.?

Ta dan kallesa da wutsiyar ido. Kaman Wanda ya fama mata wani mik i tace  Waye yake fad a da mahaifinsa.? Waye yake d aukan fansa kan mahaifinsa.!

 Oh no please.. Not again. Ya fad i yana kame Kansa kad an. Sai kuma ya dubeta a fusace  Maybe he pushed me into becoming this monster.. Don t you think.!

Sai ta girgiza Kai tana dubansa  A a saidai idan hakan d in ka zab a. K walla suka ciko idonta tana dubansa. Ta rik o hannayensa cikin nata  Shin zakaci gaba da rayuwa a bayanka ne.? Meyasa zaka bar kanka rufe cikin kurkuku.. Wann k uncin da kake ji cikin zuciyarka ba komai bane illa kasa karb an k addararka da kayi. A wasu lokuta Allah yakan saka mana jarabawar mu su zamto mutanen da suke da alak a ta jini damu. Mutane mafi kusanci damu. Bamu ke zab an ahalinmu ba, kuma hakan Rahamarsa ce. Ta d an numfasa kafin taci gaba. Allah ya jarabci salihan bayinsa Annabawansa da ahalinsu. Kaman Annabi Ibrahim (AS) Allah ya jarabce shi da Babansa. Kaman Annabi Yusuf (AS) Allah ya jarabce shi da  yanuwansa. Kaman Annabi Yaqub (AS) Allah ya jarabce shi da  ya yansa. Kaman Annabi Nooh(AS) Allah ya jarabce shi da D ansa. Kaman Annabinmu fiyayyen halitta(SAW) Allah ya jarabcesa da Uncles d insa. Duka wad annan Annabawa masu daraja sun fuskanci jarabawa daga cikin ahali. Ashe lallai muma zaa jarabcemu daga cikin namu ahalin. Wad ann k alubale da jarabawa suke k arfafa imaninmu..Sann Allah shike shiryar da Wanda yaso.. Daga haka bata kuma cewa komai ba taci gaba da tattare kayyakin da take.

Haidar ya koma ya zauna had ida zuba mata ido ba tareda ya kuma cewa komai ba. A hankali yasa tafukan hannayensa ya shafi fuskarsa.
**

Koda suka dawo gida maganganun Anisa suke yawo a kwanyarta, tayi k ok arin ta yakice tinanin amma ta kasa. A lissafi saura kwanaki uku kacal ta cika watanni uku da aure. Hakan na nufin alk awarin da ta d aukar ma mahaifiyarta yana gab da cika. Ya kamata ta waiwayi gida. Tana buk atan sanin wani hali ahalinta ke ciki. Musamman majinyacin mahaifinta. Tinanin kalaman Anisa suka ci gaba da dukan kwanyarta.  Shin Mommy ta tab a tambayarki wani abu gameda ahalinki.? Tai saurin rintse idonta ta mik e da zummar ficewa taji muryar Haidar daga bathroom yana kiranta. Ta isa jikin closet din kafin ta d anyi gyaran murya ta amsa. Haidar yaci gaba  Could you please pass me my towel.

Ta shiga bin closet din da kallo tana duban yanda komai yake cikin tsari. Nan ta hangi towel d in dan sama kad an anyi folding an jerasu cikin open shelf cabinet. Ta ciro towel din mai dan girma tai knocking a k ofan bathroom din  Ga.. Gashi nan na kawo maka.

Muryarsa ta sinkayo  The door is open.. you can come in.

Ta zaro ido waje jin abinda yace. Sai ta soma girgiza kai ita kad ai  A a.. A a kawai ka karb a. Ta k arashe tana mai tura hannunta dake rikeda towel d in ta tsakanin k ofar. Bata ankare ba saiji tai ya had e da hannunta Ya janyota cikin bathroom d in.

Ummul ta rintse idonta sosai sai ta fashe masa da kuka. ta shiga dukan k irjinsa  Mai kake aikatawa ne.. Dan Allah ka& k yaleni na fice. Please..!

For the first time da taji sautin dariyarsa. Cak ta tsaya da abinda take still ta kasa bud e idonta.

Haidar murmushi yake Har hak waransa na bayyana  Okay.. Open your eyes now.. You are here already..!

Ummul ta mak e kafad a tana kuma dukan k irjinsa  A a nidai bazan.. bazan bud e ba.

 Okaaaay.. Let s see now..  Trust me, I m gonna make you open those eyes. Har lokacin murmushi mai sauti mai bayyana hak wara yake. Abinda Ya jima baiba na tsawon lokaci.

 Wai.. Mai kake k ok arin aikatawa.?

Bai amsata ba yaci gaba da niyyansa.

A yayinda Ummul ke k ok arin zillewa bata ankara ba sai ji tai Haidar Ya janyota sun fad a cikin jacuzzi tub d in a tare.

Ummul ta ja numfashi tana mai fiddo kanta waje had ida shafe ruwan da Ya jik a mata fuska.

Ta kafesa da ido baki a ture kaman zata fashe da wani kukan.

Haidar ya kashe mata ido daya  See. I told you zansa ki bud e idonki.

Ta soma k ok arin mik ewa yayi saurin kamo hannayenta  Ina kuma zakije bayan kin riga kin jik e.

Baki a ture tace  Ba kaine ka jik ani ba... Kuma kasan Mommy ta gayyacemu cin abincin dare. Ya kamata naje sashenta da wuri dan na taimaka da wasu abubuwan..

 Kar ki damu Mommy bazata ce komai ba..

Ta d an hararesa baki a ture  Kuma na riga na shirya.. kasa na jik e gaba d aya.

Ya dan tab e baki kad an had ida lifting shoulders d insa  Shikenan sai ki sake wani wankan. Ya matso saitin kunnenta yana mai rage murya  Let s bath.. Together..

Turasa tai da duka k arfinta ta tashi . Murya na rawa ta shiga nuna masa forehead d insa da hannunta  Kaga duba kaga.. akwai abu kusan idonka.. Yakai hannunsa goshinsa sai Ummul tai amfani da damar ta tashi a guje ta zille masa. Wann karon itake masa dariyar.

 Don t worry, I ll get you next time. Ya k arashe yana mai mata alama da yatsarsa.

Anisa da tin shigowarta sashen ta soma sinkayo kaman sautin mutane nan ta sad ad kaman mai shirin satan wani abu. Ta lab e yanda take sinkayo sautin. K iris Ya rage Zuciyar Anisa bai buga ba. Kasa jurewa tai dole ta fice daga sashen.

Tana ficewa ta d auki waya ta kirawo Hisham. Cikin tsananin huci take fad in  No way Hisham. I can t wait till that day.. I m losing my patience here. Na tsani wann kucakar.. She s driving me crazy.. Ji nake kaman naje na shak eta.

 You will not do anything foolish.

Ta katsesa  Na gaji Hisham.. Bakaji yanda suke dariya cikin nishad i ba. They were having a good time. Ta saki kara tana fad in  It s so irritating.. Ka gane we can t let those two be happy while we are stuck here.. just freaking miserable. We need to act fast.!

Hisham dake ci gaba da sakin huci Ya katseta cikin tsawa  Just shut up Neesa.! Na gaya Miki bazaki aikata komai ba ba tareda umarnina ba. Na dan lokaci ne. Haidar bazai taba samun dama akan Ummul dita ba. So just trust me.! Ya k arashe idanunsa ba kuma kad awa in rage.

A fusace ta katse kiran tana kuma ci gaba da zagaya d akin zuciyarta naci gaba da tafarfasa. Sautin nishadin Haidar da Ummul Ya kasa barin kwanyarta da kunnuwarta. Ta saki k ara kad an tana durk usawa wajen. A hankali take furta  I hate you.. I hate you Ummul.!

*

Koda Ummul ta koma nata d akin murmushi ne Ya kasa barin fuskarta. Ta Tina sanda sukai juyi cikin jacuzzi tub tare sai ta lumshe ido a hankali tana sauk e sassanyar ajiyan zuciya. Wata doguwar riga silk kalan peach da ya zauna a jikinta sosai ta d auko ta saka ta yane kanta da mayanin rigar. Ba makeup a fuskarta sai d an man leb e amma sosai tai kyau. Fatarta da bai cika haske ba sann bai cika duhu ba ya k ara murjewa yayi kyau. Kwantattun sumarta irinta asalin k abilar fulani da ta d auko daga mahaifiyarta sun kwanta sunyi luf tin daga gaban goshinta Har zuwa gefen fuskarta. Kallo d aya zaka mata kaso sake kallonta. Kalan rigar sosai ya tafi da Kalar jikinta. Abinda bata saba ba sai ta tsinci kanta da duban kanta a madubi. Kunya da dariyar kanta suka zo mata lokaci d aya. Harga Allah zata iya cewa ta mance da wata damuwar gidan duniya da batun Anisa. Shi d in kawai take hangowa a duniyar ta Wanda takeji tamkar su biyu ne ciki. Parlor ta sauko tana jiransa dan yace ta jirasa zasu shiga sashen Mommy tare.

A b angaren Haidar kuwa bayan Ya d auki file din ya jima yana juyawa yana tinanin maganganunta kai tsaye sashen mahaifinsa Ya nufa.

Daddy yana zaune study Haidar yai Sallama Ya shigo.

Daddy ya d ago ya dubi Haidar da idanunsa dake rufe cikin farin gilashi na k ara k arfin gani ga wad anda shekaru Ya d an ja masu.

Tin daga yanda Daddy ya amsa masa Sallama jikin Haidar Ya d anyi sanyi. Dan yanayin amsa masa da yai yasha bambam da irin yanda yake amsa masa a baya.

Sun d auki lokaci suna duban juna kafin Daddy ya nuna masa kujera mai kallon table d insa yace ya zauna.

Haidar ya k arisa ya zauna.

Shiru Ya dan ratsa tsakani kafin Haidar yai k arfin halin cewa  Daddy.. Barka da dare.

Daddy ya amsa masa had ida jinjina Kai.

Sai Haidar ya aje folder d in saman table din Daddy.

Daddy ya girgiza Kai kad an kaman Wanda yake avoiding k wayan idon Haidar d in  What s this for.?

Haidar yai clearing throat d insa  Yarjejeniyar project d in ne Daddy.. Tareda resignation latter.. Na janye ragamar kula da kwangilar.. Sann.. Na aje aikina na company.

Daddy sai Ya d ago yana dubansa sosai wann karon.

Haidar sai Ya mik e kansa a kife  I.. I m sorry idan ban kasance wann d an da kake fata da buri na zama ba..

Ya soma k ok arin ficewa daga study d in mahaifinsa ya dakatar dashi.

 Aliyu.! Daddy ya ambaci sunansa.

Ya d ago Ya dubi Daddy.

Da ido Daddy yai masa nuni da kujeran  Koma ka zauna.

Haidar ya komo ya zauna har lokacin Kansa a kife.

Cikin tsawa da fad a kaman yanda ya saba masa a lokutan baya ya soma fad in  Ni kake ce ma ka aje aikinka..? How dare you.? Who do you think you are...! Kai har ka kai ka dubeni kace min ka aje aikinka.? Kai har ka isa.?!

Da a lokutan baya ne da ya amsa ko ya maida ma mahaifinsa martani cikin daga murya. Amma ga mamakin Daddy sai yaji ya soma magana a natse  I m sorry.. But I can t do it Daddy.! Ya fad i k walla suna ciko idanunsa. Cak mahaifinsa ya tsaya yana dubansa.

Haidar yaci gaba da girgiza Kai

62 / 95