AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   29 / 95

84K to 87K   out of 283.8K words

a tsammanin zata samu solution na yanda zatai da matar nan cikin sauk i ba. Ta dubi Anisa tace  Ni yau kin gama min komai. Ina Miki kallon marar wayau ashe zaki iya had a plan irin wann. Lallai na yarda banyi ganganci ba da nace You d become my eyes here.

Anisa ta murmusa  I m your daughter after all, Ammi.

Asshe ta jinina kai  K warai yau kin gama tabbatar min. Kuma na yarda zakiyi kaman yanda nace. Koda wasa kar ki bari D anuwanki Haidar Ya samu kusanci da yarinyar nan. Kiyi duk irin makircin da kikaga Ya dace ki tabbata basu samu kusanci ba a tsakanin watanni uku.

Anisa ta girgiza kai kad an  Amma Ammi meyasa kika canza ra ayinki akan yarinyar bayan da kince mun na zama mabudin k ulla shak uwa tsakaninsu da Haidar.. Ammi what s with all the mystery behind this marriage.. Ke yanzu kin nuna baki so amma a b oye ba tareda kin bari Aunty Kwaise ta fahimci haka ba. Ita Aunty Kwaise tana son auren tana son yarinyar da duka zuciyarta. And at the same time baki so wann matar tayi magana da Aunty Kwaise.. Ta k arashe tana nuna Inna Dije dake zube saman gado tana bacci. Ta kuma girgiza kai  Ammi wai menene b oyeyyen al amarin gameda Auren Haidar.?

Asshe ta sauk e ajiyan zuciya ta kamo hannayen Anisa  Ki yarda dani Anisa. Zan fayyace miki komai amma ba a daidai wann lokacin ba. Akwai lokacin da zaki fahimci duk abubuwan da nayi. Iyakacin abinda zan fad a Miki a k arshe shine zaki mallaki Haidar da izinin Allah. Amma fah sai kinyi aiki tuk uru Anisa. Kar ki bari Ya kusanci yarinyar nan. Daga k arshe zamu nemo mafita.

Anisa ta sauk e ajiyan zuciya  Shikenan Ammi zanyi yanda kikace. After all, bana son auren tin daga farko. Yanzu zan d auko makaman yak i na da kika sa nai watsi dasu daga farko. Ta kuma murmusawa kafin tace  Tinda inada ke Ammi, I know I m not fighting a losing battle.

Suka sakar ma juna murmushi a tare kafin Anisa tasa kai ta fice zuciyarta na mata sanyi. Zatai whatsoever it takes dan ta tabbata yarinyar nan ta fita daga rayuwar Haidar duk tsananin son da Mommy ke mata kuwa. Ta kuma rausayar da ido kafin ta shige.

Asshe ta janyo ma Inne Dije k ofa kafin ta fito daga b angaren bak in ta nufi wajen  yaruwarta daketa faman neman layin Haidar bata samu.

Zama tai gefenta ganin damuwa ya nuna k arara saman fuskar Mommy.

 Aunty Kwaise, ya na ganki haka. Allah sa dai lafiya.?

Mommy ta furzar da huci kad an  Na gaza samun layin Haidar Har yanzu. Ga amaryarsa ta iso.

Asshe ta jinina kai kad an  Relax Aunty Kwaise. Ki kwantar da hankalinki.. Yarinyar nan tana nan a gidan nan har tsawon watanni uku. Ki basa space kar ki tak ura masa da batun a yanzu. Tinda an samu Ya amince kuma yarjejeniya akai dashi so I believe zai zo Har nan kan k afafunsa.

Mommy da har lokacin ta gaza samun sukuni girgiza kai take  What if ya janye fah Asshe.? What if wancan makirar ta kuma jifansa da wani mugun asirin fah..? Asshe what if Malaminta yafi namu..? Asshe I m scared.. Tsoro nake kar duk efforts d ina su tafi a banza.

Asshe ta kamo hannun Mommy ta zaunarta saman gado  A a Aunty Kwaise ke uwa ce. Da izinin Allah k ok arin ki bazai tafi a banza ba. Haidar zai dawo gareki. D anki zai dawo gareki. Munyi komai kaman yanda Malam yace. Inada yak inin hak armu zata cimma ruwa. Just relax, ki zama calm kuma ki tunk ari Haidar a tsanake. Yanda kike ta rawar k afa akan yarinyar zai k ara tunzura Haidar ne. Kinsan halinsa hasalima kinfi kowa sani tinda ke kika haifesa. Ki bashi gobe zuwa jibi koma satin nan. A hankali sai ki tunk aresa da batun.

Mommy ta girgiza kai  Sati Asshe..? Toh me zaman me yarinyar zatai a gidan nan idan Har babu wanda tazo domin shi.. Asshe no sati yayi yawa. Kema uwa ce ya kamata kifi kowa fahimtar mai nake ji.

Asshe ta jinjina kai  Na fahimceki Aunty Kwaise. Shiyasa nake k ok arin fahimtar dake abinda na hango.

Mommy ta jinjina kai a hankali tana duban Asshe wacce gaba d aya batada wani kuzari  Asshe. Ta kirawo sunanta in a serious tune.

Zuciyar Asshe Ya tsinke. Kai da ganinta kaga maras gaskiya.

Mommy taci gaba  Akwai abinda ya kamata na sani ne..? Ina nufin, tinda kuka kawo yarinyar nan kin canza. Kaman akwai abinda ke damunki ba kaman lokacin da muka soma shirya auren nan ba. Tell me, is there something I should know.?

Asshe tai Shiru zuciyarta naci gaba da yankewa sai tanajin tamkar  yaruwar tata ta riga ta fahimci komai abinka da maras gaskiya.

 Asshe.! Mommy ta kuma ambato sunanta su duka biyun suna duban juna.

Sai Asshe ta fashe da kuka tana girgiza kai.

Hakan yai mugun tada hankalin Mommy. Bata San sanda ta mik e ta k araso wajen  Yaruwar tata ba. Ta dafata tana tambayarta meke faruwa.

Asshe na hawaye take bama Mommy hak uri tana girgiza kai.

Cikin rashin Hajiya Kwaise ke girgiza kai  Asshe meyasa kike kuka irin haka. Kuma meyasa kike bani hak uri.. Wani laifi ne kika min..?

Cikin zuban hawaye Asshe taci gaba  Na miki laifi mai girma Aunty Kwaise..

Mommy ta girgiza kai  Laifi.. Wane irin laifi..?

Anisa da isowarta jikin k ofan kenan nan tai tsaye ta kasa kunne tana sauraron wani laifi ne mahaifiyarta ta aikata ma Mommy. Cikin zuciyarta Addu a take Allah yasa taji amsoshin duk tambayoyin da takewa mahaifiyarta gameda wann murd add en aure da sukai ma Haidar.


Muryar Amminta ta sinkayo tana fad in  An sace komai Aunty Kwaise. Kayan lefe na gani na fad a da kika sa akai ma yarinyar. A lokacin da kayan ya dawo gidana bayan an kai gidansu yarinyar.. A lokacin b arayi suka biyo dare suka kwashe komai.. Maganar millions of Naira ake.. Shiyasa kikaga dik jikina yayi sanyi ko zarafin fad a ma yarinyar ma ban samu ba balle danginta.

Shiru Mommy tai tana dubanta. Sai ta jinjina kai a hankali  Kan haka kika tada hankalinki.. Idan dan wann ne Babu wani matsala tinda kwalliya ta biya kud in sabulu yarinyar ta riga ta shigo hannunmu. Akan auren nan har property na na d aga na sayar a garin nan.. Kwabon Aliyu Maitama baiyi ciwon kai cikin yak in neman auren nan ba. So ko nawa zan kashe akan yarinyar nan bazan Ji ciwo ba Asshe because it worth it. Gobe idan Allah Ya kaimu sai ita yarinyar su fita da Anisa ta tayata da shopping kafin mu shawo kan shi gogan. Kinga fitan nasu da Anisa ma zai d an sa ta kuma sakin jiki sann Anisa ta koya mata wasu abubuwan yanda zamu samun daman shawo kan Haidar Ya amince ya zauna da yarinyar matsayin mata a sauk ak e.

Jin haka yasa Anisa sakin tsaki tana juya idanu cikeda takaici tasa kai ta shige dan batai tsammanin abinda za a ce ba kenan. Ji yanda Mommy keta rawar k afa kan wann yarinyar. Ita taji ta tafi taje ta k are mata kallo taga me take dashi haka da Har Mommy ta kasa hangowa tattareda ita.


A b angaren Asshe kuwa sauk e ajiyan zuciya Tai dan dama kaya hayansu ta karb o ta coge kud ad e. Dan a wann auren Ummul da Haidar da ta had a ba k aramin jari taja ba tinda a halin yanzu mijinta baya yayinta amaryarsa yarinyar Sa ar Anisa ke cinye kud in harta da yawon k asashen waje ya daina yi da ita da amaryarsa yake. Abin sosai yake mata ciwo musamman idan ta tuna yanda tayi nata zamanin kafin ya auro yarinyar. Da alama bokan yarinyar da iyayenta yafi nata aiki ne inji Asshe. Hakan yasa ta buga business d inta da auren d an  yar Uwar nata. Dan haka koda wasa bazata tab a bari Kwaise tasan gaskiyan al amari ba.


Sanda Anisa ta tafi sashen Haidar sai cika take tana batsewa ita kad ai. Ji take tamkar cin fuska ake mata da matar Haidar. Ta ya ma za a kawo wata kucakaa ajiye gidan da sunan matar Haidar. Gidan da ita da kanta ta shirya komai to her taste wanda takeda tabbacin Haidar d inta zaiso. Bata hango Haidar tareda wata cikin gidan ba. Gida ne data shirya masu su biyu take kuma hangosu da kalolin soyayyar da zasu sha a cikin gidan harma da yaran da zasu haifa. Ta kuma rausayar da ido tana furzar da huci kad an kafin ta nufi sama.

Ga mamakin Anisa zaune ta tadda Ummul a parlor har lokacin kanta rufe cikin mayafi. Ta saki baki tana kallon ikon Allah kafin ta girgiza kai had ida juya ido  Seriously.! Da gaske kina nan kina k unk ume a wajen. Kina jiran miji yazo ya bud e fuskarki.. Lallai kuwa zaki jima kina rufe kaman kwab in cincin dan ba mijin da zai bud e wann fuskar naki.! Ta k arashe tana fincike rufin fuskan Ummul.

Damm! Haka k irjin Ummul ya buga sanda taji mai maganar ta finciki mayafin da Mommy ta rufa mata bayan sun kawota sashen.




SameenaAleeyou=???*AUREN WATA UKU..!*



*24*




*??Sameena Aleeyou&
'



Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa. Ta sani bata tsammaci farin ciki cikin Auren ba. Kaman yanda bata tab a mafarkin akwai wani rayuwa mai dad i gaba gareta ba. Saidai tafi zaton tashin hankalin daga wajen mijin. Tinda mutum ne da ko saninsa batai ba. Sann shima bata tunanin ya santa.

Ta d ago a sanyaye tana duban Anisa dake ci gaba da aika mata mugun kallo.

Anisa bata daina sakin huci ba ta finciko Ummul ta tadata tsaye  Tashi makira. Sai wani sanne fuska kike tinda kikazo. Irinku kunfi kowa iya makirci. Ta shiga zagaye Ummulkhairi dake tsaye tana k are mata kallo. Sai ta tab e baki dan ido ba mudu ba yasan kima. Dukda nad e take cikin lafaya tasan ko kusa bazasu zo d aya ba. Hasalima Anisar bazata nuna mata komai ba face farin fata.

Anisa ta rausayar da ido cikeda takaici. Tai tsaye gaban Ummul wacce Har lokacin ko motsawa batai ba  Kar kiyi tunanin zaki tadda farin ciki a wann gidan dan kinyi nasaran saye zuciyar Mommy. Bariki ji na fad a Miki wani abu. Mommy mace ce da take tamkar Hawainiya.. Babu wuya ta canza launi. And Haidar.? Ta kuma sakin murmushi tana ci gaba da zagaye Ummul  Hello, I m sorry to say sai kin gwammaci mutuwa da auren wann miskilin. Bansan dalilinki na amince ma aurensa ba amma ina mai tabbatar Miki Kinyi babban ganganci. You ve made a grave mistake, because Haidar Maitama would never ever fall for someone like you.! Ta k arashe muguwar murmushi saman fuskarta ga wani wulak antaccen kallo da take bin Ummul d in dashi.

Saida ta gama juye ma Ummulkhairi buhu buhun wulak anci kafin tasa kai zata fice.

Ummul ta sakar mata murmushi tace cikin sanyin muryarta  Baki sanar Dani sunanki ba.

Anisa ta kalleta a dak ile  Mai sanin sunana zai miki.?

Ummul ta kuma murmusawa  Sanin suna nada mahimmanci ko dan hakkin zamantakewa. Allah yasa hakan ba matsala bane.

Anisa ta tsareta da ido tana kallon salon makirci daga wajen wann bagidajiyar. sai kuma ta girgiza kai tana rolling eyes  I don t have your time.

Har tasa kai zata fice ta sinkayo muryar Ummul  Ina tunanin tinda har kika tako yanda nake kinada lokaci na. Tai maganar murmushi saman pale face d inta da taci kuka.

Anisa ta kuma dubanta da mamaki. Wanda mamakin Ya hanata magana. Bata tsammaci maganganu irin wad ann daga bakin bagidajiyar Amaryar Haidar ba.

Ganin tayi sakare yasa Ummul kuma murmusawa ta k araso kusanta  Ni sunana Ummulkhairi.. Watak ila nasan kin sani Shiyasa baki tambaya ba. Har lokacin sassanyar murmushi ne saman fuskarta Wanda ba k aramin tunzura Anisa ya kuma yi ba.

Ganin Anisa tayi Shiru yasa Ummul katse shirun da fad in  Yauwa gwara da Allah yasa kika shigo.. Dan Allah ina ne band aki wllhi tun d azu nake so na tashi nayi sallan isha amma bansan ta ina zan shiga ba.

Hararta Anisa tai daga sama zuwa k asa  Ina Miki kashedi, kar ki kuskura ki shiga d akin cen. Dan wann d akin d akin Haidar ne. Ta k arashe tana nuni da d akin.

Ummul ta murmusa kad an  Ok haka na nufin wancan kenan zan shiga. Tai nuni da d aya k ofar.

Takaici ya kuma cika Anisa ganin da gaske Ummul bata d auketa da zafi ba. Taja tsaki tana juya ido kafin tasa kai zata fice.

Ummul Tai saurin dakatar da ita  Kinga. Anisa ta juyo tana dubanta a dak ile.

 Na gode. Tai maganar har lokacin kyakkyawan murmushin ne saman fuskarta wanda ko shakka babu k ok arin b oye tashin hankalin dake saman sa take.

Wani tsakin Anisa ta kumayi kafin tasa kai ta fice a fusace.

Sauk e ajiyan zuciya Ummul tai tana mai hamdala cikin zuciyarta. Dan da dai tai tozali da mijin da aka aura mata, gwara taita karo da wann figaggiyar. Dan idan fad a da tashin hankali ne zata iya cewa cikinsa ta girma. Amma miji bata san mai zata tarar ba. Bata san wani irin k alubale zata fuskanta tare da shi ba. Haka zalik a zuciyarta Sam ya gaza natsuwa dukda kwantar mata da hankali da mahaifiyarsa tai. Ta kuma sauk e ajiyan zuciya a hankali kafin tasa kai ta nufi d aya d akin hagu da wanda Anisa tai nuni dashi matsayin na Haidar.

Kaman mai tsoron shiga haka ta tura k ofar. Zuciyarta bai daina tsinkewa ba. Sai addu an neman samun salama had ida natsuwa take cikin zuciyarta take. D aki ne mai matuk ar kyau da tsari komai na ciki sabo ne dal da alama. Tai tsaye sororo tana duban d akin dan ita dai bata San ta ina zata fara ba. Abinda ta soma tunowa shine gadon baccinsu ita da  yaruwarta Khulsum. Shikenan Sun rabu. Ta rabu da kowa nata kenan kaman yanda Umma ta umarceta. Shikenan ba ita ba danginta. Wani hali Abba yake ciki.? Yaya yanayin k arfin jikinsa.? Umma ta mata iyaka dasu gaba d aya tace ko a waya kar ta nemesu idan har ita ta haifeta. Sai taji k afafunta Sun gaza d aukarta. Nan ta silale wajen kuka na zuwa mata gadan gadan.

**

Kano&


Har ta kwanta wajajen misalin k arfe shad aya na dare taji ana buga mata k ofa. Ta mik e da kyar tana mamakin waye haka cikin daren nan. Bata kawo kowa ba sai Khulsum tinda ita ce tazo mata cikin dare irin haka a kwanan baya.

Ta k araso tana tambayar wanene lokaci guda tana ci gaba da fad in Khulsum kece nan wajen.

Ga tsananin mamakinta muryar D anta Hisham taji. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa.

 Hisham.! Ta furta a hankali

Hisham yace  Hajja ni ne.

Ta bud e k ofan tana dubansa da mamaki  Lafiya kai kuma cikin daren nan.. Watau bazaka daina irin wann tafiyar naka ba ko.

Murmushi Hisham keyi yana duban mahaifiyar tasa  Haba Hajjata tarban da za a min kenan. Hajja ko shigowa gidan banyi ba fah balle na sha ruwa balle mujega gaisuwa.

K wafa tai tana dubansa kafin tasa kai ta shige tana ci gaba da sababin yanda ya maida tafiyan dare d abi arsa.

Hisham ya maida k ofan ya rufe kafin ya take mata baya yana fad in Allah ya huci Zuciyar Mamanshi tuba yake.


Sukai zaune a parlor suna gaisawa bayan ta gama sillesa tas kan yanda ya maida tafiyar dare jiki musamman duba da yanayin hanoyin a yanzu.

Hisham ya tsareta da ido. Shi sai lokacin yake hango rama tattare da ita.

Ta d an kuma dubansa  Waima mai Ya dawo dakai ne.? Inji baka jima da komawa bakin aikin ba. Kai da kanka kace kunada babban project a kampanin ku zaka tara hankalinka waje d aya. Toh me ka dawo yi.?

 Hajjah.. Ya kira sunanta a hankali.

Sai ta d ago ta dubesa ganin sosai ya tara hankalinsa.

 Wani abu ya faru ne da bana nan.?

Tambayar da yai mata sai taji tamkar yana sane da cewa Ummul tayi aure ne kuma ba kowa ta aura ba face D anuwansa da suke Uba d aya. Ji tayi kaman d an nata Ya riga yasan sirrin da ta jima tana b oye masa.

Ta girgiza kai a d an daburce  Mai ka gani.. Kaga ni bacci nake ka katse min. Ko ma meye mayi magana da safe. Tashi kaje ga abinci a kitchen sai kai warming kaci tinda kai ka so zuwa cikin dare. Idan bai maka ba kasha ruwan shayi dama abinda ka Saba kenan.

Hisham Ya girgiza kai. Tana k ok arin mik ewa yai saurin k arasawa Ya rik e hannunta  Hajjah you look sick. Kinyi ciwo ne sanda bana nan..?

Ta sauk e ajiyan zuciya jin ba Ummul ya tambayeta ba wanda ba grin Allah da zai waye suyi waya bai tambayeta ita ba. Yaso karb an lambar wayarta ma sai Hajjan ta sanar dashi Ummul batada waya. Yaita mamakin ya za ace budurwa kaman Ummul ba waya a hannunta.

 Eh.. eh nayi dan zazzabin nan da ake fama dashi. Amma bai wani tsanani ba. Shiyasa ma ban sanar dakai ba gudun kar ka tashin hankalinka ka d ago k

29 / 95