AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   78 / 95

231K to 234K   out of 283.8K words

i cewa sadakinki shine zai zama kudin jinyar mahaifinki.. Idan akwai Wanda Ya tilasta Miki auren Haidar ba kowa bane face ni.. Ummulkhair, Haidar baida masaniya a duka abubuwan da muka aikata nida mahaifiyarsa.. Kaman yanda mahaifiyarki ma bata sani ba.!

Cikin wane irin yanayi Ummul ta d ago tana duban Aunty Asshe hawaye na gangaro mata.

Asshe taci gaba da jinjina kai tana hawaye  Haidar baisan da labarin Auren karya sihiri ba kaman yanda mahaifiyarki bata sani ba.! Ummul batada laifi cikin AUREN WATA UKU da muka shirya. Mahaifiyarki uwa ce kawai kaman ko wace uwa. She wants nothing but the best for her daughter. Tana son  yarta takaiga d akin Aure kaman ko wace  ya mace.. Tana so ta sauk e wani nauyi ne kawai da Ya rataya a wuyanta matsayinta na mahaifiya. Tana so ta cike wani gurbi nata na zama uwa a gareki. Da saninta da hankalinta ba mahaifiyar da zata d auki  yarta ta sakata cikin halak a.. Mahaifiyarki tana matuk ar k aunarki Ummulkhair..! Asshe taci gaba da girgiza kai tana duban Ummul  Mahaifyarki Bata san da Auren karya sihiri ba.! Mahaifiyarki bata san da AUREN WATA UKU ba har sai bayan da akai auren. Idan akwai mai laifi ni ce da na b oye mata. Ni nayi amfani da rauninta na shashantar da ita Har ta d auki  yarta ta jefata cikin irin Auren da Babu Uwar da zata saka  yarta. !

Tinda Asshe ta soma magana kuka kawai Ummul take ba k akk autawa. Tausayi da soyayyar mahaifiyarta ya cika zuciyarta.

Asshe taci gaba  Ni na datse soyayya da shak uwa dake tskanin  ya da mahaifiya. Ni nayi umarni ma mahaifiyarki cewa ba ita ba ke Har sai bayan tsawon watanni uku. Ni ce nan na tilasta mata ta sanar dake haka amma ba rad in kanta bane. Ni na saka shamak i a tsakaninku.. Yau gashi  yansanda Sun saka shamak i tsakani na da tawa  yar.. Anisa tana tsare kurkuku.. Da zargi masu nauyi akanta na attempting kasheki da taso yi..! Ta kuma kamo hannayen Ummul hawaye naci gaba da gangaro mata  Zunubaina ke bibiyata.. Tabbas duk abinda ka shuka a rayuwar nan zai dawo gareka. Ya rage naka ka shuka khairan ko sharran. Ummul dan Allah ki yafe mun ki yafe ma  Yata Anisa ko zamu samu sassauci.!

Ummul taci gaba da kuka sharshar da hawaye yayinda Asshe ma taci gaba da zuban hawaye. Ta goge hawayen kafin taci gaba  Anisa tayi yunk urin kashe ki ne sabida soyayyar da take ma Haidar.. Ina sane da duka abubuwan da Anisa take Wanda hankali bazai Kama ba amma na adana a raina sabida soyayyar dake tsakanin Mahaifiya da  yarta.. Na mance ba ayi ma Allah wayo.. Kaman yanda naso raba wata uwa da  yarta gashi nan Nima yanzu za a rabani da nawa  yar.. Nabi son zuciyana Ya rufe mun ido.. Nayi komai ne sabida soyayyar da nake ma yarana Haidar da kuma Anisa. Ki sani Ummulkhair.. Haidar baida masaniya akan Auren karya sihiri.. Eh Tabbas da yarda da amincewarsa aka k ulla AUREN WATA UKU sabida wani manufa na shi kan iyayensa a baya amma baisan da labarin karya sihiri ba. Ya d auki girman laifin ne kawai domin Ya zamto shield ga mahaifiyarsa.. Ya datse igiyan Auren ku ne ba don yana son yin hakan ba sai don ya zamto garkuwa a idonki dama sauran jama a ga mahaifiyarsa.. Ya d auki laifin mahaifiyarsa ne don ita d in mahaifiyarsa ce.. Ko wane D a na gari zai sadaukar da komai nasa sabida mahaifiyarsa.. Ciki harda soyayyarsa.. Kuma na sani wann shine mafarkin ki da burinki ga ahalin Haidar Tun bayan da kika shigo rayuwarsu.. Kina kwadayin kiga alak arsa da iyayensa ta gyaru tayi kyau.. Toh Tabbas ta gyaru kuma tayi kyau.. Saidai tazo at a huge cost. The cost of your marriage.! Ta kamo hannayen Ummul cikin nata su duka biyun hawaye na gangaro musu tace  Ki yafe ma Haidar domin shi d in masoyinki ne. Ni na raini Haidar da hannuwana Tun yana k uruciya.. Na kalle shi Har tasowarsa.. Kuma ban tab a ganin shi cikin soyayya irin Wanda na gani akanki ba. Sai suka soma sinkayo kukan jaririn daga window.

Asshe taci gaba da jinjina kai tana duban Ummul  A wasu lokutan mukan rufe idon mu ne mu Dole ce kawai da K addara suke sa  ya ya su girma ba tareda iyayensu biyu ba matuk a suna raye.Ki koma d akin mijinki ko dan wann D an k aramin alhakin da baisan hawa ba baisan sauk a ba. Kar ki bari ahalinki ya tarwatse. Kar ki hana ma D anki abinda Haidar Ya rasa lokacin k uruciya.. Kar ki bari tarihin abinda Ya faru da mahaifinsa Ya maimaita kanshi..! Ta sauk e ajiyan zuciya murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta. A hankali ta mik e tana gyara fuskarta  Zanje naga jikana.. D an Haidar dina.! Tana ida fad in haka ta mik e ta fice. Yayinda Ummul Tai bursting cikin kuka.

Asshe tana fitowa taci karo da Haidar a lobby cikin wane irin yanayi tamkar Wanda ruwa Ya shanye shi. Cikin sanyin jiki take dubansa. Ta ambato sunansa a hankali  Haidar.!

Bai iya cewa komai ba sai kawai Ya rungume Asshe.

Jikin Asshe ya kuma yin sanyi ganin yanayin nasa. Ta rungume shi cikin jikinta hawaye na kuma gangaro mata  I m here.. I m here Haidar.. Your Aunt is here.! Sai kawai yai bursting cikin kuka. Kuka sosai yake kaman k aramin yaro kukan da zata iya cewa bata tab a jin yai irinsa ba tun tasowarsa matsayinta na Uwar goyonsa.

Cikin rawar murya Asshe ke furta  Wann ba Zaki na bane.. Zakin da na raina baya kuka.. Na raini Jarumi.. Jarumin da ba a ganin rauninsa balle a gano lagnosa.! Tana maganar tana tuna yarintar sa sabida Sam baya kuka a yarinta sann ba wani abu da yake basa tsoro bayan wofantar dashi da iyayensa sukai a lokacin da Ya kamata su jasa jiki.

Saman wani kujera suka zauna ta dan waje. Haidar ya saka tafukan hannayensa ya share fuskarsa da ta rine ta koma jazir.

Cikin wane irin yanayi yake furta  When will all this end..? Yaushe ne komai zai wuce.? Meyasa rayuwa ta kasance haka..?!

Aunty Asshe ta jinjina masa kai  Wann sunnar rayuwa ce Haidar.. Jarabawa basu k arewa Har sai an bar gidan jarabawa wato duniya.!

Haidar yaci gaba da girgiza kai  Na kasa yarda.. Na kasa yarda da abinda ke faruwa.. Mutumin da nafi tsana a halin yanzu Ya zama D anuwana..! How is this possible Aunt.?! Ta ya zan kalli wann mutumin na kirashi da D anuwa..? Just how.?!

Cikin rashin fahimta Asshe ta girgiza kai  Wane D anuwa kake magana Haidar..? Meke faruwa.?

Yaci gaba da jinjina Kai  Daddy yana can reuniting with his long lost son. Su d in Sun hadu da juna.. Daga k arshe dai, D a da mahaifin sunga juna.. I don t know how Mommy would take it.. Bansan ya iyaye na zasu d auka ba.. Amma abinda na sani shi ne wann mutumin bazai tab a zama D anuwana ba.!

Muryar Mommy suka sinkayo tana fad in  D an uwa.. Wane D anuwa kake magana Haidar.?!

A tare Haidar da Aunty Asshe suka juyo suna duban Mommy.



SameenaAleeyou=???*AUREN WATA UKU..!*



*56*





*??Sameena Aleeyou&
'





Haidar yai shiru yana duban Mommy. Ba huruminsa bane ya zamto mutum na farko da zai sanar da ita gameda al amarin. This is something for his Dad to decide. Kaman yayi shishigi ne idan Ya soma sanar da ita.

Mommy ta kuma jefo masa tambayar ganin yayi shiru ba amsa.

 Haidar, nace wane D anuwa kake magana.?

Asshe ta dubi Mommy sai ta dubi Haidar. Sai ta d an murmusa kad an tace  D anuwansa Hilal dake makaranta yake magana& 

Mommy dai kallonsu take bawai ta gamsu ba..

Wayar Haidar ce ta soma ruri. Daddy ne mai kira sai Ya mik e Ya dan matsa gefe yana amsa kiran Daddy yayinda Aunty Asshe ta k araso ga  yar Uwar nata jiki ba wani kwari dan har kawo lokacin ta kasa sakin jiki da Mommy kaman a baya.

Daga d aya b angaren Daddy yaci gaba  Kana jina Haidar.. Sadis yana hanya zai taho ya d aukeku kaida mahaifiyarka.. Ina so kuzo ku sameni a nan masauk i.

Haidar ya dan lumshe idonsa kadan Ya waresu yana duban Mommy dake zaune gefen Aunty Asshe tinda shidai yasan kwanan zancen. Bazai wuce kan Sabon D an Daddy bane da mahaifiyarsa. Sai Ya dan furzar da huci kad an yace  Ok Daddy.. Kaman yanda kace.

Yana ida wayan Ya dawo yanda ya baro su Mommy.

A tare suke dubansa itada Aunty Asshe. Sai gani sukai ya duk a gaban Mommy daga nan yanda take zaune saman kujera. Jikin Mommy ya kuma yin sanyi da al amarin Haidar. Hannayenta ya kamo cikin nasa yana dubata. Lokaci guda yake furta  You are the most precious to Me Mommy.. And.. Whatever happene know that I m here for you.. And I got your back. Ya jinjina Kansa kad an kafin ya k arada  I love you Mommy. So much.

Har lokacin jiki a sanyaye Mommy ke dubansa musamman da taji ya matse hannun nata sosai cikin nasa sanda yake maganan.

Ta jinjina masa kai a hankali tana jin k walla na ciko idonta.  Nima Ina sonka D ana.. Ina matuk ar k aunarka.!

Ya murmusa kad an had ida mik ewa tsaye. Aunty Asshe ma murmushin tai cikeda farin ciki. Ta goge hawayen da suka gangaro mata ta mik e tana fad in zata shiga ciki taga jariri sabon angonsu.

Bayan ta shige Haidar Ya rik o hannun Mommy suna tafe sanda yaga isowar Sadis. Suka nufi motar hannunta na sakale cikin nasa. Ita dai Mommy bata san ina ake zuwa ba sai ji tai Haidar na fad in  Mommy akwai yanda zamuje yanzu.. Daddy yana can yana jiranmu.. Ina so Ki kwantar da hankalinki.. Kuma ki sani ina tare dake. Ya k arashe yana bud e mata owners corner.

Duban Haidar kurum take ba tareda ta iya furta koda kalma ba sai k irjinta dake tsananta bugu ba tareda sanin dalili ba. Tana gani ya bud e front Seat Ya shige yace da Sadis suje.

Sadis yaja mota suka fara tafiya. Tinda suka soma tafiya saman kwalta Mommy bata iya cewa komai ba. Har kawo bud e musu wani tampatsetsen gate da akai. Suka shige cikin tsantsararren Villa Suite d in Sadis Ya nemi waje yai parking.

Haidar ne Ya bud e ma Mommy k ofan motar. Tai zaune daga cikin motar tana dubansa  Haidar.. What is this place..? Ina muka zo.. Wajen wa muka zo.?

Sai Ya murmusa  Mommy masauk inku da Daddy muka zo.. Daddy yana ciki yana jiranki.

 Amma.. Ummul da Jikana suna can asibiti.. Bai kamata mu taho mu barosu ba.

Ya jinjina Kansa a hankali yana kamo hannunta  Kar ki damu Mommy zamuje mu d auko su.. But for now.. Daddy needs to see you first. Let s go. Ya k arashe yana kamo hannunta suka nufi building d in.

Tamkar rak umi da akala haka Mommy ke biyeda Haidar Har suka isa k ofan parlorn.

Daddy ne zaune daga saman kujera dake daga centre& Hajja Fannah tana daga can gefe yayinda Hisham ke zaune daga saman carpet gefen k afafun Daddy kansa kife kaman mutumin arziki.

Sosai Haidar Ya rik e hannun mahaifiyarsa cikin nasa idonsa kan Daddy Sam bai kula da Hisham dake zaune daga gefe ba.

Zuciyar Mommy yaci gaba da bugawa sanda suke shiga cikin parlorn musamman da ta hangi Hisham abokin Haidar wanda D anta Ya aminta dashi Ya kuma ci amanarsa.

Sai Mommy ta soma girgiza kai tana nuna Hisham  Haidar mai wann criminal d in yake a nan. He should be arrested. He supposed to be in jail.. Dashi da Anisa Sun had e kai sunyi yunk urin kasheku kaida Ummul.. Ta dubi Daddy  Engr mai wann azzalumin da Ya kusa halaka mana D anmu da iyalinsa yake a nan.?

Daddy ya mik e da sauri Ya nufota  Calm down Kwaise.. That s exactly why I asked Haidar to bring you here..

Hannayen Mommy Daddy ya kamo yai k ok arin zaunarta saman kujerar dake fuskantar Wanda Hajja Fannah take. Idon Hajja Fannah akansu har Daddy yai masauk i ma matarsa saman kujera, sai Hajja Fannah ta sauk e idanunta k asa a hankali tana mai kifa kanta.

Sam Mommy bata kula da matar dake zaune daga kujera mai fuskantar nata ba idanunta naga Hisham tana fad in saidai a kira yansanda su tafi dashi. Daddy ya kamo hannayenta cikin k ok arin calming dinta  Kwaise ki natsu ki saurareni..!

Sai Mommy tai shiru tana dubansa.

Daddy yaci gaba  Akwai abubuwa da dama da Ya kamata ki sani harma da Haidar. Ya dan numfasa kafin yaci gaba  Kin tuna Fannah..? Ina nufin tsohuwar Matata Fannah.?

Sai jikin Mommy ya kuma yin sanyi. Ta soma jinjina kai a hankali  Matarka Fannah da nai ajalin Aurenku a tsakanin watanni Uku tak.! Matarka da na koreta da jaririn cikin wata uku sabida son zuciya.! Muryarta yaci gaba da rawa hawaye na gangaro mata yayinda Hisham ke mata wani irin duba na tsana daga nan yanda yake zaune gumi na karyo masa kaman ba AC bane cikin parlorn. Yau dai da kumnuwarsa yake jin Kwaise Maitama tana amo laifukan da ta aikata masa shida mahaifiyarsa.

Mommy taci gaba sanda ta kamo hannayen Daddy sosai cikin nata  Engr da ita nake kwana da ita nake tashi.. Banida burin da ya wuce na ganta na kuma nemi yafiyarta.! Ta k arashe cikin kuka yayinda Hajja Fannah taci gaba da zubda hawaye daga can yanda take zaune saman kujera.

Daddy ma hawaye ne ya digo masa sanda yake jinjina kai yana duban Mommy  She s here Kwaise.. She s right here with us.. Fannah is here with us.. Ba ita kawai ba.. Harda wann jaririn cikin nata da ta fita dashi.!

Dumm! Haka k irjin Mommy ya buga. Ta d ago gajiyayyun idanunta tana duban Daddy dasu  Fannah..! Fannah da D anta suna nan a nan..?! Ta tambaya cikin rawar murya.

Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana karkatar da fuskarsa b angaren da Hajja take.

Cikin wane irin yanayi Mommy ke kaikaitowa tana duban yanda taga Daddy na duba. Cak ta mik e tsaye tana dubanta  Fann.. Fannah..! Ta furta a hankali still tana dubanta.

Sai Hajja ta d ago idonta mai zuban hawaye tana duban Mommy.

A hankali Mommy ta soma takawa har ta isa ga Fannah. Ta zuba mata ido tana kallonta. Sai ga Mommy na k ok arin duk awa gaban kujeran da Hajja Fannah take. Bata bari Mommy ta duk a ba itama ta sauk o daga saman kujeran.

Su duka biyu suna durkushe gaban juna. Mommy ta kai hannayenta masu shaking ta d aura saman na Hajja Fannah.

Daddy ya dubi Haidar da Hisham yace su taho tareda shi. Haidar yakai ma Hisham wani irin duba kaman bazai bi bayan Daddyn ba sai kuma yasa kai yabi bayan mahaifin nasa.

Parlorn Ya rage saura Hajja da Mommy. Sosai suke kuka su duka biyun an rasa mai bama wani baki.
Saida sukai ma isar su kafin Mommy ta iya bud e baki ta soma sanar da Hajja Fannah irin nemanta da tai sanda bata nan. Da irin nadaman da Tai bayan abinda ta mata sai kuma ta soma neman gafaran Fannah d in.

Hajja Fannah ta girgiza kai tana hawaye  Ta Ya zan iya yafe Miki bayan kin so ki maimaita tarihin abinda kika min akan Matar D anki Ummulkhair? Yarinyar da kika so hallak ata ta hanyar sihiri dan ki ceto naki D an.! Ta k arashe hawaye naci gaba da ganganci mata.

Saurin girgiza kai Mommy take tana hawaye  Kafin na gane kuskure na.. Kafin nayi tuba na gaskiya. Kuka ya hanata ci gaba da magana. Tai k ok arin nitsa kanta kafin ta dubi Hajja tace  Zan karanto Miki komai.. Irin zaman da na fuskanta nida D ana a gidan Engr Aliyu Maitama bayan tafiyarki da jaririn cikinki.. Shigowar Ummulkhair cikin rayuwarmu da yanda Allah Ya sauya al amarin ahalinmu bayan mun zab i mubi turba mik akk iya.. Nasan idan kikaji komai Watak ila ki Sami gurbi cikin zuciyarki ki yafe min Fannah.!

Taryan taryan Mommy ta soma karanto mata abubuwan da suka faru tin bayan barinta gidan.

**

A can d aya parlorn kuwa Daddy ne zaune daga saman kujera yaran nasa guda biyu suna daga saman carpet ko wanne yana daga nashi angle din. Kan Hisham a kife cikeda ladabi ya risina gaban Daddy ko iya d ago ido ya dubi Daddy cikin ido bayayi yayinda Haidar ke ci gaba da aika masa kallon k yama da tsana. Da kyar ma Haidar d in ya amince ya zauna a parlorn saida Daddy yai da gaske dan cewa yai bazai iya jure zama Inuwa guda da betrayer irin Hisham ba Wanda ko fuskarsa baya k aunar Ya sake gani balle Ya sauraresa.

Cikin dacin rai Haidar yaci gaba da nuna Hisham yana fad in  Everything make sense now Daddy. Wann azzalumin ya rab i ahalinmu ne domin Ya tarwatsa mu. Sai Ya fara da company kafin ya gangaro kan Matata Shiyasa yai amfani da shashancin Anisa ta zamto mataimakiyarsa. Everything is clear now.. There s nothing like coincidence.. Ya riga ya jima da shirya komai Daddy.!

Cikin wane irin yanayi Hisham ke girgiza kai yana duban Haidar  I can t believe

78 / 95