AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   64 / 95

189K to 192K   out of 283.8K words



Shigowa Ummul Tai rik eda kofin coffee da ya buk ata a hannunta. Ta mik a masa cikeda risinawa.

Ya amsa yana mata godiya. Sai ya nuna mata gefensa  Come sit here... let s talk.

Haka kurum taji gabanta ya fad i sai ta d an girgiza kai kad an  Magana kuma.?

Haidar ya jinjina Kai bayan ya sipping coffee din  Kar ki damu yau magana zamuyi ba akan kowa ko komai ba... Magana ce akanmu.. Let s talk.. about us. Ya k arashe yana kashe mata ido d aya gajeren murmushi saman fuskarsa.

Bugun zuciyarta Ya dan karu musamman da taga yanda yake binta da kallo. sai ta k arasa a d an sanyaye ta zauna a yanda Ya nuna matan.

Dak ik ai suka d an shige kafin Haidar Ya aje coffee din dake hannunsa bisa teburin gefensa. Ya gyara zamansa Ya karkato sosai yana facing dinta gwiwarsu na gogar juna.

Sai ta d an sadda idonta kad an ganin irin yanda ya tsareta. Hannayensa ya d aura saman nata dake bisa laps dinta.

Ummul ta dubi hannayensa da Ya d aura bisa nata dake bisa cinyarta. Sai ta d ago ta dubesa a d an sanyaye.

 Khairy..! Ya ambace sunanta kaman yanda Yake kiranta.

 You came into my life to make it better.. You ve changed all areas in my life.. Ta dube shi sai ta dan murmusa  Bani nayi ba duka yin Allah ne..

Ya jnjina kansa  Kece sanadi... Yaci gaba da jinjina Kai hannayenta cikin nasa  I.. know there s still a lot.. to do.. But you showed me the way Khairy.. You made me want to be a better son& You made me wanna wake up and reflect. You made me wann be.. a better business man, take my brand far.. And above all, you made me believe,.That I can be a better person. Thank you.. For coming into my life. Ya k arashe labarin na neman sauya direction.

Jiki a sanyaye ta soma k ok arin zame hannunta sabida zuciyarta dake bugawa cikin sauri.

 Dare yayi.. Ya kamata ka kwanta ka huta& Kaifa patient ne.

Ya kamo waits dinta ya zaunarta saman laps d insa. Cikin sigan rad a yake fad in  Wa yace miki ni patient ne har yanzu.? Bari ma na nuna miki na warke.

Ta zaro ido tana k ok arin turasa  Kaga.. Ni tafiya ma zan.. Bata kai aya ba ya rufe bakinta da nasa.



SameenaAleeyou=???*AUREN WATA UKU..!*



*46*



*??Sameena Aleeyou&
'




Da kyar ta samu ya k yaleta yai mata rakiya har k ofan parlorn Mommy. Suna isowa ta zame jikinta daga nasa. Sai ya mik a mata k aramar paper bag d in dake hannunsa.

Ta d an girgiza Kai  Ta mecece.?

 Don t open it yet sai kin shiga. Ya fad i yana kashe mata ido d aya . Bai kuma tsayawa sauraronta ba ya soma tafiya yana waving dinta kaman kar ya tafi ya barta.

Ta girgiza Kai kurum tana binsa da kallo a haka har ya shige.

Anisa tana nan ta kasa ta tsare tana jiran dawowarta dan kusan komai Akan idonta ya faru.

Sam Ummul batasan da mutum a parlorn ba sai muryar Anisa da ta sinkayo. Batada lokacin sauraron maganganun Anisa hakan yasa tuni tasa kai ta nufi upstairs ba tareda ta tsaya sauraron maganganun Anisa ba. Amma sai Anisa ta bud e murya tace  Auren Haidar Maitama might seem to you like a golden opportunity na samun nasarori da Jin dad in rayuwa.. Musamman duba da irin rayuwar da kika baro cikinta& But what if, this golden opportunity comes at a very high price.?

Ummul taci gaba da k ok arin dannar kanta. Dan a yanda ta tsara ba a wann lokacin zata fuskanci Anisa ba. Ta gama shirya lokacin da zata tunk ari Anisa da kalamanta. Sai ta bud e lumsassun idonta a hankali taci gaba da tafiya ba tareda ta juyo ta dubi Anisa ba.

Anisa ta take mata baya tana ci gaba da fad in  Abinda yasa kikaga na dage miki Ummul dan inada gaskiya ne. Bana so ki saki jiki cikin auren da zakiyi danasani a gaba. Kuma ciwon  ya mace ta  ya mace ce.. Ba komai cikin wann auren face k ask anci.

Ummul ta dubi Anisa da murmushi saman fuskarta. Sai kuma ta maida k ofan d aki ta rufe ba tarda tace komai ba. Dan Sam bazata bari ta b ata shirinta ba.

Anisa taci gaba da sakin huci dan ta tsani wann silent treatment din da Ummul ke bata dan bata mance karonsu da Ummul d in ba. Tasan she s sharp and smart dik yanda akai wann shirun da take tana murmushi wani abin take shiryawa tinda Tasha lalata mata shiri ba d aya ba. Taci gaba da sakin huci ita kad ai.

Ummul tana shigewa d aki ta lumshe idonta tana karanto addu o in samun sauk i da sukuni cikin zuciyarta dan sosai take Jin maganganun Anisa har cikin k ahon zuciyarta da b argonta.

Ta isa saman gado ta zauna gijif sai ta dubi  yar jakan da Haidar ya bata. Ta soma k ok arin bud ewa.

Nan taga wayar salula ce ta yayi mai d ankaran kyau. Da alama komai an saka cikin wayar. Kaman daga chaji har zuwa simcard.

Taita juya wayar kafin ta kunna. Sak o ne ya fara mata Sallama _I've bought a new book.. and open a brand new page& together with you_

Taita karanta sak on yayinda jikinta ya kuma mutuwa. A b angare na kunnenta guda kalaman Anisa ke mata yawo a d aya b angaren sak on Haidar cikin yanayin muryarsa na mata yawo. Ta rasa wanne d aya zata saurara sai ta toshe duka kunnuwanta biyu kuka na zuwa mata. Ganin koke koke da tunanin bazasu fishheta ba kawai sai ta mik e ta d auro alwala ta soma Kai kukanta ga Mabuwayin Sarki da babu kaman shi.

Tana bisa darduma tayi lamo tana duban wayar kira na shigowa Wanda tasan kiransa ne tinda lambarsa ne kawai kan wayar. Bata bi takan wayar ba haka akaita kira har dai ya hak ura. K arshe ya tura sakwanni Wanda suma batabi takansu ba.

Duk Haidar sai ya damu ya fara tunanin ko bataji dad in kyautar da yai mata bane. Kodai ya mata wani abin ne.

Washe gari da safe Fashion designer tazo har gida da manyan bridal dress catalog dan amarya Ummul ta zaba yanayin rigar da za a mata. Anisa ita ke tayata zabe. Ummul sai duban Anisa take tana mamakin wai wacce ke mata gargadi da kashedi da auren Haidar sai gashi itace mai zakewa wajen zaba mata Kayan da zata saka.

Aka nuno wani farin gown mai dankaran kyau Anisa tace  Yauwa perfect. I think this one is ok.

Kaman daga sama suka sinkayi wann muryar nasa daga bayansu  This is too revealing.. My wife can t wear this. Ya fad i cikeda gadara hannayensa sakale cikin aljihun jeans d insa yasa kai ya shige upstairs gaida Mommy ba tareda ya dubi ko yanda Ummul d in take ba. Ta bisa da kallo duk jikinta a sanyaye. Toh ko dai fushi yake da ita sabida yayita kiranta a Daren jiya bata d aga ba har sakwanni ya turo bata amsa shi ba. Gaba d aya sai taji babu dadi.

Anisa na hankalce da ita da Haidar d in. Lokaci guda tana mamakin wai Haidar ke cewa kaya is too revealing dik girma da tasowa cikin gogaggun wayayyu da yai. Lallai ta yarda ya fara nisa cikin soyayyar wann Bagidajiyar. Idan batai sauri ta rabasa da wann Bagidajiyar ba haka zata maida mata Haidar d inta Bagidaje irinta.

Haka har aka gama zaben rigunan ita dai bama tace ga rigar da aka tsaida ba. Duk tunaninta na kan Haidar.. Bata san ta damu da fushinsa har haka ba. Abinda yafi bata mamaki shine ko ta kanta bai sake bi ba.. Bai nemeta bata ma sake saka shi a idonta cikin gidan ba. Ta d auki wayar kaman zata kira layin sa amma sai ta kasa. Haka kaman wasa har ranan da ake saka ran ranan ne Mommy ta tsaida dan shagalin bikinsu bata saka Haidar idonta ba. Wani abinda ya k ara bama Ummul mamaki shine Anisa batai k asa a gwiwa wajen shirya komai ba. Ita Mommy tasa ta kaita saloon aka gyara mata gashi sann ta d auko mai lalle da makeup artist har gida. Kaman wata maid of honor haka Anisa ta zak e tana mata komai. Ummul bata daina karantarta ba.

Cikin wata farar doguwar riga da dinkin ya zauna jikinta ta shirya. An mata dauri na zamani da irin fabric d in rigar Wanda da gani zaka san an b arar da kudi wajen sayensa da d i???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nkasa. Ba a cika mata kwalliyar ba amma tayi kyau har ta gaji. Duk Wanda ya kalle ta sai yaso sake kallonta. Haka masu kwalliyan da shiryata sukaita santin kyaun da tayi. Ita dai Ummul gaba d aya ranan ta kasa gane kanta gaba jinta take ba daidai ba. Something feels wrong. Sai kawai ta danganta hakan da fushin da Haidar keyi da ita.

Koda akace ta fito su d auki hoto da Haidar sai rashin nutsuwar da take ciki ya ninku. Zuciyarta yaci gaba da bugu. Yanda kasan bata tab a sanin shi ba haka takeji. Da kyar ta iya fitowa k irjinta sai bugu yake.

Tin daga saman bene masu camera ke haskota har zuwa saukowarta parlorn basu daina d aukarta hoto ta ko wani angle ba.

Anisa ta dubeta ta saki murmushi  Relax Ummul, ki natsu a Miki hotuna masu kyau dan wad ann hotunan a manyan mujallu zasu fito.. Mrs Haidar Maitama. Ta kashe mata ido guda tana fad in a d auke su tare.

Mommy ta k araso tana dubanta kwalla kaman zai zubo mata ta k arasa ta rungumeta  Kinyi kyau daughter.. May yours be among the best. Ta k arashe murmushi saman fuskarta. Nan aka d auke su hoto. K wallan da Ummul take makalewa ya gangaro. Mommy tai saurin goge mata tana girgiza Kai  A a Ummul, yau fah ba ranan kuka bane.. Bana so hawayen nan ya bata Miki kwalliya. Ta waigo cikin k ok arin danne nata kukan tana tambayar wai ina Haidar d in ne.?

Anisa da takaicin acting Mommy ya isheta sai ta juya ido tana furzar da huci. Tana k ok arin barin wajen ta hango Haidar na shigowa cikin shiga ta farar shadda k al babbar riga harda hula. Shigan da zata iya cewa bata tab a ganinsa ciki ba. Sosai ya amshe sa dan ba Anisa kawai ba harta ita Ummul d in saida ta shagala da kallonsa.

Ya k araso aka musu su uku da Mommy. Ta shige tsakiyar su ta rungumesu su duka biyun akaita kashe musu pictures.

Daga bisani aka soma yima amarya da ango. Masu hoto suna bada direction. Aka ce ta d aura hannunta guda saman chest d insa sai ta d an d ago tana dubansa. Duban irin na mai yake nufi.? Ita fah har kawo wann lokacin bai mata magana ba gashi duk yanda aka ce ya rik e jikinta kafin ma ace yayi. Wann fah shine mutumin da a baya he s allergic to cameras. Ummul bata Ankara ba saiji tai ya d ago hannunta ya d aura saman chest d insa.

Anisa taji wani k atutun bak in ciki ya tokare mata makoshi. Ga wani kallo da suke bin juna dashi. A hankali take calming kanta cikin zuciyarta  Patience Neesa.! Patience.!! Na yau ne kawai.. Daga rana mai kaman ta yau ta zama tarihi a rayuwar Haidar dinki. Ta kuma murmusawa  I can t wait for things to get chaotic.

**

A can waje kuwa zabga zabgan bak aken jeep d in sukai parking. Motar farko Hajiya Asshe ce ta fito sai Inna Dije daga d aya b angaren. D ayar motar kuwa daga can seat din  yanuwan Ummul guda biyu ne Badi a da Azeema yayinda Umma da Mama Tani ke daga tsakiya. Suka neri suka fito sahu sahu.

Kallo guda zakai ma Umma ka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki. Tayi tsuru tsuru da ido ko motsi mai kyau bata iyawa. Badia da Azeema kuwa kasa rufe baki sukai ganin irin gidan da Ummul wai take aure ciki.. Ummul fah. Wacce kowa ke gudunta cikin ahalin su. Wann maras sa an.. Wacce ake mata lak abi da mai farar k afa.. Wann wacce maza da yawa ke guje ma Aurenta.. Allah mai iko. Gashi daga sauk an su wasu ma aikata masu uniform suka taho suna masu sannu da zuwa cikin harshen turanci cikeda ladabi suna amsan jakkunansu. D aya daga ciki tai directing nasu zuwa masauk i. Sukaja suka tsaya wann ya dubi wancan wancan ya dubi wann. Asshe ta furzar da huci kad an ganin duk sunja sun tsaya suna duban tsoro ma juna  Ku taho muje mana. Wai ko Baku gaji bane.?

Sai Inna Dije ta murmusa da shike ita ta tab a zuwa lokacin auren Ummul. Tace  Kunga ba masu yankan kai bane ko Shan jini. Ku taho muje..
Sai Mama Tani wacce ta kasa gasgata wata duniya ma tukunna take ta janyo Inna Dije tana rad a mata  Ke Dije.. Da gaske kike.? So kike kice min nan shine gidan da Ummul take ko kuma dai matar nan ta shanshantar damu ne gaba d aya Kama Suwaiba. Dije nan fah fadan shugaban k asa ne. K ur ani shine a talabijin nake gani.! Ta k arashe harda dangwala yatsa saman harshe.

Inna Dije taci gaba da janyo Mama Tani tana fad in  Kin dai gani da idonki.. Na tabbata bazaki so ki bar Ummul cikin wann daula ba. Duk bala in da za ayi bazamu fice daga gidan nan ba saida Ummul. Cikin sigan rad a suke ma juna magana.

Duk maganar da sukeyi ita dai Umma bama tasan mai ke faruwa ba jefa k afafunta kawai take tana tuna kalaman Asshe a gareta tana tuna a daidai wann rana sukai AUREN WATA UKU da tai ma Ummul da d ansu zaizo k arshe.

Azeema da abin ya fara bata tsoro ta dan jada baya tana janyo  yaruwarta Badia. Tai k asa da murya  Badia nifah wllhi naga gidan zama.. Wllhi bazan koma Kano ba ina nan tareda  Yaruwata.!

Badia ta dara kad an tace  Toh kiyi yaya da Habibinki kuma idan ya dawo miki.?

Azeema ta galla mata harara  A a Mak iyi dai ba Habibi ba. Ai ni idan kinga na fice a gidan nan saidai idan fadan shugaban k asa zan tafi..

Badia ta kuma darawa daidai sanda suka isa guest section din.

Asshe ta dubesu tace su saki jiki su huta ga abinci dama tuni an jere musu idan da akwai abinda suke buk ata ga ma aikata zasuji dasu. Zata shiga cikin gida ta sanar da isowarsu. Inna Dije ne kawai ta amsa mata yayinda Mama Tani ta rakata da harara duk cikin acting ne da suke dan su shashantar da Umma. Badia da Azeema kam basu tsaya sauraronta ba suka tashi suka soma zaga gida suna kallon aljannar duniya a cewarsu.

Bayan ficewar Asshe jikin Umma yaci gaba da rawa. Ba tareda ta dubesu ba take fad in  Yau ne.. Yau ne tai alk awari.. Wa adin auren zai cika.. Yau d ansu zai sakar mun Ummul d ita.. Zan d auki Ummul d ita mu tafi.. Shine kawai abinda ya kawoni..!

Mama Tani da Inna Dije suka dubi juna.. Tani tuni shiga bud e buden kayayyakin abincin da aka jere musu Wanda da yawa ma bama ta tab a ganin irinsu ba. Da ta ga dai bata gane wasu abun ba sai ta d auki Wanda takeda tabbacin naman kaza ne ta soma gwagwiya dama Tani da kaza. Tana ci tana Zare ido kaman za a k wace. Ta dafa Umma  Shiyasa na rakoki  Yaruwata. Kinga wann mata mai zubin akwati (Wai Asshe) kina ganinta kinga makira.. Wani abin take shirya Miki.. Ni da tuni kin sanar Dani ga yanda auren Ummul ta kasance ai da tuni anyita da wajewa an gama komai.. Haba Tani fah nake.! Ta k arashe tana kurban wani abu da bata tabbata kunu ne ko madara mai  yan yan itatu ciki ba. Ta lumshe ido tana fad in  Dole ace masu kudin nan kunci rabonku na Aljannah ehe.!


Inna Dije ta harareta sai ta dafa Umma tace  Suwaiba mu duka muna nan tare da ke bazan bari aci zarafin  yard anuwana ba. Kafin su wulak anta Ummul zamu d auketa mu tafi dan kinsan masu kudin nan su wulak anta D anadam ba komai bane wajensu. Tinda auren ma a wulak ance suka nema dan haka a wulak ance zasu nemi rabuwa bacin haka meye dalilinsu na gayyato mu a wann rana da sukai alk awarin kashe Auren. Kinga Suwaiba tashi ki shiga band aki kiyo alwala.. Muje na nuna miki yanda ake amfani da irin bandakinsu kinsan ni na tab a zuwa. Ta k arashe tana mai kamo Umma suka nufi band aki. Ta nuna mata yanda zatayi kafin ta dawo ga Tani. Ta kafe ta da ido  Ke kuma Tani ba sallah ba salati kin fara ciye ciyen abubuwan da cikinki bai saba da irinsu ba.. Idan cikinki ya tsure kika kasa zuwa wajen shagalin bikin tozarta Suwaiba da  yarta saidai na kulleki a d akin nan dan nidai billahillazi bazaki b ata min shiri ba ehe..

Mama Tani ta saki gyatsa mai k arfin gaske tace  Yo ka iya ibada ciki bai d auka ba. Ibadanki ma maje ina Dije.. Yo naga

64 / 95