AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   65 / 95

192K to 195K   out of 283.8K words

k eta ce da fansa ya kawo ki nan..

Inna Dije ta galla mata harara yayinda Mama Tani ta shek e da dariya.

**

Jikin Mommy ya d anyi sanyi. Ta kuma duban Asshe  Asshe kika ce harda Mahaifiyar Ummul akazo..? Asshe ina Jin nauyi.. Ina matuk ar Jin nauyin bayin Allahn nan.. Mu ya kamata mu fara zuwa musu ba su ba.. Kuma a yanda na shirya da anyi bikin tariyar zamu d unguma mu tafi gaba d aya mu gaida iyayen Ummul da danginta musamman iyayenta.. Mu kuma musu godiya sann a k ulla alak a da zumunci mai kyau.. Munada shirin zuwa gaba d ayamu.. Ni, Haidar harma da Engr da Kansa. Sun cancanci haka Asshe.. Dama kawai na buk aci wasu daga cikin danginta suzo ne dan itama taji dad i kar taga ba danginta ko d aya wajen shagalin. Dan farin cikin Ummulkhair. Duk jikin Mommy a sanyaye take maganar.

Asshe ta furzar da huci kad an tana mamakin dan dai Mommy batasan waye Suwaiba ba. Da bazata d aga hankalinta kan wann shashasahar matar ba.

Ta dan girgiza Kai  Aunty Kwaise ke ya kamata ki musu godiya ko su ya kamata su Miki godiya.? Yau kece zaki duk a kiyi godiya ma talaka Aunty Kwaise.? Aunty Kwaise Anya kece kuwa ba a canza ki ba.? Asshe ta k arashe tana bin Yaruwar tata da kallon mamaki.

Sai Mommy ta dubeta ta shiga jinjina Kai  K warai kuwa ni ce Asshe. Saidai ba Kwaisen da kika sani a baya bane.. Wancan Kwaise da kika sani capitalist, maison mulki, izza da d agawa ta tafi kuma bazata sake dawowa ba. Wann Kwaise ce da ta fahimci duniya da rayuwa. Kwaise ce mai Neman dacewa da tsira duniya da lahira.

Asshe ta furzar da huci kad an sai kuma tace  Aunty Kwaise nidai.. Da an kashe auren nan kawai mu basu d iyarsu kaman yanda muka tsaro daga farko kawai a huta.. Aunty Kwaise wa adin ya cika.. Kawai mu basu  yarsu kawai and save Haidar.. Ta k arashe cikin rawar murya.

Mommy sai ta d an girgiza Kai kad an cikin rashin fahimta  Save Haidar kuma Asshe. Kaman ya save Haidar.. If there s someone to save here is Ummul. Balle ma boka makaryaci ne kinga dai yanda Al amra suka kasance bayan mun bar hanyar b ata mun kama hanyar gaskiya. Kinga bana ma so ana d ago wann maganar kije ko da akwai abinda suke buk ata sann kizo kimin iso na gaishesu.

Asshe ta kuma fruzar da huci  Wai Suwaibar zakije gaisarwa Aunty Kwaise.? Matar nan fah ko a  yar aikatau d inki bata isa tazo ba.

Izuwa lokacin Zuciyar Mommy ya soma tunzura. A fusace ta dubeta wann karon  Matar da ta haifo Ummulkhairi idan ta kama na duk a gabanta na mata godiya ne zanyi haka Asshe. Domin kuwa tinda Ummulkhair ta shigo rayuwarmu banda alkhairi babu abinda muke gani. Ke shaida ce a gabanki komai ya faru Asshe.. For years ina kuka kan ahalina.. Ahalin da na ruguza da hannu na.. Akan idonki Haidar da baisan hawa ba baisan sauk a ba ya d auki burden din da ba nasa ba tsawon rayuwa. Shin ba Akan haka bane muka tassamma kauce hanya.? Yau sai gashi cikin ikon Allah Haidar ya zauna da iyayensa lafiya. Ahalin da na jima ina mafarki ya dunkule waje d aya. Ummul ta shigo ta farfado da duk wasu kyawawan d abi u da muka mance dasu ta cika gidan da nargartanta da alkhairanta.. Kinga kuwa ko duk awa nai na mata godiya ban fad i ba. Mahaifiyar Ummul ko wace iri ce Asshe tanada k ima da mutunci a idona. Danginta ko yaya suke mun zama d aya irrespective of our social differences. I expect you to do the same with them. Kin fahimta.! Ta k arashe cikeda umarni like a big sister.

Zuciyar Asshe yaci gaba da tafasa. Ta kula Aunty Kwaise tsaf zata iya zab en dangin Ummul ta mance ita ce danginta ta asali. Gaba d aya itakam kaman an canza mata  Yaruwa.

 Magana nake Miki Asshe..! Mommy ta kuma tsawatar mata.

Sai Asshe ta jinjina Kai da kyar tana k ok arin k wak ulo hawaye. Cikin muryar kuka take fad in  Aunty Kwaise yanda kike magana kin fara bani tsoro.. Aunty Kwaise karfa k warin gwiwar da kike dashi Akan yarinyar nan yasa ki mance komai.. Aunty Kwaise ni fah amana ce wajenki.. Iyayenmu Sun bar Miki amanata.. Banida wacce ta fiki kaf fad in duniya.. Aunty Kwaise dan Allah kar ki tab a mance hakan.. Idan kika rabu dani bansan ya zanyi ba& Duk abinda nakeyi kawai dan na damu dake ne.

Jikin Mommy ya d anyi sanyi. Sai taji dan dafa Asshe  Haka ne Asshe. Idan ba mutuwa ba babu abinda zai rabamu  Yaruwata. Likewise banida wacce ta fiki. A lokacin kuka da lokacin dariya duk muna tare. Ta dalilinki Ummulkhairi ta shigo rayuwarmu Asshe.

Bata k arasa sauraronta ba zuciyarta ya shiga tafarfasa. Dole dai sai ta ambaci wann mayyar yarinyar. Gaskiya ta fara yarda da batun su Dije yarinyar mayyace dan gashi ta lashe Zuciyar  yaruwarta.

Sauri sauri Asshe ta nufi kiran Dije da Tani. Suka keb e tana sanar dasu tsarin yanda zasu tarwatsa wann biki.

Asshe ta rik e kunne tana duban Tani da Inna Dije alamun kashedi  Kunaji biki ne na manyan mutane. Biki ne da zai samu halartan manema labarai. Dole  Yan jarida zasu sanin  yar gidan wane hamshak i tilon D an Aliyu Maitama yake Aure. Inaso da zaran manema labarai sun soma jefo muku tambayoyi ku fara amo duk abinda muka shirya.

Tani ta chab i zancen da fad in  Zan fed e musu daga buzu Har fata. Zasuji wacece Ummul da kuma yanda auren Ya kasance. Wayyo wayaga Tani cikin talabijin tana bayani.

Asshe ta furzar da huci had ida yin gajeren tsaki. Ta dubi Inna Dije alamun tana jiran nata ba asin.

Dije ta murmusa  Ita ce tayi sanadin mutuwan tilon D a na Faizu sabida bala in farar k afarta. Maza bila adadi sun mutu ta dalilinta.

Asshe taci gaba da jinjina kai tana sakin murmushin cin nasara.
**

Su Badia tuni Sun nufi cikin gidan suna fad in a kaisu wajen Ummul. Da kyar Anisa ta kyale su suka shige wajen Ummul d in a Cewar Anisa ana gyara mata kwalliyarta dan tuni ta canza zuwa wani shigan.

Sai kallonsu take tana yatsina fuska tana toshe hanci wai dik warin talauci suke.

Azeema tana hankalce da ita jira take su fito daga wajen  yaruwarsu Ummul suji da ita.

Suna shigewa katafaren bedroom d in suka tafi a guje suka rungume Ummul.


Ummul wacce ta gansu a bazata sai ta mik e cikin tsananin shock tama rasa mafarki take ko gaskiya.  Yanuwanta take gani. Sai ta rungumesu ta k ank ame tana mai fashewa da kuka.

Saida tai mai isarta suna bata baki suna fad in kar ta bata kwalliyarta.

Ummul ta kuma dubansu dan ta kasa yarda  Azeema, Badia.. Wai dan Allah kune.?

Azeema ta murmusa tace  K warai kuwa mune  Yaruwa. Kawo hannunki ma ki kuma tabbatarwa. Ta had e hannuwansu su duka uku waje guda. Ummul ta murmusa tana share guntun hawayen da ya digo mata da tissue  Ina Abba na.. Ya jikinshi..? Ina Khulsum da Anty Salima.? Meyasa basu biyoku ba..? Ina Mama da Umma.?

Azeema da Badia suka dubi juna sai Badia ta kamo hannun Ummul tace  Abba jikinsa da sauk i sosai Ummul.. Yana tashi yana zama saidai maganar ne da sauki. Sann har fita dashi waje yasha iska anayi. Abubuwa ne dai har yanzu ba kasafai yake ganewa ba. Likitoci sunce sai a hankali..Kinsan ciwo idan ya had u da shekaru.

Ummul ta jinjina Kai a hankali tana addu an samun lafiya ga mahaifinta.

Azeema taci gaba  Anty Salima tana tana gidanta yaranta ba lafiya kyanda suke gaba d ayansu. Amma tace muce Miki tana tayaki murna kuma taso zuwa Allah bai nufa ba. Mun taho da Mama da Inna Dije.. Da..

Sai Badia ta dan dubeta dan Umma ita ta rokesu cewa ko sunga Ummul cikin gidan kar su sanar da ita zuwanta tukuna. Basu kawo wani abu ba dan Umman ta kwana biyu cikin wane irin yanayi.

Ummul sai bata tambayesu Umma ba dan tinda sukace Mama ta taho sai tayi tunanin Umma ke tare da Abbanta.

 Khulsum fah.? Meyasa batazo ba..? Har yanzu tana fushi dani koh.? Ta tambaya jikinta a sanyaye.


Murmushin da yafi kama da yak e sukai.

Badia tace  A a ko kad an bata fushi dake Ummul&  Ta d anyi fasali sai kuma tace  Ummul ki yafe mana duk abubuwan da muka Miki a baya..

Azeema ma ta saka baki suna rok on Ummul yafiya.

Dadi gauraye da farin ciki Ya mamaye Ummul. Ta kamo hannayensu tana fad in komai Ya wuce Allah Ya yafesu gaba d aya.

Nan ta soma tambayarsu labarin gida.

Badia ta d an numfasa tace  Abubuwa da dama Sun faru a lokacin da baki nan.. Kedai sai mun samu lokaci kawai.. Yau ranar ki ce bani so wann hawayen yaita b ata Miki kwalliyarki na  yan gayu. Cewar Badia tana k ok arin gyara mata fuskar.

Azeema tace  Wai Ummul kece kika zama haka.? Kin ganki kuwa.? Saikace wata shahararriyar  yar gayu irin Wanda muke gani wayoyin mutane ana turawa.. Ta mik e tana zaga d akin Wanda Ya amsa sunansa wajen kyau da girma  Dank ari mak ari wani aikin sai amale. Rayuwa kenan Ummul kiga yanda Allah Ya sauya miki rayuwa lokaci guda.. Tabbas kinyi hak uri kuma kinga ribar hak uri.. Sai na tuna Zubairu dasu Hajiya Dudu irin tijaran da suka zuba lokacin da suka amshe lefenki dashi Zubairun. Ai wllhi yanzu kam saidai Zubairu yazo a direbanki. Ta k arashe suna darawa daga ita Har Badi a.

Ummul ta murmusa had ida girgiza kai  A a Azeema ni duk wad ann kayan kyalekyalen basu dameni ba matuk a akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya..

 Chab ai kudi sune kwanciyar hankali wllhi.. Yo ina cikin wann daular k aryar bak in ciki Ya tunk areni ai. Azeema tace tana mai hayewa saman gadon.

Anisa ce ta banko k ofa ta shigo tana fad in maza su fice za a k arisa shirya Ummul.

Azeema ta kuma harararta Tai k wafa.

Ummul ta kamo hannayen  yanuwanta tana sanar dasu kar su koma masauk i su jirata nan parlor tana fitowa.


Koda suka fito parlor Azeema dai bata zauna ba sai zagawa take tana bama idonta abinci a cewarta.

A haka Anisa ta k araso daidai sanda Azeema take tab a wani k aton flower vase. Anisa ta rausayar da ido tana fad i a fili  Dealing with Ummul is already giving me a headache. Now I had to deal with these local champions.? Ta rausayar da ido tana furzar da huci.

 Excuse me.! Ta darara ma Azeema tsawa.

Azeema ta juyo da mamaki tana dubanta.

Anisa taci gaba da nunata a wulak ance  That flower vase worth your entire family.. Tell me, idan kika fasa zaki iya biya ne.?

Badia ta d anyi k asa da murya taceda Azeema tazo ta zauna su jira fitowar Ummul. Ta dubi Anisa tace  Kiyi hak uri bazata fasa ba.

Hararsu take daga sama zuwa k asa kafin taja dogon tsaki ta shige tana toshe hanci.

Azeema ta yunk ura zata bi bayanta Badia Tai saurin rik ota.

 Ki k yaleni na shayar da wann mai k irar zabon mamaki Badia.

Badia ta girgiza kai  A a Azeema yau ranar farin cikin Ummul ne bazaki b ata mata da wani abu ba. Musamman fad a da dangin mijinta.. Ki kyaleta kawai karma ki kulata.

Azeema Tai k wafa  Wllhi darajar Ummul taci da nayi wasan kura da ita dan dama hannuna k aik ayi yake kwana biyu. Ban saba da wann salihancin ba.

Badia tace  Naji dai bazakiyi ba.. Ta k arada inata so na tambayi Ummul ina surkin namu mu gaisa.

Daga can Azeema ta hango Haidar na tahowa dukda bata sanshi ba amma kallo d aya ta masa ta gane shine angon. Sai ta shiga tab a Badia tana fad i a hankali  Ke wllhi gashin can yana zuwa.. Shine ango. Shine surkinmu.. Na shiga uku Badia kiga irin mijin da Ummul ta samu bayan duk k alubalen da ta fuskanta saikace tauraron fina finan Hindiyan nan. Ummul ta had a komai Badia kawai ta nemi lahira. Gaskiya na yarda da karin maganar nan da ake cewa Wani JINKIRIN alkhairi ne. JINKIRIN Ummul ya zama Alkhairi Badia. Wllhi ta amsa sunanta Ummulkhairi.

Jin Azeema duk ta zauce yasa Badia take mata k afa kad an dan ya kusa k arasowa yanda suke. A hankali take furta  Ke meye haka wai. Ni dan Allah ki natsu saikace wacce kikai gamo sai sunbatu kike. Ki mata fatan alkhairi kawai.. Kinga gashi nan ya iso da alama d akin da Ummul take zai shige.

Kafin Badia ta rufe baki Azeema ta mik e ta hau d aga masa hannu  Sirkinmu.!

Haidar ya juyo da mamaki sai ya shiga  yan waige waige yana tunanin kodai ba dashi ake ba.

Azeema ta kuma nunasa da yatsa  kaidai sirkinmu. Ta k araso yanda yake bata daina washe baki ba  Mu  yanuwan Ummul ne.. Ni k anwarta ce.. Waccan kuma dake zaune Yayarta ce Babanmu d aya ai da Ummul..

Badia dake zaune daga saman sofa takaici ne ko kunyar abinda Azeema take ta ma rasa wanne ne d aya take.

Sai sukaga Haidar Ya murmusa ya fasa shigewa d akin Ya nufo yanda suke. Anisa da k arasowarta wajen kenan mamaki kaman ya kasheta ganin da gaske Haidar Maitama kema kucakan nan sannu da zuwa kuma fah ransa a sake. Wai anya ba a canza shi ba kuwa. Tana tsaka da tunaninta ta sinkayo muryar Azeema tana fad in  Sunana Azeema. Ni ce ta hud u wajen Abbanmu ai.. Daga Ummul sai ni ke biye mata..

Haidar Ya jinjina kai har lokacin da murmushi saman fuskarsa. Ya nuna Badia yace  And.. you are..?

Sai Badia da Azeema suka dubi juna. Azeema ta k araso da sauri tana rad a ma  yaruwarta  Adda Badia, kinsan dai mudai boko rakiya mukayi dan na tabbata Har yau ko shakeki za ai da kyar ki iya rubuta sunanki. Su Ummul da Khulsum ne masu kwakwalwar ganewa. Turanci fah yake miki.. Tambayarki yake Ya kike.. Kice masa you are fine. Haka nakeji ake fad a. Kar ki masa shiru zaki disga Ummul.

Badia tace  You fine.

Sai Ya d an murmusa kawai yace  I ll check on.. Khairy.. Sannunku da zuwa once again.

Azeema taci gaba da waving d insa har ya shige. Badia ta fuzgota tana fad in  Ke dan Allah wai meye haka ne.? ki kama kanki mana.

 Mutanen da muke gani a tv mun gansu a zahiri Har gaisar damu yake kice na kama kaina.. Ke Nifa yanzu ko unguwarmu na koma wllhi ba ma kowa zanke magana ba ehe& Kiji wani sunan yan gayu da yake kiran Ummul dashi.. Kai wllhi na Miki murna  yaruwa Kekam taki addu ar ta amsu.

Badia ta girgiza kai  Allah Ya baki lafiya Azeema.

Azeema ta kyalkyale da dariya tana amsawa da Ameen.


Anisa da takaici Ya cikata furzar da huci Tai tana barin wajen. Dik yanda zatai bazata bari sunan wad annan Almajiran ya shiga guest list ba tin daga waje zata sa securities suyi watsi dasu.


Ana shirin fita wajen event Anisa tai kicibis da Azeema a dan wani lobby. Sai kawai ta k ara wayarta a kunne alamun tana amsa kira  I need to double-check the guest list because ba ko wasu shara bane za a barsu su shiga. You know is a high class event. Ta k arashe tana aika ma Azeema harara.

Zata wuce Azeema ta cakumo wuyarta ta dawo da ita baya  Toh ya ne.! nace ko kinada abin cewa ne.? Ta k arashe tana tunkud a drink din dake hannun Anisar ai kaw ya zube ma Anisa a jiki ya b ata mata expensive gown dinta.

Mamaki ya hana Anisa rufe baki ganin bata ko tanka Azeema ba amma tai mata wann d ibar albarka.

Girgiza Kai Anisa take tana fad in  No this is not happening.. Not my dress..! Ta dubi Azeema dake nad e hannu riga Kai kace zata d aga wani abin ne tace  You ask for it.! Tai maganar tana sakin huci tana k ok arin Kai ma Azeema Mari amma sai caraf Azeema ta rik e nata hannun ta kuma d auketa da maruka har biyu masu kyau.

Anisa ta kuma zaro ido cikin mamaki. Saima Azeema ta soma bata tsoro ta fara tunanin jada baya zata gudu Azeema ta kuma jawota tana fad in  Ashe k aryar tashanci kike k aramar maras kunya ba yanda zakije.

Anisa taji rik on manyan yan dambe ta soma kokawan k wace kanta tana fad in  Let go.. let me go.. What are you doing you witch.. I said let me go.

Wani d aki mai kaman store Azeema ta turata ta janyo k ofar da k arfin gaske Wanda taga har wani d an haske ya kawo daga wajen rik ewar mai d aukeda alamun wajen danna yatsa, sann harda wasu lambobi jiki. Bata tab a ganin irin k ofar ba. Sai ta d an matsa da baya ganin k ofan na haske.

Anisa ta fara girgiza Kai tana bugun k ofan tana fad in

65 / 95