AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   48 / 95

141K to 144K   out of 283.8K words

ba. Na tilasta masa ya zamo abinda nake so thinking watarana zaka k aunacesa zakai alfahari dashi kaman yanda ko wani uba yake& Ya kai matsayin da Har na mance cewa ni Uwa ce dik cikin k ok arin ganin burina na had e kan ahalin Ya cika. But then I realise wann burin nawa bazai tab a cika ba& Dik abinda naso ma nawa D an na hana ma D an wata ya samu.. Na rabaka da D anka da matarka& Ta Ya zanyi zaton zan samu wann farin cikin da nake fad i tashi akai tsawon rayuwata..? I am so selfish. Kuka ya hanata ci gaba da magana yayinda jikin Daddy yai matuk ar yin sanyi.

Mommy ta share hawayen da suka zubo mata kafin taci gaba  Na gode da hakurin da kai Dani tsawon shekarun nan. For letting me stay koda sabida D anmu. Na gode da ahalin da ka bamu koda bai zamto kaman ko wani ahali ba. Koda cike yake da tarin k alubali. Taci gaba da jinjina Kai  I give up Engr.. I m tired.. Na gaji.. Iyakacin abinda nake so a yanzu shine D ana Ya dawo gareni. The wealth, the name.. Duka na hakura dasu. Na zab i D ah na.. Na rasashi daga farko bazan kuma sake rasashi a karo na biyu ba.! Ta k arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata.

Daddy ya kauda fuskarsa gefe yana k ok arin maida hawayen dake yunk urin ciko idonsa. Bai kuma cewa komai ba sai mik ewa da yai ta fice cikin sauri.

Mommy ta kuma rintse idonta wasu hawayen na gangaro mata. A halin yanzu ta gama aminta bokan da suka je wajensa itada Asshe mashahurin makaryaci ne. Tinda gashi turaren da Ya bata ta bama Ummul yasa ta fad a uku. Dama ita bata tab a yarda da aikin boka ba ko can baya Asshe ce ta ingizata sukaje. Sann she was desperate ta dawo da D anta gareta. Bazata gushe ba zataci gaba da rok on Allah Ya yafe mata kaucewa da tayi dan Tabbas taga aya. Zuciyarta na cikin natsuwa da aminci matuk a Haidar d inta na tareda Ummul. Ta aminta da hankali da natsuwar Ummul. Tanada yak inin D anta bazai tab e ba cikin ikon Allah matuk a na tareda Ummul. Da wann tunani Zuciyar Mommy ya dan samu natsuwa.



SameenaAleeyou=???*AUREN WATA UKU..!*



*37*





*??Sameena Aleeyou&
'



Bayan shud ewan awanni ta mik e da kyar dan a tunaninta ya tafi musamman da taji sam babu d uriyarsa. Window ta lek a a hankali kaman mai tsoron kar a ganta. Ga mamakinta shi ta hango zaune k asar wata bishiya Ya bada baya ma yanda take tsaye daga cikin d akin. Tsuntsayi ta gani kaman dangin tattabarai Sun taru gabansa sai watsa masu abinci yake suna ci. Wasu Har kaman zasu d ale saman hannunsa. Kai da gani zaka fahimci yana cikin annashuwa da jin dad in abinda yake. Juyowa yai yana watsa ma sauran abincin nan ta hango kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Abinda bata tab a gani ba. Zuciyarta yai wani irin yankewa tai sauri ta koma da baya had ida jingina jikin gini.

Ta d auki lokaci a haka. Kafin ta kuma rintse idonta sakamakon tunowa da tai da yanayin da suka kasance ciki bada jimawa ba. Bata San dalili ba amma sai taji hawaye Sun ziraro mata. Ta jima nan a haka kafin ta bud e lumsassun idonta da suka jike da hawaye. Ta kuma leka window amma sai taga bata gansa ba wann karon. Babu tsintsayen shima baya nan. Babu ko alamunsa. Ta sauk e ajiyan zuciya a hankali kafin tai k ok arin saita kanta. Bata San ya za ai tai escaping kurkukun da Haidar ya boyeta ciki ba. Bata san hanya ba bata kuma san idan zata iya isaga Mommy ba. Saidai abinda take da tabbaci akai shine zata fice tinda tai saa makulin na tareda ita. Zata fice kodan taje ta ceci Mommy. Har abada bazata bari Mommy ta tafi prison saboda ita ba.

Sauri sauri ta isa k ofa ta murda makullin ta soma k ok arin fitowa a hankali cikin sand a. Tana tafe tana waige waige ga tsoro da Ya cikata. Saidai tana zuwa k ofan da zai fitar da ita waje taji gam an rik e hannunta. K iris Ya rage bata saki k ara ba amma sai taji an toshe bakinta. Ta d ago idonta masu cikeda tsoro tana duban Haidar dake huci yana dubanta.

A matuk ar tsare yace  Are you trying to escape.? Where do you think you are going.? Answer me.! Guduwa kike so kiyi..?

Girgiza kai take hawaye naci gaba da gangaro mata. Haidar yaci gaba da janyota yana fad in bazata bar wann gidan ba Har sai tayi abinda ya umarceta. Da k arfin gaske Ya tura k ofan d akin Ya jefata ciki.

Cikin rawar jiki Ummul ra soma k ok arin rarrafowa tana fad in  Dan Allah kar ka sake rufeni.. Dan Allah Kaji tausayi na ka kyaleni na tafi.. Na maka alk awari bazan zauna cikin rayuwarka ba.. Dan..!


 Shiiii..! Ya mata alama da yatsarsa saman labb ansa. Ya duk a gabanta yanda take nan duke tana hawaye cikin rawar jiki. Sai ta soma k ok arin matsawa baya ganin Ya duk o gabanta suna fuskantar juna. Ga zuciyarta da bai daina tsinkewa ba.

Haidar ya dan d auki lokaci yana dubanta kafin ya kauda kansa gefe. Hannu yasa ya kamo hannunta cikin k ok arin hanata ci gaba da matsawa. Tsoro Ya hango sosai saman fuskarta. Sai ya soma sassauta rikon da yai mata a hankali. D ankwalinta da ya fad i gefe ya d auko. Ummul taga Ya kuma nufota taci gaba da k ok arin matsawa Har saida ta isa jikin gado. Ga mamakinta bai mata komai ba sai rufa mata D ankwalin da yai. Ya kuma duk awa gabanta suna fuskantar juna.

Ta sadda kanta kasa tsoron dake fuskarta bai gushe ba.

A hankali ya soma fad in  Look, you can call me a monster, but I don t hate you& And..that doesn t mean I like you either.. Kuma idan har kikayi abinda na sakaki.. Believe me, I ll let you go..

Ta dago raunannun idanunta tana dubansa. Sai Ya jinjina mata kai a hankali alamun tabbatarwa.

Dubansa take shima ita yake duba. Sai ta sadda nata idon a hankali tana mai girgiza masa kai alamun a a. Cikin sanyin murya mai gauraye da rauni take furta  Ubangijina Ya bani umarni da nai maka biyayya cikin abinda bai sab a masa ba. An shar anta wa mace neman al jannah a k ark ashin mijinta. Kaman yanda shima namiji nashi aljannar yana k ark ashin mahaifiyarsa. Ka sani Mommy da kake k ok arin turawa kurkuku naka aljannan ta wajenta aka ce ka nema.? Shiru baice komai ba. Ummul ta goge hawayen da suka gangaro mata kafin taci gaba  Shin akwai D an Adam din da zai wasa da aljannarsa.? Cikin k arfin hali Tai maganar dukda zuciyarta dake bugawa.

Katseta Haidar yai da fad in  Shut up.! Ya katseta yana mai nunata da yatsa kafin yaci gaba  Who do you think you are.? Ya kuma girgiza Kai yana rage muryarsa cikeda gargad i  You don t have the right to speak to me that way.?

Sai ta tsinci zuciyarta da ba ma Haidar amsa da fad in  Ni matarka ce.!

Kaman Wanda yaji amsar da Zuciyar nata ta bayar sai yaci gaba da jinjina Kai had ida furta  Kiyi gaggawan yin abinda na umarceki for your own freedom. You don t want to live with a monster as a husband.! Ya k arashe yana tsareta da ido.

Girgiza masa kai tai  Kai ba mugu bane. Kana kuma da zuciya mai kyau.. Wanda har zaiji tausayin dabba Ya bata abinci bana jin zaik i jin tausayin mahaifiyarsa wacce tai sanadiyar zuwansa wann duniyar, ta rainesa har kawo girma..

Katseta yai da fad in  Enough.! Ya isheki haka.. You don t know anything..! Ke baki san komai ba gameda wann matar.!

Sosai Ummul ta razana da yanayinsa.

Haidar yaci gaba cikin tsananin huci  Yes you might be right.! Watak ila tayi sanadiyan zuwana wann duniyar. Amma naso ace ta barni na Mutu ina yaro da rayuwar k unci da ta bani.! Yes. Watak ila ta raine ni kaman yanda kikace. But I was sacred the whole time! Yaci gaba da jinina Kai yana duban Ummul da idanunsa da suka kad a sukai jazir  She raised me while degrading me.. While insulting me.. She raised me locking me up in a dark room. Forcing me to eat papers. She raised me punishing me for her sins.! Yaci gaba  Because of her.. I grew up feeling low self esteem, feeling insignificant& I had a hard time living in myself..! Yaci gaba da huci yana jinjina akai  And for years& It took me years to overcome the fear and the trauma..! Ya matso da fuskarsa kusan nata  Did you know na girma ina shakku da kokonto if she s really my real mother.? Do you know how it feels ka girma cikin shakku da kokonton sanin wanene kai.?!

Suka dauki lokaci a haka suna duban juna hawaye na gangaro ma Ummul. Haidar ya matso kusanta had ida sassauta murya  So don t act like you know everything.! Yana ida fad in haka yasa kai ya fice ba tareda ya kuma yunk urin rufeta ba.

Tana jin sautin tashin motarsa. Tai saurin Lek awa nan taga Ya fuzgi motar ya bar wajen a guje. Tabi bayan motar da kallo Har ya b ace ma ganinta. Sai ta tsinci kanta da masa addu an kasancewa cikin aminci.

Jiki a sanyaye ta dawo da baya ta zauna saman gado had ida rapka tagumi. Ta rasa mai zuciyarta ke ji gameda al amarin Haidar. Idan ta fahimcesa kaman dai ya amo da abinda ke masa ciwo a zuciya ne. Har k asan zuciyarta bata jin shid in mugu ne. Sai ta stinci zuciyarta da tausaya ma rayuwar Haidar d in. Dan bayan abinda ya gama amo mata ta fahimci alak arsa da mahaifyarsa ya samo nakasu ne tun yarintarsa. Sosai taji tana son sanin asalin wanene Haidar. A wata fuskar sai tana ganin kaman shida ita sunada k addara mai kamanceceniya musamman a b angaren abinda ya shafi alak arsu da iyayensu. Tunanin Umma da irin rabuwar da sukai ya fad o mata.. A hankali ta lumshe idonta hawaye na gangaro mata.

Ranan har dare bata kuma saka shi a idonta ba.

**

Hisham yai tsaki a karo na ba adadi. Da alama amfanin Dareen ya k are cikin rayuwar Haidar. Da alama Anisa ce kawai yanzu zatai masa amfani wajen cimma burinsa. Idan kuwa har amfanin Dareen ya k are baiga amfanin zamanta da Haidar ba. Watak ila idan asirin da Dareen tai masa ya karye Haidar zai fito da Ummul daga yanda ya b oye ta. Bazai iya jure rashin sanin ina Haidar yakai Ummul ya b oye ba. He knows Haidar so well. Idan zai Mutu bazai tab a sanar da kowa ga yanda ya b oye Ummul ba. Shi mutum ne da ke aiwatar da abubuwansa ba tareda shawarin kowa ba. Shi mutum ne da baida kusanci da kowa face zuciyarsa da abinda ta raya masa. Idan kuwa har haka ne Dareen batada wani amfani. Da ita da dodon nata k arya suke. Tinda asiri baiyi wani aiki ba ya kamata ya gwada tactics d in Anisa. Watak ila ta haka zai samu ya mallaki Ummul. Shi Akan ya rasa Ummul ya yarda zai iya abandoning mission d insa na ganin bayan mahaifinsa wato Engr Aliyu Maitama da ahalinsa. Da wann tunanin ya mik e yana huci yana ayyana a cikin zuciyarsa bazai tab a bari ma Haidar Ummul ba. Soyayyarsa ga Ummul ne last abu da ya kamata ya tabba bai bari Haidar ya rigasa samu ba. Hajja ta saka masu albarka dashi da ita. Ummul bata cancanci miji irin Haidar ba. Bata cancanci zama cikin ahali irin na Maitama ba. Akan ya mallaketa ya yarda ya rasa komai. Ya isa ya janyo wani drawer. K asan drawer d in ya daga tile guda sai ga wani bak in tulu an rufe samansa da jan kyalle. Dama shi yake ajiye da wann tulun Wanda hakan yasa ya rik e Dareen a tafin hannunsa. Dareen batada say sai abinda Hisham ya fad i dukda da ita da sunanta da sumarta da na Haidar aka had a akai asirin amma batada say dan bata san ina Hisham ya b oye tulun ba. Shiyasa a kullum take bin Hisham a sannu dan Dodon tsafi ya sanar dasu duk randa wann tulun ta fashe asirin zai karye sann Haidar zai rabu da ita zai nuna bai ma tab a saninta ba. Koda Hisham yaji haka sai yai wuf ya d auke tulun ya b oye dan ya samu ya rik e Dareen cikin hannunsa ta dinga yin duk abinda ya Umarceta. Wann dalili yasa Dareen batada say sai abinda Hisham ya fad i sabida Tulun na wajensa ya masa b oyo mai nisa kaman yanda Dodo ya sanar da ita. Hakan yasa Dareen ke bin Hisham a sannu gudun kar ya fasa wann tulun ya karya asirinta na kasancewa matar Haidar.

Sauri sauri ya fito daga gidan nasa tulun rungume cikin hannunsa.


Dareen na tsaye haraban gidan tana faman safa da marwa ta hangi Hisham na zuwa. Tai tsaye Cak tana dubansa k irjinta na bugawa.

Bata Ida razana ba saida ta hangi hannun Hisham rungume da bakin tulun da Dodo ya k ulla aurensu da sumarta da sumar Haidar ya rufe cikin wann tulun ya kuma tabbatar mata matuk a wann tulun na nan yanda yake aurensu da Haidar babu abinda zai samesa sai mutuwa ce zata raba.

Ta nufo Hisham cikin rawar jiki tana fad in  Finally ka zab i ka dank a min ajiyan makullin aurena da Haidar.! Tai maganar murmushi saman fuskarta.

Dakatar da ita Hisham yai da fad in  Stay right there.!

Dareen taja ta tsaya zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Cikin rawar murya take furta  Hi& .Hisham.. What s going on..?

Murmushi Hisham yake da gefen baki  You are no longer useful to me.. Kuma kinsan abinda nake da mutanen da basuda sauran amfani wajena.. I dispose them.. Just like this.. Ya k arashe yana k ok arin sakin tulun.

Dareen ta zaburo tana k ok arin yowa Kansa  No Hisham don t do this.. Please kar ka aikata min haka.. Kar ka tsinka igiyan aurena da Haidar.. Wllhi I truly love him..!

Dariyar rainin hankali Hisham yai  Love.? Did you just say love.. How is that relevant.? Ta ya zakiyi soyayya da mutumin da bashi a hayyacinsa. bai san dake ba ko ince baisan da Aurenki ba.? Ko kuma nace idan ma ya sani auren na fluctuating cikin kansa.

Dareen ta girgiza Kai tana hawaye  Watak ila baisan ya akai Aurenmu ba amma nayi alk awarin kare wann auren till my last breath. You can t break our marriage Hisham.

Ya kuma murmusawa har lokacin bak in kwaskon na cikin hannunsa  Na tuna miki yanda akai kuka hadu ne.?

Ta kasa cewa komai sai hawaye dake gangaro mata.


Hisham yaci gaba  Wani rana ne a airport. Zamu tafi wani construction work Lagos muka hadu dake a jirgi. Tinda naga yanda kike kallon Haidar na tabbata kin kamu da sonsa. Kinyi ta k ok arin shige masa amma sai kika lura bazaki samu chance dashi ba. Har dai kaman kinyi giving up. Ni na sameki nai Miki proposing idan kina son Abokina da gaske. Kika kuma tabbatar min zaki iya komai dan kawai ki mallakesa. Na baki zab i cewa zaki mallakesa amma zaki min aiki a jikinsa. Zaki zame min tamkar spy wacce zata dinga nado min komai na duk abinda yake ciki a rayuwarsa domin Nima na cimma burina Kansa. Dani dake muka had a k arfi da k arfe. Ni na nemo Miki sumar Haidar muka had a da naki sumar muka Kai gaban dodon tsafinku aka k ulla aurenku da Haidar kaman yanda Dodon ya buk ata. Ya kuma tabbatar mana duk yanda Haidar yake zai bayyana matsayin mijinki.. Zaki bayyana masa matsayin matarsa.. Haka ne.?

Taci gaba da girgiza Kai tana hawaye. Hisham yaci gaba da murmusawa  Kiyi gaggawan b acewa daga cikin rayuwar Haidar. Dan idan kika jira na fasa kwaskwon nan Haidar sai ya kusa kashe ki da hannayensa kafin ya mik a ki ga hukuma.

Dareen na huci take dubansa  Na ranste da Allah baka isa ba Hisham. Baka isa ka rabani da abin kaunata Haidar ba.! Ta k arashe tana kokawan k wace bakin kwaskon daga hannun Hisham.

A daidai lokacin Haidar ya k araso. Hisham na hangosa yaci gaba da kokawan k wace kwaskon daga hannun Dareen yana fadin  Allah ne ya toni asirinki mushirika. Ni dama na jima da fahimtar ba tsakani da Allah kike zaune da abokina ba. Kuma yau sharrinki zai koma kanki dan sai na fasa wann kwaskon da na ganki dashi. Yau Haidar zai fahimci gaskiyar abinda naita nusar dashi akanki.!

Aikaw garin kokawan k wace kwasko ya fad i k asa ji kake tasss ya fashe. Sai ga bak in hayak i na tashi. Dareen ta saki k ara tana soshe soshe yayinda Haidar ya Kama Kansa da yai wani irin sara masa. Ya duk a nan wajen yana rik e Kansa had ida sakin k ara da bai san yana yi ba. Nan ya kwanta wajen tamkar sumamme. Hisham yayo Kansa a guje yana jijjigasa yayinda Dareen

48 / 95