AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   73 / 95

216K to 219K   out of 283.8K words

sirakanmu. Ni fah sabida naga Ummulkhairi na amince na taho.. Amma ina ganin rashin dacewar hakan. Abin zai yawa ai.

Dukda k irjin Mama Tani dake bugawa sai tai k arfin halin cewa  Haba Malam.. Daga sallamanka asibiti sai ka hau hanya.. Ai dai ka jira ka d anji k arfin jikin.

Shiru yai kaman mai nazari sai Ya girgiza kai  A a Tani.. A Ina kika taba jin Uba yaje gidan sirakansa Ya saki jiki.. Wann ai bai tsari ba& Iyakacin karamci da duk wani taimako mutanen nan Sun mana. Kuma na shaida Ummulkhair tayi sa an miji da iyayen miji masu dattaku da sanin darajan d an Adam. Kinga bazan so ni kuma suga namu rashin dattakun ba.

Tani ta d an murmusa  Haba Malam. Kamawa fah take. Ba don jinya da Allah ya jarabceka dashi ba da hakan bazai kasance ba. Fatanmu Allah ya k ara maka lafiya su kuma ya biyasu Ida mafificin alkhairi.

Sai Ya dubeta kaman Wanda Ya tuna wani abu  Na shafe watanni banga Suwaiba ba..

Wai ance kishi dole saida Mama Tani taji zuciyarta ya d an sosu. Sai Tai kokarin kauda tunanin tace  Malam a yau kawai sau uku kai waya da Suwaiba.. Kai hakuri zaka ganta ne da zaran mun koma gida. Kasan Suwaiba da kunya da surkunta bazata iya zuwa nan ta duba ka ba Shiyasa bata zo ba amma ai nakan had aku a waya tin bayan da likitoci suka ce zaka iya amsa wayan talho haka ne.

Abba ya jinjina Kai a hankali sai kuma yace  Ummulkhairi fah.? Kince bata iya fita ko k ofa sabida junan da take d auke dashi. Likita yace mai tattare da had ari ne.  Ya d anyi fasali  Amma ai zan iya ganinta yanzu.. Zan iya zuwa Har yanda take ko Tani. Ya fad i yana k ok arin mik ewa da sandarsa.

Mama Tani ta rasa ta ina zata b ullo masa. Mai zata sanar dashi gameda Ummul da Aurenta.?

Ganin yana k ok arin mik ewa yasa Tani saurin kamo hannunsa  A a Malam ka dakata ka dan huta kaci abinci.. Ai.. Ai nan gidan sirakan Ummulkhairi ne.. Ba.. Ba nan bane Gidanta Shiyasa baka ganta ba. Ta fad i cikin k ok arin had o kalaman tanayi tana kauda fuska gefe.

Abba ya tsareta sosai da ido dan yasan matar tasa sosai. Ya sani idan tana had o zance.

 Tani. Ya kirawo sunanta cikeda kulawa.

Ta d ago ido a sanyaye ta dubesa  Na am Malam.

 Ina Ummulkhairi..? Ya jefo mata tambayar.

Tani ta d an sosa keyarta  Tana gidanta Malam. Dan Allah ka kwantar da hankalinka. Kaji mai likitan nan yace sam shiga tashin hankali ko damuwa ba naka bane& Kaga lokacin sallan la asar ta gabato barin taimaka maka ka d auro alwala. Ta fad i tana mik ewa.

Bayan ta masa rakiya ban d aki ta nuna masa yanda zaiyi nan ta dawo d akin tana waya da abokiyar zamanta Suwaiba. Ko shakka Babu matsalan suke tattaunawa.

Sam Tani bataji fitowar Abba daga Band aki ba sai muryarsa ta saurara yana fad in  Tani& Mai nake ji kina cewa? Za a sami Ummul da izinin Allah..? Tani meke faruwa..? Ina Ummulkhairi& ?


Ya k arashe tambayar jikinsa na rawa daga nan yanda yake tsaye. Har sandarsa rawa take.

Murmushin da yafi kama da yak e Mama Tani tai. Ta k araso tana fad in  Wai Har ka fito bakai kirana ba.

Abba ya girgiza Kai ba alamun wasa  Baki amsa min tambayata ba Tani. Da waye kike magana a waya? Sann meyasa kikace za a samu Ummulkhair.?

 Da Suwaiba nake magana Malam. Kuma tambayata take ko kun gana da Ummul tinda tasan kana matuk ar son ganin Ummulkhairin.. Shine take ce min an sameta a waya nace za a sameta in sha Allah. Ta k arashe cikin k ok arinta na gamsar dashi.

Abba yai shiru kaman mai nazari dan Sam baijin zuciyarsa ta natsu da maganganun Tani d in.

Bayan yayi sallah Tani ta taimaka masa suka fito parlor yaci abinci Ya sha magani.

Nan Mama Tani ta soma waige waigen neman Azeema. Ta mik e tana fad i ma Abba bari ta nemo Azeema cikin gidan. Dan Sam zuciyarta bai kwanta ba da rashin ganin Azeemar tinda tasan sam ita da Anisa d iyar k anwar Hajiya Kwaise had uwarsu baya dad i.

Ficewar Mama Tani da kad an aka soma k wank wasa k ofar.

Abba ya mik e kad an daga kishingid en da yake. Ya bud e idanunsa yana duban k ofan yake fad in  Bismillah.

Wata budurwa ce ta turo k ofan da Sallama saman bakinta.

Abba ya gyara zamansa yayinda murmushin Anisa Ya k aru tana tambayar Abban ko zata iya shigowa.

Abba ya jinjina Kai yana bata izinin shigowa had ida amsa gaisuwarta.

Anisa ta risina yawa mutumiyar arziki tana kuma yima Abba sannu da jiki had ida fatan samun lafiya. Harda addu o i ta jero masa. Abba ya amsa cikeda jin dad I musamman da yaga yanda yarinyar ke girmamasa sai ta tuna masa da Ummul d insa.

Anisa taci gaba da risinawa tana fad in  Abba ni sunana Anisa, kuma k anwa nake ma sirkin ka Aliyu.. Sann munyi zaman dad i da Ummul dan har mun k ulla k awa ce da Ya zarce Ya koma tamkar  yanuwan juna..

Abba yace  Allah sarki.. Toh.. Ma sha Allah.. Ai ga dukkan alamu halayyanku ne yazo d aya da Ummulkhair.. Dole kuyi abota.

Anisa taci gaba da murmusawa tana kuma sadda Kai.

Sai ya dan gyara zamansa kad an yace  Amma.. Nace ina ita Ummulkhairin.. Har yanzu ban ganta ba& Ina so naga d iyata.. Ina so naga yanayin jikin nata.

Anisa ta waro ido tana dubansa. Sai ta d an waiga baya kad an tace  Ban gane baka ganta ba Abba.. Wai har yanzu basu sanar dakai ba.?

Abba ya dubeta da mamaki  Akwai wani abinda Ya kamata na sani ne gameda Ummulkhairina..?

Anisa ta soma girgiza kai  Abba ai Ummul ta jima bata nan.. Idan ban b ata lissafi ba mun d ebe a k alla watanni shida bamusan yanda take ba..


Abba ya girgiza Kai cikin rashin fahimta yana dubanta  Ban fahimceki ba yarinya.. Kina nufin b acewa Ummulkhairi tai baku san yanda take ba.?

Anisa sai ta fara hawaye murya na rawa take fad in  Abba Auren Ummul da D anuwana Aliyu Ya k are& Ta tafi babu Wanda yasan ina ta tafi..


Daidai lokacin Mama Tani da Azeema suka shigo suka tadda Abba na dafe k irjinsa ga Anisa duk e wajen tana kuka.

Mama Tani ta soma salallami ta isa ta tallafi Abba dake k ok arin kaiwa k asa yayinda Azeema ta tafi a guje ta shak o Anisa tana tambayar mai tai ma mahaifinta.

Tani taci gaba da jijjiga Abba tana fad in  Malam meke faruwa..? Lafiya na Barka.. Innalillahi wa inna ilaihi raji un. Malam.!


Ita kuwa Azeema tuni ta shak e Anisa tana fad in sai ta sanar da ita mai tai ma mahaifinta..

Hayaniyar yaja hankulan mutanen gidan. Mommy ta shigo a fujajan tana tambayar meke faruwa.?

Azeema taci gaba da mak ura Anisa tana fad in ko ta fad a mai tai ma mahaifinta ko itama ta shak eta sai ta daina numfashi.

Jikin Anisa yaci gaba da karkarwa. Fad i take  Mommy ki yarda dani wllhi babu abinda nayi.. Gaishesa na shigo yi Ya tambayeni Ummulkhair ni kuma na sanar dashi bata nan.. Mommy bansan Mahaifin Ummulkhairi baisan meke faruwa ba.. Wllhi iyakacin gaskiyata kenan.

Azeema ta kuma yowa kanta tana fad in  K arya kike bak ar munafuka shak esa kikayi..

Mommy ta daka musu tsawa da fad in  Ya isheku dukanku..! Ta dube Azeema tace  Maza kirawo Sadis a koma asibiti.

Sai suka sinkayo muryar Abba yana fad in  A a ba sai an koma asibiti ba.. Magana guda nake son ji! Ya dubi Tani dake hawaye yace  Tani, ina Ummulkhairi..? Shin gaskiya ne Aurenta Ya k are ta tafi babu Wanda yasan ina take.? Shin wann ne dalilin da yasa na kasa ganin Ummulkhair.? Shin wann ne abinda kuketa b oye min keda Suwaiba.? Wann ne dalilin da yasa Suwaiba ta kasa zuwa ta dubani tsawon watannin nan.? Tani mai kuka aiwatar lokacin da nake kwance..? Wane irin Aure Suwaiba da  yanuwana sukaima Ummulkhair da zaisa ta guji gida bayan mutuwansa.?

Sai kukan Tani ya k aru yayinda jikin Mommy yai sanyi. Tai k arfin halin k arasowa. Ta dubi Abba sai ta dubi Tani.. Tace  Abban Ummul.. Dan Allah kar ka yanke hukunci Har sai ka saurareni& Duk abinda ke faruwa ko ince abinda Ya faru.. Babu wani mai laifi face ni.. Duka laifina ne& 

Daidai lokacin Haidar Ya shigo. Kafin Mommy ta k ara furta wani kalma Haidar yai karaf yace  Abba duka laifi na ne.. Ni nayi AUREN WATA UKU da Ummulkhair.! Ni nayi Aure mai k ayadadden wa adi da ita. Auren da zai Wanzu na tsawon Watanni uku. Ni na tilasta mata ta Aureni dan ta Sami damar biyan kud in jinyarka.! Na saka sadakin Ya zama kudin da za a maka aiki dashi muddin ta amince da Aurena.. AUREN WATA UKU.. Dan na cimma burina na mallakan wani aiki k ark ashin kampanin mahaifina.. Muryarsa ya soma shaking  It is all my fault.! Duka laifina ne ni Aliyu.. Umma da Mommy duka basuda laifi.. Laifin nawa ne& Da nai irin wann wulak antaccen Auren da Ummulkhair..

Cikin tsananin shock Abba ke dubansa. Ya soma takowa yana dogara sandarsa Har ya k araso gaban Haidar Wanda tuni ta sadda idanunsa k asa.

Abba yaci gaba da girgiza Kai yana ma Haidar kallon k iyayya  Kai.. Har ka isa.. Har ka isa ka saka rayuwar  Yata a matsayin farashi.?! Hawaye suka soma gangaro ma Abba sanda yaci gaba  Waye kai..? Wa ya baka ikon wulak anta rayuwar  Yata irin haka.! Ka amsa min waye ya baka dama.!

Haidar ya rintse idanunsa rad ad in da yakeji a zuciyarsa na ninkuwa.

Abba yaci gaba da jinjina kai  Shiyasa ka d aukoni ka kawo ni nan.? Dan ka goge zumubinka ne.? Ka amsa min.!

Parlorn yai shiru sai hawayen dake gangaro ma Mama Tani, Mommy harma da Azeema.

Abba yaci gaba da jinjina Kai yana duban Haidar dake tsaye gabansa kansa kife. Yaci gaba da nuna Haidar da hannunsa mai rawa  Ka sani, rayuwar  Yata baida farashi.! Gwamma ace na rasa nawa rayuwan.! Yata tana da daraja.. Tanada k ima.. Kuma ta wuce ayi irin wann wulak antaccen Auren da ita. Zan tabbatar maka da hakan.! Yaci gaba da jinjina kai yana haki da kyar. Lokaci guda ya dubi Tani yace  Ki shige mu tafi bamuda wajen zama a wann gidan.!

Jiki a sanyaye Mama Tani da Azeema suka nufi hanyar d aki yayinda Mommy ke k ok arin shawo kan matsalar amma ko kallo basu ishi Abba ba daga ita Har Haidar d in balle Ya tanka musu.

A haka suka fito zasu wuce Haidar yai saurin kiran Sadis a waya ya sanar dashi Ya d aukesu komin dare ya tabbata sun isa kano cikin k oshin lafiya da izinin Allah.

Bayan tafiyarsu a waje Mommy ta iske Haidar. Ta zauna gefensa su duka biyun ba mai cewa komai.

A hankali Haidar Ya furta  It s so painful and tiring Mommy& 

Ta janyosa jikinta tana Shafa sumarsa kadan  This too shall pass

Haidar yace  Yaushe ne duka wad ann zasu wuce Mommy.? It s one challenge after another.

Mommy ta jinjina kai  Wann sunnar rayuwa ce Haidar. Haka rayuwa ta gada. You cannot expect life to be hundred percent perfect.. Dole yau idan anyi dariya wataran zaayi kuka& Yau gareka gobe ga waninka.. Tsanani yana tareda sauk i.. Duka wad ann zasu zo su wuce.. All you need to do is put your trust in Him.. Ka saka yardarka wajen Allah shi kad ai. Da sannu zai yaye mana duka matsalolinmu Ya cika ahalinmu da alkhairi.



Anisa ta hangesu daga saman bene tana murmushin cin nasaran kauda iyayen Ummul daga cikin picture d in. Tinda taga Mommy bata nuna mata b acin ranta gareta ba ya kuma tabbatar mata Mommy ta aminta da ta d ari bisa d ari. Yanzu ta tabbata zatai maganar Aurensu da Haidar dan dama tayi hakan ne dan ta samu ta kauda su a wuce wajen.

*

Koda su Abba suka isa Kano bai gane gidansu ba. Dan tuni an sauya fasalin gidan an d aga gini na zamani gaba d aya gidan hasken lantarki irin manyan fitilun solar d in nan sun haske gaba d aya layin. Ya dubi Tani da mamaki ganin ta nufi wann gidan da Ya sauya fasalin unguwar gaba d aya yace  Nan kuma ina kika kawo ni.?

Azeema ta d an dubesa tace  Abba gidanmu ne fah.. Baka gane ba.

Rai bace ya dubi Tani yace  Mai nake gani Tani.? Me hakan yake nufi.?

Jiki a sanyaye Tani tace  Malam mu shiga mana tukuna.. Dare yayi sosai..

Abba ya girgiza Kai cikin b acin rai  Bazan shiga ba.. Bazan shiga wann gidan da aka ginasa da kudin da aka sayi Ummu ta ba.. Ki shiga ciki ki kirawo mun Suwaiba da duk wani ahalina dake cikin gidan. Ni Malam Isbusu na gama kwana a wann gidan.!

Tani ta furzar da huci kad an yayinda Sadis Ya k araso yana rok on Abba da yai hak uri Ya shiga gidan. Dan motan Sadis d in ma da fari bai yarda ya shiga ba saida Sadis Ya sanar dashi ba kobon ahalin Haidar jikin motarsa kafin Ya amince Sadis Ya kawosu Kano. Da kyar, har saida Sadis da Azeema suka kirawo ma Abba Dattijan unguwan da yake jin nauyinsa suka saka baki kafin Ya amince Ya shige cikin gidan. Ya kuma sanar da illahirin ahalinsa cewa basu ba Haidar da danginsa. Ko mai kamannin Haidar baiso Ya sake gani yazo yanda yake. Hakan yasa dole Haidar janye jiki da gidan musamman duba da irin yanayin rashin lafiyar da Abban ke fama dashi. Masu lalura irin wann dole lallab asu ake had ida guje ma duk abinda zai b ata ransu.

Haidar ji yake tamkar Ya zama hopeless.. He s tired and exhausted.. Ji yake Duk wani k warin gwiwar sa da k ok arinsa sun gama k arewa musamman yanzu da ya tabbata Abba baya b angarensa. Ya tabbata koda Khairy ta bayyana zai matuk ar wahala abubuwa su zo masa da sauk i.

Furzar da huci ya kumayi a karo na Babu adadi yana duban hotonsu da aka musu ranar aure dake aje gefen bedside lamp d insa an saka cikin k aramin frame.

Ya d auki hoton had ida k ura ma hoton ido. Cikin wane irin siga yake furta  where are you Khairy..? Do you hate me this much.? Haven t I suffered enough. Ya girgiza Kai kad an  Ya isa haka Khairy. I m exhausted..! Please, enough with the punishment. I can t bear the pain anymore. I can t Khairy..! Ya k arashe yana shafa fuskarta saman hoton. Ya d an d auki lokaci yana duban hoton kafin Ya mik e kaman Wanda aka zaburesa. Shiryawa yai Ya fito Ya nufi sashen mahaifinsa.

Mommy da Daddy duk suna zaune parlor. Daddy na kallon news channel yayinda Mommy ke k ok arin mik ewa tana fad in zata shiga ta kwanta nan sukaji sallaman Haidar. Suka dubi juna da mamaki kafin Daddy ya bud e murya yace  Haidar.? Is everything all right.?

Haidar yace  Lafiya Daddy.. I m sorry na shigo dare yayi.

Daddy ya girgiza Kai  No.. No problem.. K araso shigo mana.

Haidar yaci gaba da takowa Mommy na hankalce dashi.

Ya zauna daga kusan k afan Daddy. Ya gaida iyayen nasa. Bayan sun amsa Mommy ta k arada  Inji dai lafiya.?

Ya d an murmusa kad an  Lafiya Mommy.. Dama wata  yar magana na shigo muyi.

Mommy ta tsaresa da ido  Kuma maganar baza a iya yinsa da safe ba sai cikin daren nan.?

Daddy yace  Haba Kwaise ki kyalesa muji binda yake tafe dashi mana. Ya dubi Haidar  Ina saurarenka meke faruwa.?

 Daddy dama akan Kasuwancinmu dake can SouthAfrica ne.. Ina so wann karan na tafi SouthAfrica a maimakon Kai and take care of our Business there.. If that s ok with you.

Daddy yana dubansa yake jinjina Kai  Of course that s totally fine with me. In fact abu ne da nake matuk ar so kuma yake cikin tsarina.. But duba da yanayin da kake ciki yasa ban kawo maka wann bukatar nawa ba& 

Da farko Mommy ta nuna k in amincewarta a cewarta bata so D anta yai nesa da ita musamman yanzu da rayuwa ta koma masu tamkar sabuwa. Da kyar Daddy da Haidar sukai convincing dinta da fad in ba zuwa can zai Ya zauna gaba d aya ba. Kaman yanda Daddy yake tafiya lokaci zuwa lokaci haka shima zai yi.. Kuma hakan zai d an basa dama yai taking break regarding abubuwan dake faruwa.

Da kyar Mommy ta amince ita kuwa Anisa hankalinta ne Ya tashi ganin mutumin da tayi komai dominsa zai kufce mata Ya tafi wata uwa duniyar. Saida Mommy ta lallabeta da fad in ba jimawa Haidar zai a SouthAfrica ba sann da zaran Ya dawo maganar bikinsu za ayi. Kar ku mance Har kawo wann lokacin Anisa da Mommy ne kawai ke zancensu ko Haidar d in baisan da labarin ba balle akaiga sako iyaye maza cikin maganar.

73 / 95