AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   38 / 95

111K to 114K   out of 283.8K words

akai har ya fara sonta ya aureta ba. So baisan wani shawari zai ba ma abokin nasa ba. Ya d an numfasa kafin yace  Just.. Just try to distract yourself.. Engage in activities that require your full attention& Like work.. Zaka gani in no time zaka mance da ita. And you ll find someone better than her.

Hisham ya d an furzar da huci  What if my mind gets stuck here Haidar.? What if I couldn t move on.? What if banida wani future dangane da abinda ya shafi Aure.? What if this is my destiny.?

Haidar yai shiru cikin sanyin jiki ba tareda ya iya cewa komai ba.

Hisham yai murmushi mai ciwo  Sorry I shouldn t be telling you all this. Kayi tafiya ne dan ka rage damuwar dake kanka bai kamata na k ara maka da nawa ba. Anyways, I guess this is life for us. Ba ko yaushe muke samun abunda muke so ba. Ya d an murmusa kafin yace  Let s talk business maybe this will keep me busy. Yai maganar da gajeren murmushi kafin yaci gaba  Ya kamata ka dawo haka work is getting hampered because you are not here. Komai so yake ya tsaya. And kasan lokaci baya jiranmu.


Ya d anyi gajeren tsaki  I m still on my vocation. Zanje Pennsylvania daga nan.

Daga d aya b angaren Hisham Ya girgiza kai  Wai kana nufin hutun naka bai k are ba.. Ko wani business d in kakeda a can US d in.?

Gajeren tsaki ya kuma yi  Ka kira ne dan ka bani haushi.? What business kuma.?

Hisham Ya murmusa kad an  Alright fine. Yanzu dai Ya kamata ka dawo. Kaga we need to meet up. Ina nufin our team members. We ve got a lot of things to discuss.

Tsakin ya kuma yi dan ya kula da gangan Hisham ke son tunzirashi  Maiyasa zan dawo. Mai zan dawo na maka when you can schedule a zoom meeting. I just hope ba shirme da shiririta bane cikin meeting d in ba. Because you know my time is precious.

Hisham ya murmusa kad an  Look Haidar, you and I both know dawowarka nada mahimmanci. Magana muke kan project d in da bamu tab a handling babba kaman shi ba. Kuma a matsayinka na Wanda ragamar kula da aikin ke k ark ashin ka ya kamata ace by now ka ziyarci site not just once or twice. Cikin k ank anin lokaci zamu fara. Sann any moment any time Dad dinka zai iya dawowa k asar nan. Mai kake tunani idan ya dawo Ya tadda baka nan.? The story will definitely change. And all our hard workings will go to waste.. Haidar you need to forget about your tour to America and come back as soon as possible.

 I don t take orders from you Hisham. Let Aliyu Maitama do his worse. I do not give a damn.! Yana ida fad in haka ya katse kiran kafin yasa kai ya fice cikin huci saikace Hisham d in na ganinsa. Zuciyarsa na masa zafi dik sanda aka ambata masa mahaifinsa. Sunan da dik sanda aka ambata sai yaji k una cikin zuciyarsa at the same time babu yanda ya iya wann sunan dai yake amsawa. Babban kuskuren da mahaifiyarsa Tai shine saka masa sunan wann mutumi da Tai Wanda duk duniya babu Wanda Ya tsana sama dashi.

Dareen ta fito daga mab oyarta tana bin bayansa da kallo Har ya b ace ma ganinta. Zama tai tana k ok arin figuring out maganganun da taji ya tattauna cikin waya.

A b anegarn Haidar kuwa can bakin beach yaje ya zauna tunanin duniya na damunsa. K iyayyan mahaifinsa ne zalla cikin zuciyarsa. Lokaci guda maganganun Hisham na yawo a kwanyarsa. If he wants to take his Dad down dole yaje yayi aikin koda baya son komawa. Rashin komawarsa na nufin zai iya rasa chance d insa na k arshe akan mahaifinsa. Dan kaman yanda Hisham yace ne idan har Dad d insa ya rigashi komawa Nigeria toh fah zaiyi replacing d insa da wani ne. He promised to make his Dad swallow all his words sann baya jin zai janye wann k udirin nasa.

Gajeren tsaki yai yana tunanin abun yi. Mommy ce ta fad o ransa. Yai scrolling kan sunanta. Kaman mai tunanin wani abu ya jima sosai kan lambarta had ida k ura ma sunanta ido. Saida ya furzar da huci kad an dan baida wani option kafin yai dialing layin.

Sunanta Ya fara ambata tana d aga wayan in the way he does sanda yake k arami. Sai Mommy taji hawaye ya ciko idonta. Idan Ya kirata da wann sigan lokacin k uruciyarsa ta kullesa ne a d aki taurin zuciyarsa bazai bari Ya rok eta ta bud e sa ba sai ya ambaci sunanta da wann sigan. Tai k ok ari Tai ta maza ta share hawayen da suka gangaro mata  Haidar ina ka shiga tsawon sati biyu.? Mai kake nufi Dani Haidar..? Mai kake nufi da Amaryarka dake zaman jiranka tsawon sati biyu. Shin ka cika alk awarin da ka d aukar min.?

Da ta ambaci amaryarsa sai yaji abun Ya masa wani banbarak wai. Girgiza kai yai kad an  Alk awari d aya na d aukar miki Mommy shine bazan saketa ba sai ta cika wata uku kaman yanda yake a Yarjejeniyar. Amma ban miki alk awarin zama da ita cikin watanni ukun ba.

Mommy ta zaro ido waje kaman yana ganinta. Idan baizo ba ai Babu amfanin auren. Ya zama wofi kenan.

Katse shirun Tai da fad in  A a Haidar kar mu fara wann wasan dakai. I mean what about the project.? Muddin mahaifinka ya rigaka saka k afa cikin gidan nan kasan sauran Haidar. All our efforts and sacrifices zasu tafi ne a banza . Haidar ka tuna na k ulla auren nan ne dan mahaifinka ya amince ya baka project din nan.

Katseta yai da fad in  To hell with everything Mommy.

Mommy ta mik e tsaye tana jin zufa na keto mata. Sai muryarta Ya soma rawa  A a Haidar.. Haidar kar kace haka.

 You know what Mommy, you are too demanding. Yes na yarda zan auri yarinyar chan or whatsoever da kika kawo kika ce na aura because I wanted to manage the project. But zama tareda ita under same roof ban miki wann alk awarin ba. It s suffocating already da na amince da auren.

Mommy taci gaba da girgiza kai jin duk sadaukarwan da tai da duk wasu k ok arin ta zasu tashi a banza. Sai ta soma hawaye  Yanzu da gaske ka hakura da aikin Aliyu.? Mai zai faru Dani Haidar.? Mai zai faru da nawa auren.? Yanzu bazaka amince da AUREN WATA UKU dan ceto auren naka mahaifiyar ba.

Cikeda k osawa yake tattare naman goshinsa  Quit the act Mommy. Your victim card won t work on me. You brought this to yourself. You should blame yourself.

Cikin kuka Mommy ke fad in  Haidar cikin satin nan Mahaifinka zai dawo k asar nan. Na tabbata idan Har ya rigaka dawowa zaka dawo ka tadda bana nan. Idan har ni na haifeka zaka dawo Aliyu.. Zaka dawo ka ceci Aurena kafin mahaifinka ya sauk a k asar nan.. Tana ida fad in haka ta katse kiran ba tareda ta jira cewarsa ba.

Ya lumshe idonsa kad an yana tuna mafarkin da yai tareda iyayen nasa a kwanakin baya.. Yai gajeren tsaki wani b angare na zuciyarsa na fad a masa mafarki is the opposite of reality. Ya kuma yin gajeren tsaki zuciyarsa na kuma tunzura shi gameda al amarin iyayen nasa. Meyasa yakeji gaba d aya shidai baida wani alk ibla a rayuwarsa. Like his life s a complete messed up. Baisan mai yake son yai ba. Baisan mai yake ji ba. A haka ya mik e yana tafiya baisan wani direction zaibi ba.

**

Abuja..


Mommy yau din mafarki tai Haidar ya dawo suna zaune parlor Kansa kwance saman cinyarta suna hira na d a da uwa da basu tab a irinsa ba. Tinda tai wann mafarki ta tashi da farin ciki ga dukkan alamu shirinta mai tasiri ne Akan Haidar din. A b angare guda ga Daddy ya mata waya ya sanar da ita nan da kwanaki biyu zuwa uku zai dawo da izinin Allah. Gaba d aya sai tana ji kaman lokacin dunk ulewar ahalinta ne yazo. Burinta yana gab da cika. Tuni tasa akai mata kiran Ummul ta sanar da ita Mijinta na nan tafe. Yacce kasan wacce takeda tabbacin dawowar Haidar d in ta dauko mai gyara na musamman irin nasu na shuwa aka soma yi ma Ummul sabon gyara. Wani sabon kula na musamman Mommy ke bawa Ummul.

Hankalin Anisa idan yayi dubu ya tashi. Babu shiri ta fita ta nufi gidansu Leenah dan bazata iya kallon wann kayan tashin hankali ba. Bazata bari Haidar ya dawo gidan ya cimma Ummul ba.


Leenah ta dubeta a dak ile  So da kika taso kika zo nan mai kike so na miki.?

Anisa tace  Leenah let s forget about everything. Nasan ban kyauta ba amma dole ce ta saka ni d aura miki laifin. Da ace na d auki laifin da yanzu bana gidan. Leenah I have no one to turn to but you. You just can t abandon me you know. Ta k arashe tana duban kawar tata kaman zatai kuka.

Shiru Leenah tai na d an lokaci kafin tace  Neesa I m not doing this. I won t allow myself to fall into your trap again. I m not that stupid.

Anisa ta kamo hannayen Leenah  Girlfriend please mana. Zamu bari wann low class d in ta shiga tsakanin abotanmu ne.? Tayi mana guda biyu bazamu bari tayi na uku ba. Think, yanzu idan muka kyaleta ji zatai tayi nasara akanmu. And remember, we never back off for a fight.

Shiru Leenah tai kafin tace  This is your battle Anisa. You should fight it alone.. Kin gane.

Sai kuma ta faurzar da huci kad an ganin Anisa ta tsareta da ido  Fine, naji.. What do I get in return dan wann karon shiri babba zamuyi wanda bazata iya tsallakewa ba.

Anisa ta jinjina Kai tana murmushi  Idan har kika taimaka min na zama matar Haidar komai mai sauk i ne Leenah. I promise not to let you end your life Washing clothes with bleach just to keep them white.

Leenah ta jinjina Kai tana murmushi  Lokaci yayi da zakiyi abinda kike tsoro Anisa.

Anisa ta dubeta cikin rashin fahimta  Kaman yaya..?

Leenah tace  Your ultimate goal is to get rid of her for good. Right.?

Anisa ta jinjina Kai  K warai kuwa.

Leenah ma ta jinjina Kai  Good..! Then make her disappear for good..

Anisa ta kuma girgiza Kai  But how.?

 Kill her Neesa.! Poison her once and for all.

Anisa ta zaro ido waje  A a Leenah.. What what if our plan fails again..? Kaman dai sauran..?

Leena ta dubeta  Anya da gaske kin shirya Anisa..?

Anisa ta dubeta a d an tsorace  Mai a zai faru idan bataci poison din ba.?

Leenah ta murmusa  Ba ko wani poison bane ake ci Anisa. Wani shak ansa ake a iska. A hankali yake lalata lungs kafin a ank ara sai gawan mutum. Kinga irin wann babu wanda zai zargeki. Ta k arashe da murmushi saman fuskarta.

Anisa ta murmusa  Yayi. Yanzu ya za ayi mu samu.?

Leenah ta murmusa  Wann mai sauk i ne ki bar min komai a hannuna. Nasan kudi bazai zame miki matsala ba.

Anisa taita murna tana mata godiya. Akan haka suka rabu washe gari suka had u a mahad a.

Leenah ta ciro wani mistitsin kwalba cikin jakanta ta mik a ma Anisa. Anisa hannu na rawa ta amsa dan kwalban da wani ruwa mai kaman acid ciki.

Anisa na juya kwalban Leenah ke mata bayanin yanda zatai amfani dashi.

 Cikin turaren da take yawan amfani dashi zaki zuba kad an. Muddin tana shak an wann turaren bazata wuce kwanaki uku tana numfashi ba.

Murmushi Anisa tai. Cikin zuciyarta take fad in Yazo gidan sauk i dan ta kula Ummul tana yawan shafa turaren humra da ta kai mata a kwanakin baya Wanda ta sauya turaren da Mommy ta bata dashi. Tabbas zata zuba mata a ciki.

Leenah ta dubi Anisa had ida gyara zamanta  A baya nayi zaton Hajiya Kwaise bazata tab a bari D anta ya auro d iyar talakawa ba. Nafi tunanin iyayen Haidar zasu nema masa aure ne daga babban ahali. A well known and influential family. Like business partners d insu ko d iyar manyan  yan siyasa kodai d iyar masu mulki. Amma na sha mamaki yanda ta auro ma d anta wann yarinyar.

Anisa ta jinjina Kai  Ba ke kad ai kike mamaki ba Leenah. Shiyasa zuciyata ke tabbatar min akwai wani Abu a k asa k ark ashin wann auren. Massive love d in da Mommy ke nuna ma yarinyar yafi komai d aure min kai. Ko ni nan da nake tamkar  yarta sann mahaifina is a successful businessman banyi zaton zata bari d anta ya kawo mata ni matsayin sirka ba sanin ko wacece ita. Nafi zaton zata tafi da nisa sai gashi ta k are a  yar talaka. Ke da ganin wann al amari kinsan akwai lauje cikin nad i. And believe me I vow to find out whatsoever she s hiding.

Leenah ta jinjina Kai  Ta haka ne kawai zaki fahimci komai Neesa. Idan kika kashe yarinyar.

Anisa ta jinjina Kai tana tabbatar da kalaman Leenar.

Daga bisani godiya tai ma k awarta Leenah sukai sallama Leenah na fad in sai taji result.

Koda Anisa ta koma gida cikin hikima da dabara ta zuba wann ruwan lungs poison da Leenah ta bata cikin turaren Ummul.

Ta dawo d aki tai relaxing tana sakin murmushin nishad i. Nan da kwanaki biyu zuwa uku mataalarta zai kaw. Saidai a fidda gawan Ummul daga gidan. Dan ta tabbata wann karon Ummul bazata haye tuggunta ba.

A fili take furta  Mommy ki gama duk wani shirin da zaki mata. Haidar gawar Amaryarsa zai dawo ya tadda. Tana Ida fad in haka ta fashe da dariya.



SameenaAleeyou=???*AUREN WATA UKU..!*




*30*







*??Sameena Aleeyou&
'

Tinda jirginsu tai landing a Nigeria Dareen ta rasa sukuni. Ta kula akwai mihimmin abinda yasa suka yanke hutun nasu suka dawo gida Nigeria. Toh amma rashin sanin mak asudin dawowar tasu shi yafi komai d aure mata kai. Da fari tayi zaton project d insa yasa ya dawo amma daga bisani ta kula kaman dai abun nada alak a da ahalinsa ne musamman ma mahaifiyarsa. Meyasa duk irin aikin da suka tabbata anyi kan Haidar d in da iyayensa kaman bai wani tasiri tsakaninsa da mahaifiyarsa ba. Kaman dai Har yanzu shid in koda bai nuna ba can k asar zuciyarsa yana kwad ayin Ya mata biyayya. Dan taga call history nasu a wayarsa shida mahaifiyarsa. Kuma tinda sukai wann wayar ya yanke decision d in dawowa gida. Tabbas ya zama dole ta koma wajen Dodon kobuku ta sanar dashi halinda ake ciki. Tana so aimata aiki na musamman akan mahaifiyar Haidar wacce take ji a jikinta ita d in nema take ta zame mata barazana. Sann wann zuwan da zatai bazata bari Shadow ya sani ba. Aiki ne da za a mata ita kad ai. Ya kamata ta saka rana ta tafi gida Ilorin dan ta gana da Dodo Kobuku. Ta k arashe tunanin tana kallon fuskar Haidar dake kwance yana baccin gajiyan hanya. Fuskar tasa tayi fayau tamkar Wanda baida wata damuwa. Ta murmusa zallan k aunarsa takeji na bin duk wani vein na jikinta. Ta Shafa fuskarsa a hankali. Can k asar zuciyarta take furta  You are mine Haidar Maitama. Ni kad ai na. I won t allow anybody to come between us. Not Shadow, not even your own parents. Idan shiga tsakaninku is not enough zan b ullo maku ta wani hanyar. Idan ta kama na kashe rai ne akan ka zan kashe. Koda mahaifiyarka ce dan na kasance dakai zanyi Haidar. Kaid in nawa ne. Ni kad ai.! Ta k arashe tana tsura masa ido.

**

Tin farar safiya take gidansu Leenah, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Zuciyarta ya cika da tsoron abinda ka iya zuwa ya zo. Yau kwanaki uku kenan da ta zuba poison din cikin turaren Ummul. Ta tabbata izuwa wann lokaci komai zai iya faruwa dan gaba d ayan ranan ma bataji d urin Ummul d in ba. Ta dubi Leenah dake zaune hankalinta kwance tana kallon American movie ta k araso ta zauna kusan Leenah zuciyarta sai tsinkewa yake  Hey.! What if she s dead by now.? Ko kuma ta shirya min wani makircin tinda kinsan makira ce ta gaske..! Anisa tace duk a tsorace.

Murmushi Leenah tai tana jefa popcorn a bakinta  You know what Neesa, you should stop being paranoid idan ba haka ba a banza zaki sa ko wani Abu ya sameta a zargeki. And if that happens believe me I won t come to your aid. So ki kwantar da hankalinki ki tashi ki koma gidan ki tabbatar da abinda ya sameta. Ta k arashe tana duban Anisa.

Jikin Anisa har lokacin a mace yake sanin ko wacece Ummul d in tinda ta tsallake tuggunsu har guda biyu. Idan ta tsallake wann din ma ba abin mamaki bane. Babban abinda yafi bata tsoro shine wann ya k unshi kisan kai ba kaman sauran ba. Bata kuma cewa komai ba sai zama da tai can gefe tana ci gaba da tunanin abin yi. Dan tsoronta d aya ji take kaman idan ta koma gida Ummul zata kamata, reshe zai

38 / 95