AUREN WATA UKU.

Author :  Sameena Aleeyou… Category :  Love

Chapter   63 / 95

186K to 189K   out of 283.8K words

 I can t destroy you.!

Daddy ya koma ya zauna yana duban Haidar d in sosai cikin tsanani shock.

 My plan was& To use this so called project and destroy you.. I wanted to show you the kind of monster you created in me.. But then I couldn t.. I couldn t destroy the hands that raised me koda ace mun kasance munada alak a mai rauni cikeda tarin k alubale. Yaci gaba da girgiza kai. Sai murmusa kad an wann karon  I just want to be free from this prison. I.. I don t want to keep on living my life tied to all this rage and hatred.. I want live a normal life.. To start a family of my own.. Muryarsa yaci gaba da rawa  I.. I m sorry Daddy.. I m sorry idan ban kasance wann d an dake fata da burin samu ba.. I m sorry idan ban kasance wann D an da zakayi alfahari dashi ba.. Believe me.. I truly.. am sorry..

Baikai aya ba Daddy dake ta k ok arin danne hawayensa sai ya zame farin gilashinsa ya kauda fuskarsa kadan yana goge hawayen da suka mak ale masa a ido.

Kaman daga sama Haidar ya sinkayo muryar mahaifinsa  Aliyu, my son..

Da mamaki Haidar ke duban Mahaifinsa Jin ya ambacesa da D ansa abinda bai taba ji daga mahaifin nasa ba.

 Shin ka tambayi kanka koda ka farka daga coma meyasa baka ganni wajenka ba.?

Shiru Haidar baice komai ba.

Daddy yaci gaba da jinjina Kai har lokacin bai kalli b angaren da Haidar d in yake ba  Sabida bazan iya kallonka a ido ba.. Bazan iya ambatan kaina da mahaifinka because I.. I haven t been a good father to you.. And I treated you badly.. Daddy ya kifa Kansa hawaye na gangaro masa  Fad an da kaji ina maka a yanzu borin kunya ce kawai sabida ni d in ban sauk e wani nauyi da hakki na mahaifinka dake rataye wuyana ba. Hadisi ne guda cewa ko wannen mu mai kiwo ne kuma za a tambayemu gameda wann amana na kiwo da aka dank a mana. Bazan iya duban idanunka na nemi gafararka ba Haidar& Bazan iya ba..! Saiga alamun kuka cikin muryar Daddy.

Haidar ya mik e jikinsa a matuk ar sanyaye ya tako har zuwa gaban kujeran da Daddy ke zaune bisa. Duk awa yai gaban Daddy Wanda har lokacin Kansa na kife yana d igar da hawaye.

Haidar ya daura hannayensa biyu saman hannayen Daddy dake bisa laps d in Daddyn. Shiru ne ya ziyarci wajen baka iya jin alamun komai face motsin zuciya.

Daddy ya rik e hannayen Haidar tsam cikin nasa  I m sorry son.. I m sorry.. Please forgive your Dad& 

Hawaye suka gangaro ma Haidar dake duk e gaban Daddy hannayensu cikin na juna.


Mommy da ta nufo k ofan dan ta sanar da mijin nata gayyatar D ansu da matarsa dinner matsayin maraba da dawowa gida ma Haidar d in koda bazai nuna kulawarsa kaman yanda ta tsammata ba, nan ta riski wann babban al ajabi. Rana mai d inbin tarihi.. K afafun Mommy suka kusan gaza d aukarta.. Hawaye suka shiga zarya a k uncinta.. Sai Mommy ta fad i k asa tana mai sujada na godiya ga Ubangijinta. Tama rasa mafarki ne take kokuwa dai a farke take. Haidar dinta da mahaifinsa take gani cikin yanayi da bata tab a tsammanin zata gansu ciki ba. Allah buwayi gagara misali. Mommy ta kuma yarda cewa lallai duk Wanda ya dogara ga Allah toh fah Allah ya isar masa. Itakam babu abinda zata ce saidai taci gaba da gode ma mahaliccinta Wanda ya yaye duhun dake cikin gidanta da ahalinta ya yalwatasu da haskensa. Ta saki turban boka da suka d auko daga fari ta rik e turba na gaskiya sai gashi komai yana gudana cikin sauk i. Lallai wann wani rahama ne daga Ubangijinta. Lallai wann izna ce ga tababbu masu bin hanyar b ata. Wanda ya gane Allah shi yake yi ba boka ko Malam ba shi keda babban rabo duniya da lahira. Bata san sanda ta koma da baya ba ta nufi d akinta ta maida k ofa ta rufe ta fad a saman gado tana kuka sosai. Kukan farin ciki wann karon. Kukan da ya goge Wanda ta jima tanayi a baya Kama daga zuciya har k wayan ido. Alkhairin Allah yaci gaba da haska gidanta da ahalinta.

Haidar yaci gaba da girgiza Kai yana rik eda hannayen Daddy gam cikin nasa  Daddy ka daina bani hak uri. We are all human beings.. We make mistakes. What s important is that we learn from those mistakes. Yaci gaba da jinjina kai a hankali  Ni yafi cancanta na nemi yafiya a gareka Daddy. Idan inada hakki akanka hakkinka dake kaina yafi girma. Duk yanda naje nazo banida madadinka.. I should ve been more understanding with you. Cikin zuciyarsa yake tuno sanda Ummul take fad a masa  A rayuwa wasu lokutan Allah yakan saka mana jarabawarmu ya zamto people that are tied to us by blood. Sai Haidar ya mik a hannu ya d auko folder d in project da ya shigo dashi. Ya daura saman hannun Daddy suna kallon cikin fuskan juna. Murmushi gauraye da siraran hawaye saman fuskar Haidar yake fad in  Daddy I can walkway from this Business because it s my choice.. But I can t walkway from you. Do you know why.?

Sosai Daddy yake kallonsa yana hawaye. Haidar yaci gaba da jinjina Kai  Because you are my Father.. Allah chose you for me& We are tied to each other by blood because haka Yake so ya kasance. Yaci gaba da jinjina Kai yana murmushi  Daddy jininka shi yake circulating cikin jikina daga farko.. A karo na biyu Kai ka bani jininka, you couldn t walkaway from me either. Sabida ni d in D anka ne.

Daddy sai ya janyo kan Haidar ya rungume cikin jikinsa. Muryarsa na rawa yake fad in  Allah ya maka albarka Aliyu.

**

A lambum dake bayan sashen Mommy aka shirya cin abincin daren. Hasken wutan lantarki ya karad e ko ina tamkar ba dare ba.

An shirya teburin gwanin ban sha awa ga barbecue stand daga gefe.

Suna cikin shirya plates saman teburin itada Anisa Anisa tai excusing kanta sakamakon kira da ya shigo wayarta. Nan Ummul ta hangosa na tahowa. Sassanyar murmushi saman fuskarsa. Ta shagala sosai da kallonsa kaman yanda shima ya shagala da kallonta dan sosai tai masa kyau.

Yana k arasowa sai ya tsaya daga bayanta ya dan rungumota had ida rank wafo da kansa kusan kunnenta  You look.. Gorgeous.! Ya fad i cikin sigan rad a.

Ummul ta soma k ok arin turesa daga jikinta tana  yan waige waige  Mai kake aikatawa ne wai.. Idan wani ya ganmu fah.?

Bai saketa ba ya kuma rad a mata  So what.! Can t I hug my wife.?

Ta waiga ta dubi Anisa dake can gefe tana amsa waya. Ta kuma duban ma aikatan kitchen guda biyu dake gefe gaban BBQ stand.

Kaman zatai kuka tace  Dan Allah ka bari akwai mutane wajen nan fah nan..

Juyawa yai ya dubi kitchen staff d in. Sai ya dan murmusa  Is that problem.? fine. Zo muje. Bai jira amsarta ba ya shiga janyo hannunta. Suka nufi yanda ma aikatan ke gashin naman.

Haidar yace musu suna iya tafiya zasu kula da barbecue d in.

Ma aikatan suka amsa masa cikeda risinawa suna duban yanda Haidar ya janyo Ummul dake fad in ita fah bata iya amfani da irin wann abin gashin ba. Yace kar ta damu tare zasuyi.

Sosai suka birgesu kaman kar su daina kallonsu. Abu ne da zasu iya cewa basu tab a ganin ya faru gidan ba. Basu tab a ganin Haidar cikin farin ciki irin wann ba. Su dai kam Sun shaida zuwan Ummulkhair gidan Alkhairi ne.

Anisa ta juyo baki sake tana duban ikon Allah Haidar da Ummul gaban barbecue stand sai zuba soyayya suke. Gwiwoyinta taji sun sake kamar wata maras laka. A haka Mommy ma ta k araso wajen ta taddasu. Farin ciki maras misaltuwa ya kuma gauraye zuciyarta. Zuwan Mommy wajen yasa Ummul janye jiki ta kyale Haidar shi kad ai.

Haidar na fad in ta mik a masa bbq cutting board sai sann ya kula ta silale ta bar shi shi kad ai.. Ba kowa wajen ma sai shi kad ai. K ila Sun shige yin wani abin cikin gidan. Ya dan tab e bakinsa kad an.
Amma sai yaga wani hannu na mik o masa abinda yake nema. Haidar yabi hannun da kallo. Ga mamakinsa Daddy ya gani. Kyakkyawan murmushi saman fuskar mahaifin nasa. Haidar yasa hannu ya amshi board d in had ida godiya ma Daddy. Jinjina Kai Daddy yai. Sai Haidar yaga Daddy na nad e hannun long sleeve shirt din dake jikinsa alamun zai tayasa.

Sai Haidar ya girgiza Kai  No Daddy you don t have to.. Ya kamata kaje ka zauna.. I.. I ll serve you some. Ya fad i awkwardly dan abu ne da bai saba faruwa ba koma bai tab a faruwa ba tsakaninsu.

Murmushi ne saman fuskar Daddy ya dafa kafad an Haidar din  No Son, let s do it.. Together.

Haidar yai murmushi yana tuna lokacin yarantarsa wann shine mafarkinsa. To make memories with both his parents& To strengthen their bond. Ya samu kusanci sosai da mahaifinsa. To have some quality time together.. To build something together. To play sports, video games, go horse riding da dai sauransu. Sai ya murmusa yana duban mahaifin nasa sosai. Kaman mafarkinsa ne yake zama gaskiya. Yana k ok arin yanka naman saman board din Daddy ya dafa hannunsa wana hakan Ya dakatar da Haidar. Suka dubi juna sai Daddy yace  Be careful Engr, this is not a construction side.

Su duka sai suka d an dara kad an. Daddy yace  You know Son, if I were to turn back time.. Da munyi aiki tare hand in hand.. Like professional Engrs.

Jikin Haidar Ya d anyi sanyi Ya fahimci abinda sukeyi a yanzu d in Ya K wadaitar ma mahaifinsa inama lokacin da sukeda damar kasancewa tare a company sunyi ayyuka tare tare babu tsangwama babu hantara. Gashi yanzu Ya sanar da mahaifinsa Ya aje aikin company meaning ba lallai su sami irin wann damar ba. Muryar Daddy ya kuma sinkaya  Bana so na tak uraka. Da na rok eka wani alfarma.

Haidar yai saurin girgiza kai  No Daddy.. Ka wuce wann.

Daddy ya murmusa  Haidar, I can understand you, if you& don t want to manage the project due to.. your personal priorities.. But please kar ka aje aikinka.. Kar ka bar Kampanin& Let this be the last abu da zan buk ata ka mun.

Haidar yai saurin girgiza kai  No Daddy, I m your son.. Hakkina ne matsayinka na mahaifina nayi maka biyayya cikin abinda bai sab a ma mahaliccina ba. Kuma wann bazai zama abu na k arshe da zan maka ba. Umarni kawai zaka bani a koda yaushe.. Kuma na maka alk awari bazan aje aikina ba in sha Allah. Bazan bar company ba. Together we will take the company to greater heights.! Ya k arashe da murmushi saman fuskarsa.

Sai Daddy ya kamo k afafunsa Ya rungume  Thank you son. Allah ya maka albarka.

A haka Mommy ta k araso wajen ta iskesu. Farin cikinta ya ninku. Itakam a halin yanzu tana jin babu sauran abinda zata nema da ya shige taita gode ma Ubangijinta da ya cika rahamarsa ga ahalinta.

Bayan cin abincin suna zaune itada Haidar a parlor. Haidar ya kuma murmusawa ya dubeta  You know Mommy, After all these years it's today that I feel like& I'm part of the family.

Mommy ta rik e hannayensa cikin nata. Kyakkyawan murmushi saman fuskarta  We gonna have some family bondings to makeup for all the time we've lost& Kuma.. Zamu fara da shagalin bikinka. Aurenka da Ummul ta cancanci biki na gaske irin na  yan gata.

Ya dan girgiza Kai yana murmushi  Mommy na kasa yarda bisa yarjejeniyar Wata uku na amince da auren Khairy.. Dan kawai Daddy ya bani wann project d in.

 Shiii. Mommy ta dakatar dashi  Babu wann maganar Haidar.. An rufe shi har abada. D ago baya irin haka baida wani amfani. Bazaka sanar da Ummul wani abu mai suna auren yarjejeniya ko AUREN WATA UKU ba.

Sai ya d an dubeta can k asar zuciyarsa yana jin zuciyarsa ta katsa samun natsuwa har sai ya sanar da ita.. Sabida a halin yanzu Aure yake so ya gina da ita bisa zallan gaskiya.

Ya d an dubi Mommy  Mommy I want to build my marriage with her base on trust and transparency. Bana so daga baya tazo ta fahimci cewa na aureta ne bisa yajejeniya zuwa wani k ayyadajjen lokaci. I want her to hear it from me first kafin taji daga wani waje.

Mommy ta jinjina Kai  Na fahimceka Haidar.. Amma kafin nan ka d an dakata har a gama wann bikin tariyarku can gidanku da na saka nan da kwanaki biyu kacal. Idan yaso sai ka sanar da Ummul yanda al amarin ya kasance..

Sai ya d anyi jim kafin kuma ya jinjina Kai a hankali  Shikenan Mommy. Idan hakan kike so.

Ta murmusa cikeda jin dad i. Burin ko wasu iyaye shine su samu  ya ya masu biyayya a garesu. Lallai mai rai kar ya cire tsammani daga rahamar Ubangijinsa. Who would ve thought za a zo lokacin da Haidar zai d auki umarnin mahaifyarsa ba tareda jayayya ko nuna k in amincewa ba.? Ya ke  Yaruwa da Allah ya Miki jarabawa da D an da kika haifa, kar ki tab a yanke k auna daga rahamar Ubangijinki domin kuwa shid in rahamarsa mai yalwa ne. Kar ki karaya, kici gaba da mik a lamuranki ga Ubangiji. Duk Wanda Allah ya zama majib icin al amarinsa shi keda babban rabo.

Haidar ya mik e da zummar mata sallama ta dakatar dashi.

 Yauwa nace ba sai abu na gaba..

Haidar ya jinjina kai yana sauraron Mommy.

 Kanaji.. Ummul zata dawo nan sashena da zama har sai anyi bikin an kai maka ita.

Wann karon zaro ido yai kaman wani abin tausayi ya langab e kai  Haba mana Mommy does it have to be this way.. I just came out of hospital fah..I m still a patient.

 Mommy ko kin daina tausayina ne. Ya kuma fad i a marairaice.

Dariya yaso bata amma ta gimtse tace  Ba tausayinka na daina ba. So nake kai d aukin d iyata idan an kai maka ita.. Waima dakata shin kai ka biya sadakin nan ne.?

Haidar ya sauk e ajiyan zuciya kaman wani maraya  Shikenan Mommy.. Saida safe.. Amma please a k yaleta ta kawo min coffee.

 Naji& Just coffee.. Tai maganar tana jaddada masa. Ta k arada  Jeka Allah bamu alkhairi.

Haka ya fice duk jikinsa ba kuzari. Shi fah maganar gaskiya wann gadara da Mommy take masa da mata akan sadaki ya fara isansa. Shidai kawai gwara ya biya Mommy sadakinta ya huta.

Bayan ficewar Haidar shiryawa tai ta nufi sashen Daddy.

A parlor ta iske shi. Daddy ya dubeta da mamaki. For days yana k ok arin shawo kanta daga fushin da take dashi sai gashi yau ta kawo kanta har yanda yake. Murmushi yai cikin zuciyarsa yake ayyana lallai sai a bar uwa da D anta. D anta shine rauninta.

Ta k araso kanta a k asa. Kaman mai shirin zama sai kuma ta silale gabansa. Ta kifa kanta tana hawaye. Cikin rawar murya irinta mai kuka take fad in  Engr ka yafe min.. Ka yafe mun duk abubuwan da nai maka.. Na shekarun baya da na kwanakin nan.. Kuka ya hanata ci gaba da magana. Daddy ya duk a shima suna fuskantar juna. Sai ya rungumota zuwa jikinsa. Kamar wacce take jira kukanta sai ya k aru. Shima ya saka d an yatsarsa ya goge kwallan da ya mak ale masa cikin ido.

 Is Ok Kwaise. Ya isa haka.. Dukanmu  yan adam ne masu kuskure. Mafiya alkhairi sune masu tuba. Bayan tsawon shekarun nan idan akwai Wanda yafi cancanta ya nemi yafiya ni ne. I supposed to be the head of this family.. Amma duk sai na bar Miki nauyin.. Kece kika jajirce Akan wann ahalin Kwaise.. You never give up despite the challenges.. Kin tsaya Akan k afarki ganin cewa ahalinki bai watse ba. Kinyi abinda ni na kasayi Kwaise.. Thank you for not giving up on us.. Murmushi ne gauraye da hawaye saman fuskarsa. Sai suka rungume juna wani kukan na kuma zuwa ma Mommy.

**

A b angaren Haidar kuwa koda ya koma sashensa zama yai shi kad ai a balcony d insa yana tunanin rayuwarsa. Da yanda shigowarta cikin rayuwarsa Ya canza komai lokaci guda cikin ikon Allah. Yana jin wani shauk i can k asar zuciyarsa Wanda bai tab a jin hakan ga wata mace ba. He wants to build something special with her.. base on trust and transparency wanda hakan ke nufi dole ya sanar da ita wasu abubuwan daga past d insa musamman abinda ya danganci personal rayuwarsa. Aurensa da Dareen Wanda ko family d insa basu sani ba har ya faru ya k are da kuma yanda nasu auren da ita Ummul d in Ya kasance. Yarjejeniya sukai da mahaifiyarsa zata shigo rayuwarsa a matsayin matar wata uku dan kawai Ya mallaki project d in da yai niyyan tarwatsa mahaifinsa dashi. Ya lumshe idanunsa a hankali yana furzar da huci.

63 / 95