Author : Asma Baffa Category : Romance
masa laifinsa tare da sanar dasu inta kaisu abuja irin hukuncin da za'a musu amma yanzu in sunji nasiha zata san yadda zatayi a kyalesu amma fa daga wannan lokacin zasu yawaita kawo ziyara qauyen kuma kowannw lokaci suna iya zuwa
da sauri suka amsa sun yadda inda daga baya dije tace ta sallamesu su tashi su fita wai zata yiwa hafsy gwajin cutar caskalaxation π€£
duk suka miqe suka fita jiki ba kwari
sun jima da hafsy tana yimata nasiha akan rayuwa kafin ta bata abinda tazo mata dashi tace zata tafi amma kafin ta koma abuja zata dawo sai dai kada ta bari su rainata itama kuma kada ta raina kowanne cikinsu a haka sukayi sallama hafsy harda kuka tanama dije godiya
sai yamma ta dawo gida babu wanda ta fadawa abinda tayi washe garin ranar tasamu zuwa gidan su shatu ita kam ba laifi da sauki abin in akayi la'akari da auren kauye dama an san dole sai anyi wannan bautar
********
haka kwanaki suka dinga tafiya inda hutun dije ya qare daddy ya kira yace ta dawo gida koda me gari yafada mata bata so ba amma dole ta fara shirye shiryen komawa duk cikinsu ita da iyayenta suna kewar tafiyar tata
********
to bari mu leqa gidan amare kuma anyi taro lfy kowa ya kama gabansa yayin da aka bar angwaye da amarensu kasancewar kowa auren soyayya sukayi yasa suke cikin farin cikk da walwala da kulawa da juna naseer da yusra kam kullum addu'arsu Allah yakawo dije domin sun zauna sun tattauna akan abinda ya faru sun gama gano itac silar komai dan haka kowa ya qudiri aniyar yimata nasa salon rashin mutuncn toh fa zama ya fara zama domin yau kusan sati biyu da aurensu kullum daga gidan mamy ake kawo musu abinci su duka inda suka saki jiki suke shan amarci sosai ba ruwansu
a bangaren habeeb ma abin maliyan luqwi domin yasamu yadda yake so sajida ta kware a fannin soyayya macece me tsananin kissa da kisisina irin su ne matan daba boka ba malam amma karfar baka kadai ta wadatar suyiwa mutum kwaf daya duk irin yadda ta lura msmy na ji da yusra hakan yasa ta qara jawota jikinta itama domin ta lura yusrah da sauranta har yanzu
******
yau dije ta shirya dawowa iyayenta sunyi mata nasiha matuka daddy ne ya turo aka dauketa sai birnin tarayyaπ
kusan magarib suka iso gidan direct dakin su ta nufa bata bi takan mamy ba dan tasan ko ta dawo ko bata dawo ba gurin mamy duk daya ne dan haka dokin ganin basira kawai takeyi koda basira ta ganta kuwa rungumeta tayi suka shiga murnar ganin juna sai da tayi wanka tayi sallah kafin taci abinci sam basu samu haduwa da kowa na gidan ba dan ita harga Allah tama manta da wata cakwakiyar data tafi ta bari
*vote*
*comment*
*with 08066364077*
*Alqalamin khady*β
[16/12, 11:41] βͺ+234 806 493 3819β¬: ππππππ
*TA ME GARI*
NA
Khadija usman
1β£2β£
ba qaramin farin ciki innah tayi ba da ganin dije ta canza tayi kyau ta wuce ma tunanin yadda take so ta zama ita kanta dijen tayi farin cikin ganin innah inda suka bude shafin hira danma yamma ce zabbi inna tasa aka yankawa dije ta kwashi gara kuwa inda ko da wasa bata sanar da innah zaman da takeyi a binni ba itama innar ganin canzawar dijen yasa tabar tunanin da takeyi a baya na ko dijen na cikin wahala
sai bayan isha'i suka sami zama da iyayenta inda sukaita taba hirar yaushe gamo nan dije ta dubi innah tace
wai ni innah ina ko su hafsy da shatu
ai sunyi aure tun tuni sai dai kam ita hafsy abun ba dadi dan dan yayar delu ne ya aureta kin san ko gurin delu ba dadi take ji ba dan haka koda yaron ya nuna yana so duk da ba yaron kwarai ne ba ta ce dole sai anyi gashi dama yanada wata matar yanzu in kinga hafsy sai kin tausaya mata wlh ga wahalar miji gata kishiya abun ba'a magana wlh gwanin ban tausayi
tsayawa tayi da cin abincin da takeyi kafin tace Allah sarki hafsy wlh na tausaya mata aure a qarancin shekarunta haka ai an cuceta
inna ce ta kalle ta tare da fadin to me kike nufi ? bata isa auren bane ko kuwa?
wlh inna in kikaga irin yadda nake tausayawa wadanda ake yiwa aure da wuri sai kinyi mamaki musamman yanzu da naje nayi rayuwa cikin wayayyun mutane bazaki fahimci ana cutar yaranmu na karkara ba sai kinga yadda in sun tashi haihuwa suke shan wahala yanzu ba da bane amma har yanzu kunki ku gane ni yanzu ma a abuja waye zai kalleni bare ma har yazomin da maganar aure ai gani zaiyi nayi masa qanqanta
inna ce ta riqe haba tana kallon ikon Allah tare da jin kalaman dije wadda ta dage sai zuba sharhi takeyi can ta nisa tace au ke nan ma kina nufin baki isa aure ba kenan?
wlh ban isa ba a birni dai kam musamman 'yan boko gani zasuyi anyi min auren wuri dube ni fa duka nawa nake
um gaskiya na ganki fa gashi nan kirji ba komai
hmm inna kenan to wlh akan 'yammatan abuja ni ko kirgar dangi ban fara ba mutanen da zaki ga nonuwansu kamar jarka ai me qananan halitta ce zaki gansu kamar kaina
ke dije ke dije kiji tsoron Allah to a baro ake tura musu shi ko
hmm ai inna yanzu duk yadda na fasalta miki bazaki yadda ba kawai mubar maganar wace unguwa hafsy take?
tana can alqaleri
insha Allahu gobe ko zanje ai nasan ma gidan yayar delun idan naje sai a rakani
ai bama saikin sha wahala ba a cikin gidan suke
toh Allah yasa ma in gane danni yanzu kananun hanyoyin nan duk na manta su
duk da duhun dake dakin be hana inna wurga mata harara ba tare da fadin ai dayake can a sama kike yawo
wlh kuwa kamar kin sani ga hanyoyi nan kamar filin ball ka kure iya tafiyarka kamar zaka bangon duniya
ganin inta biyewa dije zatai ciwon baki yasata sauya akalar hirar tare da fadin ya zaman naki yake to a gidan kawun naki ince dai babu wata matsala
ai innah in ana batun matsala ma karki dinga kawota gidan nan mutanen kwarai ne sosai zamana dasu kamar ma hadiye juna yanda kika ga talaka da kudi ko ince miki buhari da talaka sosai suke kula dani ke tsakani da Allah bakiga yadda suke kula dani ba nima kuma ina binsu sau da qafa
to Alhmdllh naji dadi sosai ashe zahida ta canza hali wlh kullum da tunaninki nake kwana nake tashi ina tsoron kada kema kidau dabi'ar arna tunda kinje ansaki makarantarsu
inna kenan ke har yanzu baki bar maganar arnan nan ba wai waya fada miki karatun boko na arna ne kawai dan ka je ka koyi ilimi sai a ce maka arne
ai ku tuni kunyi nisa bakwajin kira dan haka ni ya isheni haka kije ke kika sani kiyita yi ba ruwana
amma ai zaki samin albarka dai?
albarka ai kullum sata nakeyi
toh nagode innata
suna tsaka da hirar baffa ya shigo aka shiga yi dashi saida suka raba dare kafin kowa ya kwanta
asuba tagari
*******
tunda safe dije ta karade gari duk gidan data san yakamata ta shiga ta shiga a gidan me gari ta yada zango inda suka kwashi hirar su da mutan gida aka sha drama duk wanda yaga dije sai yayi mamakin ta kasancewar ta canza inba an fada maka ance dije bace da wuya ka ganeta ta zama 'yar gayu komai ya canza bata samu zuwa gidan hafsy a ranar ba sai washe gari
tunda safe ta shirya cikin riga da siket na atamfa kasancewar an fara sanyi yasa ta dora wata babbar rigar sanyi a saman dressing dinta qaramin mayafi ta yafa tare da sa hill dinta baki tare da hand bag data zuba wasu 'yan kayan da zata kaiwa hafsy ta fito ta tarar da inna na gyaran masarar da za'ayi tuwo yau
sannu da aiki innah
yauwa me shigar 'yan duniya yanzu ke duk kin dauki dabi'ar mutanen nan dubi.......bata bari ta qarasa ba ta qarasa jikinta da rungumeta tare da fadin pls inna ya isa tare dakai mata kiss a kumatu tana dariya ta saketa ta nufi hanyar fita saina dawo inna
oh ni saudatu na shiga uku yanzu kuma wannan dabi'ar wace iri ce ita babba dake da cizo a kumatu wato shi cizon ma yanzu an banbanta shi dana binni dana kauye me makon nayi miki magana ki cijeni da haqori saiki turamin baki ki dunguremin kumatu Allah ya shiryamin ke dije
****
dan mashin din daya sauketa ta tsaya bawa kudi yara tuni sun zagaye ta yayin da wasu matan da 'ya'yansu suka kai musu rahoton baquwar baturiyar da akayi yasa suka fara tururuwar leqowa ta katanga
ganin ta nufi gidan ladidi me kosai ne yara suka qara duruwa a qofar gidan da sallama ta shiga gidan inda ta iske bakowa a tsakar gidan qara sallamar tayi kafin taji an amsa daga can ciki
hafsy ce ta fito sanye cikin riga da zani na atamfa duk sun kode iya hannun rigar kadai ya isa ayi maka rafar kasan riga harda tattaraπ€£
duk ta wani cakude tayi kalar tausayi
ganin bakuwar dake. tsaye ne yasata kafeta da ido gani takeyi kamar tasan fuskar amma zaiyi wuya ma dan tana ganin a talavijin ne dan haka dai ta dan saki rai tace sannu baiwar Allah
itako dije tunda ta ganta tausayinta ya kamata ji takeyi kamar tayi kuka duk nawa suke ita da hafsy yanzu fa suke shekara sha bakwai amma in suka jera kana iya rantsewa ta haifi dije ganinta a haka ya raunana zuciyar dije sosai ganin cewar bata ganeta ba yasata yin murmushi tare da fadin
*dijan gala tame gari ba auren talaka ba talaka noma da sassabe*
hafsy najin dije ta fadi haka ta saki wata dariya tare da farin ciki tayo cikin dije da niyyar ta rungumeta sai kuma ta fasa ta shiga kallonta tana fadin dagaske kece dije?kece kika zama haka ? anya kuwa?
rungumeta dije tayi kafin ta fashe da kuka nice hafsy meyasa kika fasa rungumata ko baki son rabata ne ?
ah ah dije indai kece dijeta dana sani kuma uwar mazga me bani kashi bazan ki rabar jikinki ba illa dai kada in shafa miki datti kin ganki kuwa dije tabbas Allah na sonki ji yadda rayuwa ta sauya miki ni kuwa dubeni duk na tsofe banda bauta da wahala a hannun uwar miji da kuma kishiya da shi mijin kanshi ba abinda nake tsinta dubi yadda kika koma kamar ba'a duniya kike rayuwa ba wlh dije nayi miki murnar tafiyarki binni dama nice nasamu koda kwatan abinda kika samu ne ta karasa maganar tana kuka
dena fadar haka hafsy Allah na sonki bai kuma manta dake ba ba kuma dan na fiki bane nima yasa nazama haka ki yadda da kaddarar ki kizama mai juriya da haquri har ki samu kici jarabawar ki yanzu dai muje dakin ki tukun
dakin ta suka shiga sai kace dakin tsohuwa qaramin gadon qarfe ne shima duk ya tsufa dakin ko kyan gani babu sallaya ta shimfidawa dije a gurin ta zauna inda suka shiga hira sunata nishadi tare da tuna baya
dije na lura da yadda hafsy keta mutsu mutsu dan haka ta tambayeta lfy?
dan marairaicewa tayi tare da fadin wlh dije narasa yadda zanyi ne abincin dazan sama miki naketa tunani yanzu gashi yadda kike din nan da wuya ki iya shan ruwan gidan dan na rijiya ne
kada ki damu hafsy maza samo yaro yasama mana abinda zamu ci
jiki ba kwari ta mike ta fita neman yaro inda bata sha wahalar samu ba kuwa dan sun cika qofar gidan suna jiran baturiya ta fito su qara kallonta
dubu daya dije t bawa yaran tace su siyo taliya sai kayan miya da maggi aikuwa da gudu suka karba sai kace a mota suka tafi sai gashi da wuri sun dawo dari tabasu tace su raba aIkuwa murna ba' a magana
tashi hafsy tayi ta hura wuta sunada ice fitowa tayi sukayi girkin tare har suka gama kuwa cikin mutanen gidan ba wanda ya dawo ranar hafsy ta barge haushin yunwar kwana da kwanaki kuwa dan ta debi girki daman ga mutumin kauye da son taliya kallonta dije ke yi cike da tausayawa kafin ta tambayeta matsalarta duk yanayin zaman da takeyi a gidan da kowa saida ta fada mata aikuwa take dije ta danna wata uwar ashar tsumi ya motsa nan ta shiga zazzaga bala'i kallonta hafsy tayi taga yadda ta rikede lokaci daya ta koma dijengala dinta ta da 'yar takife jahannama ga fasinja uwar suburbuda da mazga sai da tayi me isarta kafin ta nisa tace ina 'yan gidan suka tafi?
shi yana bakin kasuwa ita kuma kihiyar tawa da innarsa sun tafi suna can gidan su abokiyar zaman nawa dan kinsan duk gidan nan tsoron ta sukeyi har hi me gidan hi yasa ma inna ke binta kamar ita ta haifi dan
girgiza kai dije tayi tare da fadin hukuncin ta kanta zai fara kenan?
dafe kirji hafsy tayi tare da fadin na higa uku dije wane hukunci kum?kaddai kicemin har yanzu muguntarki na nan nidai rufamin asiri wlh karsu rama akaina
dayalla rufawa mutane baki kin san ni idan na tashi rama abu to da basira nake amfani an fada miki gaba duka zan afka musu ni nasan me zanyi musu uwar ita kishiyar taki zanci wlh ni ba ruwanaa
ke dije rufawa kanki asiri wlh wannan inta tauheki ko qafarki baza'a gani ba ruhehiya ce hi yasa ma fa ita kanta inna da hi hamidan din ke tsoronta dan mullikekiyar katuwa ce ance aljanu ne suka hura mata iska wai data hararesu
kallonta dije tayi tare da fadin ke hafsy a ina taga aljanin da har zata hararesu ?
ance tun tana qarama
kafin dije tace wani abu suka tsinkayo muryar hamidan na fadin iskancin banza da wofi wace shegiyar ce ta shigomin gida tasan kuma inna da hansai basa nan har aka taramin yara a qofar gidan yana fada ya qaraso dakin
tunda hafsy tajishi jikinta ya kama rawa ta dinga kallon dije tana yarfa hannu ita kuwa dijen ko'a jikinta illah zuge jakarta da tayi ta lalubo siririn farin glass dinta ta manna a fuskarta tare da qara gyara zamanta
yaye dan yalolon labulen dakin yayi tare da fadin nace wace hegiyar ce ta higar min gida bada izini na ba
cikin rawar murya hafsy tace am dama.....da...ma um...daga...kinga barshi in gabatar masa da kaina daga abuja nake ma'ana birnin tarayya nasan kasan sunan garin ina daya daga cikin hukumar farin kaya ta 'yan sanda masu bincike inda muke bi kauyuka muna bincika yadda suke gudanar da zamantakewar aurensu hakika mun kuma samu yadda mukayi tsammani dan gashi nan mun gani a gidanka sbd haka yanzu basai nayi wani bincike ba zan kira waya jami'anmu na 'yan sanda masu sa kaki suzo su tafi dakai mun same ka dai lafuffuka da dama duba da yadda na riski matarka duk da bata cemin komai ba ta rufa maka asiri amma banga alamar kana kula da ita ba ji yadda dakinta yake ji suturar jikinta gashi tun zuwana na aunata naga bata ci tana qoshi koma taci ta koshin bata samun me kyau dan haka zamu tafi dakai can ofishin 'yan sanda mafi kusa kafin gobe a wuce dakai abuja daga nan sai musan abinyi dakai hukuncin daurin rai da rai ko kuma daurin shekara hamsin
tunda tafara maganar hantar cikinsa ta kada jikinsa yafara mazari
*kun san ance shege na kauye sai tsoron 'yan sanda* π
gurfanawa yayi a gurin tare da fadin wlh wlh ranki ya dade alqu'arn idan da laifina a ciki in mutu a tsaye
yaseen laifin hansai ne da innah
qara hade rai tayi tace au wato ma kanada wasu matan kenan?
ah ah guda daya ce kuma itama kaddara tasa na aureta ko hafsy?
nidai ban sani ba cewar hafsy da tayi zuru tana kallon dije ikon Allah tare da yabawa da basirar ta
ah ah hafsy duk wanda yaga yanayin zamana da hansai yasan kaddara ta hada auranmu amma wlh bada son rai ba ranki ya dade in kina yiwa Allah kiyi haquri wlh ban san an fara wannan binciken ba
oh wato sbd shi zaka daina kenan
kafin yabata amsa sallamar su inna ta karade gidan tare da sababi ganinsa da hansai tayi a bakin kofar hafsy yasata tahowa gadan gadan kofar dakin tare da fadin munafiki uwar me kuma kakeyi a anan
alama yakeyi mata da hannu yi shuru yana mata nuni da cikin dakin
uwar miye a cikin dakin da kake nunamin mutuwa tayi ko me
inaga dai cewar inna da itama ta nufo dakin gadan gadan suka qaraso ya kauce ya basu guri
koda dije taga hansai duk rashin tsoronta saida ta ji gabanta ya fadi wata narkekiya ce duk da batasa yawan shekaru amma kam akwai kiba
ganin dije da sukayi a hakimce gata 'yar gayu yasasu dan rage sauti tare da kallon hamidan wacece ita kuma wannan din?
hukuma ya fada kamar me rada daga garin su baba buhari take nan ya kwashe duk bayanan da dije tayi masa ya fada musu
cike da rawar jiki harda rusunawasuka gaida dije suma nasu sharhin ta rattabo musu aikuwa nan duk jiki ya hau tsima suka shiga bata haquri ganin duk sun rude yasa tace su fita zatayi waya duk suka miqe suka fita suna makyarkyata hansai ce karshen fita dan da kyar ta mike bayanta dije tabi da kallo a ranta tace jar ubancan wannan duwawun ai sai inyi matakala dasu in zan hau katanga
suna fita ta kalli hafsy tace y kikaga ni
jinjina kai tayi dan ta kasa magana tasan dije ta ballo musu ruwa
magana tafara yi kamar me waya cikin daga murya ok sir,yes sir su ta dinga fadi kafin daga baya ta ce su shigo ta gama
duk sunyi tsiru tsuru a gabanta se raba ido sukeyi
naso naqarasa