Author : Asma Baffa Category : Romance
munafircin ne na qannen miji kinga irin abinda nake fada miki ba nan fa suka shiga neman dije gani duk sun leqa basu ganta ba yasa sajida fara zargin kodai aljanun laila ne suka fada mata qarya gashi ba damar tace ah ah tasan halin laila yanzu sai su hau sama ganin basu ganta ba duka cike da mamaki suka fito suna tunanin ina ta shiga
itako dije tun shigarsu dakin ta miqe ta koma kitchen nan ta hau safa da marwa na shirya kaya a saman dinning duk wani ruwa da kalar lemo saida ta hada a gurin saisa ya cika tab da kayan ciye ciye kafin tayi saurin fita zuwa qofar falon ta cake tana jiransu fito
tana daga tsaye taji alamar sun dawo falon dan haka ta turo kofar ta shigo da sallamarta tare da nuna alamun gajiya a tare da ita
kallonta suka shiga yi musamman laila da taga yadda ta shigo din itako sajida ta shiga karyata maganar laila dan duk wanda yaga dije a wannan lokacin yasan dawowarta kenan basu gama tunanin na sukaji dije ta buga tsalle tare da fadin
yehhhh dan dunga yaushe kuka karaso bayan saida nace ku bari mu taho tare ashe kun sato hanya kun taho lah ashe akuyatu ta fanshe ni dan tayi muku girki
dukansu juyawa sukayi suka kalli inda take magana
ganin gima giman kuloli ga dinning din cike da kaya yasa sajida sakin qara tare da nufar bayan kujera dan ta buya itama laila ta mara mata baya
habeeb ne ya shigo dauke da sallama a bakinsa inda yana shigowa yaga dije tsaye na fadin
aunty laila taso ga dan kutungayya wannan aljanin dake saki yawan munafurci yana son ku gaisa
da kyar ya mayar da
kofar ya rufe inda ya saki baki yana kallon sajida data leqo kai jiki na karkarwa
ganin hakan da yayi yasa shi fahimtar yarinyar nan ce yanzu hska tayi musu wani abun dan yasan iskancinta ai kuwa yau saita ci ubanta daga yau bazata qara ba nufarta yayi gadan gadan da niyyar cafkarta ya nadeta kawai sai gani yayi tayi gurin dinning tana fadin kada ki damu darwanatu ai kowa zai ci abincin nan waya isa kiyi girki aki ci duk ds nasan duk kayan 'yan gidan ne
ah ah kada ku damu basai kun kawo naku ba ku barmu da namu kalar
kutttt habeeb ya hadiyi wani yawu dan sai yanzu yakai dubansa ga saman dinning dinsu wanda yaga dirka dirkan kuloli ga kuma kayan ciye ciye nan tab akai dubansa yakai ga sajida wadda ya zuwa yanzu banda rawa ba abinda jikinta keyi cikin rada ya shiga tambayarta abinda ya faru hankali ta fada mishi duk abinda tasani da yadda laila ta fada mata dawowar dije da kuma yadda ta duba basu ganta ba
jin murysr dije sukayi na fadin ah ah ai basai kun dauko su ba dukansu yanzu zasu taho muci gaba daya ai kada ku damu dukansu na jin haka suka juya da niyyar kwasa da gudu amma me? kafin su kai ga fita suna rige rige da gwara kawuna dije tayi caraf ta riqe habeeb wani ihu ya saki dan in baku manta ba na fada muku habeeb akwai tsoro
dariya dije takeyi iya yinta ta kuma riqe habeeb wanda ya kama ihu iya yinsa tare da karanta ayatul kursiyyu a fili naseer da yusra ne suka fito daga part dinsu jin ihun naseer ganin laila da sajida sun rukunkume juna suna rawar dari a bakin falon yasasu qarasawa tare da tambayarsu lfy duk sun kasa magana inda naseer yayi ta maza shida musa me gadi da shima ya karasso yanzu jin ihun me gidan suna shiga suka ga dije zaune dirshan a gaban habeeb ta riqe masa maka kam tana dariya harda kwalla shiko ya bude baki yana ihu da addu'a naseer yasan kwanan zancen dan haka ya kasa qarasawa sai musa ne ya qarasa koda ya isa nan ya tsugunna ya fara bawa dije haquri domin yasan wannan aikin na jinni ne
kallon sa tayi tace nice dai dijen da ka sani ga dai aljanun can akan dinning suna walima
kallon gurin duk sukayi suka ga abinda ke kai kowa yafara zufa yana neman hanyar fecewa inda habeeb najin muryar musa ya shiga magiyar yace ta sakeshi
zan sakeka amma su dan dukununu sunce yau sai mun tayasu murnar zagayowar haihuwar dan autan su dan haka dole kowa na gidan nan ya zo yaci abin cin can
nan aka shiga kallon kallo su kuwa matan na waje tuni suka sheqa pary din yusra suka kulle inda sajida ta dubi laila tace kin gani ko gashi nan harda irin na kanki sunzo min gida ina zaman zamana gashi kinsa sun kawo ziyara kin san suna binki meyasa kika zomin bayan kin san ni dul lamarin iska tsoronshi nakeyi
cikin kuka laila tace wlh ni banida aljanu ki dena jamin jaraba kada suji su dafemin
ina na kan naki dari ba dayan ?
ai sun barni tun da aka yayeni wayyo ni wlh gida zan tafi tunda abin harya kai haka baxan kara zuwa gidanki ba ashe har uwar aljanu kk aje a gida
duk kansu tsorace suke sunata kukan nadama wai🤣
su kuwa mazan nacan dije fa tace sai kowa yaci abincin nan kafin su dan dukununu su bar gidan nan jin in ba'aci bazasu tafi ba yasa habeeb saurin amsa duk zasu ci shidai tunda ta sakeshi
a gaba tasasu suka nufi dinning inda musa jikinsa ke bala'in rawa hakama naseer suna qarasawa sukaja kujera da niyyar zama dije ce ta da karfi tace ya naseer ka jefar da tunguji ba ruwana
da sauri ya ja da baya tare da kwalla kara habeeb da yake kokarin zama ji yayi tace shikenan ya zauna akan iya tsibbanatu qara yayi tare da zamewa qasa ji kakeyi kwal ya kwale da gefen table din yayin da qugunsa yayi qara.......
*Alqalamin khady*
TA ME GARI
na
khadeeja usman
1⃣9⃣
naji rokonku masoya amma kuyi haquri bazan iya yi muku typing sau biyu a rana ba ku tuna fa dukanmu matane munada uzuri a gabanmu karantawa ba wahala cikin qanqanin lokaci zaka gama amma typing akwai wahala ina son nishadinku shiyasa na ke bada lokacina nake muku typing fatana kuyi haquri mu qarasa da yadda muka fara idan nasami dama zan iya yi muku fiye da biyun ma a rana
wata azaba yaji amma ba halin yin ihu ya zuwa yanzu dan duk a rude yake ganin yanayin da duk suke ciki yasa dije cewa
lah sannunku kunga fa yanzu sun fara fushi gara ku tashi a gaggauta walimar nan su kama gabansu kaga dan dukununu kuyu haquri ku debo naku kujerun ku basu wannan su zauna ta fada tare da qara gyara zaman kujerun gurin
cikinsu duk wanda ka kalli fuskarsa kasan kadan yake jira ace arrr ya arta dan haka cikin himma suka fara qoqarin zama a dan dosane
itama dijen zama tayi ta kame guri daya tare da fadin toh ku zuzxuba mana arwanatu
😳 sukayi sunata raba idanu jin ta ambaci a zuba abincin kowanne yana kissima yadda zai kwashi wannan girkin na aljanu itako dije ta kame tana kallon kowa a ranta banda dariya ba abinda takeyi
can kuma sai ta miqe zumbur kamar wadda ta tuna wani abun suma miqewar sukayi dan su yanzu duk wani motsin yarinyar tsoro yake basu ganin duk sun miqe ne suma yasata fadin ina kuma zakuje?
binki zamuyi cewar naseer da kyar
ai nima ba tafiya zanyi ba zanje ne na kirawo matanku suzo su taya autaress murna suma
yauwa Alhmdllh dan Allah kirawo su din
cewar habeeb da ya zuwa yanzu ya dora laifin faruwar komai akan sajida dan a bayanin data masa ya fuskanci bakuwarta ce silar komai
toh ku koma ku zauna mana in kirasu
duk komawa sukayi suka zauna inda ita kuma tasa kai ta fice a falon ta nufi part din su yusrah dan tasan suna can
tana fita naseer ya kalli habeeb cikin marairaicewar fuska kamar zaiyi kuka yace bros nifa wlh lamarin yarinyar nan tsoro yake bani wannan wace irin masifa ce tunda muka fara ganin yarinyar nan bamu taba wanyewa lfy ba wannan ai ita ce da tauraruwa me wutsiya gani yayi habeeb da musa nata mishi alama daya yi shuru sai daga baya ya fahimci me suke nufi ganin musa nayi masa nuni da saman dinning hannu yasa da sauri ya kama bakinsa kamar qaramin yaro suka shiga raba ido🤣
tana zuwa part din ta shiga kwankwasawa laila da sajida da suke jiran tsammanin warabbuka sukayi saurin nufo kofar dan sun san yazuwa yanzu komai ya kamalla barin ma laila data matsu tabar gidan dan ita yusra ta shige daki ta kulle kanta ta shiga kiran wayar mamy amma bata daga ba
da sauri sajida ta bude kofar batare da tambayar waye ba aikuwa sukayi ido biyu da dije da gudu ta nufi ciki inda suka fara rige rigen tserewa ita da laila amma dije ta shigo tana fadin meye haka aunty ?
jin tace Aunty kuma cikin muryarta ya dan sa sajida tsayawa amma ita kam laila tayi bayan kujera tanata rarrafawa dan ta samu ts fece
jiki na rawa sajida ta tattaro karfin halin daya rage mata tace ya...ya...akayi ina su habeeb
kallonta dije tayi kafin tace ban gane ina su yaya habeeb ba gasu can a part dinki yayi baki yace in fada miki wai in kin gama gudun tsoron kizo ku gaisa
kuri tayi tana kallon dije jin cewar har habeeb yace ta zo yasata yin tunanin komai ya zama normal ba mamaki malamai ya kirawo ai gara ayiwa gidan addu'a gaba daya da alama komai ya lafa dan taga yarinyar ta warware dan haka cikin dan qarfin hali ta maze tace toh jeki ina zuwa
ok ta fada tare da fadin ina Aunty yusrah itama yakamata taje a gaisa da ita dan bakin daga family dinmu ne na qauye
toh bari na kirata tana ciki cewar sajida data juya ta nufi dakin da yusra ta kulle tana zuwa ta shiga buga qofar yusra dake can bayan gado manne da waya ta qanqame jiki tanata faman kiran wayar mamy wadda sai yanzu ta samu ta dauka tana dagawa kuwa yusra ta shiga fadin pls mamy kizo ki taimakemu wlh jaraba da annoba kika kawo mana ashe cikin kwana daya datayi a cikin biyun da kkk ce tasa kowa yasan da zamanta mamy pls n'd pls kizo ki dauketa ta koma gidan ni nayafe mata duniya da lahira
jin da mamy tayi yusra na kuka yasata fadin calm dawn mana yusrah ki ci ubanta mana karfinki tafi ko kuwa shi naseer din tafi qarfinshi ne iye
bazaki gane ba mamy duk yadda na fada miki nidai dan girman Allah kizo ki dauketa
.to amma ai naji tace wa daddy'n ku ku kukace ta zauna tayi muku kwana biyu dan haka ma nabar maganar dawowar tata
wlh mamy na rantse da Allah bani bace wall.....kinga ya isa wai meya ke faruwa ne kk kuka haka dukanki takeyi ko yankar naman jikinki
wlh mamy ni gara ma ta dakeni da masifar da nake gani nidai mamy kizo ki dauketa dan Allah suna tsaka da maganar ta tsinkayi bugun kofa aikuwa ta fashe da kuka tare da fadin kin ji ta ko mamy dan Allah kiyi sauri kixo
jin haka da mamy tayi yasata saurin kashe wayar ta miqe dan ta sanar da daddy su taho
jin taki budewa ne yasa sajida yi mata magana saida taji muryar sajida kafin ta bude tana leqo kai tace ya ake ciki
dan juyawa sajida tayi bayanta taga dije bata hangota nan ta sanar da yusra sakon da dije ta sanar mata
tab wlh ba inda zani
ah to ni ina ruwana kiyi zamanki kin san dai ba mamaki malamai ne suka zo daga kauyensu dan inaga sun san da zaman lalurar ta inaga shiyasa sukayi addu'a muma gara muje kar abin ya shafe mu bayan sun tafi tunda abin har yakai ga ana min girki da walima a gida ai ni nafi kowa shiga uku
sun dan jajja kafin yusra ta yadda ta fito da kyar laila ta fito a bayan kujera suka bi bayan dije kamar abin magani amma ganin ko'a jikinta yasa su yadda da almatsutsan sun sauka ya zuwa yanzu
koda suka qarasa part din nan aka shiga kallon kallo kowa ya kasa shiga sai da dije ta juyo ta kalle su tace ya haka ku shiga mana
laila ce tace ah ah ni daga nan ma wucewa zanyi ki mikomin jakata da takalmi in kin shiga Allah ya bada zaman lfy
ai wlh baki isaba sai dai ki shiga ki dauka in kin matsu
wace matsuwa nayi ai ba dole a mota fa nike kinga bari in tafi a haka na turo daga baya a karbar min
dije ce ta kalleta tace haba aunty ta ya zaki shiga mota a haka ba takalmi me yayi zafi haka ?
ai ni sai yanzu na tuna ma ashe bada takalmi nazo ba suna mota har jakar
sakin baki sajida tayi tana kallon laila da duk ta birkice kamar ba itace daxu ke ruwan bala'I ba dan haka cikin quluwa tace ah ah tsirara kika shigo gidan ba takalmi ne kadai baki zo dashi ba amma ai karki manta mukullin motar na ciki ko?
innalillahi wa'inna ilaihir raji'un cewar laila a fili
ba yadda ta iya dole suka tura qofar suka shiga suna shiga suka hangi mazan tsaye kamar ace arr su arta ita ko dije suna shiga ta mayar da qofa ta rufe tare da fadin sannunku da zuwa ku qarasa ayi walimar daku ku kadai ake jira
nan fa guri ya hautsine zasu sa ihu tace lah aunty kada kuyi ihu wlh kunayi zasu sa bakinku ya qara girma
nan fa jikin kowa yahau makyar kyata kasancewar dinning din kujeru takwas ne nan tajawa kowa daya ya zauna duk wanda ka kalla matsar kwalla yakeyi inda duk suka dubi kayan dake gurin wanda suka kalli kwalbar carbont din dake gurin gaba daya sai idanunsu yake musu gizo suke ganin kamar jini ne🤣 kunji fa sharri😜
bude kular tayi ta leqa 'yar mitsitsiyar shinkafar dake can kasan kular ta hango dan dama fa iya wadda zata iya ci kawai ta dafa jaraba ce tasata zubawa cikin wannan kular
lahhhh amma ko baku kyauta ba akuyatu ai bani kadai nace muku ku ragemun ba suma fa duk zasuci irin girkin ku amma shine kuka rage iya cikina ta fada tare da dan hararar kujerar daba kowa
jin ta ambaci an cinye abinci sai ita kadai aka ragewa yasa kowannensu hamdala a zuciyarsa juyowa tayi ta kallesu taga duk sun kafeta da ido dariya taso kwace mata amma ta danne tace toh kunga har sun gama cin nasu abincin kunyi jinkiri amma ai ga kayan drinks nan kuci ni bari inci wanda suka ragemin din nan ta shiga kokarin zuba shinkafar harta gama ta fara ci cikinsu ba wanda ya motsa bare ya dauki wani abun
shi kam musa ji yakeyi dazai samu dama da inya fece bamai sake ganinsa tunda aikin gadin ba dole bane
itakam dije tanata cin abincin ta hankali kwance su kuwa sai muzurai sukeyi
sai da ta gama tasha ruwa kafin ta juyo ta kallesu tace sunce tunda baku cin irin wannan bari su kawo muku irin nasu
da sauri aka shiga rubibin daukar abin ci inda saboda tsabar sharri habeeb daya dauki apple wai jinta yayi kamar goribar data bushe wai kawai dan ta aljanu ce🤣
kowa a gurin yana shan abu kamar magani kuma yana kuka itako dije sai surutun ta takeyi ita kadai hakan ke qara firgita su sukuwa suka shiga 'yammatan hawaye
su mamy na qarasowa suka shiga yin horn jin shuru ba'a bude ba yasa habu fitowa ya bude gate din da kanshi ya shiga da motar
mamy cikin tashin hankali ta bude murfin motar ta fito ita da daddy wanda suka nufi part din da basu san ko na waye a ciki ba suka shiga bugawa
jin ana buga kofar da dan karfi ga alamar magana yasa su naseer qara rudewa dan duk a tunanisu ko abincin da suka ki cine abubuwan suka gayyato wasu
dan haka suka qara kidimewa tare da qoqarin tura duk abinda ke hannunsu baki
dije ce ta miqe ta nufo kofar a ranta tana fadin wane me tsautsayin ne kuma
tana bude qofar taga su daddy mamy na qoqarin tureta ta shiga tana fadin suna ina?me kk yi musu jin muryar mamy ne yasa yusra da su naseer bude murya suka sa kuka.......
*kai kai naso inci gaba amma....*
*vote*
*comments*
*with 08066364077*
*Alqalamin khady*✍
[3/14, 9:42 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*TA ME GARI*
NA
Khadija usman
2⃣0⃣
*A gaskiya mutane basuyi mana adalci ba duk da nasan masu qarancin ilimi da tunani ne sukayi abinda sukayi kowa fa da ra'ayinsa duk wadda taga bazata iya novels kyauta ba ra'ayinta ne ban kuma ga laifinta ba haka mu da mukaga zamuyi kyauta muma ra'ayinmu ne dan haka bai kamata ayita magana daya ba har takai ga anyi mana rubdugu ana zagin iyayenmu gaba daya dan girman Allah ina rokonku ku dinga mana adalci reader's ku duba irin wahala da westing time din da muke yi duk dan mu faranta muku ina rokon afuwar duk wanda magana ta ta batawa rai🙏*
cikin rudewa da tashin hankali mamy ke fadin ya salam me zan gani haka me yake faruwa ta fada tare da qarasawa cikin falon ta nufi inda su yusra suke
daddy ne ya shigo shima inda dije na ganinsa ta shiga yimasa sannu da zuwa cikin nuna farin cikin ganinshi ta fara fadin oyoyo daddy gwamma da kuka zo wlh kunzo a dai dai sai ayi tare daku
daddy ne ya dubi sauran mutane yaga yadda fuskokin su suke amma kuma yaga dije qalau da alamun farin ciki a tare da ita ga kuma mamy data azalzaleshi cewar ba lfy gidan yaran ya taso suje dan haka ya juya ya kalli inda mamy take tana tambayar yusra dake ta kuka me ke faruwa
caraf dije