Tame Gari 1 Complete Hausa Novel

Author :  Asma Baffa Category :  Romance

Chapter   14 / 33

39K to 42K   out of 96.3K words

yana son kunu sosai kowanne iri hakama kosai itama sajida tsintar kanta tayi da son cin kosan wanda ada sam bata ko son jin sunansa bare ace taci

zuzzuba musu tayi nan suka shiga aikawa kasa da hanci ba qaramin dadi sukaji ba su duka dan haka ko bakinsu ba'aji dije ce ta cinye nata kosan ta miqa hannu da niyyar debowa cikin kula danta qara taga wayammm

binsu tayi da ido inda ta kalli plate din gaban kowa taga shi habeeb saura uku ita kuma sajida sauran daya bata ko tsaya wata wata ba ta dauke nsu gaba daya cikin sauri suka kalleta amma ko'a jikinta taci mayar gabanta ta zauna ta fara ci

habeeb ne yayi qarfin halin fadin ke wannan wane irin iskanci ne mu sa''aninki ne ?

ah ah amma kuyi haquri naga ne ai ana barwa qarami dan ragowa ko zai bukaci kari to ku kuma naga kamar bakusan babba da yaro ba gashi ni ban koshi ba kuma ciki be san ayi masa kara ba musamman cikin kauye tunda ya riga ya saba da hatsi shiyasa na yi muku haka amma idan baku koshi ba ai naga akwai duk kayan hadin a gidan ni da ba manomiya ba kuma ban nemo na kawo ba bare ace zan hana kaga sai chair lady ta shiga ta qara maku wani tana gama fadar haka ta miqe ta shiga dakinta danta shirya ta wuce school

dukansu binta sukayi da ido sajida data gama kuluwa tace wai ni dear tsoron yarinyar nan kk yi ko kuma me? ta yaya kana gani yarinya tanawa mutane rashin mutumcin dataga dama amma ka kyaleta

to ke me zai hana ki dauki mataki ya fada yana me kokarin mikewa dan barin gurin

au hakama zakace ko?

to shikenan zan kuwa dauki matakin kamar yadda kace amma wlh matakin dazan dauka baxai yiwa kowa dadi ba dan ni ba ruwana da wata alakar dake tsakaninku ko kuma ran daddy'nku da zai baci wlh baxai yiyu ba ni ban haihu ba amma a fara kawomin jidalin dangin miji tun yanzu duka yaushe mukayi auren da har za'a wani kawomin wata watanma dangin dangarera inda ma qanwarka ce uwa daya uba daya amma cousin wlh ma an raina min hankali ta tafi gidan naseer mana ko dole sai nan yarinya sai jaraba da fitina baki kamar reza tunda ta diro gidan nan narasa kwanciyar hankali daga ni har sauran jama'ar gidan amma kun kasa daukar mataki ji yadda ka tsaya qanwar cikinka tana fada ma magana to wlh yau zanyi maganin
abun ta fada tare da kokarin miqewa shi kuwa habeeb da tunda ta fara magana ransa ya fara baci tsaye yayi ya zuba mata ido

itako dije ta fito kenan da niyyar tafiya ta ji sajida na sababi tsayawa tayi tana kallonta har zuwa lokacin data mike ta nufo ta gadan gadan tana kumfar baki

a inda dije take bata ko matsa ba ganin sajida ta nufota yasata fadin um um Aunty um um fa ina tausaya miki wlh kada ki qaraso

sajida da masifa ta rufewa ido ko jinta bata nuna tayi ba sai qara nufota takeyi yayin da dije tana daga inda take tafara dariyar mugunta abinda yabawa habeeb mamaki da tsoro kenan........

*sai kun dinga hakuri da duk yadda kuka samu duk yadda naso in samu lokaci fiye da haka baya samuwa*

*Alqalamin khady*✍
[3/15, 6:29 PM] El~hajj: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

*TA ME GARI*

NA
khadija usman

2⃣4⃣

*har kullum bakina bazai gaji ba haka alkalamina bazai gaza ba wajen nuna godiyata ga daukakin masoya na wlh banida bakin dazan gode muku dashi bisa addu'ar da kukeyimin ina rokon Allah yaqara bani ikon faranta muku Allah yasa ko bayan nagama muku ta me gari kuci gaba da bibbiyata tare da nunamin soyayya fiye da yanzu ina mugu mugun sonku fiye da yadda kuke son ta me gari* 😘

gadan gadan ta nufo dije ita ko sai murmushi takeyi tana tsaye kyam cikin shirin zuwa makaranta

ganin da habeeb yayi dije na dariya tana kuma tsaye tana jiran karasowar sajida babu ko alamun tsoro a tare da ita bare tasa niyyar guduwa hakan yasa yasan akwai abinda ta shirya dan haka cikin daka tsawa yace

keeeee!!!!sajida bana son shashanci me kk shirin yi haka ?

tsayawa tayi cike da jin zafinsa ta juyo tace mataki zan dauka tunda kai ka kasa ta yaya zan zauna qaramar qanwata tana min iskanci wannan wace irin jaraba ce tunda yarinya tazo ta hanani sakewa ni da gidana sannan kai ka zuba mata ido tamkar kana tsoronta to gara na kawo qarshen wannan rashin mutuncin nata wlh nagaji ko ta bar gidan nan ko kuma wlh a fita da ita da ambulance

ido dije ta zaro😳ambulance fa kk ce Aunty na shiga uku kice dukan jinya zakimin to amma bakomai da sauki tunda bana mutuwa bane ko banza na mori zaman jinya dan naga in anje dubiya mutum yana tara abin arziki gashi ko ba komai ka dada samun kulawa gurin dangi dan haka kada ki damu zo ki daki iya yinki har ki gaji amma fa ki lura gurin bugun kada ki dakeni inda zanji zafin da hankalina zai fita in fama miki ciwo naga bai gama sabewa ba ni nama fasa zuwa makarantar zo ki jibgi rabonki yau hau ce ta hauni

rawa zuciyar sajida ta shiga yi jin furucin yarinyar anya kuwa wannan yarinyar ba jinsin shedan bace kai gaskiya da sake lahaulawala quwwata illahbillah Allah ka rabamu da wannan jaraba

shima habeeb a nasa bangaren haka ya shiga zancen zuci duk yadda akayi wannan yarinyar jinsin aljanu ce duba ma da yadda take da kyau ga farinta sak na aljanun sannan ga shegen rashin ji shiyasa ma take ita kadai gun iyayenta dama ance aljanu kishi garesu shiyasa ta hana iyayen haifar jinsin bil adama gashi yanzu ta zo ta addabe su su iyayen nata nacan suna cikin kwanciyar hankali ita kuma tana nan tana gasa su

muryar ta suka tsinkaya tana fadin Aunty tunanin me kk yi kada ma kice na tauye miki haqqinki gurin yin dukan ban barki kinyi yanda ranki ke so ba bari kawai in tube ki zabi inda yayi miki ki daka amma dan Allah ki dan daki gurin nama nama dan kin dai ga yadda nake ba wani naman kirki ne dani ba tana gama fadar haka suka ga ta shiga kokawar cire hijabi tana qoqarin cire jakar bayanta

basu tsinke da lamarin ba sai da sukaga ta shiga kiciniyar daga riga da alamar zata cire

ke meye haka kikeyi bakida hankali ne ya fada a dan hasale

rasss nake yaya kai dai kawai ka tsaya kasha kallo in zaka iya gara kabarta ta huce haushinta amma dan Allah ko da na suma ban samu nasarar ganin yadda aka fita dani aka sani a mota ba ko kuma ganin wanda ya daukeni ba ku taimaka ku dauki hoto ku ajiyemin sannan a sanar da masu zuwa dubiya musamman daga kauye in sun tashi riko abin dubiya su biyo da zabi da kaji kuma danyi kada a yanka ko a soya a kawowa aunty tayimin dahuwar 'yan birni inci in more sannan dan Allah aunty ki lura gurin dukan kada ki taba fuskata ki daki iya jiki sbd kar bakina ya nakasa ya hanani cin abincin daren yau sai dai in sha kunu da safe

*oh su dije jaraba wato magana ta fada musu a fakaice* 😏

ci gaba tayi da kokarin daga rigar wai ita a dole cirewa zatayi wanda inda cirewar gaske ne da tuni ta cire amma yanzu daga ta kama can sai ta kama nan ganin da sajida tayi yarinyar na kokarin yin tsirara gaban mijinta kun santa kuma da kishi haksn yasa bata san lokacin data kama hannunsa ba tajashi sukayi ciki tana ambatar ta shiga uku ba tana shiga dakin tasa key ta zauna gefen gado ta dafe kanta shima din habeeb zaman yayi dukansu aka rasa me magana

itako dije tana ganin yadda sajida tayi ta saki rigarta ta kama dariya tare da daukar jakarta da hijabinta ta nufi waje tana dariya tana fadin waya gaya miki da cirewar zanyi yadda zamani ya koma yanzu maza da mata duk suna iya ma mutum fyade inje ku nakasani ke da mijinki kunga araha yanzu ba gashi na kubuta ba dan wannan me qirar mazan inda ta riqeni wlh baxan sake moruwa ba inaga sai dai na koma kauye a cikin wannan yanayin ta qaraso bakin gate yadda yake tun jiya haka yake wato hakan ya nuna musa be fito ba tun jiya daya shiga kenan sai yanzu ta tuna abinda ya faru nan ma dariyar ta kuma yi taso leqa musa amma sai ta tsinkayi horn din motar makarantar su dan haka da sauri ta fita ta shiga suka wuce

****

ni fa gaskiya bazan iya ba wlh wannan jaraba har ina yarinya kamar 'yar shedan na fuskanci wata rana in tana gidan nan saita sa anzo an dau gawar mu daga Aljanu sai shaidanu duk sun cika mana gida nidai wlh asan yadda za'ayi

tunda ta fara maganar yake kallonta harta gaji tayi shuru

dan jim yayi kafin yace to yanzu ya kk so ayi korarta zanyi ko kuma me?

bance dole ka koreta ba amma ta koma gidan naseer tunda ai ba kai kadai bane dan uwanta

kina ganin komawarta can din shine mafita ? kada fa ki manta gida daya muke kuma ina son ki fuskanci wani abu game da yarinyar na fuskanci duk abinda ta lura mutum baya so to shi tafi yi yanzu kinga ai shi naseer be nuna mata abinda nake nuna mata kamar dana nuna bana son zamanta a nan amma kinga ai nan din ta dawo so inaga mafita daya ce mu lallaba ta har a hankali zansa ta bar gidan amma ki duba fa yadda taketa samu yin accident muna daga gida wuta bazata bi da khadija ba sai dai ruwa ruwan ma na sanyi dan ya zuwa yanzu na fuskanci yarinyar batada hankali

shiru tayi tana nazarin maganar sa zuwa can cikin sanyin murya da marairaicewa tace amma honey ni ba zaman nata ba kaga fa cousins kuke da ita ina jin tsoron kayi mata wani kallo ba matsayin qanwa ba

siririn tsaki yaja tare da fadin kinji matsalarki ai ke kishi yanzu ke ni me zanyi da wannan figigiyar yarinyar kamar kazar mayu wadda inda nayi auren wuri dana haifeta ko ke kanki kin san inda kinyi aure on time da yanzu kinada kamarta dan haka ban son shirmen banza mafita muke nema yanzu bana son shashanci

shikenan zanyi kokarin danne zuciyata amma pls cikin qanqanin lokaci mu san abinyi tabar gidan nan

insha Allah dan na fiki matsuwa da hakan

ah ah wlh nafika

eh to yanzu kam kin fini tunda dubi yadda aka haramta miki sa jambakin safe ba ya qarasa maganar yana kunshe dariya

ganin yadda ta kalli madubi ta bata rai yasa shi matsowa kusa da ita ya fara aikin rarrashi

******

koda dije ta dawo daga makaranta direct part din yusra ta nufa ita kadai ta iske zaune a falo tana kallo harga Allah batayi murnar ganin dije ba duk da zaman kadaicin ya dameta dan me gidan ya fita masallaci ita kuma sajida batada wani sakewar fuska inba gaban mijinta ba nan fa sbd kissa kamar ta hadiyeka amma da zarar an barku ku kadai zata cukule dan haka bata fiya shiga inda take ba yake kawai take yiwa dije bayan ta zauna ta gaisheta

suna a haka dije ta miqe tace bari ta koma part din sajida har bakin kofa yusrah ta rakota ita ko dije abin ma mamaki yake bata ganin yadda inta je guri tace zata tafi ake murnar tafiyarta fiye da murnar zuwanta

koda ta shiga falon da sallama dauke a bakinta ta iske sajida zaune ita da wata mata da yara biyu cikin sakin fuska suka amsa mata su duka

qarasawa tayi harda dan rissinawa ta gaida matar ta amsa mata cike da fara'a nan ta juya ta gaida sajida itama da fara'a a fuskarta ta amsa mata karo na farko kenan a zamanta a gidan

shigewa tayi daki tana zuwa ta cire kagan makaranta ta shiga toilet danyin wanka da alwalawa dan gabatar da sallah

tana shiga Amina ta kalli sajida tace Amarya wannan qanwarki ce halan na ganta kyakkyawa da ita masha Allah ga hankali

murmushi sajida tayi a ranta tace me hankali a gwiwa dai amma a zahiri tace eh qanwata ce tunda qanwar oga ce

kai gaskiya na gaba da hankalinta wlh anan take da zama kenan?

eh sajida ta fada a takaice

suna tsaka da haka dije ta fito sanye da doguwar riga ta atamfa kanta ko dankwali babu ta qaraso gurinsu tana hamma tare da fadin Aunty wlh yunwa nakeji

kije ga abinci can saman dinning tayi mata nuni da hannu

juyawa dije tayi a ranta tana yaba acting irin na sajida wato dan taga bakuwa shine take nuna kamar ba komai tsakaninsu hmmm to bari itama ta biye mata gara taci ta koshi kafin ta fuskanci qalu balen gaba

tana tsaka da cin abinci su habeeb suka shigo su dua ukun habeeb,naseer,sai doctor yusif suna shigowa suka zauna naseer ya cire waya ya kira yusrah ba jimawa kuwa saigata tazo nan fa aka shiga hirar yaushe gamo itakam dije saida ta tabbatar ta koshi kafin ta qaraso falon ta shiga gaishesu dukansu suka amsa cikin sakin fuska

juyawa tayi taja yaran sukayi cikin dakinta ta shiga yi musu wasa

sai da akayi sallar la'asar kafin su yusuf suka fara shirin tafiya suna harrakawa dije ta gito da yaran

kallonta doctor yusif yayi kafin yace Auntyn yara kun gaji da wasan kenan da har muna shirin bar miki su

murmushi tayi kafin tace to ai ni koda an barmin ina so wlh

to tunda kina so ki bisu gidansu kiyi kwana biyu cewar sajida aikuwa Amina tayi caraf tace wlh kuwa da naji dadi dan dama in Abban Anwar ya fita rasa 'yan hira nakeyi kinga sai kiyi mana weekend ko sister

me zai hana ai ko cewa kk yi ta dinga zuwa duk week tana muku weekend bakuda matsala dan haka ke jeki shirya ki zo ku tafi cewar habeeb

mamaki ne ya cika zuciyar dije ganin yadda ake ta tallarta dan haka saita maxe tayi kamar bata ji su ba

naseer ne me fadin ai khadija batada matsala akwai dadin zama dan haka Allah ya taimaka

haka sukaita tunzura har saida Amina ta dameta ta dauko kayanta kala biyu ita kam taga ikon Allah yau

koda suka zo shiga mota har rige rigen bude mata mazan da matan keyi koda ta shiga ta zauna da sauri suka rufe ji kk yi bammmm ita abin nasu ma dariya ya fara bata

dan haka saita bude motar da niyyar fitowa

cikin hada baki suka tambaye ta

ina zaki kuma?

kallonsu tayi daya bayan daya kafin tace mantuwa nayi zan koma in dauko

da sauri habeeb yace wa sajida matso ta fada miki abinda zaki dauko mata basaita fito ba idanma yana nesa ne to ki fada mata sai ta dauko akwatin in kin dauka saita mayar kada ki samu damuwa 'yar qanwarmu..........

*Allah ya raka taki gona dije* πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ€£πŸ€£

*Alkalamin khady* ✍
[3/15, 6:30 PM] El~hajj: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

*TA ME GARI*

NA
khadija usman

2⃣5⃣

ita dije abinma dariya yabata ganin da gaske sukeyi yasata fadin

ah ah a barshi ma nafasa daukar

yauwa 'yar albarka kuje kawai yusuf Allah ya kiyaye sai munyi waya cewar habeeb

shikam yusuf dariya yaketa yi ciki ciki dan yasan wannan tunkuda dijen da sukeyi wlh ba banza ba

haka yaja motar sa suka fita mutan gidan nata daga musu hannu kamar dangi sunzo rakiyar mutum zashi saudiya🀣

suna ganin sun fice a gidan duka suka ce Alhmdllh Allah ya raka taki gona

ameen inji matan nan kowa yayi nasa wuri da matarsa

******

saida ya biya ya dan yi musu siyayya kafin suka wuce gidan

ba karamin mamaki dije tayi ba ganin haduwa da tsari irin na gidan doctor yusuf lamarin bai qara rikitata ba saida suka shiga palon gidan gaskiya masha Allah ya hadu iya haduwa

suna shiga ita da yaran suka qarasa saman kujerar suna tsalle ita kuma ta qarasa a hanki ta zame qasa dan ta zauna yayin da taga doctor yusuf yayi wuf ya shige daki tare da ledar daya yo musu siyayyar da ita yana shigewa kuwa ta tsinkayi muryar wata dattijuwa na fadin

to to andawo jaraba ta dawo da yau bakina shuru gidan tsit na yi bacci na cike da annushuwa da mafarki me dadi amma yanzu daga dawowarku har kun ajiye shaida ina shi yusuf din yake naga duk na ganku amma shi ban ganshi ba ince dai ba wani abun ya siyo kuka munafunce ni aka shige dashi ciki ba ko?

ikon Allah cewar dije data tsaya tana kallon sababi

jin dije tace ikon Allah yasata juyawa gurin sai yanzu ta lura da ita

to ita kuma wannan sadakan yallan daga ina iyayen kwashe kwashe?

yusuf ne ya fito cikin fara'a yace qanwar su habeeb ce ta zo mana weekend

washe baki tayi tare da fadin ah ah Allah sarki nako ga kama kamar an tsaga kara kice ke 'yar gida ce ai na dauka kina daya daga cikin irin kare arzikinka ta fada tana me wurgawa Amina harara

Amina wadda idan da sabo ya zuwa yanzu ta saba da halin hajiya hauwa dan haka ta qara dukar dakai sbd bata son tayi wani motsin kirki yanzu a qarewa iyayenta sababben zagin yau da kullum tun da ta auri yusuf take cikin wannan halin da hajiya hauwa wadda mahaifiya ce ga yusuf din a cewarta bata so ya auri 'yar talaka ba wadda zasu qarar da arzikinsa gara ya auri 'yar masu kudi to da yake da rabo gashi harda yara biyu

haka kawai ta tattara kayanta ta dawo gidan da zama kullum bata bacci har sai taga shigowar yusuf kuma ta tabbatar be shigo da komai ba da kanta take kulle qofar falon ta rike key din a gurinta da asuba ta zo ta bude wai duk

14 / 33