Author : Asma Baffa Category : Romance
falon a take zuciyar dije ta shiga lugude a ranta tace kinga dije ko ba komai sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma wadannan kitika kitikan da suka koshi da madara gasu nan kamar shanu ki lababa ki tsere to ai kuma sun rufe kofa ya kenan
lura da sukayi dije kamar ta tsorata yasa su kara kaimin nufota tare da narka mata na maguzawa
dakewa dije tayi amma jikinta da zuciyarta kamar sa fado kasa dan rawa ko kafin mimi ta karaso tace mata kinga balama dakata nifa ba koriyar ciyawar da kk saba ci bace naga kin nufoni gadan gadan kina tande baki dabbar mayu
ai bata karasa ba taji saukar wani shu'umin marin data rasa daga ina yazo bata gama tantancewa ba ta fulanin ta motsa jin ana neman sata jinyar dole aikuwa tayi kan mimi a sukwane cikin sa'a kuwa ta dami gashin kanta dayake kalba ce akayi mata da Attact iya qarfinta ta rike tare da cizgawa
wata kara mimi ta saki wadda tasa su kausar nufo dije da dukkan karfinta ta tunkuda mimi da kanta ya daki karamin center table din dake gurin aikuwa take kai ya fashe ganin jini yasa ta sakin wata karar a karo na biyu
kausar na ganin hakan tayo cikin dije yayin da humaira tayi gurin mimi data bare baki tana kuka tare da shafo jinin a hannunta wanda wannan shine karo na farko a rayuwarta data taba jin ciwo da jini haka
tattaro dukkan karfinta tayi itama suka kacame aikuwa nan dije ta nuna ita rainon kauye ce dan kuwa tuni ta samu lagon kausar kasancewar ita basu saba da irin wadan nan wahalhalunba da iyakar karfinta dije ta kama nonon kausar ta murde itama karar tayi nan ta shiga neman hanyar kwatar kai amma ina dije dan mugunta harda cije lebe takeyi jin da kausar tayi dije na shirin kasheta kuma ba mafita yasata gartsawa dije cizo a hannu ai kuwa jin zafin cizon yasa dije qara himma bata san lokacin data gwara kan kausar da plasman dake manne jikin t.v stand ba ji kakeyi kwararats ta sheqo kasa ta tsage
nan fa ihu ya hadu biyu ita kanta dijen daba damar kukan ne da tayi dan ta dan sha jiki su kuwa duk sun bude baki suna ihu humaira dataga abinda ya faru da wadanda suka fita tsageranci ai take jikinta ya hau bari dan dama duk burga ce sun fita kwaliti
sai yanzu hankalinta yakai ga bugun kofar da akeyi haggu da dama ma'ana dakin sajida da kuma kofar falon
duk ta rude ta rasa inda zata nufa ga ihun wadan nan na kwancen ita kuma dije tayi mata zuru masifa na cinta jira takeyi tasamu nama kawai
yanayinta ya kara tsorata humaira duk da tabi ta rude aikuwa nan ta fara kokarin guduwa dije ta rufa mata baya
tana fadin ai ba inda zaki dan uwarki yau ko ni ko ku badai kunce sai anyi yakin badar yau a gidan nan ba to sai munga karshen shi muga wakeda nasara nan ta yi cikinta da himma ganin hakan yasa humaira daukar duk wani abu data gani ta jefawa dije ita kuma tana gocewa wani yaje yasamu frame din dake manne a falon sai dai kaji rassss sun sheqo kasa
au to ai sai ki fadamin zakka kk son ku fitar shiyasa zakuyi mana barna a gidan duk da ban san nawa kk fasawa ba yayana ya siya ko ku kuka kawo 'yar uwarku dashi to bari na tayaki nan fa ta nufi dinning duk coolers din dake kai sai da ta dinga saita humaira dasu tana jifanta aikuwa kan kace me falo ya kacame da yayi kaca kaca
cikin zafi humaira tayo cikin dije bisa ga shawarar zuciyarta data bata akan cewa ta ci uban dije kawai yadda take lange langen nan suma su kausar rashin zuciyane yasa haka aikuwa tana zuwa dije tayi mata na 'yan wristelling ta kai mata wani wawan naushi amma fa bada hannunta ba da ludayin miyar da ita kanta humaira bata lura dashi ba ba shiri baki yayi tsartuwa aikuwa nan dije bata bata wata damar kuka ba sbd mugunta duk inda tasan saitin kashi ne saita buga harda goshi duk inda ta buga sai dai kaji yace kwalll ai kuwa saita saki dariya sbd zalunci gwiwar ta saita ta bada kwalll ai kuwa humaira ta bude dukkan muryarta tana ihu tana kiran wayyooo Aunty ki zo ki taimakemu wai bakuda imani ne bamai taimakon mu a hannun kinfi 'yan boko haram rashin imani ta fada tana me qara rushewa da kuka itako dije dariya ta shiga tana fadin muje zuwa mana ai yanzu aka fara ni yaseen ko rabin gajiya ban tashi yiba kawai muci gaba da kaftawa yau nayi muku alqawarin sai kunga kalar mazgar da baku taba gani ba
sajida da hankalinta ke mugun tashe ta kira habeeb yace mata yana kan hanya amma shuru gashi sai ihun 'yan uwanta take jiyowa wanda take addu'ar Allah yasa yarinyar bada mutanenta ta hada su ba suke caskala su dan tasan ita da an tabata sai sun kawo ziyara ita fargabarta ma abin ya tsaya iya wadanda suka jawo kar su ce a gidan zasu kwana yau an taba musu hantar su layin habeeb ta kuma kira nan ya shaida mata gashi nan shida naseer sun kusa zuwa tunawa tayi da spare keys din dake cikin lokarta nan ta shiga dubawa ta dauko na dakinta ta bude amma sai me ? sam takasa fitowa illah ziro kai datayi kadan batare da sun lura ba nan ta hango su kwance sunata wai wai tare da reto da jiki kamar suna takaraa makarantar allo ga dije nan kamar uwarsu tasa sun kama bakinsu da hannunsu amma fuskar nan tasu a kwabe sunata digar hawayen azaba
jin ana buga kofar ne sosai yasa sajida fitowa da kyar ta nufi kofar kamar ta tashi sama dan karma dije ta ankare da ita dan ita masifar yarinyar tsoro yake bata
dije ko tana lura da ita ta shareta dan ita kanta ta matsu a zo a rabata da wadannan kartin banzan a cewarta da bataga amfaninsu ba inda itace kamarsu ai aikin soja zata shiga dan jikinsu kalar wannan aikin ne amma sai gashi taga alama ko aikin office ma ba alamunsa anan
koda ta qarasa ta bude kofar taga ba key jiki dole ba yadda zatayi ta juyo falon kamar tasan yadda akayi nan ta shiga duba kan kujera ko kala batace ba kamar munafuka sim sim ta ganshi ta dauka ta bude kofar su ukune tsaye habeeb naseer da yusrah sai musa dake tsaye daga can bayansu wanda da za'ace arrrr yanzu zai sheka dan ya kudirarwa ransa baxai kuma shiga gidan nan ba matukar yaji ana sautin neman taimako
da sauri suka shigo inda sukayi cirko cirko ganin su mimi zaune suna reto da kawuna ga ciwuka ga falo daya hadu ya hade wadda ita kanta sajida sai yanzu ta lura da barnar da akayi
ya Allah habeeb ya fada kafin ya kalle su cikin bacin rai yace kaii uban mu ya faru haka naganku kamar kunyi Accident dubi yadda kuka mayarmin gida tamkar na mahaukata anya kunada hankali kuwa?
sai yanzu suka farga da shigowar su aikuwa da sauri suka rarrafa suka bude baki cikin kuka kausar tace wlh yaya ku gaggauta fita da wannan yarinyar a gidan nan dan wlh batada hankali wlh bakaken aljanu gareta da alama sannan suna sata hauka wlh yaya zata iya kashe ku wata rana
cikin rawar murya yusra tace to ku wane tsautsayi yakaiku fada da ita kuma ke Aunty sajida ai laifinki ne meyasa baki sanar dasu fada da aljani ba dadi
cikin bacin rai tace su basuda hankali ai daka fara fada ka kalli fuskar wanda kk yi dashi kasani in mutum ne in ma aljani ne kuma nace musu baruwana suka ki ji gashi ban sunjawa kansu ai an zuqe musu jini dan da ganin yadda suke yanzu sai an musu karin jini
to ku meya kaiku taba da transfomer ana ruwan sama ?cewar naseer
wlh kaddara kasan ance me rabon shan duka bayajin kwaba ni babban takai cina na ji yadda aka sauyanin halitta duk da ban kalli madubi ba amma dana shafa goshina wlh naji kamar ma ba fuskata ba dan sai naji kamar ta Dila
wlh in kince dila kinyiwa kanki zabe me kyau bakiga yadda kika koma ba sai kace fukar bahaguwar bakar rakuma cewar naseer daya fada yana kunshe dariyarsa
wayyo ni na shiga uku wayyo Allah yanzu ni dan banida gata babu wanda ya duba yadda nake ba wanda ya saurareni sai 'yan uwanku kuke ta tasu cewar dije data dora hannu aka ta baje baki tana ihu
wadda ihunta yayi dai dai da shigowar mamy wadda tashigo a sukwane jin ihun sakamakon kiranta da yusrah tayi a waya cikin tashin hankali lokacin da basu san abinda ke faruwa ba sai ihu da sukaji..........
*vote*
*comments*
*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 11:07 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*TAME GARI*
NA
khadija usman
3⃣1⃣
Ah ah wlh basai kin fasa ba ki tafi kawai duk lokacin da muka so ganinki ma zo ko? suka tambayi matan
eh wlh Allah ya tsare ya kiyaye hanya
Ameen ta fada jiki a sanyaye kamar wadda kwai ya fashewa taja qafa tana tafe tana waiwayensu mamy kuwa nata raka su da harara saitayi tafiya kadan sai ta tsaya su kuma sai kaji sunce ya akayi ?
saita ce kewar ku ce wlh ji nakeyi kamar in fasa tafiyar san ba yadda zanyi ne
aikuwa dole ki tafi tunda mamy ta bukaci hakan dan ba yadda za'ayi ta yanke hukunci ki ketare cewar habeeb
to banda abinka yaya ai bafa cewa nayi bazan je ba cewa fa nayi ina jin kewarku kamar in fasa tafiya
ke ni dayalla wuce muje kun tsayamin surutun banza cewar mamy dije na ji tana gani aka nausa mota aka nufi gidan daddy
*welcome back home dijeee*
*******
ba karamin jin dadi basira tayi na ganin dije ba aikuwa nan aka shiga hirar yaushe gamo danma jikin dije yayi tsami tana bukatar hutu dan haka bakin a mace yake
tun asubar fari mamy ta iso dakin dasu dije suke tace dije ta fito ita zatayi aikin gidan nan yanzu
ga mamakin mamy sai gani tayi dije tayi tsalle tare da fadin Allahu akhbar
kallonta tayi ta dan ja baya tare da fadin ke dan ubanki meye na jamin farkon kalmar kiran sallah ?
wallahi farin ciki ne mamy kai kedai Allah ya biyaki yayi miki duk abinda kk da niyyar yimin
ba amin ba dan ubanki kajimin shegiyar yarinya da muguwar addu'a ke kin san me nake shirin yi miki ne?
ai shiyasa kema na roka miki irinshi bari dai kawai kiga yadda za'ayi gara in fara aikin nan da wuri kar in makara dan ni yau ina cikin farin ciki yau zamu gama exam dinmu ma'ana yau zamuyi candy kinga ko yau ranar farin ciki ce
murmushin mugunta mamy tayi a ranta tace Alhmdllh wato yau kuke da last paper zako kici ubanki basai kin je ba naga ta inda zaki bi ki bar gidan nan
kamar dije ta shiga zuciyarta tasan me take ayyanawa sai ji mamy tayi dije tace ni dai bari nayi ayyukan da aka sani tun wuri dan kar aimin sagegeduwar zuwa
kafin mamy tayi wata magana har dije tahau karkade kujerun falon
kwafa tayi ta shige dakinta dan komawa bacci dan dama tsabar tijarar data sawa ranta ne yasata tashin asuba yau dan daddy baya nan amma data tuna yau saita kuntatawa yarinyar saita nemi guri ta zauna tana jiran dijen ta gama tazo ta fada mata nan ta cicci uwarta ta hanata kuma zuwa makarantar
tana shigewa dije tayi wurgi da filon kujerar ta kama dariya tare da rike kugu a fili tace lallai ma mamy yadda nazo birni nasaba da rayuwar hutu iya dan zaman da nayi na waye ta yaya kike tunanin zan maida kaina irin aikatau to miye ribar zamana a birnin kenan to ba abinda zanyi iyakata dake idan banyi ba ki narkeni ko ki zagi iyayena kin dade bakiyi duka biyun ba ni jikin nan ya saba da wahala dan haka a kafta kawai ta fada tana me shigewa dakinsu tana zuwa wanka tayi tare da shiryawa cikin sauri sauri tana gamawa ta nufi kitchen gun baseera dake kokarin hada abin kari ganin bata gama ba yasa dije ta sungumi katon biredi tare da exotic tasa a jaka ta fita da sauri tana fadin saita dawo a sukwane ta fice a falon ta nufi dakin su habu driver da suke dan baccin safe nan ta tasheshi yayi mamaki ganin ta shirya da wuri yau dan duka time din 6:47am
hajiya yau da wuri zamu fita kenan kowa yasan kin dawo
eh kasan da ai nasaba bi makwabta ina gaishesu to shine naga a da din ina makara shine nace yanzu bari in dinga sammako ko zan gama da wuri yau ta karasa maganar tana harararsa
ganin hakan da yayi yasa shi gane baka ta fada mishi dan haka ba shiri ya mike ya fito da mota ta shige suka tafi
shuru shuru mamy ta gaji dan haka ta fito tana fitowa kuwa taga falon yadda ta barshi cike da mamaki da bacin rai ta nufi dakin amma taga wayam kitchen ta nufa tana zuwa kuwa taga basira ita kadai nan ta shiga tambayarta dije ta sanar mata ta tafi makaranta wata uwar ashar ta narka kafin ta shiga bala'i da fadin in dije ta dawo saita ci ubanta badan ma tana son ta koya mata darasin da ko wani taji yace zaizo birni saita hanashi ba to da yau saita kadata kauye uban kowa ya huta amma yanzun ma zataci ubanta ne.
***
a makaranta kuwa dije sun fito exam inda daukaki daliban ke farin ciki da murnar kammala karatun su na secondry kasancewar makarantar yaran masu kudi ne yawanci dan haka wasu dayawa a cikinsu sun hada party hakama malaman sun hada musu party wanda sam dije ta ma manta da batun ga daddy baida masaniyar hakan shima ganin da dije tayi anata shirye shirye dan harda iyayen yara yasa ta kalli rufaida cikin marairaice fuska kamar zatayi kuka tace
ni fa besty banyi shirin komai ba wlh ko daddy ban fadawa ba gashi kuma kin san shi kadai ne zai iya zomin kuma ko wasu kaya ban zo dasu ba wlh sharp na manta wlh gashi na dana bom a gida bare in koma in dauko kaya yanzu ya zanyi kenan?
kinga kwantar da hankalinki ki kira daddy ki fada masa kawai batun kaya kuma ai har yanzu da sauran time abinda sai after 4 za'a fara yanzu kuma 12 fa muje gida cikin kayana ki duba inda wanda yayi miki saiki sa tunda kinga ba anko mukayi ba bare ace za'a samu matsala ko ?
eh kuma hakane ngd nan tasa hannu ta dauko wayarta dake cikin aljihun wandonta ta shiga kiran daddy
yana dagawa taji yace
ina taya 'yata murnar kammala karatunta na matakin secondry
dariya tayi tare da fadin nagode daddy ashe kanada labari?
eh principal dinku ta sanar dani kuma sunyi min text suna invite dina zuwa bikin graduation din da za'ayi to bazan samu zuwa ba amma na kira yayyenki nace cikinsu wanda yasami dama yazo miki amma nikam ayimun uzuri kinji ko 'yar daddy
cike da farin ciki ta amsa da bakomai inda suna qare wayar suka nufi gidansu rufaida a can suka gama shirinsu sai 4:15pm sannan suka iso gurin inda suka iske an fara gabatar da abinda ya tara
iya kyau 'yammatan sunyi kyau yayin da aka fara gabatar da sunayen hazikan dalibi inda aka shiga kiran sunayensu tare da basu kyaututtuka a fannin boko da arabic kiran da akayiwa dije ne yasa na farga da mutanen dake wurin
inda ita bata ko lura ba tasa kai ta isa gurin itace daliba mafi kokari da kwazo a makarantar duk iya shege da kiriniya irin nata akwai kokari hakan yasa tasamu kyaututtukan da ita kanta tayi mamaki
mamaki ne yakamata hango habeeb datayi kame kan kujera ya zuba mata ido inda bayan an sallameta ta fito da niyyar wucewa idonta ya sauka kan naseer dake can gefe shima da alama ma besan da zuwan habeeb gurin ba tabe baki tayi a ranta tace nasan dan daddy kuka zo anyi muku dole amma bari na qarasa in gaishesu dan na lura iya kwana dayan da nayi bana gidan su har wata kiba sunyi
*nayi ne kawai dan in faranta muku amma raina bace yake so kuyi hakuri da wannan kuma*
*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 11:10 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*TAME GARI*
NA
khadija usman
3⃣2⃣
da fara'arta ta karasa inda naseer ke zaune wanda tun kafin ta karaso ya shiga sakar mata murmushin daya bata mamaki domin dai tasan wannan murmushin na murnar ta bar musu gidan su ne
tana zuwa ta shiga gaisheshi inda ya amsa tare da fadin ina taya qanwata murnar kammala karatunta matakin na farko
nagode yayana ta fada tare da cewa ina su Aunty yusra fatan tana lfy ?
lafiya kalau tace a gaisheki tana miki murna
nagode sosai ina amsawa
shiru yayi kafin daga baya yace ashe dai qanwar tamu tanada kokari har haka kice za'a je dake
murmushi tayi batare da tace komai ba shima shirun yayi ganin haka yasa dije tace bari taje zasuyi pic da kawayenta da malamai nan ta juya ta barshi a gurin yabi bayanta da kallo
yana hangota cikin kawayenta sunata pic da kuma malamai a haka aka gama komai kowa ya watse amma daga naseer har habeeb ba wanda yasan d'an uwansa ya ziyarci gurin sai dab da magariba sannan kowa ya watse su dije gidan su rufaida suka wuce inda saida dije tayi sallah harda yin wanka kafin taci abinci sai wajen karfe takwas ta tafi gida da sanda ta shiga cikin sa'a ba kowa a falon dan haka direct dakinsu ta wuce ta ajiye kayan data shigo dasu nan suka dan taba hira dan ta gaji dayawa ba dadewa bacci ya kwasheta
********************
sannu sannu su dije sun dan kwana biyu da kare