Author : Asma Baffa Category : Romance
suka shigo garin abuja ta zuro kai ta glass tana leke kamar zata fado yayin da malam keta murmushi yana tsokanarta ita kota kansa bata bi ba kallonta kawai takeyi sukuwa mazaje bakin ciki kamar ya kashe su da gayya nasir ya qara daga glass ai kuwa saida dije tayi kara dasauri malam yace lfy ?
bakomai baba malam bari zan rama
zaki rama me?
kai dai ka bari kawai kasan bana cin bashi ba'acin nawa dole in anci nawa sai an biya
toh Allah ya kyauta
Ameen
sun karaso gidan Alhaji khamis aljannar duniya inda cikin sa'a suka riskeshi kuwa ba karamin farin ciki yayi ba ganin dan tsohonshi a gidanshi kasancewar matar gidan ta fita shiyasa basu sameta ba nan bada bata lokaci ba me gari ya sanar da dansa komai da dalilin kawo dije kwarai ya nuna jin dadinsa inda nan take me gari ya nuna baxai kwana bazai koma dole aka sa drivrr ya mayar dashi ranar
******* me aikin gidan Alhaji ya kira ya ce tasa dije tayi wanka sannan ta bata abinci kafin hajiya ta dawo
koda hajiya ta dawo ba karamar rigima aka kwasa ba dan saida Alhaji yayi mata jan ido kafin ta yadda da zaman dije a gidan
kuyi managed
yanzu aka fara zaman dije a binni yafi na kauye cakwakiya
[16/12, 11:40] +234 806 493 3819: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀
TA ME GARI
NA
KHADEEJA USMAN
8⃣
bana karanta littafin kowa a yanzu bayan *FAHIMTA,KUKAN KURCIYA,ZAINABU
Sune littatafan danake karantawa a halin yanzu dan haka ina son ayimin adalci koda anji labarina yayi kama da na wasu littafan da ake rubutawa yanzu dan Allah ina son ayimin adalci domin wlh nawa sakon danake son isarwa daban ko kadan bazan saci fasahar wasu ba zanyi amfani da tawa basirar da Allah yabani sbd da haka ina rokonku daku tayani da Addu'ar Allah yabani ikon faranta muku masoya ta me gari
wannan shafin nakine 'yar uwa rabin jiki fadimatuzzahra'u (mamy)fateema maman fateema (ihsan)ina sonki da kewarki
*************
me kika ce ya fada tare da kara kamo kunnenta ya murda da qarfi
qara tasaki tare da matso kwallar wahala cikin kuka tace
wlh bance komai ba
shegiya aljana aike sunan daya kamata asa miki kenan me siffar 'yan ruwa ya cikata tare da fadin bacema mutane da gani
kamar jira take kuwa ta kwashi jakarta ta zura da gudu tayi cikin gida
doctor yusif ne ya kalle shi tare da fadin wai kai man wane irin mugu ne ?
kawai kasa yarinya a gaba sai wahalar da ita kukeyi sai kace ba qanwarku ba haba dan Allah hakan ba kyau zaisa ta raina ku ai
kallon gefen ido habeeb yayi musu wanda shi tunda aka fara abun ma baice qala ba dan shi duniya babu abinda ya tsana irin yarinyar shiyasa ko zancenta baya son ayi
ganin irin diban dayakeyi masa ne yasashi fadin kai kuma meye ka tsare mutane da idonka irin na aljanun ainihi
hmmm kawai yace tare da maida kansa zuwa abinda yakeyi
naseer ne yace da kasan abinda yarinyar nan tayi mana wlh da kokai inta gaisheka baza ka ko kalleta ba bare ka amsa
toh me tayi muku har haka kuna ganin ta 'yar karama da ita ta yaya har zatay muku wanni abinda zaisa ku takurata haka
umm kai kake mata kallon qarama shegiyar me rai ce da kk ganinta nan ya kwashe komai na zuwansu kauye ya fada masa
yusuf dan dariya har da fadawo daga saman kujerar dayake kai yayi inda duka su biyun suka kulu habeeb tashi kawai yayi yabar gurin ya shige cikin gida shi ko naseer qumewa yayi yai banza da yusuf yanaji yanata mai magana ya kyaleshi dan haka ya mike yayi masa sallama yace ya tafi da harara ya rakashi yana fadin inka tafi kada ka dawo wata dariyar ya kumayi tare da fadin dole ai in dawo bil adama.
*******
tana shiga gidan direct dakin su ta wuce ta wurgar da jakar tare da cire hijabin ta zauna gefen katifa tana sharar kwalla tabbas yaxamar mata wajibi tabar gidan nan don me zata zauna aita cin zalinta kullum sai an sami wanda zaiyi mata wata muguntar indai anga taji dadi toh fa daddy na nan dan shine kawai ke nuna mata tsantsar soyayya da kulawa a cewarsa yaji dadin bashi ita da baba malam yayi sbd bashida diya mace toh itafa iyayenta ita kadai suka haifa yanzu tasan suna can suna kewarta kamar yadda take kewarsu wasu hawayen ne suka qara biyo kuncinta domin tunawa da tayi da yanzu suna can suna fama ita da innah akan rikicinta tana cikin haka baseera ta shigo dakin dauke da flate shake da jellop rice da pure water dan shine ruwansu da hajiya tace su dinga sha yanzu yanzu ma ta hango shigowar dijen ne ta windon kicin shiyasa ta biyota da abincin dan ita dai Allah ya jarabceta da son yarinyar nan ganinta da tayi tana kuka yasata qarasawa kusa da ita tana tambayarta lfy khadija?
fadawa tayi jikinta tare da fadin nagaji Anty gida nake son komawa ina son ganin innata nagaji da zama da muguntar da akeyimin a gidan nan babu gurin wanda nake jin dadi daga gurinki saina gurin daddy in yana gari ni gara nakoma kauye yafimin akan zaman nan din yanzu na tsani birnin bana so
hannu tasa ta share mata hawaye tare da fadin ah ah kadeeja dena kuka mana kin manta ke kika cemin so kikeyi kiyi karatu kizama lawyer ki dinga taimakon mutane da iyayenki ba?ke fa kika cemin so kikeyi innarki da baffanki su dawo birni ki gina musu katon gida innarki ta dena daka baffa yabar zuwa gona kenan kin fasa?haba dijangala ta me gari kin san dai bayan wuya se dadi wata rana se labari duk irin cin zalinki da sukeyi wata rana zasu dena ke da zaki girma ki zama hajiya ga gida ga babbar mota ku biyo layi keda me garinki kinsa shi a gaba eye kuma ma idan kince zaki tafi ni ki barni dawa?ai kafata kafarki domin ni dake yanzu mutu ka raba dan haka bana son in kara jin kin sami damuwa akan mutannan kiyi haquri kinji duk me haquri natare da riba tashi maza kici abincinki kada ya huce
maganganun basira sunyi tasiri a zuciyar dije shiyasa ta dan kwantar da hankalinta amma fa wlh ta quduri aniyar duk wanda yayi mata saita rama bakomai zata haqura ba
abincin taci kafin ta tashi tayi wanka inda basira keta bata labaran ban dariya har ta warware gaba daya
*******
haka rayuwa taci gaba da tafiya yayin da dije keta fuskantar muzgunawa itako tanata musu kalolin mugunta amma har yanzu basu dagota ba duk da ya zuwa yanzu ta qara girma kyanta na fulanin asali yaqara bayyana yayin da makerin budurci na nan na kera dije yayin data hadu da qawaye 'ya'yan masu kudi 'yan gayu duk a gunsu take koyar duk wani abu first class yanzu batada aiki sai karatu koda yaushe tana daki ko kicin tana taya baseera aiki sam dijen yanzu ta canza babu wata hayaniya taxama so cool ba yawan surutu su kansu mutan gidan wuyar haduwa sukeyi kasancewar batada amfani a wajensu yasa basu wani damu da rashin ganinta ba ya zuwa yanzu me gari yazo yakai sau hudu kuma ganinta dayakeyi ta canza yasashi jin dadi da kwanciyar hankalin qara barinta gidan kawun nata
******
a dai dai wannan lokacin ana shirye shiryen auran matasan gidan yayin da naseer zai auri yusrah 'yar qanwar mamy shi kuma habeeb zai auri sajida diyar abokin daddy ce babanta ambasserddor ne sajida yarinya ce fist class maqura ce gurin wayewa tanada ilimi sosai amma bata aiki kusan sa'ar habeeb ce dan da kadan ya girme mata amma kasancewar shi namiji ne me son classic lady kuma dayake batada wani girman jiki shiyasa yaji ya kamu da sonta inda suke zuba soyayya ta bugawa a jarida
yau bikin saura sati uku anata hidimar gyara gidan shiyasa kowa yake busy yusrah kam a gidan mamy take domin mahaifiyarta sun rabu da mahaifinta tun tana qarama maman ta kuma wani auren amma a saudiyya suke zaune da mijin kuma mahaifin yusrah ya hanata 'yarsa gashi kuma matar dayake aure batada kirki hakan yasa yusrah gudowa gidan mamy inda kusan nan ta qarasa girmanta
******
yusrah ce zaune da kawayenta a main parlor suna ta tsara yadda hidimar bikin zai kasance
dije ce ta fito sanye da riga da wando indian design kanta babu dankwali sai yalolon gashinta da bashida cika sai matuqar tsawo datasa band ta kama shi ta kuma tufke jelar tayi gammo da ita tun zuwan daddy wancan lokacin ta karbi kudi a gurinsa ta siyo kayan sawa masu kyau da tsada dan ya fada mata komai take so ta tambayeshi kada taji tsoro shiyasa yanzu batada matsala da duk wasu kayan kyale kyale ga qawarta rufaida Aliyu na sayo masu sosai dan itama yarinyar akwai son daukar wanka kuma babanta yanada kudi sosai gashi tanada yayye maza itace kuma auta shiyasa take fantamawa
kitchen ta nufa domin dauko ruwa dan ya zuwa yanzu ta sauqaqawa kanta shan pure water itama faro take sha kamar kowa na gidan
tana daf da shiga ta ji yusra tace keeeee
da kamar ta share sai kuma taga be dace ba dan tasan da ita take dan haka saita tsaya tare da juyowa ta kura mata idanunta masu kama dana mejin bacci
wata kawar yusra ce wow yusrah ina kuka samu wannan kyakkyawar baturiya zance ko balarabiya ne ma oho
me aikin mu ce
me aiki?
kalisat ta tambaya tare da juya lamarin son kudi irin na iyayen yarinyar wannan a yanzu ai jari ce ko tace kadara amma fa hadari ce ga duk gidan da sukayi gangancin daukarta aiki yanzu a ganinta bazata wuce shekara sha bakwai amma dubi yadda take ina ga takai ashirin kuma yusrah ce ta katse mata tunaninta ta hanyar cewa ke me kike so a kawo miki ?
hmmm ni indomie ma ya isa me dan yaji pls juyawa tayi ga sauran kawayenta tace ku kuma fa dayar tace ita kunun aya take so dayar kuma wai jellop din macaroni d kifi sai drinks ko wanne ita kuwa yusrah cewa tayi farfesun kayan cikin rago take so ta kuma hada mata zobo
murmushi dije tayi kafin tace iya wannan sun isa ko kuna buqatar wasu abubuwan
tsawa yusra ta daka mata tare da fadin kijini da munafukar yarinya ina ruwanki da sun ishemu ko basu ishemu ba ai mun san abinda muke buqata shiyasa muka fada miki iya su din dayalla wuce kibawa mutane wuri kiyi abinda nasaki
Allah ya huci zuciyarki Aunty
ta juya ta shiga kitchen tana shiga kamar abun arziki duk abinda suka lissafa ba abinda bata hada ba kuma harta gama Anty basirra bata shigo ba sai da ta jera komai akan wani qaton tray kafin ta nufi parlon yusrah na ganinta ta qara hade fuska wai ita oga
tsugunnawa tayi tare da fadin gashi anty nagama nan ta shiga ajiye wa kowa abinda ya buqata tana gamawa tayi hanyar fita waje yusrah ta rakata da harara kasancewar an dan fara hada hadar biki mamy sun tafi dubai hado lefe shiyasa gidan shuru
kharleesart ce ta fara dibar indomie din domin taci da zafinta domin kuwa yadda ta ganta a ido ga kamshi tanayi tasan zatayi testing tana sawa a bakinta da sauri ta dawo da ita domin wani tsinnanen yaji ne wa nda yake barazanar dauke harshenta
kallonta yusra tayi dai dai takai spoon din hanta bakinta da dukan kuzarinta da sauri ta fito da ita domin wani dan iskan daci dataji ga shi ba alamun maggi ko wasu kayan dandano a ciki shukrah wadda itama dai dai nan ta bude fillet dinta ta diba takai bakinta wani kafirin tsami daya kashe mata haqora tayi saurin hadiyewa maryam kam tana kai kofin kunun aya taji wani mugun gishiri daya kusa dauke mata fatar harshe
miqewa yusrah tayi ta shiga dandana abincin kowa jin abinda taji da sauri ta furzar cike da bacin rai ta miqe da niyyar fita ta jawo dije ta kime ta son ranta dan yau bata san ma kalar dukan dazatayi mata ba watakil saita sumar da ita a yadda takejin zuciyarta
alamar bude falon taji anyi kuma an mayar an rufe ta cikin labule
cike da masifa ta nufo gun ta yaye labulen wata razananniyar qara tayi sakamakon ganin dije idanunta a wurqile ta wani markwade harshe hannunta rike da wata zabgegiyar bulalar ice ga kuma wuqar da ake sara qashi da ita nufo ta tayi ita kuma ta fara ja baya sauran ma duk miqewa sukayi cike da tsoro kowacce na neman maboya
gidan ubanwa zaku ? dije ta fada da wata malkwadaddiyar murya
jikinsu ne yahau kyarma suka qanqame juna suna shirin yin ihu tace duk wanda yayimin ihu a cikinku saina tsaga bakinsa da wannan wuqar ta daga wuqar hannunta qanqame juna suka qarayi suna kuka barinma yusra data qame guri daya dan ita tsoron me aljanu takeyi sosai
ubanwa yasa kusa godiyarmu aiki saboda bama so ta wahala muka girka muku irin girkinmu kuma kuce bazaku ci ba ke harda tashi da tafiya kice zaki kamota ki daka ko ta nuna yusarah
baki na rawa kamar mejin sanyi tace wa..ll..a...hi ah ah bulalar hannunta ta daga ta zuba mata zatayi ihu tace kul kikamin kuka inba haka ba zan sa 'dana yazo ya yini yana dukanki da bulalar qarfe
kama bakinta tayi ta rike tana mutsu mutsu tsananin azabar bulalar daya shigeta ba'amagana jikinta yasaba da hutu gashi yau an daketa da bulalar aljanu wai a hakan ma danta roba ce inaga ansa mata ta qarfe dan haka ta qara gum da bakinta
meye nufinku musha wahalar girka muku abincin kuce bazaku ci ba ko me?
mu din banza cewar maryam wlh zamu ci yanzun nan zamu
ci ko?
da sauri suka shiga girgiza kai eh eh wlh mu mun isa musaku wahalar banza
toh kuyi maza kowacce taci abinda tasa a dafa mata inba haka ba saina sa aljani duna yaxo yayi muku durar kabaki
toh toh munji zamu ci wlh kuyi haquri bayin Allah
kowacce ci takeyi tana kuka duk harshensu ya amsa ga zufa gashi basa son ko kallon fuskar ta ai dama dagani kasan wannan kyan ba'a banza ba harda hadin aljanu
saida suka cinye komai tass bnda kuka da majina da dallo harshe ba abinda sukeyi sunata budar baki sannan ta miqe tace daga yau ko kallon banza kuka karawa godiyarmu wlh saina ci ubanku kuma naji kun fadawa wani wannan abinda yafaru duk saina biki gidajenku ni kadai nasan mezan muku ku tashi ku fita waje zan tafi inbar godiyata tayi bacci
da gudu suka nufi qofa harshe a waje baki bude kamar irin mayu suna fita suka zube gurin shukrah data sha kunu aya me gishiri amai kawai takeyi itada yusrah suko su kaleesart banda kartawa ba abinda cikinsu keyi alamar y yamutse kenan
suna fita ta rushe da dariya tare da hada kwanukan ta nufi kicin tana fadin shegun banza wlh kadan kuka gani dan na fuskanci saina gyara muku zama tana wanke kwanukan data bata tana dariya a haka harta gama ta fita ta dauki ruwanta ta koma daki har yanzu dai basira bacci takeyi Allah sarki kodan yawan aikin datakeyi ne
sukuwa suna nan zaune duksun baza baki sun baje a gurin banda kuka da kakari da nishi ba abinda sukeyi motar su naseer ta kunno kai
*alqalamin shady*✍
*vote*
*comments*
*with* 08066364077
[16/12, 11:41] +234 806 493 3819: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀
TA ME GARI
NA
KHADIJA USMAN
9⃣
narasa bakin da zan godewa masoya wannan littafin sai dai ince Allahu yabar qauna yaqara bani kwarin gwiwar faranta muku ko yaushe 😘
******
ko gama parkin habeeb beyi ba naseer ya balle murfin motar ya nufi gurin su da sauri yana tambayar lfy meya faru meya sameku naga duk kun shanya baki a iska?
yusra da bakinta ya kacame da daci ne ko bauri ji takeyi bakin duk ya dade itace tayi qarfin halin ce mishi abinci mukaci me yajin bala'i
kallonta yayi duba na rainin hankali kafin yace wannan wane irin rashin sanin ciwon kai ne ta yaya zaku je kuci abunda kuka san zai yi muku illah yanzu dan Allah dube ku kunyi wani zugwi zugwi daku kamar mayunwatan 'yan boko haram dayalla ku tashi ku shiga ciki
kada kai su maryam suka shiga yi tare da fadin ah ah mudai basai mun shiga ba dan Allah dai ka taimaka ka bamu maganin wankin ciki pls
habeeb ne ya qaraso gurin yana tambayar sa lfy ? nan ya sanar dashi wai yaji suka sha fada yayi musu sosai akan illar da yaji keyi kafin yace su shiga ciki kafin yakawo musu magani dan kar yajin da suka sha yayi effected dinsu dan yaga sunsha da yawa shiko naseer fada yayita yiwa yusrah duk yadda yaso su khaleesart su shiga parlor ki sukayi har sai da habeeb yakawo musu maganin suka tafi ita ko yusrah da sanda ta shiga ta wuce dakinta inda ta fada toilet tanata brush kamar zata qarar da kamfanin makilin sai yunkurin amai takeyi dan ji takeyi gaba daya makogoronta kamar ya qone 🤣
******
tun daga wannan rana wani kallon rashin mutunci ko na raini be qara shiga tsakanin dije da yusrah ba har saida mamy ta dawo zuwa lokacin daddy na nan domin shirye shiryen biki kudi sosai dije ta karba gurin daddy dan yin siyayyar nata kayan bikin a cewarta tunda ba'asa da ita a anko ba baruwanta nata zatayi rufaida da husna qawayenta sune suka tafi siyayyar tare kudi sosai suka kashe dan har ciko sukayi mata tare da qara mata wata siyayyar direct shagon wani me yi musu dinki rufaida ta kaisu suka kai kafin suka wuce gida duk sun gaji
suna sauketa suka wuce ita kuma ta nufo gate din gidan ta qaramar kofa ta shiga inda tana shiga ta iske su yusrah da qawayenta tare da naseer sai abokansa da alama suna tattauna harkar bikin ne
ta so ta wuce su amma ganin yadda yusra ke binta da harara yasata yin kwana ta nufi gurin da suke cike da takunta na 'yammatan zamani wadan