Author : Asma Baffa Category : Romance
dai nan dije ta bude mota suka fito
alhmdllh cewar rufaida
kallonta yayi dan besan meta gani ba
gama raba gardama nan
kallonsa ya mayar gun dayaga tana kallo
masha Allah ya furta ganin yadda siririyar farar yarinya take da kyau na ban mamaki da jan hankali kasancewar dare ne se hasken fitilu ga kuma makeup din datasha ecxatily amarya yasa shi qara kwadaituwa da kawai ya shiga da ita be damu ba dako qawar amar yar bros ce ko qanwarta shi dai kawai yasamu ya fita kunyar abonkansa da suka zo masa daga wata uwa duniya yasan duk wadda yaga yarinyar nan ai yasan ya kece raini dan tafi yusra komai qiba kawai yusrazata nuna mata shima kuma sai yanayinta ya amshi jikin nata
kinga je kiyi yadda ya dace kawai kinji sister nagode
da saurinta ta isa gun su dije da suka nufi gurin shiga holl din kamar gaske tayi musu sallama tana aarasa wa ta shiga labarta musu komai suka dinga dariya kuwa zuwa can takamo hannun dije suka nufo gurin motar da naseer ke ciki
tunda suka nufo gurin ya shiga gyara zaman hula da kafadar rigar sa suna zuwa rufaida ta leka ta glass tace ya fito
yana fitowa ta damka hannun dije a hannunsa dukansu saida sukaji tsikar jikinsu ta tashi turare ta fito dashi a hand bag dinta masu kyau da tsada ta shiga feshe su dashi inda take kamshin ya hadu da nasu na jikin yabada wani sassanyan kamshin daban
ko tunanin wacece beyi ba illa ma wani nishadi dayaji nan rufaida tace bari taje ta sanar da zuwansu
tana shiga holl din ta qarasa ta sanar da m.c isowar daya amaryar da angonta take kuwa yasa aka canza kida guri ya kacame da murnar isowarsu wasu daga qawayen yusra suka mike tare da abokan ango dan taro amarya da angon nata
suna shigowa gurin aka hau tafi da sowa yayin da waqar Abdul d one ke tashi ta lale amarya da ango
habeeb da amaryarsa qura musu ido sukayi yayin da kowanne kishi yacika zuciyarshi dan ita dai amaryar habeeb ta kure wanka so takeyi taga tafi amaryar qanin mijin nata bada kala amma gashi ko kusa ma babu hadi
shi kuwa habeeb ganin yadda qanin nasa da amaryarsa suka fito suka haska gurin yasa yadanji haushi
saida suka nufo gurin yaga ashe ba yusra bace to kodai wata me makeuo din ce ta shigo da ake canzawa mutum halitta yasan naseer da son kece raini anya kuwa?
hat suka qaraso mazauninsu kafin kowa ya dan nutsu inda nan fa qawayen yusra da dangi aka shiga mamakin to ina yusra dan ko makaho indai yasan yura yasan dai wannan ba ita bace nan fa aka shiga cece kuce
ganin lokaci ya fara qurewa yasa aka shiga hada hadar abinda ya tara
yana son kallon yarinyar amma yana jin nauyin yin hakan ganin abokai da qawaye nata zuwa suna pic dasu yasashi satar kallonta dai dai tayi murmushi
damm yaji kirjinsa yayi dije!!dije!!dije?
ya shiga ambata a zuciyarsa ganin ya ganeta yasa suna hada ido tayi masa killer smile tare da kanne ido daya
saurin kawar da kansa yayi tare da fadin how this comes?
bai samu amsa ba yaji m.c na gayyatar su a filin rawa
jiki ba kwari ya miqe suka fita shi kanshi habeeb se yanzu ya gane yarinyar nan ya shiga mamakin ya akayi haka
suna filin rawa anata musu liki da sun hada ido da naseer saita saki murmushi can ta dan qara matsawa jikinshi kafin ta rada mishi a kunne ya kaga 'yar yayen kaga yadda ko su classic lady's din sukayi mubaya'a ko
rada mta shima yayi a kunne wlh zaki ci ubanki kuwa
murmushi tayi kafin tace ani bana ikata
laifi sain shirya karbar hukuncinsa
gani yadda sukeyi suka burge mutane dayawa aka shiga daukarsu pictures da videos
**
yusrah tana ganin lokacin daya fada ya kusa ta ce ayi mata makeup din tare da munna wayarta tana budewa kira na shigowa ta duba ko shine sai taga khaleesart ce da sauri ta daga dan tasan zancen be wuce suce suna jiransu ba
hello qawata ya akayi?
kina ina?
ina gida mana ina jiran naseer ya zo mu wuce
wane naseer kuma ai sede ki nemi wani nan ta fada mata abinda ke faruwa
a haukace ta miqe ta na fadin ni naseer zaiyiwa haka ni zaka wulaqanta narantse da Allah yau sai anyi uwar watsi ko ta kan me makeup bata biba ta suri mayafinta da key din mota qawarta da suke tare ganin yadda ta fita yasa suka bita.....
ina ganin comments dinku kuna burgeni naji dadi sosai da masu kirana da masu min text nagode
*vote*
*comments*
*with 08066364077*
*Alqalamin khadyβ
[16/12, 11:41] βͺ+234 806 493 3819β¬: ππππππ
*TA ME GARI*
NA
KHADIJA USMAN
1β£1β£
*wannan shafin na sadaukar dashi ga dukkan member's na khadeeja fans novels na yaba kwarai da comments dinku dan haka ma nace daga yanzu ku kadai ne zaku sami tame gari*
bayan an dan gama caccashewa ne kowa ya koma gurin zamansa yayin da wadanda suka san yusrah naseer zai aura da suka ga ba itace a gurin dinner din ba sun cika fam da mamaki wasu suka barje haushinsu akan kudinsu suka dinga bazawa naseer liki dan a ganinsu yusrah ce ta shirya rashin mutunci musamman dangin babanta amma dangin mamanta a cike suke danma dayawansu basu san wace ce dije ba
ana haka aka sanar da amarya da ango su yanka cake su habeeb ne suka fa
ra inda yaba amaryarsa itama ta bashi cikin gogewa da kwarewa sannan aka zo kan su dije da nata gogan π
shiya fara yankawa ya wawuro tabkeke ya nufi bakinta cike da mugunta ta gane nufinsa dan haka ta shirya tare da bude dukkan bakinta ya tura mata nan take aka dauki tafi raf...raf..raf...sannan itama ta mika hannu da niyyar dauko wanda zata bashi dan mitsitsi ta yanko tare da nufar bakinsa ya so yaki bude bakin amma ganin dayayi ido yayi yawa akansu ga pic anata dauka ga masu video coverage hakan yasa ya dan bude bakin kadan ga mamakinsa sai gani yayi tasa masa a hankali dan gefen bakinsa ne ya baci da cake din be ankara ba yaji takawo bakinta saitin gurin ta ziro harshenta ta lashe tare da dora masa kiss a bakinsa qamewa yayi kamar gunki guri kuwa ya kaure da hayaniya da tafi wasu ko da suka san yusrah zai aura suka shiga rattaba nasu luguden leben shi kanshi naseer din cike yake da tararradi domin yasan yanada tarin 'yan qalu bale daga abokansa zuwa friends dinsa amma yasan ai laifin yusrah ne tunda ita taso dizga shi gara ma da akayi hakan dan ya fita kunya amma fa ba abinda zai hanashi cin uwar yarinyar nan
ansa taken nigeria a gurin wanda shi ke nuna taro ya tashi ko kafin naseer ya ankara ya nemi dije sama ko kasa ya rasa itako wata 'yar loko tasamu ta labe ta ta cire daurin kanta ta lababa ta sirnane zuwa gurin motarsu tana zuwa ta bude ta shige baya sai ganin su rufaida tayi sunata raba idanu kallonsu tayi tare da fadin ku kuma lfy naga kunata muzurai?
hmm ai dole muyi cewar husna ke kin san yadda kirjina ke bugawa kuwa haka kawai kija amana shegen duka ji fa abinda kikayi khadeeja bakiji yadda wasu dangin amaryar ke fadin sai sunci ubanki shiyasa muka silale dan da kin dada bata lokaci wlh guduwa zamuyi
rufaida tace ai gara ke ni ai idona idon naseer shaqeni zaiyi a dau gawata bare kuma yusra
kai dayalla can matsoratan banza ni wlh dana san ma haka zakuyita min da ni kadai zanyi aikina kun san zan iya ina ruwana da duk hukuncin da zasuyi min nasan dai duk wanda yayimin cikinsu wlh sai in hana daukar amaryar ma gaba daya ko inyi abinda zaisa 'yan bikin kowa ya......bata qarasa ba suka ga shigowar motar yusrah a miliyan ko kwakkwaran parkin bata gama yiba ta bude ta fito ta nufi qofar holl din da gudu tuni mutane sun fara fitowa ta kutsa kai ta cikin su inda tana shiga tafara ruwan ashar tare da ball da duk abinda tayi kacibis dashi hange takeyi taga inda zata ga tsinnanun maciya amana amma bata gansu ba riqeta aka shiga yi inda ta dinga ihu da zage zage nan ta shiga sanar da danginta da qawayenta masu ganin laifinta sakon da naseer ya tura mata na karta shirya da wuri wato hakan na nufin yanzu ya tafi da dije gurin professional walimar daya ce an shirya musu wlh saiya san yayi mata haka duk saita ci kut.....πsu haka aka rirriketa ana mata fada amma tayi banza dasu ta dinga rashin mutuncinta
shiko naseer tuni suka fice da sauran abokan shi kuma su habeeb tuni ya saita shima da tashi amaryar
naseer na kallon zuwan yusrah amma ya qyaleta
kowa yagama fitowa inda kowa ya shiga abin hawansa inda kowa yakama gabansa kusan su dije ne karshen fita dan duk su rufaida a tsorace suke ji sukeyi bazasu iya driven ba inda dije ta cika fam gashi bata iya driven sosai ba shiyasa ganin suna neman bata rai yasata fadin na rantse da Allah cikinku kowacce bashi taci kuma seta biya
ah ah khadeeja rufa mana asiri wlh ba haka bane kada kija mana wani bala'in
to tsayuwar me mukeyi ku wuce mu tafi mana
jiki ba kwari suka ja motar suka nufi gida a hanya dije tace kunga ku wuce dani gidanku kawai mukwana can dan ni gobe ma kauye nayiπ
bikin fa?
wanne biki ai inba so nakeyi a hada da jana'izar gawata ba gara in gudu qauye harsai jarababbun nan sun bar gidan daga baya in dawo dan in suka san gaskiyar abinda yafaru inaga naman jikina zasuyita yanka har sai sunga nakai takardaπ
dariya suka sa tare da fadin ashe khadija tanada tsoro
hmm ai tsoro halak ne haka kawai a taba lfy ta a jawa me sona asara mijin dazan aura duk yaga tabo a jikina me yafi raina?gara in san nayi koba komai tsawon shekara uku danayi banga innata ba zan fanshe
a haka har suka qaraso gidan su rufaida suna shiga sukayi wanka sukayi sallah tare da cin abinci suka kwanta bacci
*****
gida fa ya kacame inda mamy ta kira naseer cikin bacin rai tace tana son ganinshi
bai wani jima ba yazo yana shiga dakinta ya iske yusrah kamar mahaukaciya fuskar nan ta hade da majina da hawaye idanunta duk sun kumbura alamar tasha kuka
cikin ladabi ya gaisheda mamy ko amsawa batayi ba ta shiga tambayarsa dalilin daya sa ya aikata abinda ya aikata
bayani ya shiga yi mata inda nan take yusrah ta karyata tare da fadin wlh qarya ne mamy kinga text din fa dayamin
karba mamy tayi ta karanta tare da fadin ubanwa to ya tura wannan saqon ?
karba yayi ya duba yakaranta yaga number sa ce kuwa
cike da mamaki ya kalli mamy yace na rantse da Allah wlh wlh bani na tura sakon nan ba tabbas number ta ce amma banida masaniya akanshi amma mamy ai itama ta turamin wata cousin sister dinta tace wai dreesing dina beyi ba saina dawo na sake wani
caraf ta amshe da fadin wlh qarya ne ni babu wanda na aika nan aka shiga musu
ganin haka yasa mamy daka musu tsawa tare da fadin kai ban son iskanci
ya akayi ka hadu da dije a gurin to
be boye komai ba ya fadawa mamy
nisawa tayi kafin tace amma wannan anyi shegiyar muguwar yarinya yanzu nagane bakin zaren cikinku akwai wanda yayi mata wani abun tayi maku ramuwar gayya kenan
nan kowa ya shiga fadin abinda yafadawa dije akan zuwa gun dinner din
koda naji yanzu naji batu amma ko wannan uwarta ta haifi fitina da kanta zako tasan tayimin haka wlh saita gane batada wayo nan ta gama fadin duk abinda zata fada suma kowannensu a zuciyarsa ya gama kiyasta hukunci. dazai yima dije niko nace to ayi dai mu gani in tusa zata hura wutaπ
*******
washe garin ranar asabar aka daura auren habeeb khamis da sajida A lawan tare da na yusrah Abubakar da angonta naseer khamis duk akan sadaki dubu dari dari inda dinbin jama'a suka shaida duk dangin kauye maza sunzo harda ko mahaifin dije da megari
ansha yinin biki inda karfe takwas aka dauki amare zuwa gidajensu dake wuse zone 2 gidan yayi matukar kyau tare suka gina shi gate daya ne amma kowacce part dinta daban babu kuma abinda aka banbanta wajen ginin konai iri dayane
har aka gama shagalin biki ba wanda yaga idon dije duk masu son ganinta kuwa sai washe garin ranar ta dira a gidan koda ta iso 'yan garinsu nata shirye shiryen komawa kauye dan haka itama ta hada kayanta suna can falon baki ta iske su bakaramin dadin ganin mahaifinta tayi ba inda shima yaji dadin ganin tilon 'yar tasa ganin yadda ta canza tayi kyau ga kuma nutsuwa
shima a bangaren me gari dadin yaji inda ya shiga sa musu albarka
koda tace zata bisu bawanda yayi hanzarin hanata dan ta yi kokari dan haka koda aka tashi tafiya da ita aka shiga mota sai bayan ta shiga ne mami ta ganta inda ta ciji yatsa takira daddy akan meyasa za'a tafi da dije yace zata ganin gida ne duk yadda taso ya hana bata samu shiga ba a ranta tace zaki daw ki sameni
su dije an dau hanya yayin da zumudi da farin cikin dokin ganin innarta yasa take gani. kamar motar bata gudu tayi bacci ta tashi yafi sau nawa kafin a isa sai kusan yamma suka iso gida zo kuga murna gurin dije
*WELCOME BACK TO VILLAGE DIJE*
*vote*
*comments*
*with 08066364077*
insha Allah indai nasami lokaci zaku jini zuwa dare
[16/12, 11:41] βͺ+234 806 493 3819β¬: ππππππ
*TA ME GARI*
NA
khadija usman
1β£3β£
*rawa da girgiza zanyi gabanku in jujjuyaπππ zanyi muku albishir comments dinku na burgeniπππ*
*gaskiya naga soyayya a zahiri da badini jinjina gareku masoyana nasan soyayyar tame gari ce ta shafeni ina matuqar godiya gareku Allah yabar qauna*
*sadnaf ina tayaki murnar samun lfy Allah ya qaremu da lfy da duk musulmin Allah baki daya,Aunty safiyya huguma kema ina miki fatan samun lfy me dorewa Allah yasa anyi aikin a sa'a*
****
kallonsu dije tayi taga yadda jikinsu ke makyarkyata ita abunma sai ya bata dariya dole saida ta dan murmusa kafin ta maida kallon ta garesu tace na kira waya azo a tafi daku sbd haka ku tashi mu tafi dan bana son jira
magiya suka shiga yi kuka wi wi dan inna mairo harda fyace majina suna wlh ba laifinta bane hansai ce shima din hamidan duk akan hansai suka dora laifin ganin da tayu duk suna son zamewa su barta ciki yasata sakin kuka tare da fadin munafiki wlh qarya ne duk da laifinsu suma kuma ni yauhe ma nasa ku quntatawa 'yar mutane bakai ka gani ka auro ta ba ko nice inna da dole innace kayi abu se kayi ?
ah ah hansai kiji tsoron Allah ki fadi gaskiya wlh 'yan sanda basuda imani ko kadan kikkilemu zasuyi ko digon jininmu baza'a samu ba sbd haka ki karbi laifinki kawai a tafi dake ni a barni da dana se 'yata hafsy ta qarasa maganar tana miqa hannu da dafa kan hafsy data maqure guri guda tana kallon ikon Allah
kunga duk nagaji da surutu sbd haka kutashi mu tafi kawai ta fada tana me qoqarin mikewa
hansai ce ta miqe da kyar ta kalli dije kafin ta kaikaice ta ce ke dayalla gafara can dan kinga ma ana lallabaki wlh dukanku ina iya hadawa inci uwarku ba inda zani hukumar hegiya dan haka kin dade baki ce su shigo din su tafi dani ba
ganin yadda taketa bala'i da kumfar baki yasa fa zuciyar dije bugawa daram dararam dam dan ita kanta tasan idan ta bari wannan me kama sa jinsin ordisay din ta damketa to fa wlh saita ci kut......π
gara ta lallaba ta zame dan taga alamar wannan kaddarar hafsy ce koba kamai ta tayata da addu'a kawai π€£
ganin da hansai tayi kamar dije ta tsorata da ita yasata qara sakin sababi duk da itama qarfin halin ne dan wlh da za'a tsaga kirjinta tsab zuciyarta zata fado ta fito
kallon tsaf dije tayi mata ta lura da sababin da takeyi na iya baki ne a ranta tace kin gama yawo yarinya amma a fili saita ce
keeeeeee!!!!!
shutup your magout maout ina magana kinayi kin san wacece hukuma kuwa ?kinyi lafuffuka da dama kuma masu girma ciki harda na zagin hukuma dan haka dole ki karbi hukuncinki tare da masu mara miki baya dan haka kuna batamin lokaci pls ku wuce muje
hamidan ne yace yanzu dai ranki ya dade laifin waye ya shafeni ni?
oho dai koma laifin waye ai kai ka sani ni ba ruwana danme zaka auro yarinya ka maidata baiwa suma iyayenta saina sa an tafi dasu tunda basu kula da yarinyarsu suka dauka duka bata
kinga ranki ya dade wlh wlh laifin duk na hansai ne ko inna?
eh wlh itace da anyi abu saita ce zata zane mutum kota zaune shi sbd haka muke yi mata biyayya duba da yanayin hallitar da Allah yayi mata
oh yanzu nagano bakin zaren kana namiji matarka kw juyaka kenan to waye mijin cikinku?
nine wlh amma a suna
toh yanzu ka zabi daya shin zaka barta matsayin mijin ko kuma zaka dawo mikin in yaso a dai daita?
wlh zan koma cikakken namiji ma
toh masha Allah wane mataki zaka dauka yanzu?
sakinta zanyi dama ta isheni wlh
nisawa tayi taga dai ba kyau raba sunnar ma'aiki kuma ta lura da yadda hansai jikinta yayi sanyi daga jin an ambaci kalmar saki saita bata tausayi tace to yanzu zanyi muku wani adalci guda daya zan rufa muku asiri kowa yazauna muyi magana zama sukayi duka inda su kansu suke mamakin yadda suke bin maganar yarinyar kodan fa hukuma ba sauki
ganin su nutsu yasata zame gilashin idonta abin mamaki ji nayi su dije an afka wa'azi gadan gadan ta shiga yi musu nasiha da taushin murya
Allah kenan duk cikinsu nutsuwa sukayi sunaji inda duk jikinsu yayi sanyi saida ta gama kafin tabi kowa tanaa fada