Tame Gari 1 Complete Hausa Novel

Author :  Asma Baffa Category :  Romance

Chapter   16 / 33

45K to 48K   out of 96.3K words

dai basa ganina bakuma sa jina kada su zo daukar fansa tana wannan tunanin ko itama taji kamar motsi a dakin aikuwa da sauri taja bargo ta rufe har kanta ta fara karanta ayatul kursiyu

ni ko nace su dije ashe ana....... πŸ™Š

*****

washe gari yusuf na dawowa daga masallaci gari ya danyi haske dan dabi'arsa ce inyaje sallar asuba baya dawowa sai gari ya waye tarr yana shigowa ya riski hajiya a falo da gima giman jakunkunanta cike da mamaki ya karasa gabanta ya duka ya shiga gaisheta

ga mamakinsa amsawa tayi cike da fara'a kafin tace kun tashi lfy dai ko ?

duk lfy kalau am ya naga wadan nan jakunkunan kuma na miye?

nawa ne dama na yanke shawarar komawa gidana jira nakeyi ma ka shigo ince kasa a gyara shi yanzu dan nasan yayi kura

a zuciyarshi yace lallai khadija kin iya saiti

amma a fili saiya marairaice fuska yace haba hajiya me yayi zafi haka laifin me muka miki da har zaki ce zaki bar gidan nan lokaci daya kuma da gaggawa haka idan munyi miki laifi ne ai saiki fada mana mu gyara inma ita Aminan ce tayi miki wani abu ai saiki fadamin in dauki mataki a kanta dan baxan lamunci a bata miki ba

kafin ya gama rufe baki sukaji budewar kofa Amina ce ta fito sanye da dogon hijab dinta tare da carbi a hannunta fitowarta yayi dai dai da fitowar dije itama kusan a tare suka qaraso falon suna zuwa Amina ta gaisheda hajiya ta amsa cike da sakin fuska sabanin da dasaita samu rabon zagi

koda dije ta karaso gurin kowa ta shiga gaidashi koda ta zo kan hajiya ta gaisheta sam kin amsawa tayi sai dai ta maido mata da gaisuwar itako dije ta ci gaba da gaisheta jin ta kuma maido mata yasa tace hajiya aini ya kamata in gaisheki ranki ya dade

dukansu kallonta sukayi ganin yadda ta ke duddukar dakai itako dije tace

haba hajiya meye abin ranki ya dade anan dan Allah ki bari kada kisa su yaya su zaneni

duka fa kikace wane mutum ai ba wanda ya isa ya tabaki ya kwana lfy inaaaaaa ai kinfi karfin kowa

ganin yadda takeyi yasa dije saurin dakatar da ita ta hanya fadin wadannan jakunkunan fa baki akayi a gidan?

yusuf ne yace inafa baki a rigimar hajiya ce a motsa wai ita dole saita koma ainihin gidanta data fara zama kiji fa kawai rana tsaka tace zata tafi ai dole mu binciki kanmu ko mu tambayi dalili dan ni bazan taba yarda ta tafi ta barmu ba bayan kowa a gidan nan yasaba da ita

aikuwa dole in tafi in barku ko kuna so ko bakwa so dama can lalura tasa na zauna daku ba komai ba dan in kula da yadda zamanku zai gudana insa muku ido kasan ku yara farkon aure sai ana lura daku dan kun fiya rawar kai yanzu kuwa naga kunyi hankali ai gara in tattara in koma inda nafi wayo ko

haba hajiya gaskiya ni ban goyi bayan ki tafi ki barni ba in su Anwar suka tafi school ni da wa zan dinga zama yana debemin kewa cewar Amina

haba 'yar albarka ai zaki saba da sannu kinji kada ki damu zan dinga zuwa lokaci zuwa lokaci ina duba ku ai

kallonta dije tayi kafin tace au kice ma kin tafi baki tafi ba kenan tunda zaki dinga zuwa

ah ah ina nufin su in sun sami dama su dinga zuwa dubani ni me zanzo nayi a gidan yara kuma

dukansu saida sukayi dariya kasa kasa a haka suka tsinkayi muryarta tana fadin

ke Amina maza tashi ki dora abin kari mana kada abar bakuwa da yunwa a ranta tace duk da nasan ya zuwa yanzu Allah kadai yasan irin abincin data dibga taci na mutane taci nasu na aljanu amma a fili taci gaba da cewa ki debe duk abinda yakamata a girka kinji harda farfesun kajin nan duk ayi kada su lalace

toh Amina ta amsa tare da mikewa ta nufi kitcheen a ranta tana hamdala tare da godewa khadija data zama silar ganin wannan ranar a gurinta tana shiga ta shiga hada kayan break masu rai da motsi irin wanda yakamata ace wanda ya taka matsayi irin na yusuf ana ci a gidansa

tana tsaka da aikin dije ta shigo da sallamar ta ta qarasa inda take

ah ah haba ranki ya dade ke da kanki a kitchen kuma

dariya dije tayi kafin tace kai Aunty kema kin zama hajiyar kenan

ba dole ba irin wannan aiki da kikayi shekara da shekaru muna zaune da mata yau kinsa zata bar gida rana tsaka

au to tunda bakya son ta tafi bari inje in dakatar da ita ai ba matsala

ni na isa wlh ta tafi na dinga zuwa gaisheta ai kedai Allah yayi miki albarka wlh kin gamamin komai duk da cewa uwar miji uwa ce amma ita tata matsalar tasa na gundura da zamanta yanzu kuma Allah yakawomin mafita kice wai ta zauna ai sai dai kice in shirya yin rakiya

dariya dije tayi kafin tace ai na dauka kin fi son zaman nata ne da sai ince tasha zamanta kawai ta qarasa maganar tana dariya

itama Amina dariya tayi nan dije ta kama mata aikin suka gama sunata hirar hajiya akan abinda yafaru jiya

yau kam gida ko yara sun san ya canza inda kowa yaci yasha cikin nishadi bayan an gama ne yusuf yasa wani yaronsa yace yaje yasa a gyara gidan hajiya aikuwa cikin qankanin lokaci aka gama komai ya kira ya sanar masa an gama

.saida yadan qara sayen wasu abubuwan aka dan kwaskware gidan abinka da masu abin cikin qanqanin lokaci aka gyara ko ina fess tunda dama bawani komai gidan keda ba kawai kura ce

koda aka tashi tafiya hajiya kuka ta fara yi a ranta tana ta jama dije Allah ya isa data rabata da kujerar ta ta mulkin mallaka a gidan danta wadda bata tashi yin ritaya yanzu ba amma ko wannan ko'a cikin aljanun ta cika marar imani nan dai ta dinga sharbar majina har gida aka rakata yayin ita da dije ke zaune a bayan mota ko motsin kirki hajiya ta kasa har suka isa

sam ba wani farin ciki a fuskar hajiya hakan yasa dije rabawa ta bayanta ta rada mata a kunne naga alamar cutar sanyin nan bata rabu dake har yanzu dan haka zan kawo miki magani anjima kuma wlh kada ki sake inga kafarki kwana kusa kin koma gidan nan duk abinda kike buqata ki kira ki sanar za'a kawo miki in na bukaci kije zanzo cikin dare in sanar mikk kije naga yanzu kina ta kuka nasan kukan da kikeyi ko na miye ki kiyaye

gyada kai hajiya ta shiga yi a hankali tace naji ranki ya dade yusuf da duk abinda dije keyi yana lura da ita dan haka ya saki murmushi a ranshi yace khadija hooo duk wanda ya aureki zaisha fama
haka suka gama zama a gidan hajiya bayan yusuf ya kira wata qanwar hajiya akan ta zo su zauna tare sannan yasa a nemo musu mai aikin da zata dinga kula da gidan tare da me gadi nan sukayi musu sallama bayan ya vasu kudi tare da sanar dasu gobe zai dawo in Allah ya yarda

haka hajiya tanaji tana gani suka fice zuciyarta kamar ra fashe amma ba halin bayyanawa tana tsoron mutum aljan

*****

yau kwanan dije biyu a gidan yusuf kuma yaune zata koma gida yayin da kallo daya zakayi ma masu gidan ya zuwa yanzu ka tabbatar suna cikin nutsuwa

tunda akayi sallar la'asar dije ta shirya ta zo ta kame a falo

masu gidan ne suka fito suna dariya da alama hirar tayi musu dadi ganin dije da sukayi a zaune yasa su fadin

ah ah ranki ya dade dan yanzu sunan da suke fada mata kenan tunda sukaji a bakin hajiya me zamu gani haka kamar an gaji damu?

murmushi tayi. kafin tace ba batun gajiya illa dai inason in koma ne dan nayi kewar mutanen gidan

hmm kajita sai kace ba ita tacemin nan da can duk daya ne ba cewar Amina

bar ma ta wannan su wadanda take cewa tayi kewar tasu tunda tazo ko waya basuyimin ba sabanin da da kullum sai munyi waya da safe kinga alama ta nuna su basuyi kewarki ba kamar yadda kike cewa ke kinyi ta su

to ya za'ayi su kira kuce sunyi rashin kunya inaga shiyasa suka ki kira

ah ah ko dai ko dai??

ko dai me ?

ko dai an gwada musu irin na hajiyata ne shiyasa suka shiga taitatayinsu

dariya tayi kafin tace ina ni ina yiwa ysyyena haka kunga ni duk ba wannan ba gida nake so na kuma gama shiryawa a zo a kaini ko in hau taxi

rufa mana asiri ai mu bazamu yadda mu batawa mumina rai ba haba wane mu tashi maxa ki kimtsa in maida ke salin alin

ni nagama shiryawa ina yarana muyi sallama

nofal na bacci Anwar kuma yana gidan hajiya ko kin manta

ok hakane to bari mu mike mu saita hanya ta fada tana kokarin miqewa

Amina tace ta jirata inda tshiga ciki ba jimawa ta fito dauke
da leda a hannunta ta damkawa dije da farko kin karba tayi saida Aminar ta nuna rashin jin dadinta sannan ta karba fayi godiya har bakin mota ta raka su inda dije ta kame kyam a baya ba yadda basu yiba ta hau gaba tace ita tafi jin dadin zaman baya dole suka haqura suka kyaleta

a hanya ya tsaya ya qara mata siyayya inda suka nufi gida koda suka iso yamma ta danyi kasancewar yau weekend duk bamai zuwa aiki yasa mutan gidan suka zo garden suka zauna duka suna hira ana nishadi gabansu kayan fruit ne sai lemuka da ruwa inda duka suke hira ana babbaka dariya sam sun ma msnta da wata wai ita dije tunda kowa ya warke🀣

horn din da suka jiyo ne daga bakin gate yasa suka maida hankalinsu gurin inda sukaga motar yusuf ta danno kai kasancewar gilashin gaban a bude yake yasa ba'a suka ga ba kowa ciki sabanin na baya dayake a rufeπŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

*TAME GARI*

NA
khadeeja usman

2⃣8⃣

kasancewar bayan motar a rufe yake yasa basu ga dije ba har yusuf yayi parking kafin ya fito ya zagaya ya budewa dije data kame kam kai kace wata hajiya ce

innalillahi wa'inna ilaihir raji'un sukaji naseer ya fada

habeeb da sajida da hankalinsu bai kai ga dije ba suka ce meya faru kk wannan salati

Annoba ta dawo cewar yusra habeeb daya gutsuri apple kenan tsayawa yayi shi bai hadiye ba kuma bai fito da ita ba duk sun kasa motsawa

sallamar dije ce ta farkar dasu inda ta shiga fadin

Assalamu alaikum my brothers n'd sisters gaskiya nayi missing dinku duk da naga ku kamar bakwa farin ciki da dawowata ma dan naga fuskokinku kamar wadanda aka aikoma da mutuwa

waya isa yace baya farin ciki da dawowarki cewar naseer yana yake ko ba haka ba duka gyada kai sukayi amma banda sajida data hade rai sosai ganin hakan da dije tayi yasa itama ko kallonta batayi ba ta nemi guri ta zauna

yusuf ne ya miqa musu hannu suka shiga gaisawa bayan ya samu guri ya zauna kafin yace to ga kayan aro nan na dawo muku dashi kada ace na riketa

waya ce da kadawo da abinda aka ara maka din ? ai da nan da can duk dayane daka barta ma a can din ba matsala da sai a biyota da kayanta khadija ai tafi karfin a bada aronta sai dai kyautarta kawai cewar habeeb daya qarasa hadiye apple din bakinsa dayaji tazamar masa kamar dutse

ah ah so kukeyi matanku su yankomin sammaci suce na dauke musu 'yar qanwarsu babu ruwana

wallahi indai mune bakada matsala ai munada kakkyawar fahimta da mazajenmu komai suka yanke bama musawa cewar yusra

au hakane to tunda hakane bari inyi farin ciki dan na lura bazan sha wuya gun dauketa gaba daya ba

cike da rashin fahimtar maganar tashi habeeb yace kamar ya gaba daya kuma ai dole zatayi aure ko?

ah to idan kuma ya kasance nine zan aureta din fa

dammm kirjin habeeb ya buga domin jin furucin da yusuf din yayi ji yayi zuciyarsa tayi masa zafi cikin dan zafi yace ita kuma Aminan ka kai ta ina ?

sajida da sai yanzu tayi magana tace tana nan a gidan nasa ku maza kunya ce daku in kun tashi kara aure

ah ah Aunty na ai a aure ba batun kunya kuma kin san Amina batada matsala a wannan fannin

ba Aunty ba cewa zakayi mama habeeb ya qara fada a dan hasale kai gwafdede dakai ka kalli sajida kace mata Aunty ko kunya baka jiba

dariya yusuf yayi kafin yace to banda abinka yaya ai ko yusra yanzu Aunty zan dinga kiranta bare kuma sajida datake matar babban yaya

inka so ka kirani da baba malam karewar yaya kaga bana son iskanci malam kabar wannan shirmen naka ita wannan yarinyar duka nawa take da zaka kama fadar irin wadannan maganganun a gabanta so kk yi ta raina mutane kawai du du du me khadija ta sani cikin week din nan zasu fara zana S.S.C.E fa amma kk wani maganar aure a gabanta haba malam ai sai kaja ta raina mutane

duk abin nan da akeyi sai ka rantse da Allah dije bata gurin tana zaune abinta ta dauki lemon bawo tana sha jin sun 'danyi shuru da dramer tasu yasa ta tunawa da wayarta da daddy ya siya mata wadda ita taso ta dauka ranar da zata tafi gidan yusuf bata samu dama ba dan haka tana tunawa ta mike dan shiga ciki

ta fara tafiya ta tsinkayi muryar yusuf yace

kayanki fa princess?

batare data daina tafiyar ba kuma bata juyo ba tace biyoni dasu pls ta shige ciki abinta

girmanki ya wuce haka ai ya fada yana me kokarin barin gurin suka hada ido da naseer dake ta masa ruwan harara

au to yaya laifin me kuma nayi ake min wannan harara haka ?

baka kirana da abinda yafi yaya ka wani tsaya kanata sakin magana gaban yarinya salon kasa ta raina mutane

banda abinka meye abin raini a ciki a gara ayi komai a gabanku a matsayinku na manyan yayye

nifa inka ce yayan nan ji nakeyi kamar in kurma ihu wlh inba iskanci ba ina ni ina kai banda ma zamani daba ruwan abota da shekaru ai da sai ince kai sai dai kayi abota da qanin daddy

ai ba komai koma dai sa'an daddy ne soyayya bata tsufa dan haka bari kuga in tashi nabi ta kada ran 'yammata ya baci

yana gama fadar haka ya juya ya nufi motar ya bude ya fito da ledar ya nufi part din habeeb

da mugun sauri habeeb yasha gabanshi yace ina zaka malam?

kaji ka yaya da wata tambaya gurin princess mana in kai mata kayanta

haka kawai zan barka ka shiga ciki ka sameta a matsayinta na wadda ba muharamarka ba

kallonsa yusuf ya shiga yi yana murmushi kafin yace haba yaya kamar baka san halina ba wannan wane irin magana kk yi naga fa tun kafin ayi nisa kafara adawa anya kuwa zaka iya min jagora gurin daddy ?

habeeb da inda akwai kalmar data ke qona masa rai to bata wuce yace masa yayan nan ba dan haka cikin hade rai yace in kana iyawa ka kawo in shigar mata dashi kai kuma ka koma gida maza su hajiya na jiranka kasan dai abinda zai biyo baya inka dade

au ni wlh kama tunamin wace hajiya kuma ai kai wannan matsalar ta kau akwai lbr sai mun zauna yanzu dai bari muyi sallama da princess tukunna sauran bayani gobe zan sameka a office

sallama dawa?

ai wlh in kaga ka kara ganinta to ba yauba sai wani lokacin kuma dan na lura dakai nema kk yi ka hargitsa mata kwakwalwa ka hanata karatu

kememe ya hana yusuf shiga gidan inda karshe yabashi kayan yayi musu sallama wadd matan ne kawai suka amsa masa amma mazan banza suka mishi ya shiga motarshi yana murmushi yabar gidan

naseer da sai yanzu ya lura da kallon da yusra keyi masa yace ke kuma meye kk tsareni da ido kamar wadda ta warke daga cutar makanta yaja tsaki yayi part dinsu cike da mamakinsa ta mara mishi baya

.hakama sajida da duk abinda mijinta keyi tana kallonsa har yanda ya karbi kayan ko kafin ta iso inda yake harya shige ciki itama ta mara masa baya

yana shiga ya iske dije zaune tana daddana waya cike da bacin rai yace

keee ubanwa ya baki waya ?

dagowa tayi ta dubeshi a hankali ta mayar da kanta ga abinda takeyi a wayar tace mishi to dai yaya a dinga saita harshe in an tashi tambaya dan kasan ni fa amsa nake bayarwa dai dai da yadda aka tambayeni

yana shirin yin magana sajida ta shigo ta kafesu da ido kallon da take mishi ya qara tunzura shi yace

wato yusuf ne ya siya miki waya ko?
ke har kin kai namiji ya baki abu ki karba ko nawa kike duka da zaki rike waya yanzu duk iskancin da kikeyi ina kyaleki ne badan ina jin tsoronki ba sai dan gani nakeyi wannan jikin naki idan na tashi dukanki babbalaki zanyi dan haka ki mikomin wayar nan in mayar masa da abarsa tun kafin ranki ya baci

ko kallonsa batayi ba ta shiga kallon wayar datayi dialling har akayi picking kafin cikin sanyin muryarta ta furta

barka da wannan lokacin my daddy

shuru ta danyi alamun ana magana daga daya bangaren

murmushi ta saki kafin tace kowa lfy shine ma yace yana son magana dakai tana fadar haka ta mika masa wayar

cikin bacin rai yace uban waye ?

ubanka ne yaji an fada daga cikin wayar take yadauki murya cikin rawar hannu ya karba kafin cikin girmamawa ya shiga gaida daddy

naji kana tambayar uban waye shine nace ubanka ne yanzu ka gane ai ko?

ah ah wlh daddy ba haka bane ina tambayarta wanda ya siya mata waya ne

16 / 33