Author : Asma Baffa Category : Romance
dagowa ta kalleshi.
Yes! nasan kinji abinda nace,
Yanzu Alhaji kana nufin idan yaran Nan suka saki wadannan 'yan kauyen Nima sakina zakayi?
Tabbas kuwa sakin ma uku!!
Idan Kuma na janye fa?
Aurenki na Nan.
Shikenan na janye furucina Amma Kai kana ganin kayimun adalci? Kayiwa yaran adalci?
Wannan ke kike ganin haka Dan haka na sallami kowa ku tashi ki tafi maganar da naso yi ayita wani lokacin,kuje Allah yayi muku albarka.....
*Alkalamin khady* โ
[3/18, 8:08 AM] El~hajj: ๐๐๐๐๐๐๐
*AWESOME WRITER'S ASSO..* ๐ฎ
(Place of the excitation n'd pleasant writer's)
*TAME GARI*
NA
*Khadeeja usman*
4โฃ7โฃ
Sam yusrah kin yadda tayi ta koma dakinta,inda mamy ta goya Mata baya tace tayi zamanta har saita Gama aiwatar da shirin datake yi akansu.Shiko Daddy Yana lura dasu Amma ya zuba musu ido yace gara ma ayi hakan an samu ragin wata fitinar.
Kishi sosai mamy ke nunawa mama mariya yayin da tayi dibar Karen mahaukaciya da ita ta watsar,hakan ya Kara kuntata zuciyar mamy aikuwa ta kudurta aranta saita sake sabon shiri,Dan wallahi dole saita kada wadan Nan kauyawan rigarsu.
****"****"****
Tun sassafe ta tashi ta Dora musu abin Kari kasancewar ta kwararriya wajen iya girki,Dan haka ta shirya musu lafiyayyen break fast,bayan ta Gama jerawa a dinning ta koma tayi shirinta cikin kwalliyarta kamar a baya,sai ka rantse kace ba abinda ke damunta Nan kuwa damuwar dake tattare da zuciyarta ta zarce ta kowa a gidan,kawai dai ita kadai ta barwa kanta sanin abinda ta kudurtawa zuciyarta.
Saida ya shirya tsaf cikin shigarsa ta shirin fita office kafin suka hallara a falon,kujera taja Masa ya zauna kafin ta saki murmushi tace! Bari na Kira amaryarka ko?
Dagowa yayi ya kalleta da kyawawan fararen idanunsa,danshi harga Allah yama Manta da wata amaryarsa da aka kakaba masa baice da ita komai ba ya mayar da idanunsa kan karamin cup din dake gabansa,kafin yace! Ki zauna kawai Bari naje na kirata,ah ah wannan ai bamai yiyuwa bane ta Yaya zan wahalar da ango kawai kasha zamanka zan Kira Maka kanwar tawa da Kaina,shikenan!! Kawai ya furta ita Kuma ta juya ta fice a falon a zuciyarta tana dariyar mugunta domin wannan shine plan dinta na farko Wanda zata Fara rikita kwakwalwar Mai gidan dashi.
Shikuwa bayanta yabi da kallo harta fice ta nufi bangaren Dije a zuciyarsa Yana mamakin canzawarta Dan yayi mamaki kwarai sanin halinta da yayi akan kishinsa to Amma ba mamaki dama ance wasu matan zaka ga sunada zafin kishi kafin ayi musu Amma da zarar anyi shikenan sai kaga sun bada Kai bori ya hau,gashi ko ya tabbatar dama Bata wani Bata lokacinta ba danshi bayan ita baya ganin wata mace Dan sajida ta daban ce a gurinshi tana Kula dashi matuka iyakar iyawarta to Mai zaisa yace zai Mata wata kishiya! Da ire-iren wannan tunanin ya tsaya jiran dawowarta.
Itako burinta Bai wuce taga fuskar wadda aka kakaba wa mijinta ba,Dan ko ranar da sukaje gun Daddy Bata wani kalleta sosai ba Dan hankalinta ba'a kanta yake ba,gashi kuma an cewa su tafi ita ta Fara fita da zumbulelen hijabi ko kafin su fito har sun hangota ta shige.
Batare da tayi sallama ko knoking ba ta Danna Kai falon,tsayawa tayi tana karewa Falon kallo yadda ya tsaru tamkar a kasar turai ga kamshi dake tashi ta ko Ina,ba laifi ta yaba da tsabtar amaryar da miji Bai damu da ita ba,Kai tsaye ta nufi bedroom din Dan tana kyautata zaton Nan ne kasancewar komai tsarin ginin irin nata ne,Kai tsaye ta turn kofar ta shiga,inda ta iske Dijen tsaye gaban mirrow sanye da riga da wando na Pakistan Amma wandon pencil ne sai rigar Mai umbrella kanta take tajewa tana son sa ribbons taji alamar bude kofarta,a zatonta ko Zainab ce harta juyo zata aza Mata masifa sai tayi ido hudu da sajida,cike da mamakin meya kawo yarinyar dakin amaryar Habeeb,inma dai ita ta jawota Dan shishshigi da Nuna son dangin miji ko kasancewar ta 'yar kauyensu ,to wannan dai annoba ce daban take da sauran mutane.
Duk da Dijen ta dan ji zafin shigo Mata daki da tayi bako sallama(kaji su Dije Koda yashe ma tasan dadin auren๐) Amma saita share tare da fadin,lah!! Aunty kece da kanki?
Um nice Ina Mai dakin take?
Dije gani tayi kamar ta Raina Mata hankali Dan haka tace,tana wanka' wani abun ne a fada Mata inta fito?
Eh! kice Mata muna jiranta wajen yin bareak fast.
Ok to zan fada mata
Harta juya sai Dije tace Aunty harda ni?
Gaskiya ban San dake aka zo ba Dan haka banyi dake ba sai dai ki leka side din Naseer tunda 'yar uwarku ce ko Kya samu saura.
Hakane can bama iya saura ba ko sabo za'a dafa min tunda duk tsatso Daya muka fito an San darajar hatsi da tsaba.
Taso tankawa yarinyar saita tuna a dakin wa take karta rainata inta fito Dan haka ta juya abinta ta fice
Tana fita Dije tace! Shegiya Mai siffar samudawa wato ni Zaki rainawa hankali Wai a nufinki bakisan wadda aka daurawa aure wancan rafkakhan din mijin naki aure da ita ba, ni naci uwar rainin wayo,haka tayi ta masifa harta gama shiryawa sannan ta fita.
Tana zuwa ta tarar da su zaune da alama amaryar suke jira,batare da Bata lokaci ba taja kujerar dake fuskantar ta Habeeb ta zauna,wani kallo sajida ta watsa Mata tana shirin yimata magana Habeeb ya rigata,ta hanyar fadin,ke wannan wane irin iskanci ne! Ke dama gaki ga yadda kike Kai fall fasinjoji Zaki tashi ki fitowa mutane ba dankwali!
Ai a tunanina ba laifi bane Dan mace ta nunuwa mijinta baiwar da Allah yayi Mata,Kuma ma Ina laifin wannan kwalliyar tawa ai Kai da gani kasan dama Dan irinka sabon ango akayi ta.
Kwata-kwata rasa abin cewa yayi,itako sajida wani sabon tashin hanline ya risketa sakamakon Jin Wai Dije itace Amaryar Habeeb,wannan karon duk yadda taso kissa tayi aiki Ina!! abin yaki yiyuwa sakamakon Jin zuciyarta da tayi tana Mata suya da Kuma tunawa da tayi da wasu abubuwan da suka faru a baya,Wanda alamu sun Nuna karara Habeeb nason yarinyar Amma Koda tayi Masa magana ya kanainayeta da dadin baki irin nasu na maza,shiyasa a lokacin ko tayi tunanin wani abun sai ta tuna yadda yake santa da Kuma yadda yake Nuna Mata baida ra'ayin yin Mata biyu,hakan yasa ta sakankance ta yadda dashi Ashe kwaf Daya yake shirin yi mata! Wayyo ita kanta Ina zata San kanta.Duk yadda taso ta danne abun kin yiyuwa yayi,Dan haka cikin bacin rai tafar magana,
Me nake shirin gani Habeeb? Ko ince nake shirin ji? Kana nufin Khadija ka aura? lallai namiji buhun Kaya ! Namiji buhun barkono! Namiji bishiyar lalle ko ince iccen magarya,wallahi ka cuceni ka rasa da wadda zaka hadani sai da wannan yar tatsitsiyar yarinyar Kai ko kunya ma bakaji ba,duk yadda nake Kula da kai Dame na rageka?
Tunda ta Fara maganar ya kafeta da ido,yayin da Dije ta Nuna ko a jikinta ta Fara aikawa cikinta abinda yake bukata,sai da taji ta koshi kafin ta dago ta dube su sannan taja kujerar baya da niyyar barin gurin,sai ta tsinkayi muryar sajida na fadin wallahi sai dai ka zaba ko ni ko ita Dan bazan iya kishi da kanwar kankwata ba,wannan ma ai raini ne Kai ko kunya bakaji ka tunkari wannan ficikar yarinyar a matsayin miji.
Zancen yaushe kuma! Wallahi Aunty kada ki yadda kawai ki bashi zabi ko ke ko ni din,Nima zanga ko inada matsayi a zuciyarsa ko banda,sai dai fa kafin ki yanke hukunci kiyi tunani Dan zawarci a wannan shekarun naki hmmm nayi shuru tasa Kai ta fice tana dariya.
*Pls.ku Kara hakuri*
*Alkalamin khady* โ[3/18, 8:08 AM] El~hajj: ๐๐๐๐๐๐๐๐
*AWESOME WRITER'S ASS..* ๐ฎ
(place of excitation n'd pleasant writer's)
*TAME GARI*
NA
Khadeeja Usman
4โฃ8โฃ
Tana Jin sajida nata balla ruwan bala'i tana cusa Mata ashar,Amma ta share ta fice abinta,shikuwa gogan Yana zaune ya zuba wa sajida ido kawai,ganin yadda taketa kumfar baki ,Saida yaga takai aya kafin yace,
Idan ni na aureta banji kunya ba,ke ai gashinan kin tsaya kina cacar baki da 'yar ficikar yarinyar da Kika raina,Kuma in baki Manta ba da kike cewa na zabi Daya ko ita ko ke! Shin kin Manta ita din zabin mahaifina ce? Kin San kuwa babu yadda za'ayi Dan uwana ya karbi zabin da aka mana,ni saboda nine fitsararre bijirarre ince bana so! To ai Koda hakan zata kasance sai dai na sakeku ku duka biyun in zauna hakan ba mace.
Habeeb!! Ashe dama zaka iya rabuwa Dani? Ashe dama duk fadar da kake yi kana cewa aurenmu ba saki ba yaji kishiya har abada ashe duk karya ce,sai yanzu nake gane kuskuren Dana tafka,da girmana da shekaru na ka binne ni a Bai bai,kasa na yadda da dukkan yaudararrun kalamanka,na Manta da cewa ku maza ba'a baku amana,shikenan naji na Kuma amince bazaka iya rabuwa da ita ba kasancewarta zabin mahaifinka,amma ni dole ka rabu dani,Kuma wallahi bazan zauna zawarci da cikinka dake jikina ba,zuwa zanyi na tunkudar dashi tunda ubanshi Bai damu dashi ba sam,.
Tunda ta ambaci tanada ciki ya nemi nutsuwarsa ya rasa,da mugun sauri ya ture kujerar dayake Kai ya karaso inda take tana matsar kwalla,kokarin Kama hannunta yake Amma taki yadda,be barta ba har Saida ya samu nasarar rike hannun nata kafin ya kura Mata ido nadan wani lokaci,duk da taki dagowa ta kalleshi,amma hakan baisa ya kauda idonsa daga gareta ba,Jin yaki cewa komai yasata dago kanta sukayi ido hudu dashi,ta so ta janye idonta Amma takasa,hakan yasa suka kurawa juna ido na Dan wani lokaci.
Shine ya Fara magana ta hanyar fadin,yanzu ashe Zaki iya rabuwa Dani? Dama Zaki iya salwantar da jinina dake jikinki saboda kin da kikemin? Ashe bakya Sona? Kisan Kai fa kike shirin yi! Da sauri ta dago ta kalleshi,yes!! Kisan Kai Mana Kuma harna mutum biyu,domin muddin Kika zubar da abinda ke cikinki wallahi Nima mutuwa zanyi,a da bana son kisami ciki da wuri,Amma daga baya sai Allah ya jarrabeni da son haihuwar,wallahi Ina son baby fiye da kaina,Ina son Inga na haihu dake saboda kinada matsayi mafi girma a gurina,Yana Gama fadar haka ya jawota ya rungume ta tsam a jikinshi,ya shiga bubbuga bayanta alamar rarrashi,kafin yafara Rada Mata a kunne,haba masoyiyar my kifin gwangwani,ki kwantar da hankalinki,ai babu wata macen data Isa ta kamoki bare harta zarta ki,waccan ni wallahi badan kin tuna da ita ba da ni nama Manta da zamanta Kuma kema shaida ce,kiyimin adalci!
Tabbas maganganun sa sunyi matukar tasiri Dan haka ta saki jikinta ta Kuma Kara yadda da duk abinda ya fada mata,
Rakoshi tayi zuwa parking space har Saida taga fitar shi kafin ta dawo da tunanin nemawa kanta mafita,Dan Zama guri Daya da wannan aljanar tsautsayi ne ai! To wazata Kira suyi shawara ,kawai gida yakamata taje,tana shiga ta dau waya ta kirashi ta shiga sanar Masa zata gida,
Meyasa baki fadamin tun Ina gida ba sai yanzu?
Wallahi ji nayi gidan yayimin zafi Ina son zuwa ganin ummana zuwa gobe sai in dawo.
Me yasa har sai gobe?
Saboda Ina son haduwa da Daddy kasan kuwa baya dawowa sai dare dole sai dai in kwana.
Amma kin San ban iya bacci nikadai ba ko?ya kike so nayi?
Hakuri zakayi sweet husby yau Daya dai!
Shekenan ki gaishe su ki kulamin da kanki da Kuma baby na.
Ok don't mind bye!
Ok bye!!
Tana kashewa Jakarta kawai ta dauka da key din mota ta fice.
******
Tun fitar ta Dije ta gani domin tana gurin mama mariya Nan ta yini,ganin yamma tayi batada shirin komawa bangarenta yasa mama mariya tambayarta bazata tafi taje tayiwa mijinta girki ba sannan ta kimtsa kanta!
Bata fuska Dije tayi tare da fadin to ni girkin me zanyi Masa bayan ma Bai damu Dani ba! Ni tunda aka kawoni yaune fa kawai magana ta hadani dashi
[3/18, 8:08 AM] El~hajj: ๐๐๐๐๐๐๐
*AWESOME WRITER'S ASS..* ๐ฎ
(Place of excitation n'd pleasant writer's)
*TAME GARI*
NA
Khadeeja Usman
4โฃ9โฃ
Kina nufin kicemun har yanzu baku tsaya kun fahimci junanku ba?
"To mama ya zanyi Masa! ni zan jawoshi kome" nifa wallahi dama wannan auren nayi biyayya ne kawai amma wallahi bana sonshi inada Wanda nake so!,kawai kunyar Daddy tasa na amince.
To ai kin gama magana tunda har ya kasance kin amince din Dan Daddy'n naku,to bara kiji ki tsaya ki nutsu ki kwantar da hankalinki kibar duk wani sakarci ki kula da mijinki inba haka ba kina gani kishiya zata Miki fintinkau,ki Zama 'yar kallo,bare ke da kikeda wannan kishiyar uwar Mata ai ko ni keda ita saina girgiza bare ke 'yar tsakuwar Nan...
"Dariya Dije tayi sannan tace to ai kinada mamy" Kuma kinsan a haife ta haifi Anty sajida.
Rabu da wannan wayake ta Tata! Ai bata Kai wannan gogewa da Zama 'yar zamani ba,yanzu dai duk mubar wannan maganar wallahi indai baku tsada hankalinku kun tsaya kun fahimci junanku ba! To ko zan sanar wa da Alhajin inya so ayita ta kare asan abinyi a raba auren kowa ya huta.
Duk da harga zuciyarta Bata Jin son Habeeb Amma da mama mariya ta ambaci a raba auren Saida gabanta ya fadi,taji kuma bata bukatar hakan,Dan haka saita marairaice fuska kamar me shirin yi kuka,
Ni fa ba haka nace Ina son a raba auren ba kawai dai...sai Kuma tayi shuru.
Yo ai ba fada kukayi ba Amma kun Nuna cewa ku din 'yan zamani ne ai Dan haka gara ayita ta kare!
Ni dai gaskiya bana son a maidani karamar bazawara,asa 'yan maza su koma yimin Dan Kira gara koma meyi inyi.
Yauwa ko ke fa,ki zage damtse ki kwaci mijinki hannun kishiyarki bawai ki rabasu ba ah ah kowa tasa ta fishsheshi ki kafa gwamnatinki kema!
To ta Yaya?
Au kijini da sakarcin banza! Duk hudubar da aka dinga nanata muku da za'a kawoku ta tashi a banza kenan? Bakiga 'yar uwarki yadda tayi maliyan lukwi abinta ita da mijinta ba, to Bari kiji.....
Nan ta shiga zayyanowa Dije abubuwa masu matukar muhimmanci da tasiri a rayuwar aure,Nan Dije fa ta nutsu ta shiga hadda da bita.
Bari in tashi in tafi In Fara tun yau wallahi Dan ca zanyi a raba kwana,Dariya mama mariya tayi a ranta tana jinjina rashin kunya irin ta diyan zamani inba haka ba,taya Dije har tasan wani raba kwana.
To naji uwar mata kafin ki tafin jirani Ina zuwa! Cewar mama mariya data nufi dakinta.
Fitowa tayi dauke da kofi a hannunta ta mikawa Dije tace maza shanye shi.
Karba tayi takai bakinta inda tana dandanawa tayi saurin dauke cup din tare da fadin,wallahi mama ba dadi,
Ai dama bance Miki da Dadi ba Dan haka shanye shi maza inkuma so kikeyi kishiyarki ta fiki to Dan bakisan shirinta ba.
Ai kafin mama ta rufe baki Dije ta kafa Kai ta kusa zuke abinda ke ciki.
Dariya ce ta kwacewa mama Dan a yadda ta fuskanta Dije nada Dan banzan kishi tsabagen shirme da jaraba ne yasa bazaka gane ba Amma ta hango fa akwai cakwakiya.
Tana gama Sha mama ta Bata wani turare tace ungo wannan shafawa zakiyi shi Kuma a gabanki Yana gyara gaban mace matuka da kuma sa kamshi karba tayi ta mike tare da fadin to mama sai na dawo.
Kul!! Naga kin dawomin Nan Dan Nima babanku yau Nan yake.
Dariya Dije tayi tace Kai mama bako kunya!
Kinci gidanku keda kunyar ni maza wuce kiyi uzurin gabanki.
Dije na fitowa ta shiga part din Zainab,Nan ma wasu Dalasiman ta shiga biya Mata tare da dada koya Mata wasu darrusan,ganin so suke su cike Mata kwakwalwa yasa ta mike ta fice tayi nata wurin.
**********"""*********
Tsaye na Hango Dije a kicin anata faman girke-girke hada wannan Gama wannan harta gama duk abinda ranta yake so,Bata San takamaimen yanzu lokacin dawowarshi ba amma dai Bari ta jera komai akan tsari,hakan tayi sannan ta shige daki ta cire kayanta tare da daura towel ta afka toilet,wanka ta santalo kafin tazo ta sallara kwalliya,sosai tayi masifar kyau,rasa kayan da zata Sa tayi saita tuna da akwatunansu na lefe da Daddy ya Basu jiya,budewa tayi ta shiga duba kayan ciki,Kaya ne masu kyau da Kuma tsada,Dan haka hannunta ya sauka kan wata Arebian gown maroon colour,zarota tayi ba qaramin kyau rigar tayi Mata ba Dan haka tasa undies tare da zura rigar,kuma cikin ikon Allah kamar an gwada da ita tayi mata dass a jikinta tana kokarin Kara gyara kanta taji alamun horn,lekawa tayi ta window aikuwa taga shine ke dawowa da Naseer,da sauri ta Kara murza powder tare da Kara fesa turare ganin karfe shida harda 'yan mintina,dankwalin rigar na hannunta tayi saurin fita falonta Dan hakan na cikin karatun da aka koyar da ita.
Sallama sukayi da juna inda kowa yayi nasa wuri, Direct part din sajida ya nufa inda Yana zuwa ya murda kofar jinta yayi a rufe gam,Nan ya shiga knoking Nan ma shuru,tsaki yayi kafin ya fito da wayarshi ya shiga Kiran layinta,shuru Bata daga ba har yayi Mata missed call kusan biyar dole ya hakura ya mayar da wayar aljihunsa Yana me Kara Jan wani tsakin dayafi na farko,tabbas ya gaji ga yunwa gashi Yana son yayi wanka ya zaiyi to? Ko part din mamy zaije to ai fishi takeyi dasu har yanzu ya salam! Ya furta a hankali dole ya koma office kenan yayi wanka yasamawa kansa abinda zaici duk da wannan tunanin da yayi baisa ya tafin ba saima jingina da yayi da bayan kofar.
Duk abinda yakeyi tana kallonshi,zuciyata na raya Mata shin taje ta sameshi din Kota share,tunawa da tayi inta ci gaba da rayuwa dashi a haka itace Bata da riba danshi yanada matarshi,hakan yasa ta mike ta fito kamar Mara gaskiya ta tunkaro gurin dayake, kasancewar idanunsa lumshe suke Kuma flat sheos ne a kafarta shiyasa Sam Bai ji takunta.
Jin wani daddadan kamshin turare daya had da sassanyar iskar dake bugawa yasashi bude idonshi a hankali,fess ya saukesu akan 'yar kyakkyawar farar yarinyar,duk yadda kauda idonsa akanta kasawa yayi illah ma wani Abu dayaji Yana fuzgarshi zuwa gareta,Yana tsaka da tunanin yaji muryarta tana fadin sannu da zuwa Yaya!
Kasa amsawa yayi Dan ji yayi wannan kamar ba Dijen Daya sani ba fitinanniya,Mai tsiwa da jarabar tsiya.nan ma Bai Gama tunanin ba yaji ta Mika hannu tare da sabule jakar dake sakale a kafadarshi,tare da Kama hannunsa zuwa bangarenta,kamar wani soko haka ya bita zugwi- zugwi har suka karasa ta murza