Author : Asma Baffa Category : Romance
saita Rama inta warke....
*Alkalamin khady* โ
[7/9, 9:00 AM] El~hajj: ๐๐๐๐๐๐๐๐
*AWESOME WRITER'S ASSO...* ๐ฎ
(palace of excitation n'd pleasant writer's)
*TAME GARI*
Na
Khadeeja Usman
6โฃ0โฃ
Yau Bai samu damar dawowa da wuri ba, kasancewar yayiwa wani aiki a asibiti,Sam Bai kula da sashen sajida bude yake ba,Dan haka direct part din Dije ya nufa kamar yadda ya saba.Yana shiga Bai taddata a falo ba Dan haka ya kutsa Kai cikin daki,kwance ya hangota saman bed ta kudundune da alamun tanajin sanyi,hakan ya tabbatar Masa da zazzabin ne ta dawo Mata,tilasta Mata yayi dole suka tafi asibiti a Daren ko hutawa baiyi ba,allurar paracetamol yayi Mata Dan yasan Bata son shanshi,sannan ya daura Mata ruwa,sai wajen 12 suka dawo gidan,inda ya cika da tsananin mamakin ganin part din sajida da wuta,karasawa yayi da ita dakin ya hada Mata ruwa Mai zafi tayi wanka,abincin Daya gani saman dinning yaje ya debo abinci a plate,Saida ya tilasta Mata sannan taci kadan,Dan gudun kada tayi amai yasa ya kyaleta,magani ya Bata Tasha sannan yasa ta kwanta, Saida ya tabbatar tayi bacci sannan ya mike ya nufi part din Sajida Dan yaga waye ya kunna wutar dakin.
Yana shiga ya iske falon gyare tsab dashi yanata tashin kamshi,Sam Bai lura da ita ba sai muryarta ya tsinkaya tana fadin "you're welcome my man",Yana shirin yin magana yaji ta rungumeshi,janyeta yayi daga jikinshi cikin daure fuska yace,
"Ke waya baki izinin dawowa?" Ba cewa nayi ki zauna har saina nemeki ba! Ya fada as husky voice.Sosai ta marairaice fuska cikin salonta na kwarkwasa ta Fara fadin,
"Haba nurul hayati,kana tunanin duk abinda ya faru ban fika Jin ciwo ba,nice fa zanfi kowa cutuwa,Kuma wallahi ni Koda na Sha maganin da zummar maganin ciwon Mara Nasha,ban San cewa hakan zata kasance ba,nayi mamaki da ka kasa fahimtata,ta karasa maganar tare da sakin kuka,duk da Yana Jin haushinta,Amma sai yayi nazarin maganar ta tabbas ta yiyu abinda ta fada ya Zama gaskiya,Dan haka ya kalleta a fili yace,
"Amma ai cewa nayi saina nemeki ko? Waya ba ki izinin dawowa?.
"Kayi hakuri my wallahi na kasa samun nutsuwa da rashinka kusa Dani Sam bazan iya rayuwa babu Kai kusa dani ba kayimin uzuri mijina ka yafemin,sosai take kuka ta rungumeshi,hakan yasa tausayinta kwarai,bayanta ya shiga shafawa alamar rarrashi.
"To ya Isa haka kukan kinji,ya fada yana bubbuga bayanta alamar rarrashi,Kara lafewa tayi tana sauke ajiyar zuciya,Dan batama yi tunanin shawo kanshi zai zo Mata da sauki haka ba.Hannunsa ta Kama ta nufi bedroom dashi,ruwan wanka ta hada masa,Saida ta taya shi wankan sannan itama ta sake yi,sannan suka fito, kasancewar dare yayi sosai yasa Bai ci abincin data tanadar Masa ba saboda bayacin abincin dare late,bayan sun Gama ne tunaninsa ya koma ga Dije ya shiga tunanin koya jikin nata?,duk abinda yakeyi tana lura dashi,Dan haka ta shiga Masa salon iri-iri Wanda ya shagaltar ta dashi harya Manta da batun Dije.Sosai ta Nuna Masa tayi kewarsa inda shi ma da kanshi ya Nuna hakan,sunsha soyayya sosai inda daga Nan sai bacci Kuma Wanda har yasa su makara.
Tunda asuba ta farka taga bata ganshi ba,sai tayi tunanin masallaci yaje,Dan haka tana yin sallah ta Kuma komawa bacci,sai wajen goma ta tashi shima da kyar,Dan yanzu sosai take morewa bacci,Koda ta tashi yau ba zazzabi sai dai Dan rashin kwarin jiki da batada,tana shirin Fara gyara gidan taji sallamar Zainab,sosai taji dadin shigowarta,Dan haka ta yakar hakora, tambayarta tayi jikinta sannan tace,
"Dama zuwa nayi inga yadda Kika kwana da jikin,Dan nasan tunda waccan me kirar samudawan ta dawo yau ana can ana kashe arna"โฆ
Sai a lokacin Dije ma ta tuna da dawowar sajida Dan Sam tama Manta, murmushi tayi tare da tunawa da lallai Kam Bata ganin Habeeb,tunda gimbiya ta dawo.
Kallon Zainab tayi tare da fadin, "ke yarinya ba dole yayi rawar kafa ba,first love dinshi ce fa! Ni wallahi nama Manta da ta dawo,nasan Yana can ana ta kashe shi da luv shiya sa,Dan haka Ni Bari in tashi in samama kaina abinda zan afawa zumbili na".Tare suka shiga kitchen din sukayi girki Mai sauki,sunayi suna hira, har suka Gama,bayan sun Kare ne sun ci sun koshi sannan Zainab ta gyara Mata gidan,Dan Dije kasa tashi tayi sai bacci,Sam batayi wani tunanin Habeeb ba.
*****
Kwana biyu cif ya kwashe batare da yasata a idonshi ba,duk yadda yaso zuwa dubata sai tasan salon da tayi Masa ta shagaltar dashi,yau ta Kama girkinta ne,Dan haka yaketa zumudi ya tashi aiki,sosai ya fahimci Sajida shiyasa yau ya kudiri niyyar sai magrib ma zai koma gidan,yasan duk bala'i dai lokacinta ya fita.
Saida yayi sallah sannan ya dawo,Yana shiga ya isketa zaune saman sallaya ta idar da sallah tana addu'a,wanka ya shiga Dan haka tana idarwa ta Mike ta zauna saman gadon tana jiran fitowarshi,ya Dan jima sannan ya fito,da kallo ya bita,sai yaga kwana biyun dabai ganta ba harta Kara mishi girma da Kuma kyau, murmushi ta sakar Masa,shima ya mayar Mata da martani,Sam baiyi tunanin bazatayi fushi dashi ba sabanin hakan Daya gani,itako Dije anata bangaren Bata ga abin fushi ba Dan ta dauka haka akeyi in kanada kishiya har sai kwananka zakaga miji,sosai suka Nuna sunyi kewar juna,inda Nan da Nan suka suka shiga aikawa juna sakonnin soyayya.Bayan sun Sami nutsuwa ne suka Kara yin wanka,kwance take jikinshi tanata Mai korafin jikinta ciwo,cikin salon shagaba.Babu ko knocking sukaji ana Murda kofar alamun ana so a shigo.
Janyeta yayi daga jikinshi yaje ya bude kofar batare ma Daya tambayi waye ba,Sajida ce tsaye sanye cikin Riga da wando theree quarter,Bata Bari yasamu damar tambayarta meya kawota ba,illah rabawa datayi ta gefenshi ta shige,sakin kofar yayi ya juyo tare da fadin,
"Ke malama lafiya Zaki shigowa mutane daki Kai tsaye haka!"
Farrrr tayi da ido itako Dije kallon ikon Allah ta tsaya yi,Dan wata dariya ce tazo Mata,wadda takasa danneta,ganin hakan yasa Sajida nufar inda Habeeb yake Dan ta kunsawa Dije bakin ciki,sakalo hannunta tayi a wuyansa tare da kashe murya,Wanda shi Habeeb tsabar bakin ciki ma ya hanashi ko motsi,cikin wani salo tafara furta, "Haba my man! Shine ka barni cikin kewar ka,kasan na Saba da Jin dumin jikinka, musamman kwana biyun Nan,ka nunamin Inada muhimmanci a rayuwarka,kasa na yadda nafi kowacce mace kamar yadda ka fada,Dan haka.......Bata karasa ba sukaga hasken flash,dukansu waigawa sukayi,sukaga Dije tsaye rike da wayar Habeeb tana musu hoto,Yana shirin yimata magana yaji tace,
"Dan Allah tsaya Yaya sauran Daya,gani nayi kunyi min Kama da wata tunkiya da ragon Inna da nake wasa dasu lokacin Ina karama,sai Naga Anty Sajida sakkkk tunkiyar wallahi.....๐
Comments with
*Alkalamin khady* โ
[7/9, 9:00 AM] El~hajj: ๐๐๐๐๐๐๐๐
*AWESOME WRITER'S ASSO..* ๐ฎ
( _palace of excitation n'd pleasant writer's_)
*TAME GARI*
NA
Khadeeja Usman
6โฃ1โฃ
Sakin baki Habeeb yayi Yana kallon Dije,dan yama rasa abinyi,itako Sajida iyakar Shaka ta shaka,.Basu ankare ba suka ga ta nufo su tana fadin,"yaya kudan gyara muyi ๐คณ selfie Yaya saika Dora a secren server din wayarka kowa yaga matanka.Cikin zafin nama Habeeb ya mika hannu da niyyar wafce wayar, aikuwa sai gani yayi ta kwasa a guje zuwa falo,Sajida da tun dazu ta rabu da jikin Habeeb tsabar takaici kamewa tayi a gurin,shi kuwa rufa Mata baya yayi,zagaye falon suka kamayi,inda daga karshe ya cafke ta,ya shiga kokarin kwace wayar,boyeta tayi a jikinta, hakan yasa ya matseta tare da kokarin lalubar wayar,har suka fada saman kujera,mutsu-mutsu ta shiga yi,ya rasa yadda zaiyi da ita,Dan haka yafara Mata cakulkuli,dariya take yi sosai tana gaggantsarewa,shi kuwa hakan datakeyi ya Fara jefa shi cikin wani yanayi,sosai take shigewa jikinshi,Wanda hakan ya Kara canza akalar lamarin,Wanda yasa suka Manta da batun waya suka shiga romancing din juna.
Cikin wannan yanayin Sajida ta iske su, Wanda tsabar bakin ciki Bata San lokacin da taji hawaye na zubo Mata ba,Dan haka ta nufi kofar fita,cike da Dana sanin zuwanta part din,gaskiya wannan plan din na mummy Sam ba basira a ciki,gara Nima nasake taku,wallahi saina ci uban yarinyar nan,haka ta karasa bangarenta tana ta sakawa da kwancewa,tare da kudirewa ranta saita ci uban Dije.
Su kuwa tsuntsaye sosai suka shagala,inda suka kasa jurewa har Saida suka Isa babbar head quarter,sosai suka samu nutsuwa,sannan suka yi wanka,magani Dije Tasha yayi Mata allura Nan ta zube a jikinshi tanata mishi shagwaba,shi ko duk yabi ya sukurkuce Mata Dan a rayuwa Yana son mace Mai shagwaba,Dan haka ya kyaleta suka ta shan shagalinsu har bacci ya dauke Dije.
*******
Yau Akayi sunan Yusrah,inda yaro yaci sunan Daddy wato,(Khamees) suna kiransa da sudais,sosai akayi shagali,kowa yayi rawar gani,domin kuwa yaro yaga gata,su mamy da Daddy sun yi rawar gani hakama Habeeb,bare Kuma angon karni.Sosai su Dije suka dau wanka,ansha pic kala-kala,sai muce Allah ya Raya sudais.
*****
Yau kwana biyu da yin suna, Alhamdulillih! Jikin Dije ta Dan ji dadin shi ko Dan treatment din data Samu kwana biyu,zata iya cewa tun ranar da Sajida ta shigo part dinta basu Kara haduwa ba,sai ranar suna, tasan abinda tayi matan Nan ne yasa ta yin shuru kwana biyu,Kuma dama tana sane tayi hakan,gobe ma ta Kuma.
Tana zaune ita kadai,taji duk zaman ya dameta,gashi mama mariya Bata Nan,Dan taje gida wani biki da akeyi,Wanda su kansu su Dijen su so zuwa Amma kememe mazajen suka hanasu,ganin ta gaji da zaman ita kadai gashi Sha biyu ne yanzu na rana,Dan haka ta yanke shawarar tafiya gurin Zainab Dan ta Dan rage lokaci,fitowarta kenan tana shirin rufe kofa ta tsinkayo tahowar Sajida ta nufota,dakatawa tayi da rufe kofar inda dai-dai Nan ta karaso,tana isowa Dije tace,
"Ah Aunty,kece mu shiga Mana",duk da tasan da akwai abinda ya kawota,Amma ganin Bata Nuna ba yasa itama ta bita hakan,ba yabo ba fallasa suka shiga,inda Sajida tana shiga gadan- gadan ta nufi gaban T.V din dake manne a bango,ga mamakin Dije gani tayi Sajida ta fito da muciya daga jikinta tahau farfasa kayan wajen,duk abinda takeyi Dije na kallonta Bata Kuma yi yunkurin hanata ba,Saida ta tabbatar ta fasa duk wani abu datasan zai fashe,sannan ta tako zuwa gaban Dije,wani shu'umin murmushi ta sakarma Dije kafin ta juya tace,kinyi kuskure khadeeja,Habeeb na Sajida ne ita kadai,naso kin bar gidan Nan salin alin tun kan na Nuna Miki kalata,Amma Naga bakyajin magana,kin samu guri kin mike kafafu,to ki sani kishi da mace kamar Ni ba abune Mai sauki ba,Dan haka ki jira abinda zai biyo baya,tana Gama fadar hakan ta juya ta fice,yayin databar Dije tsaye da tsabar takaicin barnar da tayi mata.
Zama tayi saman kujera,tare da dafe kanta,yayin da takejin wani tukukin bakin ciki na taso Mata,bawai na komai ba,sai na barnar da Sajida tayi Mata,amma babu komai wallahi zata San tayi.
Ji tayi an turo kofar da sauri,yayin data tashi a firgice tana kallon kofar,Habeeb ne sai Sajida a bayanshi,gani tayi Yana Binta da kallo,inda ita Kuma ta maida kallonta ga Sajida,gani tayi ta sakar Mata murmushi,a ranta tace,hmmmm! Na fuskanci baki sanni banne har yanzu kalata Daya Kika sani Bari na Nuna Miki na biyun,Habeeb na shirin yin magana,yaji Dije tace,
"Haba Dan Allah Aunty! Yanzu Saida Kika fada Masa duk abinda ya faru? Kin San halinsa yanzu hankalinshi zai tashi,shiyasa nace kada ki fada Masa Dan nasan halin sa yanzu zai damu,Ni Kuma bana son ganinshi cikin damuwa,kin San masu irin lalurar mu in ta taso barna mukeyi,Ni yanzu babbar damuwata ma Bai wuce tunanin wace barna zasu sani nayi Nan gaba ba,gashi bani kadai ba,Kar su sa mafarki da burin mijina ya zube,amma Dan Allah Yaya kodaa sun taso kaga nafara barna,kada ayi kokarin hanani Dan nasan bazasu cutar Dani ba,ke Kuma Aunty pls Dan Allah kidaina sanar da Yaya irin wannan lamarin,Kinga mijin mu ne ya fita nema,Bai kamata mu dinga daga Masa hankali ba, yakamata mu dinga Masa addu'ane a duk lokacin da ya fita,Dan haka Yaya ka kwantar da hankalinka ba abinda ya faru banji ciwo ba garin fashe-fashen Ina lafiya baby'nka ma lafiya yake,takร rasa makaganar tana Kama hannun Habeeb tare da dorawa saman cikinta ta shiga yawo dashi.......
Dan Allah ku Kara hakuri,Ni kaina na Matsu na Gama muku book din Nan wallahi.
*Alkalamin khady* โ
[7/9, 9:02 AM] El~hajj: ๐๐๐๐๐๐๐๐
AWESOME WRITER'S ASSO..
( place of excitation n'd pleasant writer's)
TAME GARI
NA
Khadeeja Usman
6โฃ2โฃ
Sosai ta shiga tashin hankali da Jin kalaman Dije na karshe,Wanda tsananin firgita da jinsu yasa mamaki da Kuma takaicin maganganun yarinyar na farko suka bace a kwakwalwarta,kalaman Habeeb ne suka dawo da ita daga duniyar tashin hankalin data fada,ji tayi Yana fadin,
"Haba baby! Meyasa haka? Nidai zan iya jurar komai a wannan larurar taki,Amma bazan juri salwantar unborn dina ba,Dan haka ya Zama wajibi muje gurin masu magani Dan a rabaki dasu,Dan Kar wataran su cutarmin dake".
Shigewa tayi jikinsa,inda cikin sigar shagawa tace,
"Ah ah my Yaya! Kada ka Kara furta cewa zaka rabani da su,Dan idan sukaji ka wallahi sai wani bakai ba,Dan kasan dai fada da aljani ba Dadi,kawai dai sukan sauke fushinsu ne akan abinda ya Bata musu,Amma ka taba gani sun cutar Dani"?
Yana shirin yin magana,ta Dora yatsanta saman bakinsa shhhhhh....alamun yayi shuru,kada kace komai Yaya,Dan maganar daka fada dazu na batun rabani dasu ma,sun ruga da sunji komai,Dan haka sai nayi yaki wajen Basu hakuri.Tunda yaji ta furta haka ya wani canja kalar fuskarshi ya koma kalar tausayi,tare da fadin Dan Allah baby ki Basu hakuri wallahi nasan karonmu dasu ba Dadi,bisa kuskure na furta kalaman rabaku,ban San tare aka haifeku ba,wallahi ban son tuna ba......"
Katseshi tayi ta hanyar fadin, "kada ka damu yaya,ai Kai na jikina ne yanzu bakada matsala dasu,Dan sun Riga da sun sanka,sun San matsayinka a gurina,Nidai tunanina kawai wannan barnan ya za'ayi a gyarata? Tayi maganar cikin sigar tambaaya.
"Baby wannan duk ba wata matsala bace kada ki damu,yau za'a canza wasu insha Allah, bari ma na Kira wasu collogue na wani company da suka shirya Mana office dinmu su zo suga yadda za'a Kara tsara wurin kinji,fatana Allah yabaki lafiya.
"Ameen yayana!Dije ta fada tana me kashewa Sajida ido Daya,wadda ya zuwa yanzu Sam Bata fahimtar wani abu da sukayi, maganar cikin Dije ita ta tsaya Mata arai,dawowar tunaninta, shine yayi dai-dai da kashe Mata ido Daya da Dije tayi,gani sukayi ta juya ta fice tare da fashewa da kuka.Dukan su basusan dalilin kukan ba,ita dai Dije abinda ta bari, tana kukan ne Dan ganin batayi nasara ba,duk da batasan me ta fadawa Habeeb ba,illah dai tayi farin cikin kashe gobarar datayi duk da batasan mafarin tashin ta ba.
Ajiyar zuciya ta sauke,tare da fadin,
"Yayana pls kaje kaji matsalar Aunty,kaga ta fita tana kuka,ta karasa maganar tana shafar gefen fuskarshi,Kama hannun nata yayi ya sumbata kafin yace,
"Ki kula da kanki kada ki taka kwalba,zan Kira yanzu zansa a gyara.
********
Yana shiga ya isketa tana kuka,ya jima tsaye sannan ya karasa saman kujerar,tallafo ta yayi zuwa jikinshi,amma me? Saita shiga zamewa,tare da buge hannunshi,cike da mamakin abinda tayi mishi ya tsaya Yana kallonta.A nata bangaren kuwa,tsananin takaici da wata irin tsanar shi taji ya ratsa zuciyarta,gani takeyi yaci amanarta,tunda har yayiwa Dije ciki,gani takeyi ya daina sonta kwata-kwata,Dan haka ta Kara tsananta kukanta,shiko yama rasa me zai ce Mata,Dan haka ya zuba Mata ido kawai Yana kallonta.
Itako saka kawai takeyi da warwara Dan batasan ma abinda zata yi ba tukun,duk wani abu data kulla akan yarinyar Saiya warware,ta dauka Kiran Habeeb da tayi ta fada Masa cewar yazo ga Dije Nan aljanunta sun tashi harta farfasa kayan dakinta,ta dauka zatayi nasara Habeeb ya Kora Dije gida,tunda yasan wahalar da suka Sha a gidan da ita,Amma Kuma sai labari yasha bambam ta tonowa kanta abinda zai iya zamar Mata ciwon zuciya.
Ganin taki daina kukan ne,Kuma taki bashi damar jin matsalarta, yasashi tashi ya fita Dan
Yin abinda ke gabansa.
Yana fita ta Kara fashewa da kuka,tare da daukar waya ta Kira mahaifiyar ta,tana dayawa cikin kuka tafara fadin,
"Na shiga uku mummy! Na mutu, wallahi mummy I will die, she's pregnant mummy"!
Cikin sanyin murya tace,
"Kinga ki nutsu kiyimin bayanin abinda ke faruwa,Dan ban fahimci inda maganar taki ta dosa ba?
Cikin Kuka ta labartawa mahaifiyar ta abinda yake faruwa.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace,
"Sajida abinda zance dake yanzu shine,kawai kiyi hakuri,kiyi naki 'yan dabarun,Dan wallahi Ni kaina Ina cikin matsala,Dan mahaifinku Ashe ya Dade da yin aure a boye ban sani ba,duk tafiye tafiyen dayake cewa yanayi Ashe suna tare,jiya da daddare sai gashi ya dawo tare da matar harda yara hudu Kuma duk maza,Ni gashi duk taronku Mata Allah ya bani,Kuma ke kadai nasamu Kika auru,Dan haka kiji da kashe taki wutar nima inyi kokarin neman ruwan kashe tawa,tana kaiwa Nan ta kashe wayar.
Wani kukan takara dasawa zuwa can ta mike,tare da share hawayen ta,tabbas zata dau mataki,babu macen data Isa ta haihu da Habeeb,tunda ta tabbatar yanzu ba ita ba haihuwa,yanzu wazai Bata shawarar? Wa take dashi yanzu,Dan ita Sam Bata wani damu da Jin auren mahaifinsu ba,Dan dama ai yasaba,Banda abin mummy ma meye na wani kishi!( Niko nace hmmmm sajida ai shi kishi ba ruwanshi da tsufa... Fata dai ayi Mai hankali da tsafta.)
Haka ta gaji ta mike ta shiga nemarwa kanta mafita.
*******
Tunda safe take leke ta window tana Allah-Allah Habeeb ya fita,Dan yau dakin sajida yake,sai wajen karfe goma sannan taga ya fito,cikin shigarshi ta manyan kaya dinkin zamani,yayi Mata matukar kyau,sai dai fa yau bataga Yar kadaferiรฑ anzo yin rakiya ba,ko lfy oho musu! Ita dai burinta ya fitan,sai da taga megadi ya bude Masa kofa ya fita itama ta koma ta Kara kimtsawa.
๐ณ Karamar jaka trolly Naga Dije ta jawo,kome zatayi da ita oho?
Direct part din Sajida ta nufa,tana zuwa ta tura kofar,zaune ta ganta kan kujera ta Dora kafa Daya kan Daya tana yin breakfast,Jin an bude Kofa yasata maida hankalinta ga kofar Dan a tunaninta ma Laila ce da sukayi zata zo yanzu.
Kallon Dije tayi data Sha dogon hijabi har kasa,sannan ta tsaya Mata a ka ta rike kugu da duka hannunta biyu sai wani zare Mata ido takeyi,cikin ko in kula tace "malama ke Kuma lfy? Kika zo kikayi ma mutane tsaye a ka".
Hmmm "lafiyar kenan! Dama zuwa nayi na Dan taba kuruciya,Dan na kwana biyu ban tuna baya ba".
"Kamar Yaya kenan?
"Kada ki damu, zuba ido kiyi kallo,gani tayi Dije ta cire hijabin jikinta,ai da sauri