Author : Asma Baffa Category : Romance
qarasawa tayi ta durkusa ta ajiye cup daya a gabanshi sannan ta nufi gurin habeeb shima ta ajiye masa nashi shi kam ko kallonta beyi ba dan haka ta mike ta nufi hanyar fita
har takai kofa taji muryarsa yana fadin idan naqara ganinki a dakin nan wlh saina lahira yafiki jin dadi shegiya me siffar aljanu nunar rana kawai
itadai bude kofar tayi tay ficewarta inda shi kuma ya jawo coffee dinsa yafara sha jiyayi na yau yafi na kullum dadi dan wani kamshi da dan zaki zaki yayi dan haka ya dinga sirba baji ba gani shima naseer haka yayita sheqe abinshi inda shi kuma beji wani canji ba
hamma yake tayi baji ba gani yayin da yafara ganin uku uku dan haka ya mike ya nufi bedroom yana tangadi kamar dan maye sam yarasa wannan wane irin bacci ne yazo mai lokaci daya
naseer daya bishi da kallo yana ambatar lfy dai bros naganka ka sauya
cikin murya irin ta wanda bacci yakama sosai yace lfy qalau kawai bacci nakeji bari in dan matse duk da naga yamma tayi
ok a tashi lfy
bai bashi amsa ba ya shige ciki kawai shi ko yaci gaba da abinda yakeyi
yana cikin haka kusan minti talatin yaji cikinsa yayi wata irin murdawa da ya dan share amma daga baya yaji bazai iya ba dan kamar ba haya yakeji dan haka ya mike ya shiga toilet din dake falon yana ko shiga yafara antayo abinsa rai fesss
itako dije tana fita kicin ta koma ta tarar da basira harta koma daki freidge ta bude ta fara kwashe lemukan ciki kamar wadda aka sa guda biyu kawai ta bari ta dauko su ta bude tare da zuzzuba wannan maganin kashin aciki kowanne sachet daya daya kana ta mayar ta rufe alamar motsin tafiya taji cikin sauri ta rufe friedge din ta tashi ta nufi cabinet tajawo filet ta kama daurayewa kamar me wanke wanke
mamy ce ta shigo kitchen din tana kiran sunan basira ganin dije a tsaye tana aiki yasata tambayar ina basira ta shiga?
batajin dadi ne shine nake tayata kanta ke ciwo ta sha magani ta kwanta
wani wawan kallo mami ta watsa mata kafin tace hmmm ai dama aikin shiyafi dacewa dake a gidan nan maza ki daukomin lemo a friedge ki kawo mana dinning muna jira zamuci abinci
toh ta amsa ita kuma mamy ta juya ta fita
dariya dije ta fara yi tare da fadin komai kuke so zanyi muku amma ni da lfyr ku zan fanshe
lemukan ta diba ta nufi falon inda ta iske mamy da yusra har sun fara cin abincin ajiye lemon tayi da niyyar juyawa taji yusrah tace
ke aljana me siffar tumatur uban waye zai zuba miki lemon toh
dawowa tayi ta bude ta zubawa kowa ita gwara ma da suka ce ta zuba musu din dan da sun taba murfin da da kansu zasu gane an bude lemo a zuciyarta tana jinjina kalar muguntar da zata yiwa yusrah dan da Alama tata saita fi ta kowa barin gurin tayi da sauri ta nufi dakinsu
inda su hajiya aka baje koma aka dankari abinci da drinks. kasancewar lemon da sanyi kuma na roba ne shiyasa suka kusa shanye su dan kadan suka bari
sun dan jima suna hira kafin mamy taji cikinta ya murda alamar tanajin bayan gida
mikewa tayi ta shiga bedroom dinta ta afka toilet
ita ko yusra ta dan jima kafin itama taji yanayin na hajiyar itama ta mike ta shige dakin inda ta afka toilet tafara zabga nata tutun
*******
shi kam naseer abin ba'a magana domin kuwa ya zuwa yanzu ya tabbatar cikinsa yadan rikice dan haka ya dinga zarya zuwa toilet abun mashi har bashi tsoro yakeyi duba da yadda yaketa zaryar toilet ga muntar sa harya fara zafi
bangaren habeeb kuwa baccinsa yakeyi kamar wani matacce
bangaren su hajiya kuwa abin fa ya ci tura inda suketa zaryar zuwa toilet ganin abin yana neman wuce gona da iri yasata lalubar wayar habeeb dan ya zo yakawo mata magani ta kira yakai sau biyar be daga ba hakan yasa ta kira number naseer shima din shuru domin yana toilet ya na ta zabga abin tana kokarin kara kira yusra ta shigo dafe da cikinta tana dukawa mamy na bude baki da niyyar tambayarta taga ta kwasa da gudu tayi toilet din dakin itama cikinta sake murdawa yayi inda ta tashi da niyyar shiga toilet din taji shi gam a bame koda ta dan yunkura tana rawar disko irin ta wanda kashi inya matsi mutum taji kawai ya zubo mata
ku biyoni
*vote*
*comments*
*khady ce*β
[16/12, 11:40] βͺ+234 806 493 3819β¬: ππππππ
TA ME GARI
NA
khadija usman
7β£
wayyo Allah cikina mamy ta fada tare da dukan kofar toilet din cike da maseefa takama fadin wai ke yusra uwar me kikeyi a bandaki har yanzu ko kashin danko ne ai ya ci ace kin gama to waima ina na dakin da kike shine sai kin taho nan
a wahalce yusrah ta bude kofar toilet din kafin daga bisani tasa hannunta ta toshe hancinta kafin tace mamy wlh gudawa nakeyi dazu kam da dan dama dama amma yanzu kamar ruwa nake yinta ni tsoro ma nakeji kar inje ko amai da gudawa zanyi
cikin mamy ne yayi wata qara bata san lokacin data buge yusrah ba ta afka toilet itako yusrah bin wajen da mamy ta tsaya tayi da kallo tare da fadin mamy kema gudawar kk yi ashe?
******
kwance take kan katifa amma tunaninta nacan gurin masu zawon gidan dan haka ta mike ta fita zuwa falon akan idonta yusra ta fito tana tfy a dudduke kuma a botsare ta kuma dafe ciki kallonta dije tayi kafin tace sannu anty
harara ta wurga mata tare da fadin dan uwarki ciwo kikaga inayi da zaki cemin sannu
kuri tayi da ido takama dariya kasa kasa sannan tace ah ah dana ganki haka ne saina ga kinyi kama da masu ciwon zawo amma kiyi haquri tsaki tayi kafin taja qafa ta bar gurin inda dije na ganin ta shige ta kife a gurin tana dariya saida tayi me isarta kafin ta mike ta nufi kitchen tana shiga ta bude drower ta fito da bucket din da ake zuba kaji idan an soya ta zauna zaman dirshin tare da dauko lemo jin alamun ya huce ba sanyi yasata tunawa da ita ta kwashe su dazu ashe tsaki tayi ta mike ta nufi friedge din falo ta dauko exotic me sanyi ta zauna ta fara yagar naman tana shan lemo kuma saida taji kamar cikinta ze fashe kafin ta mike da kyar tana hamdala har tazo fita a kicin din ko me ta tuna kuma oho? sai naga ta juyo ta shiga store ruwa ta dauko carton daya ta nufi friedge dasu duka ta bude ta dura maganin nan a cikin kowacce gorar ruwa kafin ta jera su a friedge dan tasan suna cikin wannan halin bazasu buqaci lemo ba sai dai ruwa saida ta gama shirya su ta miqe tabar kitchen din takoma daki
******
sam yakasa gane meya rikita cikinsa haka lokaci daya dan ya zuwa yanzu yayi bayan gida sau ba adadi dan haka da himma ya qarasa inda wayarsa take ya dauka danya kira docter yusif abokinsa yakawo mishi magani ganin missed calls din mamy yasashi fara kiranta amma bata daga ba yasan bazai wuce zancen aiken datace zatayi masa ba shi kuwa a wannan yanayin dayake ciki ba inda zai iya zuwa dan haka jin bata dauka ba yasa shi kuma be sake kira ba dan haka ya kira doctor yusif yana dagawa yasanar dashi abinda zai kawo masa ya kashe wayar
minti talatin sannan doctor yusif ya iso direct part dinsu ya nufa yana zuwa lokacin naseer yana fitowa kenan daga toilet yana ganinshi ya mika masa hannu pls bani maganin nan kada in mutu dariya yusif yayi kafin yace lallai abin nan yadameka sosai so gashi ko karba yayi kafin yace pls dan bani ruwa a friedge din nan
yana dubawa yace ba ruwa sai lemo
kai pls kaje cikin gida ka daukomin pls
fita yayi yaje kitchen yadauko yana fitowa yaga mamy ta fito ta nufi dakin da yusra take
mamy ina yini?
juyowa tayi ganin yusif a tsaye yasata hamdala tare da fadin lfy qalau ya aiki ?
lfy qalau alhmdllh
abokinka kuwa yana nan dan nakira wayasu duka basu dauka ba
eh yana nan bejin dadi ne wai
subahanallah meke damunsa ?
wlh wai zawo yakeyi yanzu haka wani abun yaci kin sanshi sarkin ciye ciye a waje
sai yanzu tayi tunanin irin cimakar dasuka ta ci kuma duk laifin yusra ne ita tasa sai an siyo gashi nan taja musu shegiya gashi yanzu taja musu rudewar ciki
jin cikinta ya dan juya yasata fadin am kanaji yusif inka shiga wajen nasa ka kawowa yusra maganin itama tasha dan itama cikinta ya dan birkice
ok mamy ya fada tare da juyawa ya nufi hanyar fita
ka danyi sauri dan Allah
insha Allah yanzu zan dawo
be wani jima ba sai gashi yadawo aikuw a da sauri mamy ta nufi kitchen tadauko gorar ruwa tun a can ta bude maganin tasha dasauri ta nufi dakin yusrah ta bata itama tasha
********
toh fa abu kamar wasa gida ya kacame da 'yan zawo abincin da basira tayi ba wanda ya kalleshi se dije da duk abinda su mamy ke ciki ta sani hankalinta kwance ta zage ta dirki abincinta
******
washe gari sai wajen qarfe goma yatashi da kyar ya iya bude idonsa domin nauyin dasukai masa jikinsa yakeji wani iri duk ba kwari haka ya lallaba ya tashi ya shiga toilet dan yayi wanka yayi sallar magrib wanda shi a tunanisa bai jima yana baccin ba
ganin toilet din kaca kaca yasa ranshi ya baci shin wane dan iskan ne yayi haka da wurin yana cikin haka yaji an turo qofar da qarfi koda ya duba naseer ne baiko bi ta kanshi ba ya sabule wando ya fara nishi harda 'yan hawaye domin yazuwa yanzu gudawar ma taki zuwa sai majina toh inama yaci abincin dazai narke yazama kashi tun jiya yake yin abu daya ina yaga lokacin zaman cin abinci gara ma ruwa danshi yana sha sosai maganin da yusuf ya kawo masa kuwa duk ya shanye su amma a banza ga mamy ma ya kirata tace mishi itama hakan take amma tasan be rasa nasaba da ciye ciyen da yusra tasa sukai tayi tsakanin jiya da yau ya tsinewa yusra tare da ja mata Allah ya isa yafi sau nawa
zuba masa ido habeeb yayi ganin yadda yaketa faman nishi harda 'yar kwalla ga uwar zufa dayakeyi kuma inba abin ya girmama ba yasan ba yadda za'ayi naseer ya iya irin wannan lalurar a gabansa dan haka hankalinsa tashe ya nufi gurinsa yana fadin sannu bros meke damunka haka?
nishi yayi kafin yabashi. labarin cimar da sukayi jiya inda ya fada mishi su mamy ma nacan na fama
subahanallahi ai ban sani ba meyasa baku fadamin ba
duk da halin dayake ciki saida ya fella masa harara kafin yace ta ina za'a sanar dakai ka kwanta bacci kamar gawa kasan ko tashi nawa nayi maka amma bakaji ba
ya Allah wlh ni kaina ban san wane irin bacci nayi ba me nauyi haka yanzu haka wlh be isheni ba
kaga malam nidai dan girman Allah taimaka kasamin drip kar ruwan jikina su ida qarewa jini ya biyo baya
toh ai abari dai inyi wanka in rama sallolin da ake bina ko
toh yi maza kayi naseer yafada tare da mikewa yayi tsarki ya fita yana dafa bango
******
hankalin habeeb ba qaramin tashi yayi ba domin kuwa gidan duk na 'yan gudawa ne dole ya kwashe su duka ya nufi hospital dinsu dasu domin dole asa musu drip da sauran allurai wannan kashi sai kace annoba
itako dije komai akeyi akan idonta inda taketa dariya basira ta kalleta tace ke wai lafiyarki kuwa?
wlh qalau nake kawai murna nakeyi ina cikin farin ciki su da sun dauka in ta zama suna dimata kamar jaka ina kallonsu wlh kadanma suka gani daga yanzu duk wanda ya qara yimun wani abu na mugunta saina sa shi rawar nanayeπ
kallonta baseera tayi cike da mamakin maganar ta tace kina nufin kece silar rashin lafiyar 'yan gidan nan?
sosai ma kuwa Aunty ai baki sani ba ma wlh kadan suka gani tunda suka sa nadawo dijeta ta ainihi
kallonta kawai basira takeyi tare da yaba qoqari da muguntar yarinyar dole itama tayi hankali da ita dan kar wataran tasata rawar nanayen itamaπ€£
miqewa dije tayi ta tafi ta bude friedge ganin babu sauran ruwa ko guda daya yasata qara fashewa da dariya harda kwalla kafin tace sai ni dije uwar mazga ba'a min ba ma nayi bare anyimin
*****
kwanan su mamy biyu a asibiti duk sun rame inda gudawar ta tsaya cikin ikon Allah
yusracan dada ramewa hakora sun bayyana daddy dake zaune gefen gadon da mamy ke kwance yana ta fadan meyasa suka ci abinda sukaci waje wasu basa inganta tsaftar kayansu gashi nan sun jama kansu ai nan yagama me isar shi kafin daga baya ya shiga dawai niyar kula dasu
kwanansu biyu a asibiti ana musu karin ruwa kafin aka sallamosu zuwa gida
koda basira ta gabatar musu da abinci cewa sukayi basa ci kayan fruit kawai suka dinga sha dan sunyi losing Apetti basu jin dadin komai
itako dije rai fesss domin makarantart ake tafiya hankali kwance
yauma shigowarta kenan ta hange su mugaye a zaune cikin garden su uku sanye take cikin unifoam dinta riga da wando da farin hijab qarami
tana shirin shigewa taji muryar naseer na fadin
ke Aljana dan ubanki baki iya gaisuwa bane ?
qarasawa tayi inda suke daya bayan daya ta gaishesu ba wanda ya amsa sai baqon da suke tare dashi
mikewa tayi da niyyar tfy naseer yajawota ya zuba mata rankwashi aka sai da ta danyi kara bata san sanda ta furta kaci bashi a fili ba......
mu kara wuta
ku biyo ni
*vote*
*comment*
*Alqalamin khadiy* β
[16/12, 11:40] βͺ+234 806 493 3819β¬: ππππππ
*TA ME GARI*
4β£
*dole in faranta muku masoyan ta me gari*
*jinjina agareku da godiya me tarin yawa masoya na kamar*
*JATTAKO NOVELS FANS*
*SADNAF NOVEL FANS*
*KHADIJA NOVEL FANS*
*HAJJAJOH NOVEL FANS*
*da duk sauran groups din da ban ambace su ba kuna raina*
****
jikin habeeb har rawa yakeyi sbd tsananin bacin rai haka ma ga Naseer sunma rasa me zasu ce ganin yanayin da suke ciki yasa me gari rike hannunsu tare da cewa dije ta tafi gida aikuwa ko kafin ta fita saida ta qara musu gwalo kowanne a cikinsu ji yakeyi idan ya riketa zai iya shaketa har saita mutu
malam ne ya shiga tausarsu da naseeha da nuna musu halin kuruciya ne
dan kawai tanada kuruciya sai akace tayi wa mutane halin dabbobi cewar naseer
kallonsa habeeb yayi kafin yace ai wannan yama wuce halin dabbobi ai sai na jakuna da tumaki irin na kauyen nan ma
sosai ran me gari ya sosu ganin yadda kiri kiri suketa zagin dije bama hakan yafi bata mishi rai ba irin yadda yaketa tausar su amma suna ta nuna kiyayyar su gareta inda har suke fadin baxasu je gidan su ba sam kenan hakan na nufin zasu tsiro da lalacewar zumuncin gidansa hmmm lallai dole yasan abinyi dan haka baxata taba sabuwa ba tashi yayi ya barsu anan sunata mita suka fasa fitar ma ko ina
*****
kwana megari yayi yana saqa da warwara kafin daga baya ya cimma matsaya tunda asuba a masallaci da suka hadu da yaransa da jikoki gurin yun sallah ya tsayar da malam inusa yace yana son magana dashi cike da ladabi ya amsa ya tsugunna gyaran murya yayi kafin yace kasamu labarin abinda yafaru tsakanin yaran nan nawajen khamisu da dije?
eh nasamu lbr gurin su ayuba jiya da dare har na bata kashi ma sosai
toh Alhmdllh amma banso ka daketa ba sai dai nagama yanke wani hukunci wanda ban sani ba ko zai yimaku dadi a matsayinku na iyayen khadija
insha Allahu baba duk abinda ka yanke nasan me kyau ne bazai cutar damu ba
masha Allah Allah yayi maka albarka
Ameen
dama bawani hukunci na yanke ba illa na turata birni can gidan shi kamisu din inyaso tasamu ilimin zamani itama sannan su fahimci junansu da zumunci me karko dan iya jiya da suka san juna naga alamar gurbin kiyayya a idon yaran sbd kuruciya shiyasa nake son ta zauna gidansu nasan zata samu rayuwa me kyau kuma zata nutsu domin inka duba kiriniya irin ta dije abin se addu'a
jimm yayi kafin ya nisa yace toh baba malam badamuwa Allah yasa haka yafi alkhairi sai dai mahaifiyar ita dijen sbd kasan gidansu sun tashi da akidar kin karatun boko shiyasa ko yanzu ta hana dijen tayi
kada ka damu inka koma kace ina nemanta zanyi mata bayani da kaina insha Allah nasan zata fahimceni dan tanada saukin hali
hakane nan yayiwa mahaifinsa sallama ya nufi gidan zuciyarsa cike da damuwa dan yana son dije kuma gashi a halin dije kauye ma ya aka kare bare binni kawai ba yadda zaiyi ne akan umarnin mahaifinsu
ba karamin fama malam yasha ba kafin inna saudi ta fahimceshi inda daga baya ya yi mata nasiha nan ya fada mata yau zasu tafi dan harda shi
koda aka fadawa dije abin mamaki murna ta dinga yi dan tana son rayuwar binni da kuma karatun boko dan haka ta shiga hada kayanta inda innarta ta dinga kallonta zuciyarta na tunanin inda 'yarta zata rayu gidan hajiya zahida macen dake kyamar mutane ko zuwa sukayi saita nuna a fili daga baya ma tace ta daina zuwa kuma kamar abin magani duk abinda ta ce ya zauna a gun Alhaji khamis
'yan tafiya sun shirya tsaf yayin da ba wanda yasan da tafiyar dije har saida aka zo tfy sannan akaga da malam za'aje kowa yayi mamaki zuciyar su habeeb kamar ta buga akan dole suka yi shuru dije ta shige mota ita da malam akaita daga musu hannu inda kawayenta keta murna da kuma kewar uwar mazga yayin da dayawan mutane ke murnar ala raka taki gona
*DIJE A BIRNI*
tunda