Author : Asma Baffa Category : Romance
bata santa ba nasir jaye da troly koda suka shigo suka ga meya faru iyakar kuluwa mamy ta kulu yayin da naseer ya fara bala'i yana qara fadin ya tsani yarinyar nan shiko habeeb tunda ya mareta huci kawai yakeyi yayin da yake qara jin tsanar yarinyar har cikin ransa
budurwar dake tsaye ce ta yamutsa fuska tare da fadin mamy pls where did u get dis poolish basterd girl?
hamm yusra she's from Alhaji's village !!amma gaskiya kinyi sake mamy dubi fa da abincin da zata cinye amma dai daddy yaqara yawan abincin gidan ko dan kin san mutanen qauye da ci basu san wani mentaining ba burinsu kawai ciki yadauka musamman tuwo basa masa wasa bare anga farin tuwo
tsaki habeeb yaja kafin yace ai zataci ubanta wlh yau bazata ci abinci a gidan nan ba
nasir ne yayi caraf da cewa iya yau kawai ai wlh sai jibi kafin taci
wlh ni kwana uku ma yakamata tayi dan ubanta intaji wuya dakanta zata koma kauye ai shegiya me siffar 'yan ruwa dariya duka suka sa banda habeeb da ya qara hambareta ya juya ya fice nan suka gama mata tujara kafin suka barta a gurin bayan mamy tasa basira ta kwashe tuwon daya zube ta kuma tabbatar kar abawa dije abincin dare
a gurin suka barta tanata kuka yayin da tayi me isarta data tuna innarta da baffanta can kuwa saita yi shuru ta furta a fili ina dalili zan zauna ana cutar dani yaseen bazan yadda ba gara in koma dijeta ta da dije masifa dije bala,i dije annoba jahannama ga fasinja uwar mazga bari inga wato kai kace yau bazanci abinci ba yau toh wlh kaine bazaka cishi ba har sai gobe kajawa kanka kai kuma uban 'yan mugunta kace bazanci ba har sai jibi toh kaima sai jibin kaci ku kuwa masu cewa sai nan da kwana uku toh kuwa sai lokacin zakuci dukanku dariya tayi ta mike tana taba inda ya mareta ta jinjina kai ta tashi ta shiga dakinta
kudin da daddy yabawata last week yace inta tashi siyen wani abun basaita tambaya ba dan haka ta boye su bata ma siye komai ba su ta je tadauko ta fito zuwa farfajiyar gidan
gurin bala driver ta nufa inda yana ganinta ya shiga washe baki
qarasawa tayi cikin sakin fuska ta duqa har kasa ta gaisheshi ya amsa cike da jin dadi kafi. tace dama aikoni akayi yace toh toh ya akayi?
gashi hajiya tace kasiyo mata maganin kashi
wane irin maganin kashi kuma?
eh wai bakuwar nan ce dasuka zo tare yau kwananta goma batayi kashi ba shine tace a siyo mata wanda zaisa tayi sannan wai da maganin na wanda in an yaye yaro ake bashi dan yayi bacci wai yaye za'a kawo mata yau shine tace a siyo mata shi
toh kaao kudin amma ina su Alhaji karami ai su suke shigo da magani gidan in ana buqata
wai mantawa sukayi shiyasa tace yasiyo sachet goma sha biyu biyu dan a ajiye sbd gaba
toh yafada tare da miqewa ya tafi dan akwai wani pharmacy nan bayan layin
guri tasamu tazauna dan ta jirashi har ya dawo
hhhhhhhh mudai je zuwa
waitng your's comments
[16/12, 11:39] βͺ+234 806 493 3819β¬: ππππππ
*TA ME GARI*
NA
khadija usman
*gaskiya naga soyayya yau Alhmdllh naga sakonninku masoya wannan buk din banyi niyyar posting yau ba amma gashi nayi muku kyauta sadaukarwa ga dukkan masoya dijangala ta me gari* π
3β£
wata irin bugawa kirjinsu yayi a tare inda nasir ya bude baki da niyyar yin ihu tace kanamin ihu bakinka zai tsaya a haka har abada gum yayi banda zufa ba abinda ke ketowa ita ko se raba ido takeyi a dole aljana habeeb dake zaune bakinsa fal da fura dan yakasa hadiyewa karasawa tayi cikin dakin yayin da dukansu yau saida sukayi fitsari dariya ce fal cikin dije amma takasa yi ta gintse kallon kwaryar gaban habeeb tayi taganta cike da fura tab wadda duk iya shansu basu isa su shanye ta ba bare ma taga 'yan binni kadan suke cin abinci ko a film in an nuno hmmm tace a zuciyarta ta furta yau zakusha azabatul ula kallon su tayi taga yadda suke makyarkyata tace wato bakwajin magana ko ? ko a cikin bil'adaman naga ku takadirai ne kun takamin yara sunacan sun sami gocewar kashi a tsakiyar kansu amma ku kuna nan kuna shan fura ba ruwanku ko sannan danace kada ku dauki abin hawanku sai gobe shine kuka tura jibirila dan me gari ya dauko ko sbd kun raina izayar jinni toh tunda yarana suna halin jinya yanzu kuma bari in kwantar daku dan mai maganinsu ya fadamin yace sai sunyi shekara dari uku da saba'in kafin su warke abin takaicin ma gasu 'yan biyu ne ko yayesu banyi ba duk jarirai ne basu wuce shekara dari da ashirin ba gashi kunja musu jinya tun suna rarrafe dan haka tunda kuma ku biyu ne yanzu zan yi muku abinda kukayi musu kashin tsakiyar kanku zan malkwadar yadda zakuyi jinya tare
wayyo Allah nadan girman Allah kiyi haquri wlh wlh bamu san da yaranki a gurinba dan ya rasulillahi manzon Allah sallallahu alaihi wasallam dan binta 'yar ma'aikin Allah nanfa suka shiga rokarta duk da dai shi nasiri a iya bincikensa besan da wani kashi a tsakiyar kai ba amma ba mamaki a halittar aljanu akwai shi su kuma ta tsinka musu jijiyar kai yau sun shiga uku shi wlh da yasan haka ne wlh da be zo kauyen nan ba shiyasa mamy bata son su zo a fannin habeeb ma haka kukan zuci yakeyi yayin daya saki baki furar ta zubo dan iya tashin hankali yana ciki a rayuwarsa ba abinda ya ke tsoro irin aljani yau saiga shi garin tukin ganganci irin na naseer yaje ya tsokano musu su kunji fa sharri readersπ€£
katse musu tunani tayi ta hanyar ce musu zanyi muku afuwa amma da sharadi
da sauri sukace mun amince wlh ko meye mun yadda mudai ki dena zuwa mana
toh in kun yadda zaku shanye furar nan duka yanzu
π³zaro ido sukayi waje tare da fashewa da kuka musamman nasir da a duniya ba abinda ya tsana irin fura
cikin marairai ce fuska da kuka ya hada hannunsa biyu yace dan girman Allah kiyi hakuri wlh bana shsn fura danasha amai zanyi ke zan iya kwanciya ciwo ma
oh to to tunda baka shan fura bari a sake maka hukunci zan daure cikinka kadaina kashi da fitsari tsawon shekara goma zan kanne maka ido daya zan toshe maka kofar hanci daya da rabin bakinka zan......
ya isa dan Allah kiyi hakuri wlh zan sha kafin tayi wata magana tuni sun fara shan furar inda suka dinga kokawa da ludayi a cewarta basa sha sosai zata kawo musu irin tasu ta aljanu aikuwa suka bada himma sosai inda suketa sha cikinsu ya cika dam gashi furar ko rabi batayi ba dan su a ganinsu ma kamar qarata akeyi bata ankara ba kawai taga sun fashe da kuka a tare abinda yabata dariya kenan wai babba da kuka abinda bata taba gani ba sai a talabijin dan haka batasan lokacin data kama dariya ba su suna kuka ita tana dariya gashi dai furar nan shanta suke
motsi taji alamar za'a shigo gurin ganin sun duka suna kallon fura suna kuka yasata saurin barin gurin ta labe bayan dakin dan wani lungu ta fara dirje bakin fuskarta
da sallama malam ya shigo gurin turus yayi ganin su sai gunjin kuka sukeyi suna shan fura
subahanallah ya fada yana me kiran sunan su jin muryar malam yasasu dagowa suna fadin yauwa malam aljana wlh tana dakin nan sun rude gaba daya yayin da itako tana jin suna aljana ta dira ta katanga tayi dakin kakarta tana fadin ni nayi gida dan nama fasa zuwa gaida bakin saida safe nazo
au da duk kina ina ja'irar yarinya nama aza kinyi gida
toh ban tafi ba sai yanzu nayi niyya ehee
mificin hannunta tajefo mata ta kauce tana dariya ta fice daga gidan
sosai naseer ke amai ya galabaita matuka inda hankalin malam yatashi sosai dan shima habeeb zazzabi ya rufeshi ba shiri malam yasa aka dauko mota aka nufi asibitin cikin gari dasu dan basu taimako dan shi lamarin yana bashi mamaki wai aljana kuma duka su biyu ke ganinta saida aka sa musu drip dukansu aka musu allurai kafin suka yi bacci amma a dan wannan lokacin duk sun rame
********
tunda abin nan yafaru bata qara zuwa gidan malam megari ba dan ita tama manta da wasu baki yau kusan kwana hudu kenan tadai ga innarta na yawan zuwa gidan me gari
yau da wuri ta tashi ta share gidan tsaf duk da shekararta sha hudu yanzu amma tana aiki sosai sai dai in bata so ba yau dinma dan tanason ta bi su sadiya cikin gari dan zasuje gidan yayar sadiyar ne dan haka takevtaya inna aiki dan karta hanata
****
a gajiye suke likis sbd tafiyar kasa da suka sha dan haka tasamu gefen hanya ta zauna tana mayar da numfashi kamar wadda tayi gudu cikin tsananin gajiya ta dubi sadiya tace yaseen bazan iya qarasawa gida a kafa ba wannan ai sai in mutu kafin inkai
to ai laifinki ne dije an bamu darinmu ta ihemu mu hau mahin kika tahi kikace a rabeta kowa ya kahe nahi to gahinan ai sawun mu ya fada mana dan ni wlh ji nakeyi kamar ba a jikina kafafuna suke ba
toh ni uwarku ce da in nace kuyi abu he kunyi a wane dalili toh wlh duk wadda taqaramin harri banyi abu ba tace nayi hena mazgeta hegu kawai
.gum sukayi sun san sauran dan duk wadda tace kala yanzu uwar mazga zata kaddamar musu
kunga ku tahi mu tare me mahin ya kaimu gida
to ina kudin ? cewar shatu
ku zo kuji dabarar dana shirya duk suka hada ka wunansu guri daya kome suka ce oho naga dai sun rushe da dariya sannan suka mike suka fara tarar dan mashin
sun tari mashin yakai goma ba wanda ya tsaya sai daga baya wani saurayi ya tsaya yace ina zaku ne 'yammata?
nan Gawo nawa?
toh ku bada nera sittin tunda ku uku ne
ah ah malam cewar dije uku hamsin in yayi maka
dariya abin yabashi wai uku hamsin dan haka yace to ku hau nan suka dane mashin dukansu sannu har suka iso cikin gawo dai dai gidan me gari inda dan wani tudu yake suka ce masa ya isa ya tsaya yanata zuba musu surutu sukuwa wannan ta kalli wannan ta kalli wannan da haka kuwa sai yaga hafsi da shatu sun kwasa a guje dije ta yunkura yayi caraf ya riketa aikuwa dan da nan kallo yadawo garesu inda yara suka fara taruwa harda 'yan manya manya kan kace me guri ya cika dam tuni lbr ya isko gidan megari yana zaune dasu habeeb dake shirin komawa gida gobe dan Alhmdllh sun sami sauki dan megari yayita amso musu taimako maganin iska kuwa da tsari duk anyi musu shi suna zaune suna tattaunawa akan gidajen da basu je ba yau zuwa gobe zasu je na kusa kusa na nesa kuma sai sun kuma dawowa ana haka aka zo aka fadawa me gari wai ga dije can tayi sata an kamata cikin sauri ya mike duk da jikin tsufa amma kalmar tayi muni sata!!!sata fa toh meta sata ?
ganin yadda maganar ta shigeshi yasa su habeeb tambayar sa wacece dije?
kanwarku ce diyar gurin inusa
ku tashi muje duka suka miki suka bi shi
koda suka iso gurin sun iske dandazon mutane an taru koda akaga me gari kowa ya ratse yabashi hanya ya isa gurin inda yaga dije tsaye me mashin ya rike mata hijabi itako ko a jikinta tanata gwagwiyar goruba
rasa ma me zai ce yayi inda ya qarasa yana fadin malam dan Allah sakarta mana
wlh baba bazan saketa ba sai an biyani kudina
nawa ne kudin naka?
naira hamsin ne
yanzu kai da duk akan nera hamsin katarawa mutane wannan jama'ar
toh ai hakkina ne naga kuma akan sana'ata ne
toh garin yaya kudi ya hadaku?
nan yakwashe komai yafada masa aljihu ya laluba ya ciro nera dari yabashi yace yabar canjin sannan yasaki dije malam yakama hannunta suka nufi cikin gida su habeeb sam basu lura ba dan suna waya ne da mumy sai da suka gama suka juya suka hango bayan me gari rike da hannun wata yarinya ze shiga gida nan suka nufi gidan suma
tsaye ya tadda matansa da sauran ahlin gidan duk tsaitsaiye suna jimamin abin nan yabasu labarin ainihin abinda yafaru kowa ya kalli dije wadda har yanzu bata cewa kowa kanzil ba tanata dai cin goribarta ana haka su naseer suka shigo kasancewar dije ta juya baya nan suka tambayu meya faru nan malam ya shiga sanar dasu cikin zolaya habeeb yace tab ashe kuwa yau sai na bawa budurwar kauye kashi dai dai nan dije ta juyo akayi ko sa'a tasha kwalliyar nan sai dai yau jambaki tasaka kanta kile sabanin baya
wani uban ihu naseer yasaki inda shima habeeb ya karba suka fara fadin gata nan itace suka kwasa da gudu sai dakin inna dudu suka rufo
mamaki ne yakama kowa yayin da dije ta zube a gurin tanata dariya ganin haka malam ya dauka shedananta ne dan haka be bi ta kanta ba ya nufi dakin da suka rufe anyi anyi su bude sunki dije ce ta taso tazo dai dai kofar windo ta leka tace in baku bude kofar nan ba saina kwakule muku idanu da sauri suka taso suka hau kokawar bude kofa tun daga nan malam ya fahimci karatun suna budewa dije ta kara fashewa da dariya zasuyi ihu me gari ya buga musu tsawa yace dama wannan ce aljanar datake tsorata ku?
eh itace wlh itace shi kanshi me garin yaso yin dariya ganin yadda duk jikinsu ke kyarma
to ai itace kanwarku diyar babanku inusa a shakiyancin dije nasan zata aikata fiye da haka
dimmm sukayi gaba dayansu inda suka kai dubansu ga dije wadda ta dallaro harshe tare da yimusu gwalo tace ni ba aljanah bace gyadata kuka takemin ta zube ina shirin in tsince naji fitsari na juya inyi koda na juyo naga kun takemin ita shine nayi maganinku
tunda tafara magana zuciyar mazan tahau lugude musamman. habeeb da yayi asarar hakorinsa guda na kasa saboda abin wayyo Allah
muje zuwa readers yawan comments yawan page
[16/12, 11:40] βͺ+234 806 493 3819β¬: ππππππ
*TA ME GARI*
na
khadija usman
6β£
*wannan shafin sadaukarwa ne ga dukkan member's na khadija fans novels hakika naga ruwan comments da kuma masu bina pc nagode sosai Allah yabar kauna*
ta jima zaune kafin daga baya taji alamun dawowarshi mika mata yayi tare da canjin tace ya rike canjin ta karbi maganin a bakar leda ta shiga cikin gidan
tunani ta shiga yi shin wai ta inama zata fara ne wai wazata fara yiwa illa habeeb,nasir,mamy,ko uwar mugaye yusra ah ah takan ya habeeb zan fara tunda shi yafara min mugunta
mikewa tayi ta shiga kitchen cikin sa'a ta riski basira na zuba coffee cikin cups kallonta tayi tace sannu da aiki Anty na
murmushi basira tayi yayin data kamo hannun ta cike da tausayawar abinda aka mata dazu tace sannu dije kiyi haquri da abinda ke faruwa gidan nan ki dinga taka tsantsan da hajiya dan wlh batada imani suna iya hanaki abincin kwana ukun dasuka ce dan haka kada kidamu zan dinga boye miki a daki da zarar kin tashi ci zan nuna miki inda zan dinga ajiye miki
dariya dije tayi kafin tace kada ki damu Anty ai daga yau har zuwa kwanakin da suka dibar min zanci abinda raina ke so ke dai kawai kisa ido kiyi kallo nice fa dije wlh a kauyenmu anno ba ake cemin duk gidan dana leqa saina sasu jinya dan haka sai sun san nice sukawa haka da naso in canza amma naga basu san kara ba gara ayi gwari gwari
mamaki ne yakama basira inda take kallon dije daketa zaro zance ba wakafi ba aya duk da take qaramar yarinya dan ita a ganinta bazata wuce shekara sha biyar ba amma ta iya tsara zance kamar redio amma kuma in akayi la'akari da dabara irin ta mutanen kauye wannan ba komai bane
farantin data dora kofunan akai ta dauka da niyyar fita dije tace ina zaki kuma Aunty ?
wadan can 'yan sudan din zan kaiwa shayi wai da yamman nan kin san su
ah ah kawo inkai musu ki huta ai kinyi aiki kin gaji naga ma kamar bacci kikeji dan haka jeki kwanta ki dan huta zan qarasa aikin kije ki
toh kadafa kije suyi miki wata muguntar kuma
ah ah ba komai ai haquri zan basu kada ki damu
mika mata tray din tayi ta fita dai dai wani dan corridor ta labe ta fito da ledar daga jikinta ta bude juya maganin tayita yi dan ta rasa na bacci dana kashi kawai shahada tayi ta babbala sachet daya a cikin biyun ta juye cikin daya kofin dayan na hannunta ta fara barewa shima da alama kam wannan shine na baccin tafada a bayanne dan naga shi inna ta siyawa Ahmadu lokacin data daukoshi yaye shima duka guda goma ta juye ta dinga juyawa har duka suka narke kafin ta mike ta boye sauran a wani loko inta dawo ta dauka ta nufi part dinsu
ta dan jima a tsaye kafin daga haya tayi knoking
shigo kawai basira taji ance murda handle din kofar tayi ta kunna kai parlon da sallamar ta habeeb zaune daga shi sai boxer da singlet yana zaune yana duba system dinshi da alama wani aikin yakeyi me muhimmanci duba da yadda yamaida hankalinshi gaha daya ga abinda ke gabanshi
shiko naseer jallabiya ce a jikinshi yana zaune yana danna waya da alama charting yakeyi
naseer ne ya amsa sallamarta inda ya dago idonsa tare da wurga mata harara uban me yakawoki dakin nan ?
um dama itace batajin dadi shine tace in taimaka in kawo muku
tsaki yaja kafin ya maida hankali ga wayarshi