Tame Gari 1 Complete Hausa Novel

Author :  Asma Baffa Category :  Romance

Chapter   5 / 33

12K to 15K   out of 96.3K words

da inuwar budurcin bata dade da sauka bisa kansu ba riga da siket ne na wani blue din material a jikinta wanda aka yiwa ado da kyalkyali na yellow din flowers dan haka tasa takalmin me matsakaicin tsini tare da siririn mayafinta yello kanta babu dankwali hakan ne ya qara bayyanar da yalwataccen gashin kanta dayasha gyara yanata walqiya da dan murmushi akan fuskarta ta nufo gurin su inda hankalin Amir abokin naseer ke kanta

wow so beautifull bros ya dan daki kafadar naseer do u look what i see?

dagowa naseer yayi domin ganin me Amir ke kodawa haka ganin wadda ke nufo su ne yasashi sakin sirirn tsaki tare da juyawa yaci gaba da maganarsa dasu maryam

duk abinda yayi dije ta lura dan haka ta qara fadada murmushinta ita ko yusrah baqaramin dadi taji ba da yadda naseer din yayi

cikin siririyar muryarta tayi musu sallama da sauri qawayen yusra suka amsa tare da wage baki kamar ze yage dan fara'ar da suketa yimata hakama abokan ango dukansu kamar masu tallar makilin a ranta tace ikon Allah sukuma wadan nan haka Allah ya hallice su babu aji bare aje maganar jansa


cikin salon karya harshe tace barkanku da hutawa Aunti's dina


har rige rigen amsawa sukeyi cikin sakin fuska


ykk qanwar mu ya kuma shirye shiryen biki?

all is fine so ya gajiya da yawace yawace ?

duk alhmdllh

toh fatan dai yayana be barku kunata dibar kura a bakin zannuwa ba

cike da rashin fahimtar maganar ta suka juya suka kalleta

nup kada ku damu bawai ina nufin wani abu bane naga kun zubamin ido kamar zaku hadiyeni ina nufin fatan dai yana cika muku jaka da tsaba ko dan nasan halin yaya naseer badai mammako ba

sai yanzu yadago ido ya dubeta tare da sakar mata harara amma sai yaga ta waske tare da fadin

sannunku abokan ango ykk?

lfy beauty cewar Amir dayafi kowa zakewa

yayi kyau tafada kafin taci gaba fatan dai kuna cikawa 'yammatan jakunkunansu ko dan nasan halin samarin yanzu duk 'yan kamus ne


dariya Amir yayi tare da gyara tsayuwarsa danya qara burgeta yace ah ah qanwarmu ai mu ba irin wadanda kk sani bane mun bude bakin aljihu basu da matsalar komai

hmm au hakane ?

ta tambaya tare da yatsina fuska

sosai ma kuwa ai gasu nan indai ba butulci zasuyi mana ba sun san mun bude bakin aljihu sunata kwasa

hakan yayi kyau abokin ango dan wahalar banza😂ta fada tare da qoqarin barin gurin


yake kawai Ameer yakeyi bakin ma yaki rufuwa dariya ce ko kuma murmushi duk ya rasa tayi itako ta sa kai da nufin barin gurin sai kuma ta dawo ganin yadda yusra ke yi mata wani kallon raini tare da naseer dake harararta

gaban naseer taje ta dan rusuna tare da fadin gani yaya?

ubanwa ya kiraki ?

ubana mana

ta fada tare da qifqifta ido kasan ance babban wa magajin uba kaga ko ai kai ubana ne ko?

rasa me zaice mata yayi sai yusrah datayi qarfin halin fadin ke wai wannan wane irin iskanci ne haka anan kinga sa'anninki ne


miqewa tayi tare da fadin ah ah wlh ko daya daga sa'annin baffana sai yayyena sai kuma wadanda ban sanma a wanne mataki zan ajiye su ba dan nasan da sunyi aure da wuri da ko a haihuwar raquma nice auta cikin 'ya'yansu tana gama fadar haka ta qara gaba tabar kowa shaye da mamakinta

kwafa yusra tayi tana jinjina rashin mutuncin dazata yiwa yarinyar danta lura tashen balaga takeji


******

tun daga wannan lokacin babu wanda ta kuma haduwa dashi kowa yana cikin hidimar biki inda suketa shirye shirye


****

rana bata karya yau saura kwana biyu daurin aure yayin da mutanen qauyen gawo suka iso dije ce ta sama musu masauki danta lura indai ta hajiya mamy ne sai dai su wulaqanta dije tasa ran zuwan innarta amma sai taga ba'a zo da ita ba har kuka sai da tayi nan aka shiga rarrashinta ita da basira suka shiga dawainiya da mutanen inda daga baya ta bar baseera ta tafi dansu rufaida nata jiranta dan suje qunshi tunda batada waya da sauri ta fita ta bar gidan tana zuwa kuwa ta tarar suna jiranta nan suka shiga mota suka tafi sunata mata mita dan rufaida akwai son biki kai kace bikin yayanta za'ayi


anyi musu qunshi ja da baki tare da gyaran jiki barakallah masha Allah sunyi kyau sosai matuqa sai dare suka dawo gidan duk wanda yaga dije a cikin mutanen kauye saida ya yabata masu taya iyayenta murna nayi masu hassada a zuciya nayi

ranar akayi kamun yusrah inda aka gabatar da komai cikin wadata

****


yau ake dinner dan haka kowa yake burin qure wanka

sauri takeyi ta qarasa part din da 'yan garinsu suka sauka dan zasu je gurin makeup da sukayi booking sam bata lura da shi ba hakan yasa ta dan bugeshi kadan

wata irin angaza yayi mata kafin tayi wani yunkuri yakai hannu da niyyar marinta cikin sauri ta kauce

a hasale yafara magana ke wace irin mahaukaciya ce iye dan ubanki bakya ganin gabanki in kina tafiya kamar budurwar qauye au ashe fa banyi kuren harshe ba itace wato ke kin girma ko shine rannan harda yiwa mutane rashin kunya ke ga 'yar birni wai tsaya ma duk wannan saurin da rawar jikin da kikeyi duk na menene?

idan ma na zuwa gun dinner ne wlh kiyi saurin fasawa dan wlh naga qafarki a gurin saina ci ubanki saina babbala ki gurin manyan mata ne wato classic lady ba irinku wadanda ko dadewa da yayeku ba,ayi ba wuce ki bani guri shegiya me siffar aljanu


kalamansa sunyi mata zafi matuka ta so yin kuka amma saita ga meye nata nayin kuka a wanne dalili hmmmmm kawai tace tare da qarawa gaba taje tayi abinda zatayi ta fito tana fita still ta hadu da yusrh daqawayenta suma da alama fita zasuyi dan su shirya tagansu da akwati


yauwa ke zonan dan uwarki

kin kula su tayi tasa kai da niyyar ficewa

wani sauri yusrah tayi tare da fadin ke ina miki magana kina jina nasan duk wannan rawar kan da rawar kafar da kikeyi danki fita bazai wuce dan kije gun dinner bane to wlh kk sake naga kafarki a gurin nan sai kinci kut........dan gurin manyan guys ne da big girls ba cakuri cici irinki indai ba tsintar bottle din da akasha drinks zaki tsinta ba


wucewarta tayi batare data tsaya qara jin me yusran zata ce ba tana fita ta shiga tunanin maganganun su duka biyun wato suna nufin ita batakai wadda zata je bikinsu ba?suna nufin ajinta yayi low dayawa da har zesa takasa taka gurin?juya maganar ta shigayi cikin ranta ta jima tana saqa da warwara kafin daga baya tasami mafita murmushi tai tare da yin kwafa a fili ta furta



big guys
classic lady's

a kafta😜


******

shiri sosai kowanne bangare keyi musamman bangaren amaren dan ko wacce so takeyi taga ta burge ta bada kala cikin taron dan haka kowacce ke babban shiri

dije ce ta shigo gidan direct part din mamy ta nufa dake upstairs tasan su yusra na can na shiryawa a zaune ta same su ana shirin fara yiwa yusrah kwalliya da sallamarta tashiga dakin wasu sun amsa wasu kuwa suna sabgar gabansu da qarasawa tayi inda yusrah ke zaune tanata hura hanci tace sannu Anty

meye kuma ?

ta fada tare da hararart


ba komai dama zuwa nayi in baki haquri akan abubuwan da suka faru a nasan nayi miki laifi kiyi haquri nasan idan bamu samu lokaci yau na rokeki ba nasan bazan samu wata damar ba kuma pls aunty kiyafemin

kada kai yusra ta shiga yi tare da girgiza kafa nasan dai badan Allah kika rokeni ba nasan bazai wuce dan kije gurin dinner dinnan bane kuma wlh bazaki ba kinji na rantse dan haka wuce ki tafi munafuka


lah wlh Aunty bahaka bane ka.....naji ta katseta fice kawai nan duk ba sa'anninki qara matsowa tayih arda fadawa jikinta aunty na zanyi missing dinki sosai finciketa tayi tana fadin zan ciuwarkifa ina wasa dake ne


sim sim ta juya ta fita yayin da wasu daga cikin qawayen yusrah ke mata fadan rashin kyautawar datayi duk tayi banza dasu


tana fita ta saki dariya tare da fadin woa ni dije wato ke kin saki baki in baki haquri kedin banza

waya ta fito da ita ta shiga dannawa ganin akwai password a jiki yasata buga tsaki ta bar gurin direct part din mazan gidan ta nufa duk da tasan zuwa yau ya cika da baki dan tasan dole akwai masu zuwa daga nesa

koda ta isa mamaki tayi dan ba kowa tura qofar tayi a hankali ta shiga 'yar magana ta jiyo daga bedroom taji muryar naseer na fadin ai ni inaga daga yau nayi musu sallama shiyasa gara in kwashe su tun yanzu inkai su can tunda yanzunma dole saina dauki kayan dazansa ba gara inyi me gaba daya ba

habeeb yace gaskiya ka kawo shawara me kyau nima bari nabi sahunka kawai na huta

sadaf sadaf ta dinga yi inda ta hangi wayarsa da wallet ajiye saman center table......




toh ko me dije ke shirin yi ?


na gaji typing akwai wahala inyi ma ba comments😜😜


gara na rage

*vote*
*comments*
*with* 08066364077

daga alqalamin khady✍
[16/12, 11:41] ‪+234 806 493 3819‬: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀


TA ME GARI


NA
khadeeja usman


🔟


wow gaskiya naga dije nada masoya dayawa inta ballo muku ruwa ba ruwana🤷‍♀wato tana wuta kuna binta da fetur ko 🤣


sai da ta duba wayar ta tabbatar tashi ce sannan ta dauka tayi saurin fita labewa tayi jikin wani corridor kafin ta danna wayar wani irin farin ciki taji ganin babu security nan nake ta shiga neman number yusra my sweet wife taga ansa da sauri ta shiga gurin rubuta sako gajeren sako ta rubuta tayi sending ma wayar yusrah saida ta tabbatar ta ya shigo kafin tayi delete dinsa a wayar naseer cikin sanda ta koma ta mayar da wayar har yanzu be fito ba dan haka tayi saurin ajiyewa ta fita


dakin su yusrah ta nufa tare da sallama kamar dazu

an farawa yusrah kwalliya dan haka ta nutsu amma ganin dije yasata fadin uban me yakawo ki kuma ?


qarasawa tayi ta lababa ta ajiye wayar kafin tace dama yaya naseer ne ze fita yace inzo in fada miki wai ki duba wayarki ya turo miki sako

to naji maza bacemin da gani

sim sim ta fice tana dariyar mugunta

wayarta ta laluba ta duba sai taga sakon nashi kuwa

slm sweety na pls abin nan an qara lokacin zuwanmu sai zuwa 11 wai sbd akwai wata qaramar walimar da aka shirya mana mu da qawayenku so bana son ki gaji dan haka ki jira dakaina zanzo daukarki nida big bros da bridge dinsa amma qawayenki su shirya suyi gaba kada ki kirani yanzu ina busy in nazo akwai magana


murmushi tayi bayan tagama karantawa tare da fadawa kawayenta su kam shewa suka sa suka shiga yimata tsiya kallon meyin makeup din tayi tace a bari sai zuwa anjima dan kar ayi ta baci


******


dije ke bawa rufaida dasu husna lbarin abinda yafaru sun san halin mutuniyar dan ko a school in malami yayi mata abu saita san hanyar dazata rama dan haka koda tagaya musu ihu suka shiga yi tare da dada qarawa wutar fetur nan ta shiga fada musu plan dinta

****

masha Allah tabarakallahu ahsanul khalikeen iya kyau dije tayi kyau matuqa inda ta dauki wankan wata arniyan gawun ta red din material tare da ash din head gaskiya koni dana ganta na yaba dan tayi kyau sosai ta fito tamkar amaryar sai baza kamshi takeyi


duk sunyi kyau sosai inda suka fito daga gurin suka shiga mota dan yanzu kusan 8:45 da alama an kusa farawa dan haka cikin sauri dije ta dubi rufaida tace muyi sauri mu qarasa dan Allah kada kwabata tayi ruwa

dariya husna tayi tace hmm yau fa akwai cakwakiya dan haka qara wuta kinji duk suka sa dariya kafin suka nufi gida

dan nesa kadan rufaida tayi parking kafin suka maida duban nasu ga qofar gidan inda sukaga anata tururuwar shiga mota can suka hango qawayen yusra nata shiga mota sbd kusan kowacce nada motar kanta yasa kowaccensu bata bi takan abokan ango ba suka shiga motocinsu sukayi gaba a cewarsu sa dan caccashe kafin zuwan amaren

daga yusra sai wata friend dinta da me makeup aka bari sbd ma kada wasu su dameta yasata kashe wayarta har sai time din daya fada mata ya kusa saita bude tasan kuma bayada number wata qawarta badan hakan ba ma ita da kunnawa sai gobe


suna kallon kowa a hankali guri yagama watsewa sannan suka hango motar da za'a dauki amarya ta nufo gurin ganin yadda motar tasha ado da fulawoyi da balow dole ya burgeka da sauri dije ta kalli rufaida tace now is our time murmushi rufaida tayi kafin ta bude murfin motar ta fito ta nufi gurin waccan motar


naseer an hakimce a baya sanye cikin ash colour din shadda datasha aiki bakar hula yasa akansa sai yayi wani kyau da kwarjini ango kenan

number yusrah yaketa kokarin kira amma anata ce mishi a kashe har ranshi yadan fara soyuwa


rufaida ce ta karaso wurin tare da dan kwankwasa glass din tace


Assalamu alaikum angonmu

dan sakin fuska yayi wai shi a dole yau ranar farin ciki ce a gareshi be kamata yayi fushi ba kafin ya amsa dan yasan bazai wuce daya ce daga cikin qawayen yusra ba dan yasanta da shegen shige shige ga yawan qawaye dan haka yace ya akayi ne ina amarya ta?

dariya tayi kafin tace amaryarka na nan qalau sai dai zuwan nawa ma nata ne ita ta aiko ni da saqo na jima tasaye lnata jiranka gashi kowa ya watse an barni ni kadai inata jira in isar da sakon masoya

murmushi yayi kafin yace toh fa sakon me?


nasan baka sanni ba ni cousin sister muke da Aunty yusra ta bangaren abbanta to kasan dangi kowa da nasu al'adan mu a namu yau ranar dinner dangi ne zasu wuce da amarya inya so kaima ka tafi daban sai anje gurin saiku hadu ku shiga tare

ikon Allah yafada tare da zaro ido dan abin ya dan sosa Ranchdan haka yace

a wanne yare kenan

ai a ganina kafi kowa sanin kowacce yare ce yusra tunda gashi har zaka aureta

ganin yadda tabashi amsa ya tabbatar da dangin mahaifin yusrah 'yan kwamus ne gara yabisu sannu kada suce zasu hana auren gaba daya🤣

toh yanzu meye abinyi kenan?

abinyi mu wuce kawai dan kar aita jiranmu dan sun dan jima da tafiya

ok come in yafada

murfin gaba ta balle ta shiga driver yaja suka tafi

dije na ganin dun tafi tacewa husna yessss da alama plan dina yayi aiki ja mu tafi kawai husna kallon dije ta shiga yi tare da fadin wlh khadija in aka kaiki gidan kishiya ta shiga uku daga ita har mijin

sbd annoba ce ni ko
ta fada cikin hade rai


nidai bance ba


kima ce mana ni ina ruwana kawai abinda nasani duk wanda yayi min abinda raina beso ba wlh sai ya san yayi min

Allah ya shirya

Ameen


taja mota suka tafi bawata hirar arziqi tsakaninsu ganin in tayi wasa itama dije na iya shirya mata nata rashin mutuncin yasata sakin rai ta dinga janta da hira har saida taga ta warware🤣

*uwar mazga kenan*😂



******

guri yayi guri ya hadu iya haduwa tun dazu su habeeb da amaryarsa suka hallara qawayen amarya har sun gaji da tiqar rawa inda dangi da 'yan uwa kowa ya matsu a fara abinda ya tara su kowa ya gaji abokan naseer se kiransa sukeyi a waya inda yaketa ce musu gashi nan zuwa suna hanya habeeb ma se kiransa yakeyi da duk wani na kusa amma se yace suna hanya kowa ya gaji M.C murya harta fara dashewa dan yadda yaketa cigiyar amarya da angon 🤣

****

suna qarasowa gurin driver na gama parking rufaida ta bude ta fita a cewarta zata wai zata sanar da zuwansu yusrah ta fito daga inda aka boyeta saisu shiga kuji fa kamar wata kayan sata🤣


motarsu dije na isowa suka faka daga wajen guest in din kafin daga baya suka shigo suka yi parkin amma basu fito ba

saida ta kusa minti talatin kafin ta dawo gurin ranta a bace ta bude motar ta shiga ganinta da yayi haka ne yasashi tambayar
ta ya'akyi ne qanwarmu ?

hmm wlh nida Aunty yusra ne waina sanar da ita wane colaur din kaya kasa na fada mata shine wai ita wlh tasan bakayi kyau wai ai daga kalar dressing din dakayi sai qawayenta da sauran danginmu suce baka waye ba suyita mata dariya
dan haka ita inje in sanar maka kaje ka sake dressing



tunda tafara kora masa jawabi ransa in yayi dubu ta ba wandabe baci ba dan haka cikin bacin rai yafara fadin


ita din banza tasan nawa na kashe ai wlh ko namiji ya ganni yasan dai shigata tayi amma shine tayimin wulaqanci oh kawai dai tace cin mutunci ta shiryamin a gurin amma wllh zata gane kurenta gurin ma baxani ba

haba yaya kamar ya bazaka ba bayan....

katseta yayi tare da fadin ubanme zan shiga inyi wazan burge a gurin bayan wadda nayi dominta ta kushe tun kafin ma tagani

hakane amma ai be kamata ka koma ba gurin fa duk kai ake jira mu nemi mafita kawai

wace irin mafita data wuce kawai in sanar da bros suyi abinda zasuyi kawai ni banda ni


gaskiya bata kyauta ba amma inaga yakamata kaima ka qona mata rai kamar yadda tayi maka

hmm ta yaya?

ta hanyar aron amarya

aron amarya kuma kamar ya kenan?

zan shiga ciki ne in duba wadda naga kayanku sun zo d same colaur ko sunyi shige kawai mu qara tsarata ku shiga gurin nasan dole zataji haushi amma tunda ita tace kalar kayan daka sa beyi mata ba ai kaga koma mezai faru daga baya ai kasata taji ba dadi kamar yadda taso kaji kunya

yana shirin bata amsa yajiyo muryar m.c nakara cigiyarsu sai kuma ga kiran habeeb ya shigo yasan kwanan zancen dan haka yace kinga je ki nemo kawai in yaso ran kowa yabaci

dai

5 / 33