Tame Gari 1 Complete Hausa Novel

Author :  Asma Baffa Category :  Romance

Chapter   1 / 33

1 to 3K   out of 96.3K words

ο»Ώ[: TA ME GARI*

NA
khadija usman

*BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM*

1⃣

Na rantse da Allah bazan yadda ba sai an biyani nikana tun

kin isa ma wlh kika sake kika je kika fadawa innata yaseen sai kinci ubanki cewar dije dake kara tattake garin dake zube a kasa kuma an barar din duk ranar da kika qara cemin dijan gala tame gari tuwon gidanku ma zanje in barar wlh

su Shatu dake gefe suna kallo ba damar suyi magana dije taci uwarsu dan haka sukayi gum ko yi hakurin sun kasa fada hafsi kuwa sai rizgar kukanta takeyi dan tasan yau idan taje gida kashinta ya bushe gurin delu dan saita mata dukan mutuwa kuma tasata nemo mata wani garin koda ta tuna ai saita kara bare baki dije ce ta kalleta tace wai ke uwar me nayi miki da kiketa min wannan kukan danma ban faffasa miki baki ba hegiya me idon gyada

shatu ce ta karaso kusa da ita tace kin san delu dukanta zatayi idan taje gida kin san dai ba imani ne da ita ba

shuru dije tayi na dan wani lokaci kamar wadda ta tuna wani abun sannan kuma tace toh kinga ke kika jawo wa kanki tunda kika tsoka ne ni amma kiyi haquri kinji tahi nasan yadda zamuyi amma sai kin bani hakuri

da sauri hafsi tace yi haquri dan Allah

toh naji ya sunana

Anti dije

wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta dan tana masifar son sunan nan na 'yan binni dan haka da sauri tacewa hafsi taso muje gidanmu in baki dawar ki kara kaiwa nikan

da sauri hafsi ta mike dan tasan ko yanzu takai nikan sai ta ci ubanta dan ta jima dan haka da sauri suka je gidansu dije koda suka je dije bata boyewa inna saudi komai ba aikuwa ta basu dawa suka kai nika har gida dije suka raka hafsi aikuwa delu kamar ta ari baki taita jarabar ta dayake 'yan dukan basa kusa sun dai samu rabon zagi amma bata daki hafsi ba

********
mota ce kirar honda Accord LC ta shigo cikin garin Gawo kasancewar rashin kyawun hanyar ga kuma da alama wanda ke cikin motar yasha tafiya mutum biyu ne ciki matasan samari kyawawa daka gansu kaga wadanda hutu da nera suka zauna a wajen tuki yakeyi kamar wanda aka yiwa dole kafin ya waiga ya kalli dayan yace cikin kasalalliyar muryarsa

Habeeb wlh nagaji dayawa na matsu mu qarasa cikin garin nan in yada zango kan gadon tsohon nan

wanda aka kira da habeeb yayi murmushi kafin yace hmm kaima kenan bare kuma ni dana sha tafiya kwana nan gashi yau ma son ganin wannan me ran karfen yasa na biyoka

hmmm kai dai bari ai wannan tsohon inaga rokon Allah yakeyi mana shiyasa bama iya daukar lokaci bamu ganshi ba ko daddy ma fa kullum shi batun shi baba malam kusan koyaushe yana kan hanya

toh Allah yaja da kwana dai

Ameen ya Allah

kam bala'i ta fada yayin da taga motar na kokarin shigewa alamar ma na ciki besan me yayi ba giginyar dake hannunta ta dauka ta saita glass din motar ta wurga cikin sa'a kuwa ta daki glass din side driver sannan taje ta hada da bakin habeeb wanda yagama amsawa da ameen yanzu

wani wawan birki ya taka tare da kiran ya Allah sbd ganin abun da yayi kamar a mafarki dubansa yakai inda habeeb yake yaga nan da nan bakinsa ya haye ya wani kumbura kamar bakin jaba ga kuma jini na zuba yaso yayi dariya harga Allah amma ba hali dole ya ambaci kalmar subahanallah ya fara kokarin bude motar ya fito danya zagaya gurin habeeb dan shi har yanzu baisan ta inda abin yafaru ba amma dai kawai yaga wulgawar abu

tsaye take ta rike kugu da hannu daya dayan kuma wata katuwar giginyar ce datafi ta farko girma
kwalliyar fuskarta kawai yagani yaji gabansa ya fadi dan wlh babu tantama wannan aljana ce

wa'innahu sulaimanu wa'innahu bismillahir rahmanir raheem ya fara ambata cike da tsoro da faduwar gaba domin dai babu tantama wannan aljana ce duba da yanayin ta gata fara sol saika ce zabiya ga kuma uban bakin kwalli data shafa a bakin nan kamar 'yar auta ga jagira cinku ta hade da kwallin dataja hawayen masoyi

jikinsa ne ya hau kyarma inda ita kuma dije take ta fahimci meyake nufi aikuwa a zuciyarta tace anzo gurin

harara taci gaba da wurga masa tanata juya ido inda shikuma hakan ke kara firgita shi cikin karkarwar jiki ya qarasa inda habeeb yake ya sunkuyar da kansa kasa sakamakon nauyin daya yi masa sbd giginyar ta bugi kansa ga haqorinsa guda daya daya fita ga bakin ya kumbura yayi tsayi kamar shantu cikin rawar jiki Nasir yakarasa inda yake ya bude murfin motar yana me karanta duk addu'ar data zo bakinsa dago kansa yayi ya dubeshi jin yanata kwarara addu'a sai ya fahimci lallai gamo sukayi domin ya hango aljanar tsaye da irin tasu giginyar ta Aljanu tanata juya ido duk da jirin dayake ji hakan bai hanashi rudewa ba shima ya kama kokarin fitowar nan suka kankame juna shida nasir wanda har kwalla yafara yi dan tsoro musamman duba da yayi da yanayin gurin babu komai sai tarin bishiyoyi da besan kona meye ba amma dai yasan harda na kuka kuma sune gidan aljanu

cikin wata irin murya da malkwada harshe dije tace ku bil adama daga ina

wani irin fitsari ne ya kufcewa naseer shiko habeeb ji yayi kamar ya suma dan kanshi saida ya amsa

ko bakwa ji ne ina tambayarku?

cikin in i na nasir yace yi....yi..ha.k..uri.daga Abuja Abuja wlh muka zo

shine aka ce dan kunzo daga binni kubi takan 'ya'yana suna tsaka da yin wasan su wato sbd kun raina mu ko

ah ah wlh ba...bahaka bane wlh ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba dan girman Allah kiyi haquri wlh bamu sani ba

toh naji zan hakura amma sai dai kubar abin hawanku anan ku qarasa da kafarku inda zaku ko kuma ni inkai ku

ah ah wlh mun gode suka fada a tare zamu karasa da kafarmu ina ke ina wahala akanmu

hahahahahaha
tayi dariya sannan tace saini dije uwar aljanu ku wuce amma fa bazan kyaleku ba duba da yadda kuka raunata 'ya'yana yanzu haka suna bangon duniya wajen me magani dan haka sai naje naga yadda jikinsu yake tukunna kafin in san wanne hukunci zanyi muku

kuuuuu cikin nasir yayi wata kara dan girman Allah kiyi hakuri wlh bamu san dasu bane ina mu ina aikata haka muna sane

toh naji ku tashi ku tafi gobe kuzo ku dauke wannan motar amma ba yau ba

to toh toh mun yadda wlh

sam habeeb yakasa tafiya yayin da naseer ne ya kamashi da kyar yasaba a kafada ya miki hanya bako waiwaye harda hadawa da dan gudu bako waiwaye

tunda dije taga haka ta zube a gurin tanata dariya harda hawaye a irin wannan yanayin su shatu suka qaraso suka risketa nan suka shiga tambayarta sam kin fada musu tayi gashi ba damar su matsa ta dankari banza dan karfi ne da ita kamar yaki inji su duk ta fisu karfi

sai da tayi me isarta kafin ta mike tace mu tafi

hafsi ce tayi karfin halin tambayarta ina gyadar da kika samo ?

ban sani ba tafada tana harararta

ai kuwa tayi gum suka ci gaba dactafiya da zarara ta tuno yadda bakin habeeb ya koma da kuma yadda taga Naseer yayi fitsari saita kuma kyalkyalewa da dariya sudai su hafsi nasu ido amma ba damar tambaya sai uwar gayyar ta so bada labari dakanta

*****
tafiya yakeyi ya hada zufa ga habeeb na cikin wani hali da taimakon Allah da taimakon wasu matasa daya sansu a gidan baba malam suka qarasa da shi gida

πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€



*TA ME GARI*


2⃣

*ina neman afuwarku sakamakon jina shuru da kukayi a littafina ZARGI NE SILA Insha Allahu shima zan karasa muku shi nan kusa uzuri ne yasha kaina*


ba karamin tashin hankali baba malam ya shiga ba ganin halin dasu habeeb suka shigo cikin rudewa ya shiga tambayarsu lfy ko hadari sukayi

sam naseer baya cikin nutsuwarsa abinda kawai yake iya fada shine gamo mukayi malam aljana wlh aljana ce

subahanallah!!!

malam ya fada kafin ya ce aje a kirawo muntari me chemist don ya duba habeeb domin yaga yana jin jiki da alama


bayan an gama masa duk abinda yakamata ayi masa harda allura malam kuwa rubutu yayi musu tare da tofa musu addu'oi sbd dukansu sun firgice daga baya suka samu bacci su duka kowa yanata al'ajabin abun wai aljana toh ko a ina suka ganta oho

****

da wakarta ta shigo tana rerawa inda ko sallama batayi ba ta shigo innah dake zaune tana dama fura tace kai kai dije nidai naga ranar da zakiyi hankali wlh ace da girmanki amma kina abu kamar wata karamar yarinya ni wai makarantar Allan ma anya idan na turaki kina zuwa kuwa ?

turo baki tayi gaba sannan tace ina zuwa mana toh ba'a can na iya karatun sallah ba kuma dai bari in fada miki tsakani da Allah ina zuwa in labe wani lokacin bayan ajin su mairo ta gidan me gari in ta kallonsu ana koya musu karatun arna

haba inna saudi ta rike tace oh ni saude nagamu da ja'irar yarinya wato duk hanaki din danayi wato baki jiba ko saida kika dinga zuwa Allah ya shirye ki

Ameen dan kuwa yanzu ma a shirye nake kamar carbi

kasa magana inna tayi a ranta tana jinjina kiriniya irinta dije tarasa dalili ko dan taga ita kadai ce ohoo haka dai taci gaba da damun furarta ita ko dije ta shiga cikin daki ta kwanta a cewarta saitayi bacci kuma kada a tasheta tana kwanciya ta tuna da abinda yafaru dazu aikuwa ta sheke da dariya wadda saida inna ta taso ta lekata taganta sai dariya takeyi harda rike ciki girgiza kai kawai tayi ta saki labulen dan ita lamarin dije sai addu,a wani lokacin idan tayi abu kamar me aljanu


*Asalin labarin*


Malam muhammadu
dan asalin jigawa ne yanada mata hudu da tarin yara matarsa ta fari nada yara shidda maza ta biyu kuwa yaranta tara bakawai mata biyu maza ta ukun nada yara biyu duk maza sai Amaryarsa dake da yara goma sha daya tara maxa biyu mata Alhmdlh gidan akwai zaman lfy da hadin kai domin ya gina gidansa da zaman lfy dazumunci mariya itace matarsa ta uku itace keda yara biyu inusa da Auwalu duk cikin matan sa tafi hakuri da kawaici hakan yasa yaranta suma sukayi sanyun hali irin nata sam basu da hayanikuma dukansu manoma ne sosai yayin da dukansu sukai aure kuma barakallah dukansu suna nan da rai malam inusa nada mata daya wato saude Allah be azurtasu da haihuwa ba tsawon lokaci sai daga baya suka fara samu amma kuma yaran wabi sukeyi saida tayi haihuwa hudu haka kafin daga baya tasamu cikin dijee cikin hukuncin Allah kuma ita ta rayu khadija ta taso yarinya kyakkyawa fara ce sol irin fararen nan ne sosai sai dai fa batajin magana duk wata tsokana da caskale ta kware akai dan haka yara sa'anninta ke tsoronta inda har suka samata suna bata sani ba wato uwar mazga🀣

a cikin 'ya'yan malam muhammadu dayawa daga cikinsu sun sami cigaban rayuwa inda sukayi karatun boko wasu sun sami aiki a birni wasu kuwa kasuwanci yakaisu kuma cikin ikon Allah ansami daukaka da wadata inda malam muhammadu yake da matansa suke samun kulawa a yanzu haka shine matsayin me gari wanda su habeeb 'ya'ya ne ga dansa babba wato khamis dake aiki a abuja sam basu dade da dawowa daga U.S ba inda suka shafe shekara goma sha biyu a can dan a can sukayi karatun su na secondry har zuwa jami'a indadukan su suka karanci fannin likiktanci shi habeeh ganygoicial shi kuma Naseer consultant ne yanzu haka satinsu biyu da dawowa shine suketa zaga dangi dan suna son kauye basu da kyama sam

*cigaban labari*

uwar mazga nata sharar bacci cikin baccin ma mafarkin su habeeb tayita yi wai har da zawo naseer yayi aikuwa take ta qara rushewa da dariya wadda ta qara jawo hankalin inna ganin da tayi tanata bacci ba ruwanta yasata tashinta dan itafa ta gama gasgata aljanu ne da dije


*****
inna saudi ce ta fito dauke da kwarya cike da fura inda dije dake zaune gefen babanta yana cin tuwo tanata zuba mishi surutu inna saudi tace malam na fito bari inyi sauri inje in dawo inga jikin nasu dije taso muje ki rakani dan dare ne yanzu yafi mu tafi mu biyu


ah ah ni ba inda zani ai munyi fada da baba malam shiyasa jiya da hafsi tace min dijangala tame gari na barar mata da gari ni yanzu nayi yaji saiya zo biko


dariya sukayi dukansu inda malam inusa yace yi tafiyarki kinji kyale wannan uwar rigimar

ai bama saika ce ba ni nayi gaba saina dawo

a dawo lfy innata

Allah yasa

tasa kai ta fice

gyara zamanta tayi tace baba wai ni waye beda lfy ne a gidan me gari ?

yayyenki ne na abuja wai gamo sukayi da aljana a hanyar su ta shigowa gar......ai be qarasa ba yaga ta mike ta suri takalma tana bari inje in raka inna sai na dawo ta zura da gudu tabarsshi da sakin baki kafin daga baya yayi murmushi yace Allah ya shiryamin ke dije ta


****
bata riski inna a hanya ba dan ba hanyar datayi tsammani tabi ba kusan a tare suka isa amma innah sam bata ganta ba ta shige gidan bayan sun gaisa da surikanta ta shiga bangaren mai gari ta gaisheshi tare da su habeeb wadanda suka warware amma kumburin bakin habeeb na nan idan nasir ya kalle shi saiya qara fashewa da dariya iya kuluwa habeeb ya kulu jiyakeyi inda ba aljana bace tayi musu haka ba wlh da mutum ne bema san me zaiyi masa ba a haka inna ta musu sallama tana dada jajanta abin kafin ta miqe tayi musu sallama ta fita


a kofar gida ta riski me gari zaune bisa kujerar sa ta tsoffi ta lababa ta shige gidan indayana kallonta amma ya qyaleta dan yasan halin mutuniyar tunda bataso kulashi ba toh gara ya kyaleta

dakin kakarta ta je ta gaisheta da sauran matan gidan sunata tsokanarta malam yaje biko kenan

lababawa tayi ta dauki kwalli cikin kayan kwalliyar dake cikin wani karamin kwando kafin tace

goggo habi ance anyi baki a gidan nan suna ina ?


suna can sashen malam dan basuji dadi ba kam dan gamo sukayi.

zaro idoo tayi😳gamo fa a ina?


can tsallaken lawoli dan sai dazu jibrin yaje ya dauko motar su ma dan can suka barta

oh Allah ya kiyaye gaba bari naje in gansu



toh maxa kam dan dare yafara yi kizo ki tafi gida in kuma nan kwana to

ah ah niba zan kwana a nan ba

oh dai ke kika sani

sai da ta tsaya lungun bangaren ta zazzana kwalli ta fito aljanar sakπŸ‘Ήkafin ta nufi dakin datake jiyo maganar su da alama waya daya yakeyi daga cikinsu

cikin sanda ta qarasa qofar dakin cikin sa'a tana zuwa ana kawo wuta inda haske ya gauraye dakin baki daya kasancewar habeeb ya juya bayane yana shan fura da kyar da dabara sbd bakinsa shi kuma nasir yana waya hankalinsa be kawo inda take ba shiyasa basu ga tsayawaer ta ba

Angaishe ku fitinannun bil adama masu kunnen kashi....
[16/12, 11:39] β€ͺ+234 806 493 3819‬: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

*
*vote*
*comment*
*share*
[16/12, 11:39] β€ͺ+234 806 493 3819‬: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€


*TA ME GARI*

na
khadija usman

5⃣

cikin kwanaki kadan aka gamawa dije komai na makarantar ta arabi da boko kasancewar Alhaji khamis ba mazauni bane yasa dije ke fuskantar rashin jin dadin zama ga dukka mutanen gidan dan su nasir ba qaramar wahala suke bata ba saukinta daya bangaren masu aiki take shiyasa take dan samun rangwame duk tayi sanyi da dana sanin zuwa binni sam inbanda karatu ba abinda tamaida hankali akai


dawowarta kenan daga makaranta ta shiga tayi wanka dan dama bata son kazanta duk shakiyancinta man basira me aiki take shafawa duk da vaseline ne amma bawani duhu datayi koba komai cimar kauye da ta birni akwai banbanci kuma ga A.C dake ratsata daga school har gida dan makaranta me tsada aka sata kasancewar tayi primary daga nan inna tace bazata yadda taci gaba da karatun arna ba shiyasa ta hakura su kuma anan suka sata a J S S 3 bada jimawa ba jasu zana juinior waec kuma alhmdllh tana fahimta sosai ko yanzu data gama shafa mai niyya tayi tadanyi kwalliyarta amma data tuna in tayi anan za'a yi mata dariya hakan yasa tafasa yi tunda bata iya ta 'yan birni ba har yanzu dan kayan kwalliyarta tun na gida ne


fitowarta yayi dai dai da fitowar habeeb wanda ya zuwa yanzu yasa an mayar masa da hakorin roba a inda yasamu gibi baza'a taba ganewa ba tafiya yakeyi yana waya da alama hirar ta soyayya ce duba da yadda yaketa lumshe ido tare da karya murya

fitowa tayi zuwa kitchen dan tadau abincinta sanye take da riga da sicket na atamfa se yawo takeyi cikinsu kusa. dinkin kauye sam bata lura dashi ba har saida takawo kusa dashi kamshin hadadden turarensa na indunusia ya bugi hancinta wuceshi tayi ta shige tadauko abincin ta dai dai tazo fitowa sukayi karo miyar agushi ce da tuwon shinkafa duk ta hada a kwano daya hakan yasa malmalar tuwon tayi kasa yayin da miyar tasauka jikin farar T.Shirt din dake jikinsa ta gangara kasa aikuwa take ya saki wata 'yar qara sakamakon miyar nada dan zafi dan kun san manyan coolers na riqe zafi sosai

dan ja haya tayi kadan a dan tsorace dan sam bata bukatar wani abu ya hadata da wadan nan azzaluman dan haka kawai ma in sun so wahalar da ita sukeyi suyita cewa tayi musu kukan aljanu ko wani abun in takiyi su daketa bare kuma yanzu data tabbatar tayi laifi ai bata gama tunani ba taji saukar tagwayen marin dasai da kanta ya bugu da fredge din dake wurin wata qara tasaki wadda mamy ahigowarta kenan ita da naair da wata budurwa wadda

1 / 33