Tame Gari 1 Complete Hausa Novel

Author :  Asma Baffa Category :  Romance

Chapter   23 / 33

66K to 69K   out of 96.3K words

da akayi akwai cakwakiya cikinsa amma ba yadda zaiyi dole yayi biyayya dan yasan dashi da iyalinshi duk karkashin hukuncin baba maigari suke komai ya zartar dole su aminta dan haka cikin tausasa murya ya shiga kwantarwa da Inna hankali,amma ina sam bata fahimtarj shi,ganin hakan yasashi daga muryar shima tare da fada mata inta matsu taje tasami maigari da kanta tayi masa bayani,wadda yasan da kamar wuya hakan ya yiyu,amma ga mamakinsa sai ji yayi tace inkamun izini zanje in samu baba!,

a dawo lafiya ya fada wanda yakai kallonsa ga bakin kofar inda yayi ido biyu da Dije da hawaye shabe -shabe,kureshi tayi da ido kafin daga baya ta karasa gurin Innah ta fada jikinta suka fashe da kuka.

tabbas ya tausayawa iyalin nasa sai dai shima ba yadda zaiyi da hukuncin mahaifinsa dan ya tabbar dalilin sa na yanke wannan hukuncin yana da karfi sosai,kuma bai isa ya musa masa ba kawai abinda yafi ya lallaba su ya rarrashe su tare da yiwa tilon 'yar sa addu'ar Allah ya basu zaman lafiya ya kuma kareta dan haka cikin tausasa murya ya shiga yi musu magana.

Nana Khadija!!

"ya kira sunan ta a tausashe",

cikin dashewar murya ta amsa masa.

nasan ya zuwa yanzu kinji duk abinda yake faruwa ko?

kai ta gyada masa alamar eh!

to Alhmdllh,ina son ki kasance me yimana biyayya akan hukuncin da mahaifina ya yanke akanku gaba daya wadda kin san bake kadai aka yiwa haka ba ku hudu ne,kuma duka kowa ba'ayi shawara dashi ba illa mu iyayenku,munyi hakan ne dan mun san mun isa daku kuma zakuyi mana biyayya,kada kisawa zuciyarki tunanin wani abu yazo yadameki kisawa ranki auren nan alkhairi ne ko da bakwa son junanku sannu a hankali zaku koya na rokeki da girman Allah,ki daure ki karbi hukuncin da mahaifina ya zartar a kanku kiyi mini wannan alfarmar ki.....ya isah baba dan Allah kabar rokona haka!,

Dije ta katseshi cikin kuka.

Wallahi baba na yadda na amince da duk hukuncin da kuka yanke nayi muku alkawarin duk runtsi duk wuya bazan baku kunya ba ta karasa maganar tana fashewa da wani kuka mai cin rai.

to kukan na miye khadija? nasan bazai rasa nasaba da kinada wanda kike so ba,ina son kiyi hakuri naso a rayuwa nabaki damar ki zabawa kanki mijin da kike so amma hakan bai yiyu ba amma nasan haka ALLAH ya kaddara wani baya auren matar wani Allah yasa muyi alfahari da auren ku Ameen.

jikin Innah a sanyaye ta furta,kaddara ta riga fata babu yadda zamuyi,zanci gaba da tayaki da addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a rayuwarki.

Ameen ! ko ke fa,abinda yakamata ki fada kenan tun tuni,yanzu bari naje nayi sallar la'asar naji an kira sallah,ya mike ya fita.

yana fita Innah ta dubi Dije cikin karaya tace,

Wallahi Dije ina jiye mike zaman kishi da koda sa'arki ce bare wadda ta haifeki ma da gani,ikon Allah kenan ni uwarki banyi zama da kishiya ba gashi ke zaki je kiyi.

kada ki damu Innah"wallahi lafiya zamu zauna indai nice bazaki ji wat baraka daga gareni ba insha,Allah

hmmm!! yaro man kaza" bazaki fahimta ba yanzu kawai Allah yasa alkhairi.

a zuciyarta ta amsa da Ameen,kafin ta zame ta kwanta kan cinyar Innah jin wani zazzabin gaggawa na shirin kamata.

*******

Washe gari tunda sassafe Daddy yabar jigawa ya nufi Abuja inda yana isa ya iske mamy da surukanta baje a falo suna ta ciye-ciye,da fara'arsa yayi sallama ya shiga falon.

sunyi mamakin ganinsa a wannan lokacin,amma suka basar tare da amsa sallamar tasa suka shiga gaisheshi,nan ma cikin sakin fuska ya amsa kafin ya haye samansa mamy tabi bayansa tana fadin shima yaji ba dadi ya gudo.

tana shiga ta iske shi yana kokarin cire babbar rigarsa,dan haka ta karasa tana fadin sannu da zuwa,ashe kana hanya babu ko labari.

Wallahi kuwa naso in kira kuma saina fasa nace kawai sai dai ku ganni.

Ai na dauka sai nan da kwanakin daka diba zaka dawo din?

Eh to da naso hakan amma wani uzurin gaggawa ya tasomin.

kaga Alhaji kawai bawata kwana-kwana kace dai kaima kauyen ta isheka,dan dama nasan karfin hali kawai kayi dan kar a ce ka guji asalinka,gashi da kaga uwar bari ai kadawo.

yaji zafin maganganunta ji gayi kamar ya fada mata abinda ke faruwa amma sai ya daure yabari akwai lokaci dan haka yayi murmushi yace,

Ina mutum ina gudun tushensa da asalinsa kawai dai na fada miki uzuri ya tasaoni bagashi su wadancan yaran naki da basu da abin yin ba suna can na baro su ba.

wayake ta wadan can shashashun,ai sai suyita zama tunda basu san ciwon kansu ba,ga matansu nan a nan duk lokacin da suka gaji suka dawo su kwashi abinsu.

ai kuwa yakamata su ci gaba da zama kusa dake sa fi samun kulawa.

A ina zan ajiye su?

ai wannan ba matsala bane gidan nan nawa danace miki na siya a hannun minister kin san girman sa yasa nace bazan zauna ciki ba dan yayi shi danshi da family dinshi ne gaba daya dan su zauna sai Allah ya aiko masa da wannan kaddarar dole ya said shi,to basai mu koma can gaba daya ba.

Dagaske kake Alhaji ko da wasa?

Dagasken gaske kuwa!

Ammq ko da nafi kowa farin ciki,da burina ya cika ace nice a wannan gidan.

kada ki damu burinki kamar ya gama cika kawai ki fara shirye-shirye nan da sati ma inaga zaku tare.

kaga Alhaji bari kaga inyiwa yaran nan albishir batako tsaya taji mai zaice ba ta fita da sauri ya rakata da dariyar mugunta.

cikin kankanin lokaci aka shiga kwaskware gida kasancewar dama a kimtse yake feni kawai akayiwa ko wanne part,tsarin gidan yayi kyau da tsari cikin kankanin lokaci komai yayi neat kasancewar nera tayi kuka inda su kansu surukan mamy sunji dadin komawar su wannan tamfatsetsen gidan kowacce sai kai ha kara girma,yayin da kowanne bangare ke kokarin yin barin nera dan burgewa da gwangwaje yaran nasu.

shiko Daddy dakansa ya sayi furnitures masu kyau da tsada duk part din nan hudu aka sa na mamy dana amaryarsa iri daya sak komai yasa,hakama na Dije da zainab bai banbanta komai ba suma har colour.

sai da ya tabbatar a cikin kwanakin daya diba konai ga kammala kafin ya rufe dukannin parts din su Dije,ko da su mamy sukaje ganin nasu kusan sumewa sukayi dan dadi.

shi ko Daddy ko mamy bai sanarwa ba ya kama hanyar jigawa.

****

Tunda aka daura auren basu hadu da junan su ba,Dije ko har yanzu zazzabi ke damunta ko da maigari ya tambayi baba yunusa ina Dijen nan yake sanar mishi halin da take ciki.

Habeeb yasa aka kira ya fada mishi halin da matarsa ke ciki yace yaje ya dubata.....

*managed pls*

*with*
*Alkalamin khady* ✍
[3/18, 8:06 AM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*AWESOME WRITER'S ASS...* 🏮
(Place of excitation n'd pleasant writer's)

*TAME GARI*

NA
Khadeeja Usman

4⃣3⃣

*Hakika kowanne bawa da irin tasa jarrabawar,ni tawa yawan lalura ne,Amma wasu sun kasa fahimta ta,babu yadda za'ayi kalau lafiya inki Yi miku posting,ni nayi niyya na Fara rubuta muku tame gari ban San cewa Zan Kai har haka ban gama ba,Dan Allah ku dinga Mana uzuri mu writer's maganganu ku masu kaifi agaremu su ke Kara sa zuciyarmu rauni Dan Muna ganin Muna iya kokarin mu Amma ku kuna fada Mana ba dadi,babu dole duk wadda taga tagaji da bibiyar buk din to ta sawwakawa kanta da karantawa.*

*Sannan bazan gaji da rokon masu bina pc suna Neman buk din suyi min uzuri Dan Allah,masu min magana bana samun damar dubawa Suma suyi hakuri duk Ina sane daku Kuma Ina matukar godiya.*

**** ************** ****

Tana kwance saman gadon Inna ta kudundune sbd sanyin da takeji,muryarsa ta tsinkaya Yana gaida Inna,wadda ke amsawa cikin Jin kunya da nauyinsa,kasa tashi yayi daga tsugunnon da yayi,bare ya tambayi Ina take,lura da yanayin sa da Inna tayi yasata fadin,

"ka shiga Tana ciki".

Dafarko yi yayi Kamar baiji ba,sai da ya Dan jima kafin ya mike ya nufi dakin inna.

A ciki ciki yayi sallama wadda indai ba kunnen maciji ne dakai ba bazaka taba Jin abinda yace ba.

Samun guri yayi ya tsaya,yayin da ita Kuma taji alamar shigowar mutum,hakan yasata kokarin yaye bargon data rufa dashi,sai dai kafin ta yaye din bayyanar kamshin turarensa ya sanar Mata da ko waye din tsaye .

Komawa tayi ta lafe yayin da shi Kuma ya Kara gyara tsayuwarshi bashida niyyar yin magana.

Jin da yayi tsayuwar ta isheshi yasashi fadin,

Ke ni na gaji da tsayuwa ki tashi mu tafi asibiti,nasan kina jina likimon Munafunci kikayi.

Da ta so ta kyaleshi Amma saita kasa Dan hi tayi in Bata tofa albarkacin bakinta ba to zata iya shiga wani yanayi.

Dan haka cikin muryarta ta marasa lafiya tace.

"So na dauka tabarya ka hadiya,shiyasa ban tausaya wa tsayuwar da kayi ba",
[3/18, 8:07 AM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*AWESOME WRITER'S ASS..* 🏮
(Place of excitation n'd pleasant writer's)

*TAME GARI*

NA
Khadeeja Usman

4⃣4⃣

*Kuyi hakuri nasami miss number ne a page din daya gabata amma fatan zaku fahimce ni*

Itama yusrah jiri-jiri ta Fara gani,hakan yasa ta nemi guri ta duka tare da dafe kanta datake ji lokaci daya Yana Mata wani mugun ciwo.

Shi kuwa Daddy Yana Gama musu jagora tare da Nuna musu kowanne sashi na bangaren amaryar sa wayarsa ta Fara ruri alamun Ana Kiran sa,hakan yasa ya fito ya nufo wajen,sai da ya gama wayar sannan ya nufo wajen daya hangi su mamy Amma ya Nuna Bai gansu ba Dan ya Kara kuntata musu Dan yasan ya zuwa yanzu sun shiga kidima da wani yanayi na kasa tantance meya ke faruwa.Yana fitowa ya hange su kuwa yashe a kasa,ita ko yusra h tana duke,cikin ko in Kula ya karasa inda suke,duk da yaga halin da suke ciki Amma ya Nuna Kamar Bai damu ba,Daya daga cikin direbansa ya Kira,cikin kankanin lokaci kuwa sai gashi Nan ya Kira su Habeeb yace suzo su taimaka asa uwarsu da matansu a mota akaisu asibiti.

Dukansu hankalinsu ya tashi ganin halin da suke ciki,musamman Naseer Daya san Yusrah nadauke da ciki Kuma yaga halin datake ciki,babu Bata lokaci suka sasu a mota suka nufi asibiti dasu,shi ko Daddy baiko bi ta kansu ba Dan ya San ya zuwa yanzu abinda ke damunsu kishi ne,Kuma burinsa ya cika,Dan haka Ya fito da waya ya Kira Hajiya baturiya yace Mata ya maganar da sukayi fatan komai ya kammala.

Amsa Masa tayi da an Gama komai ya zuwa yanzu dama jiran wayar sa takeyi.

Shikenan zuwa goben sai ayi komai ko?

Shikenan Allah yakaimu

Ameen!

Nan sukayi sallama ya Kira restaurant din dayayi order abinci cewar su kawo yanzu,aikuwa ba Bata lokaci sai gashi sun kawo abinci Mai Rai dai lafiya,Nan fa mutanenmu suka shiga kwasar gara da harrakawa.

***********

Itama yusrah kafin a karasa asibitin ta karasa sumewar hakan yasa ko da suka Isa duka daki Daya aka Basu tare dayi musu taimakon gaggawa kasanceawar tun suna hanya suka Kira Yusuf dayake Yana asibitin suna zuwa kuwa aka antaya wa su Hajiya mamy zurkudediyar alluran bacci,bayan an Gama musu duk abinda ya kamata an tabbatar sun farfado.

Suna asibitin Daddy ya Kira su yace su zo Yana son ganinsu.

Sun Dan jima kafin su zo suna zuwa yajasu part din mamy.

Bayan sun zauna ne yaga sun nutsu yayi gyaran murya tare da Yin addu'oi na musamman sannan yafara magana.

Nasan a matsayinku na 'ya'ya agareni nayi muku abinda ku kuke ganin ban kyauta muku ba,duk da cikinku babu Wanda ya nunamin hakan baiyi Masa dadi ba sai dai nasan kunyi shuru ne Dan kuyimin biyayya,Alhamdulillah naji dadi Kuma nayi farin ciki da Allah yabani yara masu biyayya

"Allah yayi muku albarka".

Ameen!!

Suka amsa gaba daya

Sannan Daddy yaci gaba,kuyi hakuri da auren Dana daura muku batare Dana tambayi Ra'ayin Daya daga cikinku,ko kuna da ra'ayin Kara aure ko bakuda shi,to banayi hakan bane Dan wani abu,ko dan na Bata ran matanku da mahaifiyarku ,sai dai nayi ne Dan gyara da duba duk abinda zai je ya dawo Nan gaba idan nabari abinda matanku da mahaifiyarku sukayi yaci gaba da faruwa,shiya sa nadauki wannan matakin,to Amma Ina son ku sani,Kamar yadda ban nemi izininku ba nadaura muku aure,haka Suma yaran da aka daura muku auren dasu babu wadda aka nemi Jin ra'ayinta Kuma suka amince,to dukanku munji dadi da kukayi mana biyayya Allah yasa yadda kukayi mana Allah yabaku masu Yi muku Kuma.

Ina son Kamar yadda kuka mini biyayya ku rike amanar da Allah ya Baku ku Kula da matanku,kuyi adalci tsakaninsu,ku tabbatar kunyi adalci dan gudun tashi da shanyayyen barin jiki ranar gobe kiyama,ku rike amanar da kuka dauka kuyi kokarin sauke nauyin dake rataye a wuyanku,Allah yayi muku albarka ya albarkaci aurenku da zuriyarku baki Daya,Ameen!!

Nan yaci gaba dayi musu nasiha Mai ratsa jiki da zuciya,sai da ya gama kafin ya shiga sanar musu plan din daya shirya akan su mamy har sai sun gane kuskurensu,Nan ya fada musu shirin dayayi gobe,dukansu sunji sun Kuma gamsu Dan haka ya fada musu plan dinsa na farko Daya shirya.

Kuyi managed

*Alkalamin khady* ✍
[3/18, 8:07 AM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*AWESOME WRITER'S ASS..* 🏮
(Place of the excitation n'd pleasant writer's)

*TAME GARI*

NA
khadeeja usman

4⃣6⃣


Kamarya!! Na kwantar da hankalina,bayan Ina ganin gayyar mutanen garinku a gidana,wato bayan wannan kodaddiyar Mai zubin mayun,harda Karin mutum biyu aka samu,no wonder,ashe shiyasa na dinga mafarkai kaje gidan marayu da sansanin 'yan gudun hijira ka debo mutane ka kawo su gidan nan,Ashe wannan gayyar ne suka bugo Mana sammako,ni wannan rashin son 'ya'ya irin na saude da inusa ban San Ina zasu kaishi ba,inba haka ba 'yar kwaya Daya ku gagara riketa,duk nasan kwadayi ke dawainiya da su,shine wato Dan sunga ita ta samu gurin Zama shine harda tattago wasu da hadota dasu,to wallahi Sam bazan lamunta ba dole su tattara su koma inda suka fito a yau basai gobe ba.Ta karasa maganar tana wani huci,idonta na kan mama mariya dake hakimce kan kujera,Jin maganganun da mamy ke Fadi yasata harde kafa Daya kan daya.

Duk abinda ta fada baisa Daddy ya Nuna Mata bacin ransa ba ko kadan,Dan yasan abinda zataji yanzu shine zai daga hankalinta,ya wargaza nutsuwarta,dan haka cikin sanyin murya ya Fara Mata magana.

Haba uwar gidana,me yayi zafi haka,kada fa ki Manta kece sarauniyar gidan gaba Daya Kuma shugaba a cikin gidan,ai irin wannan Bai Dace da tauraruwa Kuma lantarkin gida ba,Dan haka kiyi hakuri kizo kisamu guri ki zauna kiji me zan fada muku.

Wani sanyi taji a ranta,Wanda yasata sakin karamin murmushi ya lura da hakan,ita ko a zuciyarta tana ayyana idan har Zama suka zo yi to kuwa saita maida su kamar bayi,Dan duk masu aikin gidan sallamar su zatayi,daga mazan har matan Kai har maigadi ma,da wannan tunanin ta karasa ta zauna tana karkada kafa da hura hanci,Nan surukan suka shiga gaisheta,sabanin yusrah data mike ta fada jikinta tare da sakin kuka Mai sauti.

Cikin kidima ta shiga tambayrta me aka Mata ?

Cikin kuka ta Fara fadin wallahi mamy kice Masa ya sakeni,Dan wallahi bazan Kara Zama dashi ba,mugune Azzalumi Wanda Bai San kima da darajar soyayya ba,wallahi na tsaneshi,idan har Bai sakeni ba wallahi zan kashe shi daga shi har matsiyaciyar yarinyar.

Ban gane ba? Wace yarinya ce wannan da take Neman tarwatsamin farin cikin yarana?

Nuna Zainab yusrah tayi da hannunta.

Au! Au! Kice ku naku shirin na musamman ne,wato da tuggu da makirci Kika iso gidan,shine daga zuwanki yau Kika Fara shiga tsakanin Mata da miji ko? To wallahi baki Isa ba,inma uwarki ce ta kitsa Miki daga wannan bakin kauyen naku to kisani zaman maraya Dana karkara akwai bambamci,to Wai ma uwar me Kika kulla da har yaran da suke masifar son junansu kamar Laila da majnun suka samu sabani,har take cewa ya saketa?

Mamy Wai aurenta yayi.

Ke bana son iskanci wanne irin aure Kuma?to kodai kema kin shiga tarzomar mafarkin ne kamar yadda nayi?

Sajida dake zaune take Jin tamkar zuciyarta zata tsake ta fito,Dan ji takeyi duk wani abu da zasu ji to ko Rabin abinda takeji bazai kaiba,Amma sanin abinda ta shiryawa zuciyarta yasa ta danne tare da sakin murmushin dayafi kuka ciwo tace,tabbas mamy ba mafarki yusrah tayi ba gaskiya ne cewar duk mazajenmu sun Kara aure kamar yadda Habeeb yayi mun bayani, sakamakon rashin Jin maganar su da mukayi muka baro kauye Wanda sai yanzu nakejin tabbas bamu kyauta ba,abinda mukayi am........

Ke dayalla dakata ni bama na fahimtar ki sosai,shin mazajen naku ne suka Kara auren batare da ni mahaifiyar su na sani ba ? Shin Kuna nufin kucemin Kuma daga kauye suka dauko matan nasu? Kai wallahi karya ne.

Wallahi mamy gaskiya ne abinda Anty ta fada Dan Dana yiwa Naseer magana Akan inbai sakeni ba saina fada Miki sai yace ai harda kema anyi Miki Wai ina kyautata zaton ma itace wannan zaune kusa da Daddy.

Wayyo! Wayyo! Na shiga uku ni karima,kishiya da girmana Hamisu da gaske ne abinda suke fada? Ka fadamin inji ni aka yiwa kishiya,? Kishiya ma daga kauye? Wallahi bazai yiyu ba,nasan shirin mahaifinka ne,Dan ya tozarta ni,ni da zuri'ata,wallahi Bai Isa ba saina warware wannan mugun kullin da akaimun,yanzu na fahimci abinda ya faru,Amma yanzu zanyi maganin abun,Ina son yanzu ba sai andau lokaci ba Kai Habeeb da Naseer a matsayina na uwar data haifeku,ku warware wannan tsinannen auren yanzu ku sakar musu yaran su kafin nima nasan abinyi akan tawa,ta karasa maganar tana huci.

Dukansu kallon juna suka tsaya yi,yayin da shi Kuma Daddy ya tsaya Yana kallon mamy Dan yayi tsammanin fiye da hakan ma daga gareta,Saida maganganun data fada akan mahaifinsa sun Bata ransa Amma shi yasan matakin dauka yanzu.

Magana nake muku cikin tsawa ta fada,wadda dukan su su hudun suka shiga yanayin damuwa shikam Naseer a yanzu ji yakeyi daya saki Zainab gara tace ya saki yusra Dan ko zagin data Masa ya Isa ya saketa,shi kuwa Habeeb duk da baijin wani son Dijen a ransa Amma baijin ya tsani auren ko ita kanta,Kuma shi a tsarin shi ma babu saki ko da wa ya aura,Dan haka duk sukayi shuru.

Wallahi idan har baku sake su ba yanzu-yanzu na rantse da Allah saina tsine muku...

Ke kuma ki sani adadin sakin da sukayi kema adadin naki kenan! Cewar daddy Daya Mike cikin bacin Rai,yasan inda a abinda mamy ta tsana Bai wuce ace tabar gidansa ba,matar da ko 'yan uwanta Bata son zuwa wajensu,Dan haka ta girziza da jin furucinsa Wanda yasata saurin

23 / 33