Tame Gari 1 Complete Hausa Novel

Author :  Asma Baffa Category :  Romance

Chapter   10 / 33

27K to 30K   out of 96.3K words

dake son babbar mace wadda ta iya tattali irinta me zaiyi da wannan berar wadda inba kayan fitina da jaraba ba ba abinda ta ginu akai dan haka cikin dan hade rai tace ai ke yakamata ki sanar min alaqar ba shi ba

kallonta dije tayi ta nazarci matar tun dazu ta karance ta akwai kishi dan haka saita kiyasta a ranta kawai inta yi mata wani rashin kyautarwa wlh ta hakan zata azabtar da ita

itako sajida haushin yarinyar ta tsinci kanta da ji dan sai yanzu ma taga meye dalilinta na tsayawa ta biye mata yarinyar da bata wuce sa'ar kausar ba autar su dan haka saita sa kai da niyyar ficewa daga dakin muryar dije taji na fadin

.yauwa Aunty jeki bashi haquri ni bawani dadewa zanyi ba zan koma gida amma dan Allah a dan taimaka a qara yawan abincin gidan kar ayi la'akari da girman mutum shi ci ba'a nan yake ba kada ki ganni siririya wlh rainon kauye ce dan haka a taimaka kada a tauye ma cikina hakkinsa kuma kada ki manta kice masa ya baki labarin zuwansu qauye last

ko ta kanta sajida bata bi ba tasa kai ta fice itama ta fito sajida na kokarin shiga dakinta ta tsinkayi muryar dije na fadin

aunty inane madafa?

kamar ya ?

ashe fa matar yaya 'yar gayu ce na manta wlh

i mean kitchen?

nuni sajida tayi mata da hannu inda tai shigewarta daki

tana shiga dije ta kwashe da dariya tare da qarasawa kitchen din ruwan tea kawai ta hada tasha dan duk jikinta ciwo yakeyi har yanzu musamman gurin da nasir ya riqeta a nan ta shanye shayin ta gama ta koma masaukinta tare da bude jakarta ba kayan bacci ciki dan haka ta kwanta abinta a haka da kayan yusra🀣

tana shiga dakin ta sameshi gaban mirrow yana fesa body spray a dan hade rai ta qarasa ta karba ta shiga fesa masa duk yana lura da yanayinta kasancewar ta mace me iya tattali da soyayya sajida ta waye kwarai ta san hanyoyin mallakar miji cikin sauki ba boka ba mallam tasan kissa kala kala hakan yasa ta mamaye zuciyar habeeb domin shi dama dan son rayuwa ne kuma saiya samu me tarairayarsa duk yadda yake da jin kai da miskilanci to fa a gaban sajida tamkar yaron goye yake kuma yana iyajin zai iya mata komai a rayuwa dan haka koda yaga yanayinta yasan akwai damuwa damuwar kuma bazata wuce akan zuwan dije ba dan yasan sajida akwai kishi dan haka saida yabari sun gama shirin kwanciya kafin ya jawota jikinsa cikin salon tasa soyayyar ya shiga fadin

what's wrong with my princess ?

uhmm ?

shuru tayi kafin zuwa can yaji tace

mece sahihiyar alaqarka da khadija?

cike da mamakin tambayar datayi mishi yace kamar ya ban fahimta ba inaga ai kinfi kowa sanin matsayinta a gurinmu ko?

hmmm amma ai tace in tambayeka ainihin sahihiyar alaqar dake tsakaninku wai a kauye shine nake son jin ko akwai wata a qasa ne

murmushi yayi a zuciyarsa tare da fadin lallai yarinyar nan bala'i ce ko ince annoba ifritu wato tayi nazarin hallayar sajida harta zurma ta ita kuma duk da girmanta da shekarunta ta kasa fahimta wannan akwai shegiyar yarinya wato so takeyi ya bata labarin abinda tayi musu a qauye abinda ya barshi a sirri baya fatan matarsa tasan abin kunyar daya faru shine take son fallaso shi ai wlh gobe korata zaiyi gidan nasir suje can su karata tunda su sun saba wristilling da ita

jin yayi shuru ne yasata fadin kayi shuru baka bani amsa ba

oh baby matsala wlh wlh kinji na rantse miki wlh babu wata alaqa tsakanin mu in ba matsayinta na qanwa garemu ba ke ni wlh banma santa ba sai zuwan da mukayi time din da muka dawo nigeria daga nan tsohon nan ya hadomu da ita shine silar zamanta a gidanmu so banda wannan alaqar banga wata ba amma ban san dalilinki na tambayata ba

hmm ai dole in tamvaya ganin yadda kayi mata dazu a gidan naseer kuma gashi yanzu ta dawo nan amm.......shiiiiiii ya fada tare da dora yatsan shi a saman lips dinta haba baby ya kk son maidani baya ne me kk tunani namijin dake da mace kamarki shine zai iya hango wata to kisani wlh inda ana ciro zuciya to dana ciro mikitawa kinga yadda nake sonki nake ji dake ke wlh ni ko wacce mace kallon 'yan daudu nake musu kuma ma in zaki hadani da wata ina laifin ma ki hadani da ta kwarai saiki hadani da hambirin hayam wlh kin cuce ni kin san yadda na tsani yarinyar ma kuwa wlh sbd daddy yasa nake raga mata kuma bana son raini shiyasa kika ga ban. fiya shiga shirgin kowa ba sai naki ke kadai keda habeeb kisawa ranki ko'a lahira bazan miki kishiya ba bare gidan duniya da sai naga wadda taimin zan aura dai ko ? to duk ba wadda tayimin sai fadimatuz zahra'u sajida,batula,Aliya,kamila,sharifa,zakiyya.....zai ci gaba ta katse shi ta hanyar mannewa da jikinshi tare da aika masa da rikitattun sakonnin da suka sa ya kasa qarasa wa ya shiga maida martani ita ko ta dage wajen ganin ta biyashi tukwicin kalamansa masu tsadar gaske a wajenta nan suka lula duniyar masoya

Asuba ta gari

*******

ana kiran sallar asuba a kunnen dije koda ta farka tayi sallah ta yi addu'ointa kamar yadda ta saba kafin daga baya ta miqe ta afka kitchen break fast me rai da motsi ta hada sannan ta jera saman dinning kafin ta koma daki wanka tayi tare da shiryawa cikin unifoam dinta sannan ta fito saman dinning ta nufa ta fara karyawa amma bataji alamar mutan gidan sun shirya fitowa ba gashi har kusan 7:15 sai da ta gama karyawa tsaf kafin ta miqe ta nufi dakin dataga sun shiga jiya

kwankwasawa ta shiga yi

ya akayi ne waye ?

taji muryar sajida na fadi

au to bakuwar gidan ce naga shuru ne me gidan be fito masallaci ba shine nace bara in sanar muku ana shirin tada sallah ya gaggauta koya samu jam'i don kin san sallah in rana ta fito ba kyau gara a yita da duhun asuba

bude qofar sajida tayi tare da kallon dije jin abinda ta fada mata wato dai so takeyi tace basa tashin asuba kenan shine ta fada a fakai ce ganin ta cikin shirin makaranta yasata fadin to tasalla munji mun tashi ai a bari mu gama kimtsawa sai mu fito ko?

ah ah in dan ta dije anty ku koma bacci nidai kiramin me gidan a sallameni in tafi naga zan makara

gyaran murya yayi daga bayan sajida shirye yake tsaf cikin kayan suit ash colour sunyi masa kyau matuqa cikin hade rai yace lfy nake jin hayaniya

lfy qalau yaya dama zuwa nsyi ince na shirya zan tafi school

toh a dawo lfy

to wa zai kaini?

au dama baki taho da me kaiki din ba yayi maganar yana me fitowa a dakin sajida ta biyo shi suka nufi waje inda suka bar dije tsaye da sakin baki

ganin da gaske fita zasuyi gashi dai bataga ya karya ba oh yanzu nagane ta fada a zuciyarta wato sbd ni aka ki yin abin kari a gidan nan hhhhh tayi dariya kadan ashe kuwa akwai kura dan wlh ko da bala'i sai naci na qoshi tana ta sambatun ta har suka fice bata sani ba saida taji alamar rufe kofar kafin ta juya a hankali tabi bayansu

.direct gurin motar sa ya nufa yana zuwa ya bude mazauninsa ya shiga inda yabar murfin bude sajida ta tsaya riqe da murfin suna maganar su ta masoya

tana fitowa ko ta kansu bata bi ba ta nufi part din nasir ta shiga kwankwasawa

nasir da suke tsaye suma suna bankwaba da juna yaji ana buga kofa yayi saurin sakin yusra ya nufi kofar yana fadin sai mun dawo dan yana kyautata zaton habeeb ne dan ya fada masa in zai wuce asibiti zai wuce dashi dan yanason yaga likitan fata dan yadda kura ta yayyageshi🀣a cewarsa

yana bude kofa sukayi ido biyu da dije

.besan lokacin daya furta

la'ilahailla anta subahanaka inni kuntu minazzalimin

lfy me ya kawoki da sassafen nan ?

ganin yadda yayi yasa dije kusan sakin fitsari dan dariyar data guntse

yusra da tana dab da shiga daki taji yayi wannan addu'a yasata dawowa dan taga meya gani aikuwa itama na ganin dije tace ya salam meye kuma kika manta ai da kin fadawa mamy ta kira waya ai sai a aika miki shi

ai badaga gida nake ba anan na kwana

cikin hada baki sua ce a ina din?

a gidan y habeeb

sauke ajiyar zuciya sukayi kusan a tare kafin nasir yace

Alhmdllh qanwarmu sarkin hankali ai gara da kk kwana a can ni yanzu ma kinga abuja zamu tafi ni da yusra dan haka basai kin zo mana sallama ba in zaki tafi ki gaisheda su mamy tsarabar ki insha Allah daban take in mun dawo yana fadar haka ya juya ya koma suka kullo kofa harda sa key

dariya dije tasa kafin ta gaji ta mike ta nufo inda su habeeb suke wadanda duk abinda ke faruwa suna kallo sai dai basu san me suke fada ba sun dai ga komawar nasir da dariyar da dije tayi

tana qarasowa bata ce qala ba ta bude murfin baya ta shige ta qame ta kalli window

cike da mamaki a fuskar kowannensu sajida ta bude baki zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar daga hannu kafin cikin hade rai ya juya yace

ke dan ubanki bakida hankali ne meye na shiga motar mutane uban waye drivern ki?

cikin marairaice fuska tace kayi haquri yaya wlh dama tsayuwar da mukayi da yaya nasir ne yace in fada maka wai daddy yace ka ajiyeni a school daga can zan wuce gida ma nafasa zaman

jin ta ambaci tafiya yasa sajida saurin fadin ai kawai ba komai sweety ka ajiyeta din inaga shi nasir din yafasa fitar tunda kaga ya koma watakil dan yaga za'a fita da jerry dinsa ce

jin sarauniya tayi magana yasashi fadin ok kawai

sallama sukayi inda ya fita daga gidan be ko bi takan naseer ba

kasancewar yasan school din tasu direct can ya nufa da ita yana tsayawa ta bude ta fita tare da fadin saina dawo yaya

.ki dawo ina?

gidan ka mana ai ni naga wuri .........

*Alqalamin khady*✍
[3/14, 9:34 PM] El~hajj: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

*TA ME GARI*

NA
khadeeja usman

1⃣8⃣

*ina matuqar godiya da addu'arku gareni Alhmdllh nasami sauki tare da kuzari da karsashin ci gaba da suburbudo da sambado tare da sheko muku ta me gari uwar mazga hakika kuna dadamin qwarin gwiwa ta yadda nake jin zan iya yini zungur ina muku typing amma sbd halin yanayi zan bawa kaina haquri inyi muku na 'dan lokaci zakufi jin dadin saπŸ˜‚*

tana gama fadar haka ta juya ta shige makaranta ta barshi da sakin baki inda ya shiga fadi a fili wlh bazan yadda ki zauna min a gida ba bari kawai in kira daddy ince masa ki koma can kuma sai yace kai nasan halin yarinyar nan yanzu haka bazata koma bs kawai fadamin tayi dan inyi haushi sbd ta mayar dani kare hmm zanyi maganinta haka yayita tuki yana sambatu da masifar ba gaira ba dalili har ya isa asibitinsu yana zuwa ba jimawa ya fara aiki

itako dije tana shiga cikin makaranta direct office din principal ta wuce ta sanar dashi daga yanzu a dinga biyawa daukarta da motar makaranta ta fada musu inda ta koma dayake dama a cikin bill din makarantar harda kudin transport suke hadawa sai dai in ka so kasa a kawo danka amma su ba ruwansu shi yasa koda dije ta fada ba'a samu matsala ba

tana fitowa ta nufi class nan suka hade dasu rufaida aka shiga hira kafin malami ya shigo suka fara lesson

****

Amarya kenan kin ganki kuwa yadda kika canza kinyi wani kyau dake kamar wata black american

dariya sajida tayi kafin tace ke laila wlh banda sharri

wlh ba maganar sharri fadamin meye sirrin ne me habeeb ke baki

kulawa da soyayya ta fada tare da yin fari da ido

shegiya qawata kodai to har an sama mana baby ne

baby fa kika ce tun yanzu ?ai sai mun shekara kafin inyi ciki ke yadda habeeb yake dan son rayuwa yanzu in nayi ciki ai sai a hankali shima kanshi yafi son mu huta ai

tafawa sukayi tare da fadin kusha sha'aninku bird loves naso inga habeeb ranar aurenku inga bakin nan sai gashi ina malesia na tsinkayi lbrn bikin gashi ba halin in dawo sbd wani uzuri

.hakane kam Allah be nufa dake za'ayi ba yanzu gashi kinzo har gida ai bari in tashi in sama miki abinci ko me kike so ta tambayeta tana qoqarin miqewa

komai ma kin san ni banida zabi

ok ta fada tare da kokarin miqewa ta shiga kitchen

da sallamarta ta shiga falon inda ta iske laila hakimce da remote tana canza tasha batare data juyo ba ta amsa sallamar har saida ta ji dije nayi mata ina yini kafin ta maido da dubanta gun

wani kallo tabi dije dashi ta amsa gaisuwar a yatsine ko ba'a fada mata ba tasan wannan qanwar habeeb ce domin kuwa tana kallonta ta hango kamar su sai dai kawai ta fi shi haske dan ita fara ce sosai hmm tab di lallai akwai aiki wato har an fara kawo 'yan leken asiri lallai sajida batada hankali ita ina zata yadda da a kawo mata wata dangin miji ai ko kawowa za'ayi gara a ce ta dauko a danginta balle wannan yarinyar da gani idonta feke yake

tund dije ta lura da kallon da matar ke binta dashi taga kuma ta lula duniyar tunani kawai saita qarawa wutar ta mai tayi shigewarta dakin data kwana jiya

laila na tsaka da tunani sajida ta fito hannunta dauke da jallop din makaroni daya sha kayan vegetables da busashshen kifi sai kamshi yakeyi

qarasowa tayi kusa da ita taja mata dan qaramin center table din dake gefen kujera ta ajiye mata abincin tare da komawa ta qaro mata ruwa da lemo ta na ajiyewa ta zauna ita kuma laila ta sauke gwouron numfashi tare da fara cin abincin

saida ta gama tsab kafin ta kalli sajida tace

qawata wani abu nagani a gidanki daya dagamin hankali

.cikin razana sajida tace me kk gani ?

wata yarinya nagani yanzu ta dawo da alama kanwar mijinki ce naga daga makaranta ta dawo sajida ina tunaninki ina iliminki da wayewarki suka tafi tun yaushe aka daina yayin 'yar zaman daki wannan budurwar yarinyar ai kawota kawai akayi ta hanaku sakewa inba haka ba su dai ba ci suka rasa ba ba sha ba bare ace sun takura ne suka kawota nan dan haka wlh kisan abinyi ke banda ma uwarsu daya ubansu daya ai da sai ince ko kawota ma akayi ta gama gane miki sirri karshe ta aure miki miji

rasssss gaban sajida ya fadi tare da nazarin maganar laila

ganin yadda duk yanayinta ya fara canzawa yasa laila qara dogon sharhi aikuwa nan sajida ta fada mata tsakanin habeeb da dije da dangantakarsu ai kuwa nan laila ta dinga kwarara wa sajida ruwan zuga tare da fadi mata illar zama da dangin miji dan mijinki na babba sai a kawota nan a kaita gidan naseer mana nan sajida ta fada mata yadda suka kwashe dasu naseer

tab iskancin banza ajanun banza aljanun wofi mu za'a gwadawa aljani ni danayi gadonsu dari ba daya ne akan kakata data mutu suka dawo kaina dan dama tun tanada rai munfi da ita shiyasa koda ta mutu suka ce ni suke so wlh duk qaryar rashin mutunci takeyi yarinya qarama da kicifi tun yanzu

ganin yadda laila ta dage tanata zazzaga masifa ne yasa sajida fara lallaminta domin da alama akwai aljanun fa a nan dan yadda ta fara daga murya

itako dije tunda ta shiga daki tayi wanka ta canza kaya ta nufo falon domin nemawa kanta da'amin inji ta saita tsinkayi maganar da laila keyi saida ta gama ji tsab har takai lokacin da sajida ke rarrashinta babu wanda ya lura da fitowarta direct kitchen ta nufa tana shiga ta shiga gyara duk wani abu da sajida ta bata tare da dora nata girkin kasancewar kitchen din rufe yake hakan yasa basuji kamshin girkin ba bare kuma girkin na mugaye ne dama dirka dirkan kulolin data gani ta dauka ta juye a ciki shinkafa ce fara sai miya datayi leqowa tayi falon inda ta gansu laila har yanzu tanata ma sajida famfo qara lababawa tayi ta dauko abincin cikin sanda ta ajiye saman dinning din kafin ta koma kitchen din ta gyara sji fes kamar ba'ayi amfani dashi ba

kafin ta kuma lababawowa ta shige dakinta tare da mayar da unifaom dinta sannan ta fito da rarrafe ta zagaya bayan kujera ta labe

jin kamar qofa tayi motsi yasa su saurin waigawa sajida da zuciyarta ke kusa dan sai ysnzu ma ta tuna da yarinyar cewa tayi gida zata tafi to uban me ya dawo da ita bari ta tashi taci uwarta kawai inya so ta kadata ta koma gidan su nasir suje can su qaraci gayyar rashin hankalinsu can inma kashe su aljanun zasuyi su kashe su sai me nan ta miqe laila ta dafa mata baya suka nufi dakin suna zuwa suka tura qofar ga. mamakinsu bakowa toilet sajida ta nufa ta shiga fadin ke khadija !! khadija!!

jin shuru yasata tura qofar ta leqa bakowa cike da mamaki ta juyo ta dubi laila tace kika cemun ta dawo kuma?

ban gane nace miki ta dawo ba to karya zanyi miki ko me?

ta fada cikin hade rai

to kuma gashi bata nan duk da nasan munyi magana da habeen da safe cewa gida zata wuce

toh nidai naga yarinya ta shigo kuma da unifaom fara ce siririya ko

tabbas itace amma ai muna falon ko dai kafin in fito ta fice baki lura ba

wlh ba wani fita datayi dan tana shigowa kina fitowa sai dai in wani salon

10 / 33