Tame Gari 1 Complete Hausa Novel

Author :  Asma Baffa Category :  Romance

Chapter   15 / 33

42K to 45K   out of 96.3K words

dan kar aje ko ya boye abinda ya siyo a mota saita yi bacci ya dauko

iya kyautatawa yusuf nayi mata duk wani jin dadi ya dauke mata shi amma sam bata gani taki barinshi ya sarara

su biyu ne yaranta daga shi sai qanwarsa farida wadda yanzu haka tana aure a kd ne bata fiya zuwa ba sbd batajin dadin yadda mahaifiyarsu keyi gashi amina nada kirki sosai

to ku haka ake bakuwa kusata ta zauna qasa ta fada tana me karasawa inda dije take zaune

tashi kinji ai daga ganinki ke jinin arxiki ce kin saba da hutu ji fatarki ina ke ina zama a kasa tashi ki zauna kinji duk inda yayi miki ki zauna ki mike kafa ai tunda jinin su habibu ce ke bakida matsala dan yaran kirki ne sun san mutunci

ita dai dije ta kasa magana haka hajiya ta dinga tantadinta harta gaji aka kira sallar magrib kowa ya kama gabansa Amina ta kai dije dakin da zata zauna

bayan tayi sallah ne tana zaune kan dadduma Amina ta shigo dakin da sallamarta dauke da faranti a hannunta

amsawa tayi tare da qara gaisheta ta amsa cike da fara'a kafin ta ajiye ta nemi guri ta zauna tace ya bakunta

.sunkuyar da kai dije tayi kafin tace Alhmdllh nan da can ai duk dayane

to Allah yasa haka kika dauka harga zuciyarki

wlh dagaske nake Aunty

ina yaran ne?

kin san suyi jaganiya yauban gaji ina musu wanka har sunyi bacci

toh da wuri haka ?

wlh kuwa ga abinci nan kici sai dai kiyi haquri da abinda kk gani ban sani ba ko baki saba da cin irinshi ba kiyi haquri tun safe kafin mu fita hajiya tasa aka dafa amma dayake kin zo da kafar dama nasan gobe za'a canza insha Allah

yauwa Aunty dama abinda ya dan dameni nake tunanisa yanzu kenan

meyasa kika zauna tana ci miki mutunci haka duk da ban sanki ba ban san halinki ba amma na yaba miki Allah inda nice ko hmmm da tuni an wuce gurin

kallonta Amina tayi tare da yin 'dan murmushi kafin tace kuruciya kenan ai ko kece khadija ba abinda zakiyi illah hakuri ko dan albarkacin kina auren danta sannan ko ba komai nasan wata rana sai labari tayi duk yadda take so nasan wata rana in ance tayimin ba bazatayi ba

tabdijam wlh Aunty baki sani ba ne irin wadannan tsoffin zeyi wuya subar mutum ya sarara gasu da shegen tsawon rai yanzu wannan saita iya qara hamsin ko ma fiye nan gaba

dariya Amina tayi tace kai khadija to ya za'a gansu kuwa lokacin

ai qanqancewa sukeyi kiga sunata komawa kamar masu cutar tamowa qarshe sai dai kiga ana sasu a baro in kuma sunada gata ne zakiga ana turasu a keken nan na jarirai da suke koyon zama

kai khadijaπŸ˜‚

Allah kuwa Aunty halan baki taba gani ba?

ah ah Allah bai taba gwadamin ba

to kuwa kiyi addu'a sosai dan ga alama nan a gidanki

dariya Amina tayi tana qoqarin mikewa tace ni dai ci abincin kafin in dawo musha hira

to tana dai bari ayi hirar ko?

ai na fada miki ke da sa'a kika zo gidan tunda har fada tayi wai laifinmu ne da bamu kirata munce zamu taho dake ba gashi yanzu munja mikk cin tazarce dan haka kada ki damu ke din da hajiya kun jone

murmushi dije tayi a ranta tana kissima yadda zata saita hajiya

Amina na fita dije ta jawo farantin gabanta din ta bude

wake da shinkafa ne mai da yaji ai kuwa dije dadi taji maimakon taji haushi dan ta dade marabinta da ci a ranta tace inba ma dai abin da izgili ba ai wake da shinkafa abin marmari ne dan dai kawai anyi hakan ne da mugunta

sai da taci ta koshi sannan tayi sallar isha'i tana tsaka da sallar taji an turo kofar dakin

au to ana nan ana gaida ubangiji kenan to Allah ya amsa ta nemi guri tazauna

saida dije ta gama addu'ointa kafin ta juyo tayi mamaki ganin hajiya zaune amma saita maze ta shiga gaisheta

cike da fara'a ta shiga amsawa kafin daga baya ta fara zubawa dije surutu ganin da dije tayi tasamu abokiyar yi yau yasata cire hijabin datayi sallah ta gyara zama

kallonta hajiya tayi kafin tace Allah me halitta kenan

yanzu ke wannan farin nske baya damunki ji beki fa waima da dare kenan ina ga rana

au dama fari yana damun mutum sai kace na Allah ya isa

eh mana kin ganki kuwa nifa inba idona ne yakemin gizo bahar wani yellow yellow naga kinayi ko ma dai harda shawara farin nan naki

ah ah ba shawara bace ai da kin lura da kyau da zakiga kwayayen lantarkin da aka jona min suna kawo wuta😠

rike baki tayi tare da nuna al'ajabi tace wuta kuma a jikin mutum yarinya?

eh mana ai zamani ne yazo da hakan ke kanki nasan da'a zamaninku akwai wannan fasahar to wlh da ke za'a fara gwadawa a kanki

ah ah wallahi daina jamin jafa'i tunda Allah ya tseratar dani oh ni hauwa'u yanzu har takai ga bature yayo wayar da za'a jona jikin mutum to meye amfaninta

ga amfaninta nan kin gani irinku masu gani suki kyalewa yake haskawa hanya yanzu ba gashi har kinga yadda fatata take haske ba

uhmmm lallai lamarin babba ne ta fada tana me rike haba

itako dije kuluwa tayi cewar da tayi farinta da kuma shawara ke damunta shiyasa ta matsu ta tashi ta tafi ganin taki tafiya saima qara malkwado wani zancen takeyi yasa dije miqewa ta shiga toilet batare datace da ita ko kala ba

wanka tayo ta fito daure da towel a jikinta

aikuwa caraf sai ji tayi tace oh ni 'yasu ke ko wannan yarinyar kina cin abinci kuwa ? ji kashin wuya kamar a zuba tiyar hatsi

ai in kinji ci daya ma kenan ni ko ke cin abinci wannan kashin wuyan nawa da kika gani wani sirri ne bari ma in fada miki daya a ciki ko wanka da kikaga nayi yanzu bada sabulu nayi ba dan ni sabulu na najikina

😳 jikinki kamar ya?

ai sbd ramar tawa da tayi yawa wata rana ina wanka lokacin an siyo mana wani sabulun wanka girmansa yakai kwanan sha to shine fa ina cikin wanka dashi na nemeshi na rasa nayita nema ban gani ba hae na haqura nace bari nayi da ruwa kawai ina zuba ruwan naga kumfa na tashi shine fa na fara lalube koda na duba sai naga ashe lokacin da nake murzawa ya subuce ya fada cikin kashin wutan nan nawa da kika magantu akan shi to da nayi niyyar in dauko shi kawai sai nace bari in barshi na huta idan na tashi yin wanka ba saina sha wahalar murza sabulu ba

qarya kikeyi dan uwarki 🀣🀣🀣

taji hajiya ta fada

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

*managed pls*

*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 6:31 PM] El~hajj: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

*TA ME GARI*

NA
khadija usman

2⃣6⃣

*ina jinjina gareku khadija fans novels 1,2,da kuma 3 tare da tame gari fans da kuma hausa novel 1,2,3 da zama na amana 2 Facebook gaskiya na yaba sosai da comments dinku ina kuma godiya da addu'arku gareni kamar yadda kukemin kuma Allah ya biya muku bukatunku*

*bazan manta daku ba kuna raina kuma ina ganin comments dinku gaskiya ina godiya Allah yabar kauna*

*jattako novels fns*
*sadnaf novels fns*
*zauren mai dambu group*
*Hikayar marubuta*
*online writters groups*
*Arewa novels fans*
*da duk wadanda ban fade su ba suna raina wlh ina kuma mugu mugun ji da ku*

ah abin harda zagi kuma hajiya babba

ai dole in zage ki ke yanzu inba kin rainan wayo ba ta yaya zaki cemin wai sabulu ya bace a jikinki ko da dan mitsili ne bare kuma girman kwanon sha anya ma kuwa kinsan kwanon sha kuwa?

a haifeni a kauye kice ban san kwanon sha ba hajiya ni ko na sanshi kawai ki yadda da maganar da na fada miki

na rantse da Allah bazan yadda ba dan ko'a tarihi ban taba jin makamancin abinda kk fadamin ba sai kace sabulun aljanu

*yauwa anzo wurin dije ta fada a zuciyarta*

au to wai da ke kin dauka sabulun na mutane ne?

to amma ai ke kikace wanda ake siyo muku na kuwa san babanki ne ke siyowa ko kuma ai mutum ne shi ko kuwa kina son kicemin yasan dandalin aljanu acan ya siyo muku

to da nace miki ana siyo mana ai bakiji nace miki ga wanda ya siyo ba ko?

eh kuma fa hakane amma ke inba karyar jaraba ba a ina kikaga aljanun da har zasu siya miki sabulu

murmushi dije tayi kafin ta nufi kofa ta murza mata key ta dawo ta rufo toilet ma sannan ta fara leqe leqe kamar munafuka

hajiya ta bita da kallo kafin tace ke wai uwar me kk leqawa haka sai zagaya ni kk yi kamar kin kama akuyar mayu

shiiiiii dije ta dora hannunta a saman bakinta ina zuwa kedai

saida ta gama 'yan dube dubenta kafin ta kalli hajiya tace wani sirri zan fada miki bana son kowa yaji shiyasa

sirri kuma?

wane irin sirri duk ke 'yar nan duk duniya ki rasa abokin da zakiyi sirri dashi sai ni anya ba yankani kike shirin yi ba kuwa dan ni wlh inda abinda nake tsoro yanzu bai wuce mutuwa ba in kin san abinda zaki aikata min kenan gara ki sanar dani dan manzo

kai hajiya wlh kin fiya tsoro to dama maganar da kk takalo ce ta Aljanu kin ganni nan to inada su sunkai miliyan daya a kaina

innalillahi wa'innailaihir raji'un miliyan daya fa kika ce ?to ni dai ko a mazahabar jama'u ban taba jin kan mutum ya dau Aljani fiye da dari ba daya ba shima cikon na darin danna mutuwa ne shiyasa amma ke kice har miliyan daya sai dai in kece aljanar da kanta

to Alhmdllh tunda kin fahimta shikenan

na fahimci me ?ba dai da gaske ke din aljanar bace?

eh ah'ah

rabi mutum rabi aljan nake

😳ke 'yar nan fadamin gaskiya in san abinyi tun wuri

ai gaskiyar kenan abinda yasa ma kikaga na tsaya haka sbd naga yadda kika karbeni ni shiyasa ni bana cutarwa da kike ganina ina rayuwata ne cikin bil'adama amma ina azabtar da duk wanda yake kuntatawa jama'a su kuwa masu shiga tsakanin masoya ko ma'aurata kashe su nakeyi gaba daya masu gani ba kyalewa kuwa kamar masu tanka halittata su kam bakin nake murgudewa in tsiyayar da idanunsu ta yadda bazasu moru ba sannan in.........

wayooo na shiga uku hajiya ta fada da karfi

yusuf da Amina da tun dazu suka zo da niyyar susha hira da dije suna dab da shiga suka tsinkayi hirar hajiya da dije akan sabulu suka tsaya suji yadda zata kaya ai tunda sukaji dije tacewa hajiya ita aljana mutum.ce yusuf ya tuna da yadda naseer ya basu labari dije tayi musu aikuwa nan ya kama dariya Amina ta kalleshi kasa kasa take tambayarsa

janta falo yayi ya fara bata labari kafin yace nasan ta fuskanci halin da muke ciki shiyasa ta bullo mata ta wannan hanyar

marairaice fuska Amina tayi kamar zatayi kuka tace haba Abban Anwar baka tunanin hakan ya cutar da ita kaga fa tsohuwa ce in jininta ya hau fa?

hakanma bazai faru ba nidai kawai fatana Allah yasa wannan yarinyar ta zama silar shiryuwar hajiya ta barmu mu zauna lfy kinga ni tashi mu zaga ta bayan window musha kallo kinji my choice

jiki ba kwari ta mike ya kalleta yace haba mana ki saki jikinki pls kin san dai hajiya mahaifiyata ce bazan so abinda zai cutar da ita ba ko nasan halin yarinyar a sai dai ta firgitata kamar yadda ta firgita wadancan kartin tunawa tayi da labarin daya bata aikuwa ta kama dariya suna tsaka da haka suka jiyo ihun hajiya da gudu suka fita suka zaga ta window suka danyi slide dinsa kadan suka kama kallo

ni fa ki daina min ihu me nayi miki ?

kinga dan Allah yake muminar aljana kiyi haquri daga ganinki hwlh anga me afuwa wlh ban aikata ba duk abinda kika ga inayi ciwon sanyi ne yake tabani badan ma kar ince ki tambayi yusuf ba nasan bai sani ba da nace ki tambayeshi to tun ina budurwa na hadu da matsalar sanyin kwakwalwa inya bugani sai inta abu irin na marasa hankali ni dama tunda na ganki nasanke ba mutum bace amma da naga kuna yanayi da su habibu saina yadda ashe ke mutum aljan ce nasan suma basu sani ba amma ina rokonki da kada ki kasheni inada marayu kinga ni ke kula dasu gashi......

to wai laifin me kikayine da zan kashe ki?

nasan nayi kuma kema nasan kin sani kawai kina son kiyimin kisan rashin imani ne bayan kin murgudemin baki kin tsiyayarmin da idanu ki tausayamin ki duba tsufacda furfurata ki duba qananun yarana

au har yanzu kina haihuwa dama?

ah ah yusufa da farida mana in an hada da irin shekarunki ai kinga su jarirai ne ko?

hakane ina zuwa

kaya ta ciro tasa dan sanyi takeji kafin ta dawo ta zauna akan bedside drower ta dora data kan daya

kafin tace hajiya

cike da rawar baki ta amsa ya zuwa yanzu tayi zaman dirshan bisa tiles

na'am ranki ya dade me haskrn sallah dan naga ke din musulma ce ko a cikin aljanun kinada imani bakya wasa da ibada

duk naji yanzu dai ki fadamin dalilinki na hana yaranki sakewa da iyalansa kika zo kika takura musu kika......

kinga duk basai kin fada ba nasan kin sansu wlh sharrin ciwon sanhi ne kamar yadda na fada miki amma ina nan ina neman magani

oh kenan shi kesa kike aikata abinda kikeyi ?

sosaima kuwa ni tsorona ma kada yasa in aikata kisan kai gara in nemi magani tunda wuri

ai indai magani ne kin gama samu dan ni har maganin dayafi nashi ma ina bayarwa

cikin hajiya ne yace quuuuuuu cikin sauri ta yamutsa fuska tace ah ah bama sai kin bayar ba dayake na karbi wani ina kan aiki dashi yau ma wa'adin zai cika nasan gobe na warke

to shikenan naji amma yanzu dole ki karbi hukuncinki na yin katsalan dan da tanka halittar Allah da kuma shiga shirgin daba naki ba

haba yallabiya kiyi haquri sharrin shaidan ne da kuma....

ganin da dije tayi duk hajiya ta hada zufa duk da sanyin A.C dake dakin ga kuma fanka saita bata tausayi dan haka ta rage abinda tayi niyyar yimata sbd gudun kada taje jinin tsohuwa ya hau ta shiga uku garin gyara ayi barna

shikenannaji tunda kin bada haquri kuma kin smu maganin cutar dake damunki ba matsala zan kyaleki amma daga yau kullum da dare zan dinga kwana gidan nan sannan da rana zan ding zuwa zagaye batare da kowa yasani ba inga halin da ake ciki idan naga baki warke ba sai in dora da nawa maganin

wlh nama sn zan warke

sannan kada ki sake inji in fadawa kowa ni ba cikakkiyar mutum bace dan ba wanda yasani

wace ni ai ni banida wannan subutar bakin nifa banda yanzu magana ma bata dameni ba ta fada tana me marairaice fuska

sai da dije ta dan yi murmushi ganin yadda ta danyin

ita ko hajiya da qarfinta ta yunkura tace Allah ya baku haquri ni zan tafi dan wlh bacci nakeji

kije ina ai ke tare zamu kwana dake da waya kawoki?

wlh dama zuwa nayi in shiga bandaki tsautsayi ya ritsa dani

oh dama anan kike shiga toilet din dakinki babu ne ko
me?

kaddara wlh kaddarar haduwa da ke tkawoni

ko kafin dije ta bata amsa har takai bakin kofa dije na shirin yin magana taga tsohuwa ta bude kofa ta sheqa da gudu ba ko waiwaye

aikuwa nan ta fada saman gado ta dinga dariya su yusuf ma dariyar suka shiga yi suka zagayo koda suka shigo dakin dije nata dariya saida yusuf yace sannu da gama rikitamin uwa

bata daina driyar ba gnin hakan yasa amina tace kaga mu gudu fa kar a ritsa damu ko na gasken sunzo

nan suka juta suka fita har sun wuce yusuf ya nufi dakin hajiya yana zuwa ya tura yatji shi bame gam ya kwankwasa amma shiru kk ji dariya yayi a fili yace Allah yasa ki gyara Ameen

*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 6:32 PM] El~hajj: πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€πŸŒ€

TA ME GARI

NA
khadeeja usman

2⃣7⃣

up
up
up
irin wannan cigiya haka masoya tame gari lallai dije tasha jaje to an nemota da kyar tace a gaisheda masoyanta dan haka ina muku fatan alkhairi tare da jinjina da miqa godiyata gareku masoya ta me gari masu yimin magana ban samun amsa musu da wuri suyimin uzuri ba lallai dan an gani online ya zamana ina kan whatsapp bane ta yiyu wani uzurin nakeyi amma naji wasu masu abar a kusa sun fadamin magana amma banji haushi ba nasan so ne ya kawo hakan amma kuyi haquri

jin da hajiya tayi ana buga kofar yasata saurin shigewa toilet ta rufo har saida taji bugun ya lafa ta jima a cikin toilet din jin da tayi an daina bugun yasata dan bude qofar ta ziro kai kasancewar a tsorace take sai taji kamar muryar dije na fadin ku bita bandakin ku kamota ai kuwa da sauri ta fito ta fara qoqarin shiga cikin wardrope din amma kasancewar ba irin wadda mutum zai iya shiga bace abu ya gagara ganin hakan yasa ta tura kanta kasan gado tare da jan ciki harta shige duk wani motsi da zatayi gani takeyi dije na kallonta yayin data dinga karanto duk wata aya data sani kai harda hadisai gashi ba damar tayi juyi haka ta kwana a gurin batare da tayi baccin kirki ba har aka kira sallar asuba a kunnenta kafin ta zamo ta fito ta shiga toilet da kyar tayo alwala aikuwa tunda tahau sallaya taketa jera salloli tare da addu'ar Allah ya kareta daga sharrin jinni🀣

ita ko dije saida tayi me isarta kafin ta miqe ta dauro alwala ta haye gado ta kwanta cikin zuciyarta tace oh ni dije ina karya da aljanu ina cin uban mutane Allah yasa

15 / 33