Tame Gari 1 Complete Hausa Novel

Author :  Asma Baffa Category :  Romance

Chapter   19 / 33

54K to 57K   out of 96.3K words

makaranta ana jiran result sam taki yadda su hadu da mamy abinda dije bata sani ba ko mamy na lura da ita tanata saka da warwarar yadda zata bullo mata ne ta kadata kauye kowa ya huta cikin hikima batare da daddy ya gane ba

****

bikin rufaida ake shirin yi duk da kasancewar mahaifinta dan boko amma baya bawa 'ya'yansa mata damar karatun gaba da secondry har sai kinyi aure hakan yasa rufaida ta fidda miji ansa rana suna son junansu su dije ne kirjin biki anata rawar kafa da shirye shiryen abubuwan da zasuyi tare da kayan da zasu saka dan haka take jiran daddy ya dawo ya bata kudi

yau friday daddy ya shigo gari sai bayan isha'i yana zaune a falo yana kallon news mamy na zaune tana masa hira jefi jefi dije tayi sallama ta iso falon

da fara'a daddy ya amsa tare da fadin ah ah lovely daughter kina lfy?

saida ta zauna daga gefen kafafun sa kafin ta fara gaisheshi ya amsa tare da yi mata murna da kuma tambayarta ya yaga ta dawo gida ko ta gaji da zaman gidan yayan nata ne

murmushi tayi batare data bashi amsa ba ta sadda kai kasa mamy da idonta kamar zai fado sbd hararar datake aika mata amma dije tayi kamar bata bata gani

tambayoyi daddy ya shiga yi mata akan zamanta a gidan yayanta inda dije ta karkace ta dinga antayi mala malan karya harda mai fuka fukai akan wai yadda suke kula da ita daddy nata fara'a da jin dadi a ranshi dan yana son 'yan uwanshi sosai amma hajiya karima sam bata maraba da duk wanda ya fito daga tsatson Alhajin daga kauye a baya tasami nasara da dama wajwn biye biyen malamai amma yanzu tarasa dalili ko tayi aikin baiyi yadda take so

sun jima suna hira dije nason sanar dashi tana bukatar kudi amma tanajin nauyi dan haka take ta nuku nuku

yana lura da ita dan haka yace daughter ko kina bukatar wani abun ne?

sadda kai ta karayi tace am dama bikin rufaida za'ayi saura sati biyu shine zamuyi shirye shirye

to ba matsala gobe sai a baki kije ki sayi abinda kk bukata ko?

muryar mamy sukaji tana fadin ah kice munada shagali ai kada ka damu Alhaji basaika bata komai ba wannan aikin ai nawa ne dole in hada 'yata tafi ta kowa akwai wasu kaya da hajiya ma'u ta kawo sai a kaita ta zaba sauran abubuwan kuma na bata kudi ta siya ko

cike da jin dadin maganarta daddy yace to ni an hutar dani ma kenan amma na bada wani abun a rage ai

ai Alhaji basaika bada komai ba ni duk zanyi komai dan yarinyar nada kirki sosai

dije da tunda mamy tayi magana ta dago ta kalleta ta fahimci abinda take shirin aikata mata amma ba damar tayi magana haka jiki ba kwari ta mike tayi musu saida safe yayin da mamy ta bita da kallon sai kin raina kanki

******

shuru shuru har daddy ya gama abinda zaiyi ya tafi dije bata ji an qara mata maganar kudi ba sai bayan ya tafi mamy ta kirata ta shiga zaginta tare da sanar da ita indai tana raye to baxata kara bari taci kudin daddy ba sannan in tana son kanta da arziki ta tattara kayanta ta koma kauye

bakaramin damuwa dije ta shiga ba jin muguntar da mamy ta shirya mata yanzu ina mafita?

ba yadda za'ayi dai ta sanar da rufaida dan tana mata kokari akan komai yanzu kuma bikinta za'ayi yakamata ta taka rawar gani to yanzu yazatayi kenan ?

tunani ta shiga yi kafin daga baya tasami mafita tsalle ta buga tare da fadin yessss sai ni dijen.mai gari nawa

baseera dake zaune tana linke kayanta ta dago ta kalleta tace yadai lafiyarki kuwa ?ko sunzo ne in san nayi?

dariya dije tayi kafin tace kedai bari kawai wata tsiya zan tsula wlh a gidan nan

sakin baki baseera tayi kafin tace ke khadija tsiyar me kuma?dan Allah kada tarihi ya maimaita kansa ki hada harda ni

dariya dije tayi kafin tace wallahi ni har kin tunamin ma dan sam na manta da wannan lokacin dan a cikin shika shikan ta'addancin danayi bana sa wannan a ciki saboda kankantar sa

yanzu ke khadija wannan ne karami to shi babban ya yake kenan?

ki tambayi su yaya habeeb zasu baki labari

zaro ido tayi kafin tace rufamin asiri nidai dan girman Allah ki rufamin asiri kada ki hada dani

ai ke kada ki damu ko inawa kowa wlh banda ke Aunty na mamana badan kin haife ni ba ta karasa maganar tana dariya

haka suka dinga hirarsu cikin nishadi kwanciyar hanksli amma zuciyar dije nacan na saka da warwara

****

dare yayi dan kusan qarfe daya da wani abu ake nema kasancewar zafi akeyi sosai duk da A.c dake kunne da fanka hakan bai hana mamy jin zafi ba a cewarta dan haka ta fito falo ta dan kishingida har bacci mai nauyi ya dauketa

dije da saboda abinda ke ranta baccinma ta kasa yi saboda haka ta fito cikin sanda dan sam bata lura da mamy ba saida taji munshari

Alhmdllh ta fada a ranta inda direct ta nufi dakin mamy kai tsaye ta shiga bincike ko'ina inda tana bude wata hand bag din mamy tayi tozali da kudi rafar 'yan dubu dubu

dariya tayi inda ta dauki dauri biyu tasa kai ta fice tana dariya a ranta tana kissima dramer da za'ayi gobe

*niko nace su dije an fara 'dan hali ne ko kuma me?* 🤔

****

tunda asuba da dije tayi sallah ta fito falo ta zauna tare da tsintsiya a hannunta da mofa dake cikim bucket da ruwa tana nan zaune dataji kamar motsi saita mike da saur ta fara shara a haka har mamy ta fito shirye cikin shiga ta alfarma da alama fita zatayi

tunda dije ta ji motsi ta mike ta fara shara tanayi tana sharar kwallah kamar wadda aka cewa ubanta ya mutu

mamy ce ta kalleta cike da mamaki ganin yadda kwalla wata ke bin wata tace ke kuma uban me yasameki kike shara kina kuka kamar wadda aka sa dole

banza dije tayi da ita taci gaba da yadda takeyi duk da ta dan soma gajiya

ke ba magana nake miki ba ban son iskanci fa wallahi zan ci ubanki kijini da 'yar iskar yarinya

batare da dije ta dago ba ta ce kema zaifi miki kyau ki fara kuka tun yanzu dan ni na kusa gama nawa

cikin rashin fahimtar maganarta tace ban gane ba

kin kusa mutuwa
mamy shiyasa nake kuka

kijini da 'yar buta...........uba ubanki ne ke kashewa da zaki kalleni kice na kusa mutuwa to a ina kika sani

juya baya dije tayi ta ciro hakoran robar data siyo masu kamar na horo na wasan yara tasa wanda tun jiya taso tsorata mamy dashi da dare amma data samu kudin dataje nema kawai saita fasa ta barta ta huta yau sa gamu

to ko ke mayya ce wallahi kinyi kadan kice zan mutu yau kujini da shegiya kin juya min baya kamar allo juyo ki kalleni ki fadamin mana in daki bakinki sai hakoranki sun zube

jiyowa dije tayi sukayi ido hudu da mamy

wata razananniyar kara mamy tasaki yayin data yadda jakarta ta nufi daki amma ina dije ta cimmata ta rike mata kafa

runtse ido mamy tayi ta shiga ihu iya karfinta yayin da dije tayi saurin cire abin dan ta sami damar yin magana tace ki ciremin hokaran mana ko kin fasa?

*zan yi kokari. yi muku posting kullum.yanzu ku kara hakuri typing akwai wahala wallahi*

*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 11:18 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TAME GARI*

NA
khadija usman

3⃣3⃣

innalillahi cewar mamy ta fada da karfinta baseera da taji ihun mamy ta leqo amma ganin dije a tsaye ga mamy ta kure da bango yasa ta fahimci dije ta fara aikinta kamar yadda tace dan haka ta sakada daga gefe tana kallon yadda za'a kwashe

su kuwa su habu driver da me gadi sun jiyo ihu amma basuda tabbacin daga inda ya fito dan haka suka baza kunne dan jin inda zai qara fitowa jin shuru ba'a kuma yi ba yasa suka qara maida hankali ga hirarsu

in banda rawa babu abinda jikin mamy keyi yayin da take ta tuna da mafarkan datake yawan yi akan dije ashe yarinyar dama garken aljanu ne akanta shiyasa ta addabi rayuwar kowa kenan duk irin tsarin datake sha na mayu da aljanu gashi beyi aiki akan wannan yarinyar ba yau abin yazo kanta sam takasa dagowa ta kalli dije

itako dije hakan ne ya qara bata dama ta kara maqe murya ita ala dole jinsin aljanu (niko nace dije ina tausaya miki ranar da dubunki ta cika aka ramfo ki) kince zaki ciremin hakora to ki tashi ki fara aikinki mana dan kin san sai kin nemo katafila wajen babbago shi to kada ki bata shekaru kinayi gara ki fara da wuri zan tausaya miki in rangwanta miki albarkacin kina matsayin uwa ga masoyiyar mu dan haka bari nasa a kawo miki kayan aiki irin namu zasu sauqaqa miki duk da bai zama lallai ki iya daga wasu daga ciki ba amma zan taimaka miki dan cikar burinki

wallahi ni banida wani buri a rayuwata cewar mamy baki na rawa idonta rufe ta hada hannu biyu gaban dije ni da kike ganina tun ina qaramata burina bai wuce inyi aure in haifi yara biyu ba kuma Allah ya cikamin bayan wannan yanzu banida wani kuma

ah ah kinada shi mana

wallahi banida shi

karima kina fa dashi

ranku ya dade dan daga jin muryar nan wlh kunfi dubu dan haka ku yadda banida shi

munce kinada shi kariiimaaaa dije ta fada cikin 'dan daga murya

ai mamy bata san lokacin data tuma a kasa ba tayi rufda ciki ta saki kuka wanda in bata manta ba ko kar tayi karya da saita ce marabinta da kuka tun na amarci 😂amma yau gata tsofai tsofai da ita an sata kuka wayyo ita karima

muryar dije taji tana fadin bama son musu a iya binciken da nayi mun gano kinada manyan buruka a rayuwarki ciki harda korar uwar dakinmu daga gidan nan

ni din banza ni na isa in raba hanta da jini ai khadija tafi kowa cancanta da zama a gidan nan ni duk duniya akwai yarinyar danake so irin ta

karya muka yi miki kenan?

wallahi ko uban ubana bai isa yace kuna qarya ba kuda a halittar ku sam baku san wani abu wai shi karya ba ta yaya zance kuna qarya ai ban isa ba takarasa maganar tana me jan majina da matso hawaye

to tunda kin san haka meyasa kike shiga shirgin daba naki ba mun so mu sauqaqa miki shiyasa muka sa ta koma gidan 'ya'yanki amma kika san yadda kikayi kika dawo da ita nan wannan ma bai isheko ba wato saida kk hana mai gidan biya mata bukatar data tambaya alhalin ke bayi mata zakiyi ba

wallahi yaseen kwarankwasa kinji na rantse ba laifina bane dawowar ta gidan nan wlh sharrin yarana ne dan dama shi habeeb tun yana shan nono na fuskanci baida son mutane shi kuwa naseer tsegumi to yawan tsegumin su yasa nace ta dawo gida kuma kinga abin Allah saiya hadasu da munafukan mata wlh ba yin kaina bane su suka dinga zuga mazan to dama abu ya tadda hali musamman naseer da yusra sarakan munafurci su suka qara iza wutar duk da nasan gaskiya nasan khadija batada fitina to sbd bana son sunanta ya baci shiyasa naje na taho da ita kuma batun Alhaji danace kada ya bata kudi wlh ni nayi niyyar yimata komai da take bukata dan yanzu haka ma can nayi inda zan gwangwajeta da kaya na alfarma inda nake son tafi amaryar ma haduwa da tsari dan kun san khadija ba baya ba wajen kyau sannan ga.......

ya isa haka amma kin makaro dan yanzu haka har su akuyatu wadanda muke cousins da su sun dauki wani abu a jakarki yanzu zasu tafi suyi sadaka da su domin almajiran mu sun cika kofar gidan nan

cikin mamy ne yabada kuuuu wata muguwar gudawa ta taso mata jin wai an kwashi kudi a jakarta za'a rabawa almajiran aljanu wayyo ta shiga uku bata ankare ba ko taji ta jika wandonta da dan karamin zawo

jin dan doyi da dije tayi yasata fadin warin me nakeji haka ta fada tana toshe hancinta

mamy data tabbatar bako tantama zawi tayi yasata fadin wlh inaga jaba ce ko beraye sukayi tusa a store duk da zuciyarta na rawa ta fadi hakan dan tasan sun gama sanin me tayi amma bari tayi karyar kare kai Allah yasa kada su gano

muryar dije ta tsinkaya tana fadin wato zawo kk yi kenan ba laifi ai abin yabada kala tusar bera data jaba ta hade da zawonki

to yanzu kinga ance akwai sauran almajirai kusan miliyan uku basu samu sadakar ba kuma sunce suna nan ba inda zasu suma sai an basu dan haka yanzu muna neman izininki ki bamu wannan da hannunki muje a basu a basu hakuri

mamy dake duke wani kuka ta fashe dashi dan a rayuwarta ita mace ce me son kudi ta yaya zata iya rabawa aljanu sama da miliyan uku kudi to ai ko bil'adama ne batada wannan zarafin bare jinnu har yanzu kanta duke yake ta kasa kallon dije dan wannan hakoran data gani tun farko sun razana ta

dan girman Allah kuyi hakuri wallahi banida wannan arzikin

to ba dama kince uwar dakinmu zaki je ki siyawa kaya ba to ki bayar dasu ayi sadakatu jariya

banda abinku bskwaso uwar dakin naku tafi ta kowa ne ?

mu kk tambaya?

ni na isa in tambayeku wlh subutad baki nayi

to munji mu dawo kan maganar mu kince ke kina son khadija to meyasa bakya son dangin.mijinki ?

waye yace bana sonsu mutanen kirki irin wannan ai ni nafi kowa sa'ar dangin miji ko ince 'yan uwa ma

kin fada ba dai dai ba cewar dije data gaji da tsayuwa ta zagaya ta zauna kan kujera

mamh datake jiyo.muryar dan nesa da ita yasa ta kara hautsinewa dan duk a tuninta wani salon ne

to kin san kina sonsu meyasa bakya zuwa inda suke kullum.kk kyamarsu sannan kina.....

wallahi a cikin satin nan nake shirin zuwa dan dama can ina tunanin farraku akayi mana tsakaninmu amma yanzu ya karye ga dukkan alamu

to munji amma bamu yarda ba

tana shirin sake magana sukaji ana kwankwasa kofa da sauri dije tace kinyi baki 'ya'yanki sunzo gaisheki mu zamu wuce mu barki da uwar dakinmu ama anjima zamu dawo

ta mike ta nufi kofa ta bude duk da zuciyarta na raya mata tayi sakin layi datace yaran mamy ne bayan batada tabbas

su din ne kuwa inda cikin sakin fuska ta basu guri suka wuce ta shiga gaishesu

mamy data mike tana ta kokarin kintsa fuska da son shiga daki don wanke jikinta taga shigowar su habeeb take ta kara yadda da lamarin

tana gab da shigewa dakin ta tsinkayi muryar habeeb yana fadin ah ah mamy lfy kuwa naganki haka?

hmmm kai dai bari kawai ta fada tana me kallon inda dije ke zaune wadda ta dago ta kalleta tace lah mamy meya sameki haka nima fa yanzu na lura ?

apolo nakeyi ta fada tana me tafiya da baya da baya dan karsuga shatin kashin dake jikinta

ikon Allah cewar naseer

*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 11:19 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TAME GARI*

NA
khadija usman

3⃣4⃣

*domin ku kawai masoya tame gari nayi kewarku kwana biyu wlh abin ne sai a hankali ina fatan zaku kara hakuri fiye da yadda nasanku,sannan masu bina pc suna tambayar buk din dan Allah kuyi haquri wlh banida time din tsayawa inta turashi abin ne dayawa kuma kullum abin daduwa hakeyi Alhmdllh ina sonku fiye da yadda kk son tame gari*

a polo mamy ?

tun yaushe?

kai ni bana son jarabar magana ku jirani ina zuwa ta fada tana me afkawa daki

tana shiga ta rufe kofar nan ta shiga tsinewa aljanun dije albarka tare da fargabar bata san ko nawa suka dauka a jakarta ba suka bawa musakan aljanu to inma ba son zuciya irin na jinni ba su da suna iya zuwa banki su dibi wanda ransu ke so amma wai su tsaya dibar nata dan su rabawa wasu dan salon mugunta da anyi magana yanzu haka suce basa cin haram ta jima tsaye tana tsinewa dijen tare da ninkin tsanar ta a zuciyarta ji tayi kamar an taba qofar ai a sukwane ta afka toilet tana shiga ta fada a fili Allah ya isa tsakanina daku wannan wace irin jaraba ce yanzu wato dama yarinyar nan iyayenta sun san tanada fasinjoji shiyasa suka kadota nan shi yasa ashe yaran nan suka dinga rokata in zo in dauketa ashe su kadai suka san azabatul ular da suka sha ni gashi an ganamin azabatunna'ura banji ba ban gani ba kawai dan na hana abata kudi to wlh da sake gurin malam zan tafi ya bani tsarin kar tasan kar inzo ingama da shegu zaki gane kurenki ne tanayi tana wanke kashin jikinta yanzu dubi kiga marabina da inyi kashi a wando tun na yaye amma yau kiri kiri an sani nayi Allah ya isa wlh da haka harta gama ta kimtsa jikinta cikin dan hade rai ta nufo falon dan tama fasa fitar kuma yanzu tunda aljanun sun sauka uwar yarinyar zataci inya so ko sun dawo tabasu hakuri duk da bata fatan su dawo din dan wannan hakoran data gani in batayi qarya ba zata iya cewa sunyi hauren giwa

*kai mamy a rage ta gobe* 🤣

karasowar ta falon yayi dai dai da shigewar dije dakin su inda su habeeb suka duka suka gaida mahaifiyar su cikin girmawa ta amsa tana me tambayarsu lafiyar matansu

duk suna lafiya suka amsa yayin data lura da yanayin naseer yana ta fara'a kamar mai tallan hokorin maka cikin kulawa tace naseer ya akayi naganka kamar cikin farin ciki

kara fadada fara'arsa yayi inda ya shiga sunkwiyar dakai sannan yafara magana am dama jiya ne yusra tayi zazzabi to shine nayi

19 / 33