a hankali a hankali zafin zai gushe har wata rana ma sai na manta ina da kishiya. Ina dariya na ce.
"Daman ana mantawa?
Itama ta na dariyan ta ce" Sosai ma. Barin ma in ba gida ɗaya za ku zauna ba"
Sai na ce mata ban sanin masa ba nan na ke faɗa mata ni fa har yau bai faɗa min ba amma na ji yana waya ashe shi ne ya roke su kar su faɗa,min har sai bayan shi ya faɗa mini da kansa.
Cikin dariya ta ce" Ya yi miki irin na Ɗan"uwansa nima ai bai faɗa min da farko a gari na ji. Ni ko na yi irin taki ban nuna masa na sani ba."
Nima ina cigaba da ba ta labarin a wajen wata yar uwata na ji labarin. Anty Zabba ta ce na yi jarumta na cigaba da bin shi a haka na ga iya gudun ruwan shi. Hira ta ɗauke mana hankali har sai da aka kira sallar isha'i sannan muka yi sallama sai na ji zafin da ke taso min a saman ƙirjina ya na raguwa samun wanda mu ka yi hira ƙwatakwancin mai damuwa ko na ce gyambo irin nawa.
Muna gama wayar ban koma falo ba sai da na yi sallar isha'i sannan na koma falo wajen su Jidda sai na iske ma suna salla bayan sun idar nace Jidda ta ɗibo min abinci tun da ɗazu da rana ban ci ba. Da gaske ne na ji sauƙi sauƙi a cikin raina tunda har ban ma yi barci da wuri ba sai da na jira dawowan Yallabai wajen tara na dare, ina ta kallonsa ina tunanin daga wajen Gimbiya ya ke amma sai na yi saurin kauda wannan tunanin kamar yadda Anty Zabba ta ba ni shawara.
Shi kan shi na san ya ga chanji. Domin ni da kaina na haɗo masa ruwan lipto ya sha bai ci abincin ba ya ce cikinsa ya cika mun zauna da yara muna kallo har goma na dare sannan na ce su je su kwanta saboda makaranta gobe, mu kuma sai wajen sha ɗaya muka shiga kwanciya domin Yallabai ne ya ce sai ya ƙarisa kallon wani american film ɗin da muka fara kallo a MBC ACTION.
Saboda ya ga na ɗan sake masa ya na ta ba ni labari ashe tun fitan shi suna tare da Uncle Abba sai daren nan suka je ya gaida Nene shi ya kawo shi gida sannan ya wuce.
Ina gyara gashin kaina na ce" Allah ya kai shi lafiya "
Su Yallaɓai an samu fuska ya na tarawan jiki duk da har ga Allah ba na cikin Mood ɗin haka nan na bashi dama, kuma daman al'adata kwana biyu ya yi ya ɗauke ni da na ke yi kwana biyar a baya. Yau ban san da me zan kare kaina ba. shi kan shi ya ɗan ga chanji domin ban yi masa wani rawan jiki ba, kar dai ya ce na yi masa kamar gunki ne ya sa na ɗan motsa masa kaɗan na ga mamaki a saman fuskarsa amma bai furta min ba ni kuma ban bashi damar mgana ba, domin niki niki na yi da raina ina ta faman sha masa kamshi.
Da asuba ma da na ga take taken shi na son ƙarawa sai na yi masa barcin ƙarya dole ya ƙyaleni. Bayan su Jidda sun tafi makaranta ni da shi ne kaɗai a gida, Marwa ta zo kwasan sauran kayanta ita na samu ta yi min gyaran gida muna ta hira da ita tana ma gidan sai ga Saude na ce ba na ce ta zauna a gida ta warke ba sai ta ce min ai ta ji sauƙi.
Su suka ɗeɓemin kewa domin Marwa ta yi min abincin rana sai wajen ukun rana suka tafi. Yallaɓai kuma daman tun safe ya ce min yau da yamma ko da daddare ya na so zai yi mgana da ni, ina jin haka a raina na ce daga baya kenan. Sai na ji kamar ba na son jin ma abin da zai gaya min saboda ba zai zama wani sabon abu a wajena ba. Har na saka ma kaina dangana na ce zan tsaya na saurare shi ko domin na ji abin da zai ce min. Sannan ina son na san ta in da aka haihu a ragaya, to eh mana domin har yau ban ji labarin yadda wannan auran bazatan ta ya faru ba, shin daman can an shirya sa ne ko yaya abin ya ke! Bai ba ni wannan amsar ba mutum ɗaya ne ko zuwa biyu ko Yallaɓai ko kuma ita kanta Gimbiyar.
Wajajen ƙarfe biyar da wani abu na yamma muna falo tare da Yallaɓai shi ya na aiki a saman system ɗin sa ni kuma ina kallo a Mbc bollywood domin na fahimci suna series masu kyau da ma'ana. Jefi jefi muna hira duk da ƙarfin hiran na bakin Yallaɓai ne ya na ba ni labarin aikin su na kaduna da irin alherin da ya ke fatan samu kallonsa kawai na ke yi, a baya ne in ya na faɗa min haka na ke jin daɗi amma yau sai na ji ko kaɗan ban wani damu ba, in zai lura ma ni ina ta taɓe masa baki ne labarin duk ya gundure to Allah na tuba yanzu ai komai ya samu ba nawa ba ne ni da ƴaƴana ba, namu ne har da ita kanta Gimbiyar wa yasanin ma ko da kuɗin ya ke saka ran yi mata hidima da kuɗin ma ya kawo min kishiya.
Fitsari ya tashe shi nan tiolet ɗin falo ya shiga ya kama ruwa. Ya tashi kenan ba daɗewa wayarsa da ke gefensa a in da ya tashi ta fara haske kaamar tana silet ne ina zaune amma na kasa tashi domin na daina saka ido akan wayar Yallaɓai domin tsira da kwanciyar hankalina. Duk da ina ankare da shi ni dai tun bayan faruwan auran na su ban taɓa ganin sun yi waya ba kamar ta ɗan rage kiran shi a bisa baya. Wata zuciyar ta ce min ke Sadiya in suna wayar ma za ki sani ne! Balle ma suna gari ɗaya ai suna ma haɗuwa su yi abin da a waya ma ba za su iya ba.
Tunanin haka kawai ya sa na yi tsaki mai karfi na tashi da niyyar na bar masa falon. Amma sai zuciya ta rinjaye na ƙarisa wajen wayar ina ganin tana cigaba da hasken alamun mai kiran ya kasa haƙura.
"Daughter."
Gabana ya faɗi ya yi wani raga raga, kirjina ya amsa dum! Har sai da na dafe ƙirjinan nawa saboda na ji nauyin da ya yi min na neman rinjiya na. Dai dai lokacin Yallaɓai ya fito daga tiiolet ya na daura mazugin wandon shaddan da ke jikinsa.
"Sadiya ta a taimaka a wanke min tiolet ɗin mana."
Duk ƙokarina da nuna jarumta yau na kasa, me ya sa ta ke kiran shi? Ba kullum suna tare ba! Don kawai yau bai fita ba ta ganshi ba shi ne sai ta kasa sukuni sai ta neme shi! Ƙila ya fara ɗanɗana mata daɗin shi ne ba za ta iya hakura da shi ba, ina jin tahowar Yallaɓai ya na mgana amma turiri na ke ji na fitowa daga zuciyata har ina jin zafin a cikin bakina.
"Kawai kin yi ma tiolet ɗina tawaye shi sai a yi sati ba a kalle shi ba."
Ya faɗa dai dai yana ƙarisowa wajen da na ke tsaye.
"Na ga kina tsaye! Me ya faru?
Na so ne na juya cikin lumana na bar masa falon amma kishi ya sarrafa zuciyata domin a fusace na juyo, ko kallon Yallaɓai ban yi ba da wani uban sauri na wuce sa har ina bangazan kafaɗansa.
"Sadiya.."
"Sadiya.."
Haka ya riƙa kirana, amma ko juyowa ban yi ba, da wani irin zafi na buga masa ƙofar falon bam! Na kuma san sai da ƙaran ya shiga kansa ina tafe ne zuwa ɗaki amma ina ganin nisan shi a yau, ni dai kafata kawai ke tafe da ni ban san ya aka yi ba na ganni zaune saman cafet ina kuka bayan na shigo ɗakin barcin mu na rufe ƙofa duk ƙoƙarina na kar na yi kuka sai da na yi. A raina ina faɗin Yallaɓai ya cuce ni da ya yi auran nan a lokacin da ban yi zato ko tsammani ba.
Ni dai tun da na shige ɗaki ban buɗe ba, ban kuma fito ba ina jin Yallaɓai ya gama bugun duniya da kiran sunana na yi masa banza. Sai da na ji fitarsa masallaci sallar mangariba na buɗe nima na shiga tiolet na yi alwala na zo na yi salla a lokacin su Jidda suka shigo sun dawo daga makaranta tun ɗazu wai Abba ya ce ba na jin daɗi, sai amsa musu da eh tunda ya ce ban jin daɗi ai shikenan zama na yi kan darduma ina ta salatin Annabi har sai da na samu natsuwa ana kuma kiran sallar isha'i na miƙe na yi ina idarwa na yi shirin barci na koma na kwanta. Ni yanzu ma waya ba ta gabana saboda na fahimci ita ke barazana da kwanciyar hankalina.
Yallaɓai sai bayan isha'i ya dawo ya kuma shigo ɗakin sai na fara nishi kamar ban da lafiya. Sai ya ruɗe ya ƙariso gare ni yana tambayata meke damuna na dafe kaina na ce kaina ne, ya ce zai bani magani na ce ai nasha. Bawan Allah ya bani tausayi haka ya zauna a kusa dani ya na ta min sannu ni fa daman guje ma mganarsa ne a yau ya sa na yi haka ganin yaƙi tashi a kusa dani ya sa na fara barcin ƙarya, ganin haka yasa ya gyaramin kwanciya ganin ina zufa sai ya kunnamin fanka ya fice bayan ya rage min hasken ɗakin gabaɗaya.
Yana fita na mike zaune ina mai harɗe hannayena a saman kirjina. Na daɗe ban yi barci ba ina ta tunanin wai yau Yallaɓai ba nawa ba ne ni kaɗai kai lamarin akwai girma. Tun ina jiyo ƙaran tibi daga falon yara har barci ya ɗauke ni sai asuba na tashi, da rawan jiki ya fara min sannu har ya na taɓa goshina.
"Ya kan na ki? Ya yi sauƙi?
Sai na gyaɗa kai ina faɗin ya yi sauƙi saboda na ji yana faɗin in ba zan iya ba na ɗaga zuwa asibiti sai wani sati da sauri na ce zan iya.
Yallaɓai ranar ya yi ma yara da mu kan mu abin kari, doya ya soya mana sai abincin jiya da ya ɗumama duk tare za mu fita shima ya na da zuwa jana'iza baban wani yaron shi ne ya rasu a can sheƙa. Su Jidda suka fara tafiya mu kuma takwas da rabi muka fita ni da Yallaɓai sai da ya fara kaini asibiti sannan ya wuce jana'izan da za a yi ƙarfe tara na safe ya na ta ma sauri, ni kuma har muka rabu ban iya ce masa daga asibiti Ɗorayi zan wuce ba na bari sai na gama da asibitin sai na kira shi na faɗa masa.
Yau ban samun ganin Dr.Aisha Bukar da wuri ba, saboda ba ta zo da wuri ba , sai 12pm na rana na baro asibitin. Daman na je mata da Test ɗin da ta rubutamin a ƙarshen zuwana tun da yanzu bayan sati uku na ke dawowa. Yau ma ta ƙara rubuta mini wani amma tace shi ne na ƙarshe, daga shi za ta ɗora ni kan mganguna.
"Dr kina ganin zan ƙara samun ciki har na haihu?
Na faɗa cikin karaya saboda ni dai na gama sarewa.
Sai da ta kalleni kafin ta maida hankalinta kan fayel ɗina ta na rubutu.
"E mana. Me zai hana? Likitoci ai ba Ubangiji ba ne, duk abin da muka faɗa hasashe amma ba gaibu ba ne. Balle ni ban ce miki kina da wata matsalan da ba za ki sake haihuwa ba. Za ki sake haihuwa haife haife ma in sha Allahu."
Haka aka sha faɗa mini amma kuma kalaman Dr Aisha ya sa na samu sukuni, na yi mata godiya da ya ke mun saba sosai da ita. Sai da na fito bakin asibitin na kira wayar Yallaɓai bai ɗauka ba sai na ƙara kirana har sau uku amma bai ɗauka ba.. gani a bakin hanya ina son hawa adaidaitan da za ta kaini Ɗorayi.
Dubaran tura masa saƙo ya shiga kaina. Da sauri na shiga bangaren saƙonni na lalibo Yallaɓai tun saƙon Anniversty da na tura masa bai ko ba ni amsa ba, ban damu na shiga yi masa rubutu.
"Ina so daga asibiti na je gida na gaida Alhajinmu."
Na daɗe fa a bakin hanya raina har yafara ɓaci har na yanke shawaran ƙarisawa Office ɗin sa tunda ya ce min daga wajen jana'iza office zai zo, da ya ke ba nisa offishin na su na can gaba ne ko a ƙafa ma zan iya takawa. Ina wannan tunanin sai ga saƙon sa.
"Ok."
A takaiçe haushi ya kama ni na yi ja dogon tsaki na maida wayata jaka na samu adaidaita da za ta kaini ɗorayi. Ina sauka a a bakin layi na tako zuwa cikin layi na haɗu da wasu matansa anguwa muka gaisa. Na shiga gida ana ta kiran sallar azahar na samu Gwaggo a tsakar gida ta na alwala gidan shuru.
Ina sallama Gwaggo ta ɗago ta na amsawa.
"Ah maraba Dubu ke ce tafe? Na amsa mata ina gaisheta ta amsa lokaci ɗaya tana tambayan Yallaɓai da yara, nace suna lafiya.
Ɗakinta muka shiga ina tambayan Alhajinmu ta ce jiya ya je can yashe sai yau zai dawo.
"Topha lafiya ko Gwaggo?
'Lafiya lau. Kan auran autan su Muntari ne kinsan bikin saura kwana goma."
Gwaggo ta amsa min.
Shaf na manta da bikin kuma daman na yi alƙwarin sai na je wannan karon.
Nima sauke jakata na yi na tuɓe hijabi na fita na ɗauro alwala na zo na yi sallah bayan na idar Gwaggo ta ce ɗanwake ta yi na je na zuba na ci, ina son ɗanwake jikina na rawa na tashi na je na zubo na dawo ɗakin ina ci muna hira sai da na gama na sha ruwa sannan na ce mata daga asibiti na ke.
"Allah sarki ina fatan dai ba matsala ko?
Sai na amsa mata da " Muna saka ran haka Gwaggo."
Sai ta yi min fatan Allah ya sa a dace ta ce min akwai na gargajiya a can gida ta yi mgana za ta karɓo min na ce to bari in na gama shan na asibitin tukkuna. Tun da Alhajinmu baya nan Gwaggo na faɗa ma ƙarin auren Yallaɓai itama ta sha mamaki har sai da ta furta..
"Topha aure haka bagatatan Sadiya?
Ni kuma sai na ce mata an ɗaura ne amma ba a yi tariyan ba, duk da ban sani ba amma alamu sun nuna mini haka. Gwaggo ta yi fatan alheri nima kuma ta yi min nasiha ta ce sai na yi hakuri na kauda kai na ce mata in sha Allahu.
Ina gida tare da Gwaggo muna ta hira sai gabda la'asar na yi ma Gwaggo sallama na ta fi gida bayan na ce a gaida Alhajinmu in ya dawo.
Ina komawa gida na yi salla na shiga kitchen kuskus na dafa mai kayan lambu da hanta. Sai na yi lemun ginger na saka a fridge ya yi sanyi, Yallaɓai ya ba ni mamaki ko ya kirani? Har wayata na dinga dubawa amma bawan Allah bai kirani ba sai kuma abin ya dameni ai ya ga saƙo na ko? Wata zuciyar ta tunaar da ni yanzu fa ba ke kaɗai gare shi ba bai zama lalle sai ya damu da ke kamar baya ba.
Ina ta so yakice tunanin haka a raina amman na kasa gaskiya kishi akwai wahala gabaɗaya har na fara rama a tsaye saboda zullumi da tunani ban sani ba.
******
Gwammaja.
Wajajen takwas da wani abu na dare ya shigo anguwan gwammaja a motar shi. Ko a cikin gidan ma ya daɗe a mota ya kasa fitowa bayan ya kashe motar. Gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi ko na ce ya mutu.
Ƙwaƙwalwarsa ta tsaya cak ya kasa ma wani tunani tun safe ya ce tun bayan barowansa wajen gaisuwan nan ya ji kamar zazzaɓi zai kama shi, ya je office ya yini amma ya kasa taɓuka komai kamar mara lafiya.
Ya na gani Sadiya na kiran shi ya kasa ɗaga kiranta to me zai ce mata! Akwai wasu kalaman da zai iya kare kanshi ne da su ne? Ya ga saƙon ta ok ɗin ma da ya tura mata hannunsa na rawa ya tura mata, domin gani ya ke yi duk abin da ya ce ko zai ce a baya da yanzu Sadiya ba za ta daina masa kallon maƙyarci ba kuma ma ci Amana ba, duk da ba haramci ya aikata ba.
Amma dai ba daɗi shi kan shi ya sani bai kyauta ma Sadiya ba
Sai a lokacin lda suka haɗu da Yaya Abubakar a wajen jana'iza bayan sun gaisa ya yi masa murnan aure ya kuma ce Sadiya ce ta sanar dasu. Tun daga lokacin ya ji jikinsa ya mutu. Ashe ashe tuni Sadiya kallonsa kawai ta ke yi bai sani ba! Sai a lokacin ma ya riƙa tunano attitude ɗin da ta riƙa bashi tun ranar Anniversary ɗin su, bai taɓa kawo ma kansa labarin auran sa da Gimbiya ta ji ba, Bai taɓa tunanin roƙon da ya yi ma ƴan'uwan shi da alfarman da ya roƙa ba su yi masa ba. Ya a ka yi sadiya ta ji wannan mganar? Sai a lokacin ya tuna abin da ta yi jiya lokacin da ta ga Gimbiya na kiran wayarsa a she duk a lokacin ta na dannewa ne amma ta sani kawai kallon shi ta ke yi.
Ya tuna a lokacin ya na hanya zai koma office daga wajen jana'iza ya kira Abba ya na faɗa masa Sadiya ta sani ba tare da shi ya faɗa mata ba.
"Laifinka ne Tafida me ya sa ka yarda ma aka ɗaura auran ba ka koma gida ka faɗa mata ba?
"Na so haka Abba amma Nene ta ce yanzu yanzu mu tafi Rano."
Ya bashi amsa cikin karaya. Kalmar ɗaya Abba ya sake faɗa masa sai ya ji ya ƙara jin mutuwar