ina kula da ita. Lokacin Mimisco ba su kasar ita da mijinta Anty Bahijja da Anty Maimuna kowacce na da iyalanta Halima ce lokacin kuma ta na makaranta ni ce na zauna da Nene har ta samu lafiya sannan na koma gidana a lokacin Yallaɓai ya ce na gama masa komai a duniya shi ne yau zai manta baya ya kalli tsabar idona yana faɗin Gimbiya ce ta yi masa komai ni kuma ban yi masa ba tunda zuciya ta ba alheri a cikinta, anan na kwana a falo a kan kujera ina kuka kukan baƙin ciki da takaici dare kuma mafi tsawo a wajena, ya ce wai daga na ce ya yi min kaza sai na ce ƴan'uwan sa sun yi min kaza ban da namiji mai manta alheri ni me na ce sun yi min? Ya manta yadda a baya na bauta musu na yi musu biyayya, amma yau duk ya manta sannan ya ce ni na tsani matarsa yaushe na ce na tsane ta? Kawai dai laifin nawa ne ya yi masa ƙaranci shi ya sa daga ya ce na yi kaza sai ya ce na yi kaza amma na kudira a cikin zuciya zan kiyaye ma komai na Yallaɓai yau ko korata ya yi a gidan shi ba zan buɗe baki na ce masa don me ba! Tunda ya iya kirana mara alheri na tabbata a gaba zai iya aikata komai.
Har gabda asuba idona biyu sai a lokacin na samu barci sai sa na ji Jidda na tashina har sun yi salla, na tashi da karfin zuciyata amma idanuwana har sun kumbura saboda kuka. Tiolet din su na shiga na kama ruwa, sannan na zo muka yi azkar tare na shiga kitchen na ɗora musu abin breakfast ko ɗakin ban fatan komawa Yallaɓan ne ba na son gani saboda gabaɗaya baƙin sa na ke gani a cikin zuciyata shi ya sa ko hanyar ɗakin ma ban sake bi ba, a kan dining na jera masa abin karinsa na shige ɗakin su Jidda acan na yi wanka Allah ya sa na leƙa Yallaɓai ya shiga tiolet sai na lallaɓa na dauko kayana da abubuwan amfanina na fice na barsa ma ɗakin.
Yadda na ɗau gaba dashi haka shima ya ɗau gaba da ni. Tun daga ranar ban ƙara kwana a ɗakin ba a ɗayan ɗakin na ke kwana, kuma kafin ya dawo mun shige ciki ban son na kwana da yara su fahimci wani abu, in kuma da safe ne kafin ya fito na gama masa komai na ijiye masa na koma cikin ɗaki. Wani lokacin ya ci wani lokacin kuma ya bar min kayana, ni kuma ban damu ba domin duk abin da Yallaɓai zai yi min ko zai ƙara min ba zai ba ni mamaki ba.
Ranar junma'a Musbahu ya kawo min cefane duk da bai faɗamin ba a raina na ce ƙila Gimbiya za ta koma ne illau ko da yamma ya zo gidan ina jin shigowarsa na shige ciki sai can na ji tafiyarsa sai ga Jidda ta shigo ta kawo min man shanu da kuɗi 10k sannan ya ce a faɗa min Gimbiya ta koma gidanta ƙala ban ce ba na karɓi kuɗin na ijiye man shanun kuma na kai kitchen na ɗora tukunya na soya shi, a daran nan sai ga Ya Aina ta zo duba ni Baban Marwa ya kawo ta ai na ce na ji sauƙi nan na roƙa na ce Marwa ta zo ta min weekend don Allah, baban ta ya ce ai Marwa ƴa ta ce umarni kawai zan ba da sai a faɗa mata sun ɗan jima kafin su tafi kuma na ji daɗi ɗan'uwana mai daɗi, a da ji na nake yi kamar a cikin kurkuku duk in da na yi tunanin zuwa sai na ga ba zan iya tambayan shi ba gwara na haƙura in ma shekara za mu yi a haka sai dai a yi.
Washegari asabar su Jidda sun tafi Tahfez a ranar aka kawo min Hijabai daga zariya Musbahu daman ke karɓan min a nan Zaria road motar in ta shigo cikin gari sai ta tsaya nan ya karɓa min, shi ya kawo min har ya na ce min na ijiye masa guda biyu ni kuma na tasa shi da tsiyan ko ya samo mata ne.
"Sai Yallaɓan ki ya sallame ni tukunna ko zan ɗauko maganar aure."
Ina dariya na ce" Haba tun yaushe ya sallame me ka."
"To ina ga ko Sabon Office ɗin nan na ƙasa in da muke na wa ne?
Cikin zolaya ya faɗa, ni da ya ke ban ma san da shi ba amma ban nuna ba sai na ce ƙila na ka ɗin ne, mun yi ta hira har muka gangaro maganar gidan Bulo ya na faɗa min an fi wata biyu ba a aiki, Yallabai duk ya bari wajen na neman mutuwa.
"Anty Sadiya ki yi masa mgana don Allah kar ya bari wajen ya mutu. Tun da ya na jin maganar ki."
A raina na ce a da kenan, yanzu kam sai dai Gimbiya. Amma ban nuna masa ba sai kawai na ce zan masa mgana. Tuni na manta da takaicin Yallaɓai, na fara kiran mutane ina faɗa musu an kawo hijabai su siya na salla tunda babbar salla ke kusanto mu. Har Ma'u na kira na yi mata tallah sai ce min ta yi ai ta ji labarin ina sai da Hijabai ban yi mata tallah ba ne ya sa ba ta siya ba amma tunda yanzu na yi mata talla za ta zo gida ta duba ni dai a raina na ce kya ji da shi munafuka
Ya Muntari ma na yi masa talla na ce ya siya ma Rahila da yara. Har Nasir da Mutaƙƙa sai da na ce su siya ma matan su da yara. Kuma duk sun ce matan za su zo gida su duba. Ranar dai ban yinin kunci ba cikin walwala na yini ranar Yallaɓai bai zo gidan ba sai can dare na ga saƙon shi saboda haushi na goge shi ma.
"Ya kuke? Fatan kuna lafiya"
Na gani amma sai na goge na kama harkan gaba na. Washegari Lahadi sai ga Kawu Abba ya zo ya ma ɗauka Yallaɓai na gidan ne na ce masa ba nan ya kwana ba ya na gidan Amarya shi kuma ya ce ya na ta kiran wayarsa ba ya samu ya shigo garin ne kuma ya na so su haɗu.
A gidan ya karya ni na haɗo masa abin karyawa, muna ta hira da shi, kuma har lokacin bai samu wayar Yallaɓai ba sai daga baya ya ce ni na jara ba kiran shi a wayata mana ko zan same shi.
"Ka yi haƙuri Kawu ka cigaba dai da gwadawa in baka same shi ba sai ka je gidan mana."
Na faɗa ina kallon shi, sai kawai ya tsaya ya na kallona kafin ya ce" Me ya faru ne Sadiya? Tafida ya yi miki wani abu ne?
Idanuwana suka cika da kwalla na yi saurin basarwa.
"Bakomai."
"A'a da komai fa."
Ya faɗa ya na kallona lokaci ɗaya kuma ya na nazartan yanayina.
*Janafty*
*TKG*
FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622
13.
Kaina na mayar ƙasa ina wasa da gefen hijabina. Sai na sake ɗagowa ina kallon shi jin ya yi shuru sai muka haɗa ido dashi da sauri na ƙara sadda kaina ƙasa domin har ƙwalla sun cika min ƙwarmin idanuwana tuna irin cin mutumcin da Yallaɓai ya yi min.
"Me ya faru?
Ya sake tambayata sai na yi saurin shanye kukan da ke taso min har ina yin mirmishi wanda na aro shi na yafa a saman fuskata duk domin na kauda ma Kawu tunanin cewa wani abu ya faru. Sai dai kash ya riga ya fahimta sai dai na basar kawai.
"Allah ba komai Kawu."
Na faɗa ina masa mirmishi sai kawai ya gyara zama kafin ya ce" Na ji kin ce dai bakomai amma ban yarda ba komai ɗin ba Sadiya."
Ina kallon shi na buɗe baki zan yi magana sai ya dakatar dani da hannu lokaci ɗaya ya kira sunana.
"Sadiya."
"Na'am."
Kai tsaye ya kalleni kafin ya cigaba da faɗin" Kin san dai ni san ba zan taɓa yarda wani abu bai faru ba ko? To gwara ki yi shuru a tafi a wani abu ya faru ni ba zan matsa miki sai kin faɗa min ba amma kuma ba shi zai hana na ƙi baki haƙuri ba"
Sai na kalleshi amma ban yi magana ba, ni ko a gida kowa ya sanni ba ni da daɓi'ar kai ƙaran miji duk abin da ya yi min a cikin gida za mu yi ta ƙare shi ya sa a yanzu na ke jin nauyin furta cewa Yallaɓai ya yi min kaza, kamar yadda ya ce ne ina mgana tuni za a ce zafin kishi ne ya sa na ƙi kwantar da hankalina shi ya ma faɗa da bakin shi ballatana wani daga waje.
"Sadiya."
Ya katse min tunani sai na ɗago ina kallon shi.
"Ki yi haƙuri."
Sai na gyaɗa kaina kafin na ce" Bakomai Kawu."
"Ban san me Tafida ya yi miki ba. Amma dai koma mene ne don Allah karki riƙe shi a cikin zuciyarki. Ba wai ina kare shi domin ya na nawa ba. Kema tawa ce wallahi. Sai dai ba shi zai hana na faɗa miki wata gaskiya ba."
Na ɗago ina kallon shi, ba tare da na yi magana ba..
"Sadiya Tafida ya na sonki. Kuma duk macen da zai aura ko anan gaba sai dai su biyo bayan ki. Haƙuri za ki ƙara saboda kin san mu maza in muka ƙaro aure sai wasu canji canje su yi ta faruwa haka Allah ya hallicemu mu Maza wani lokacin muna da son kai da Matan alheri. Ki yi haƙuri ki yi masa uzuri na tabbatar miki da cewa ke ce giwar mata a wajen sa."
Ina kallonsa ne amma ni kalamansa ba su wani kama zuciyata ba, shi kuma ganin kamar ban yarda da shi ba ya sa ya jinjina min kai.
Sai kawai na yi mirmishin takaici kafin na ce" A da kenan amma yanzu Gimbiya ta sha gaba na."
"Ba ta sha gaban ki ba Sadiya. Ai ke ba macen da ta isa ta sha gaban ki a wajen Tafida Allah."
Mirmishin na sake yi ba tare da na ƙara mgana ba. Ni kaɗai na san yanayin da na ke ji a cikin zuciyata kawai dai ina dannewa ne.
"Ina da dalilina masu ƙarfi da ya sa na faɗi haka. Ba wai kuma don ki ji daɗi ba sai zallar gaskiya. Tafida fa kin san tare muka tashi dashi akwai wasu abubuwan da a mu'amala ne muka karanci juna ba ta hallaya ba. Ki amince da cewa ke Giwar mata ce a wajensa. Ki sani ke auran saurayi da budurwa kuka yi Tafida ya fara sonki tun zuciyarsa na da danƙo ya zauna dake zaman aure na shekaru zuciyarsa na buɗewa a kanki. Ki sani soyayyar da ya ke yi miki ba ya yi ma Amaryansa da ya aura. Bar ganin wai ko sun daɗe tare. Ba zan ce miki ba shaƙuwa tsakaninsu ba akwai amma ba so ba ne, ba kuma zan ce miki yanzu da suke zaman aure zuciyarsa ba za ta ribace shi za ta ja shi zuwa gare ta ba Amma ki sani ko ta ja shi ba za ta iya zurfin kai shi ta ki mazaunin ba. Shi ya sa na ce ki yi haƙuri ki yi masa uzuri wataƙila halin ɗan adam ne na ajizan ci kuma daman shi zaman aure zo mu saɓa ne kuma zo mu sulhunta."
"Haka ne"
Na faɗa ina jinjina masa kai.
"To kin gani. Ki ƙara hakuri. Amma fa ba shi zai hana in ya yi miki ba dai dai a ci ubansa ba."
Sai da na yi dariya shima dariyan ya yi kafin ya ce" E mana ai ba wu ce duka ba."
Ya na mgana ya na danna wayarsa sai ya kalleni kafin ya ce" Kin ga sai yanzu na samu wayar ta shi."
A speaker ya saka kiran har sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka murya a shaƙe daga ji barci ma ya ke yi.
"Ya a ka yi ne."
"Ban sani ba. Mallam watssake."
"Me ya faru ne?
"Ga ni a gidan ka."
Cikin muryan barci Yusuf ya ce" Wani gidan kenan?
"Wanda na fi sani."
Kawu ya bashi amsa lokaci ɗaya.
"Gidan Sadiya.?
Kafim ma ya bashi amsa ya yi saurin cewa"Ka ƙariso nan mana ina nan ni."
"In ƙariso ina?
"Gidan Daughter mana. Daman ba ka taɓa zuwa ka ga gidan Amarya ba."
"Wacece kuma wata Daughter."
Sai da ya yi shuru kafin ya ce" To Saudatu."
Tsaki kawu ya ja kafin ya ce" Tafida kana da sanabe wallahi. To ba zan ƙariso ba in za ka zo ina jiran ka kazo in kuma ba ka zo ba sai ka faɗa min na kama gaba na."
"Kawu."
"Na'am Tafida"
"Gani nan zuwa."
Daga haka shi daga can bangaren ya katse kiran duk ina zaune in jin su, Kawu sai masifa ya ke ya na faɗin" Wai ka auri mace amma kana kiran ta da wata ɗiyar ka? Tafida ba shi da hankali fa, kai suna ba na uwarka ba na ƙanwar uwarka ba."
Ni dai ina ta dariya, mun ɗan cigaba da hira sama sama har ya ke faɗa min ya zo duba wani fili ne a nan cikin gari.
"Ko dai auren ya tashi ne Kawu za a yi ma Amarya ginin gida."
Na faɗa ina masa dariya da sigan zolaya.
"Ko Aure na yi ai ban iya barin Rano Sadiya can a ka haife ni a can kuma nima zan gina nawa Ahalin in sha Allahu. Kawai dai ina siyan filaye ne anan cikin gari saboda Ajiya ne in ka bar kuɗin kuma za ka ksshe su ne a banza."
Na ce haka ne, shi da kanshi ya ke faɗa min ya siya filaye anan garin huɗu kenan kuma takardun ma ai suna hannun Tafida na yi ta jinjina kai ina mamaki lalle Kawu Abba ya tara ko na ce ya na kan tarawa.
"Kawu Allah ya sa ka samo mana mata wannan shekaran mu gwangwaje."
Ya na mirmishi ya kalleni kafin ya ce" Amin Sadiya. In sha Allahu nima ba na so na wuce wannan shekaran addu'a za ki yi min Allah ya ba ni tagari matan ne na wannan zamanin duk sun zama sai a hankali."
"Allah zai kawo ta gari in sha Allahu."
Ya amsa da Amin kafin ya ce" Na ga ma wata iri a gidan ki kwanaki ina ta so na yi miki mgana ayyuka suka sha kaina.'
Cikin mamaki na ce" Iri? Wani iri!? Sai ya kwashe da dariya kafin ya ba ni amsa an kira wayarsa sai kawai na tattara kwanukan da ya karya na fice na bar shi a falon ya na waya. Ina kitchen ina ta mamakin to wacece Kawu ya gani? Ko Saude ce? Wata zuciyar ta kira min sunan ta, sai kuma na tuna ai ya san Saude tunda ya na yawan zuwa gidana kuma ya na ganinta duk a iya tunanina na kasa gane wani iri ne wannan ya gani a gida kuma har ya yaba. A cikin raina ina fatan Allah ya sa ta gida ce, ina ganin mutumcin Kawu Abba ba domin ya na kawun Tafida ba sai domin ya na da kyakyawan halin da duk macen da ta same shi ta more.
Ban zauna ba na fara gyaran Kitchen domin Saude ma sai ta dawo daga allo za ta zo ni kuma ba na so na zauna in na zauna zai yi wahala na sake tashi, ina aikina gefe ɗaya kuma na haɗa tea ina kurɓa ko zuwan Yallaɓai ban ji ba, sai jin muryansa na yi a saman kaina lokaci ɗaya.
"Madam ina kwana."
Sai na juya na yi masa kallo ɗaya na ɗauke kaina na daɗe ban gan shi ba tun daren ranar da muka yi faɗa da shi.
"Ina kwana."
.
Na mayar masa da gaisuwan shi kamar ba na so, na kuma cigaba da aikina na ma manta da wanzuwar shi a wajen ya gaji da tsayuwa ya ga ko kallo bai isheni ba sai shi ne da kan shi ya gaji ya ce." Madam ko zan samu shayin nan na mganin mura? Mura ta kamani tun jiya."
Ya faɗa ya na jan hanci ko juyowa ban yi ba na ce" Za a kawo."
Daga haka na isa gaban gas na kunna ina ɗora ƙaramar tukunya gajiya ya yi da tsayuwa ya kama gaban shi, ni kuma na raka shi da tsaki ni yanzu Yallaɓai ya fita kaina tunda ya gama ba ni mamaki ya yi min abin da ban taɓa tunani ba ko da ya ba ni haƙuri zai yi wahala na manta kalaman shi a kaina.
Ina cikin dafa masa shayin ne sai ga Marwa na kalleta ina faɗin" Sannu sai yau? Tun jiya ina ta jiran ki. Baban ki fa ya ce Umarni kawai zan ba da za ki zo "
Tana dariya ta ce" Umma jiya aikin dare na yi sai yau da safe na dawo gida."
"To kin ja ma kanki ba yau za ki tafi ba."
"Daman sai gobe."
Kallonta na yi kafin na ce" Sai dai jibi ko?
"Umma jibi ina da aikin Safe ne."
"Sai ki tafi daga nan ɗin ko?
Sai ta yi shuru ta na dariya ni kuma ina hararanta. Kafin ta cire Hijabin da ta shigo da shi na ce tsaya na ta ce shayin nan ta miƙa ma Yallaɓai da ta wuto su a falo, ita na ba ma shayin ta kai masa sai ga shi ta dawo ta na ce min" Umma ɗayan baƙon fa ya ce shi ina na shi Shayin?
Ina dariya na ce ta juye sauran a fulas ƙarami ta ɗau Mug ta kai musu falon daman akwai siga a can saman dining za su yi amfani da shi.
Zuwan Marwa ya sa na koma na zauna ta karɓe ni daga aiki ina falo ina duba wayata ana ta siyan Hijabai tun da salla ta karato bai fi saura kwana goma ya rage ba, ina nan zaune Yallaɓai ya leƙo ya na cewa na zo mu yi sallama Kawu zai