Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   45 / 48

132K to 135K   out of 141.5K words

haka ma  ta na nan da yaron ta mai suna Abdallah ta na garin Rano sannan ta na aiki a asibitin Gwammati na garin Rano, bayan ita kuma a wannan shekaran muka yi bikin Anti ƴar wajen ya Murja ta yi aure anan garin Kano. Bayan na ta kuma muka yi na Jawahir da Musbahu a rana ɗaya. Jawahir ta na kaduna Musbahu kuma a garin Kano ya ke zaune a kuma gidan kan shi tun da shi ne Manaja na kamfanin Yallaɓai sannan shi ke rike da gidajen bulo ɗin su gabaɗaya a ƙarkashinshi suke, Adnan kuma ya na nan BUK ya na master ɗin shi. Datti ma ya gama kasu ya na Abuja gidan Ya Auwal ya na aiki da wani kamfanin littafai bai yi aure ba. An yi rashe rashe tun da har Baaba sani mun rasa daga yashe. Bangaren Yallaɓai kuma sun rasa Innayi sai dai fatan Allah ya yi musu rahama.

  A yanzu da na ke da matakin shekaru talatin da bakwai a duniya. Yallaɓai kam ya haura arba'in ya kama gidan Hamsin amma daga ni har shi in ba mun faɗi shekarun ba, ba mai sanin haka saboda mun mori jiki sannan ga jin daɗi musamman shi da ya ƙara zama babban mutum sosai. Ni kuma har gobe ban daina gyara jikina ba, har kuma zuwa lokacin ban ƙara samun ciki ba shekaru goma kenan tun ina mganin asibitin da na gargajiya har daga ƙarshe na haƙura na yi shekara ban ƙara shan wani mgani ba, daga na hausan har na gargajiya. Na fauwalama Allah duka lamuran shi duk kuma abin da ya yi min to dai-dai ne. Ba zan ce a shekarun ukun nan da suka gabata ba mu yi ta samun matsala da Yallaɓai ba mun samu sosai, sai dai wani abun kana barin shi ya wuce domin a zauna lafiya. Tsakanina da Gimbiya sama sama kamar baya ta na gidanta ina gidana amma duk da haka bai hana ta makirci da kissa ba.

Tun haihuwan Khalipa na fahimci ta na da son kanta sannan makira ce. Ita ta ɗauka ni ban iya makircin ba ne shi ya sa ba na yi mata. Na iya kawai dai ni ina zaune da ita da zuciya ɗaya ne. Ina mamakin kishin da ta ke nunawa a kan Yallaɓai ta manta ni ce matar shi ta farko daga baya ya aureta amma yadda ta ke nunawa kamar ta fi ni kishi ne. Tun da khalipa ya isa fara tafiya ko na ce ya fara cin abinci duk in da Yallaɓai zai je tare su ke zuwa kamar ɗan gwal. Da ya zo ya fara tafiya kusan in dai Yallaɓai na gidana shima ya na gidan tare da uban. A cewar shi ya saba da shi ko ita Gimbiyar bai saba da ita kamar yadda ya saba da Yallaɓai ba shi ya sa ko yaye a gidana ya yi rabin yayen shi, da sunan ga su Jidda sannan kuma Khalipa ba ya kwana a kusa da kowa sai a jikin Baban shi. Kawai dai a takaice regular costumer ne shi a gidana. In Yallaɓai na gidana to shima ya na tare da shi in kuma ya na wajen Gimbiya to shima ya na can. Abin haushi ma da takaici sai a tsakiyarmu ya ke barci, ko an kai shi ɗaki su Jidda ya na barci da ya farka muna cikin barci za mu ji kukan shi dole sai a jikin uban ko a kusa da shi zai kwanta. Ni lokacin da na reni ƴaƴana ni kaɗai na sha wahalata amma ni gashi ta haifa ta bar ni ina shan wahala,  ga shi yaron ba ya jin mgana ga mugun wasa ga ƙarfin tsiya har Baby yanzu gagaranta ɗauka ya ke yi. Sai Jidda tun da ita kam ta zama ƴan mata kusan shekaru biyu da fara period ɗin ta. In na yi magana Yallaɓai ba ya bi ta kai sai ya ce yaro ne duk ranar da ya ke gidana tare da yaron nan muke kwana a kan gado ko ƴaƴana ba su yi min haka ba, sannan mgana kaɗan in na yi a kan Khalipa sai Yallaɓai ya juya min mgana ya ta so min shi ya sa na saka masa ido a yanzu haka a cikin yanayin da muke kenan na gaji matuƙa ba ni da lokacin sakewa da mijina Khalipa na naniƙe da shi wanka ne kaɗai ba ya bin sa amma ko masallaci tare su ke zuwa.

A lokacin da ya dawo daga Saudiya na ga uwar tsaraban kayan wasan da ya kwaso musu sai da na yi magana da cewa Yallabai hala dai ba ibada ya kai ka saudiya ba. Siyan kayan wasa ka je yi ko?
Ai daga wannan maganar ya fara min masifa wai ina mgana ba ta taunawa ko Baby ai ba za ta yi wannan mganar ba, sai da na yi nadamar yi masa mgana kwana biyu ya yi ya na gaba da ni. Daga faɗin gaskiya domin jaka ce shaƙe da kayan wasa ba dole na yi tunanin daman abin da ya kai sa ba kenan ni kaina gidana ga su nan da yawa ballantana gidansu da Jidda ta ce min ɗaki ne guda da kayan wasa na khalipa da Anwar. Na yi ta haƙuri ina kauda kaina yanzu haka Gimbiya sunan da su  Anty Bahijja ke kiranta da shi shi ne Uwar maza. Shekaranjiya ma mun haɗu gidan Naja suna ta haihu ana ta yi mata kirari da Giwar gidan Tafida uwar maza mace mai kashin arziƙi domin a cewarsu tun da Tafida ya aure ta ya ke ta ganin buɗi na arziƙi ni dai ban tanka ba tun da daman ai tun bayan faruwan lamarin nan sun sanni na san su, shi ya sa in suna abin su ba na biye musu suma kuma sai dai habaici da shakuɓe amma ba sa yi da ni kai tsaye.

Munnira ce ma ta ce ita uwar mata ba uwa ba ce? Anty Maimuna ta ce uwa ce amma uwar maza ita ce da gida. Sai da muna adaidaita za mu tafi gida ni da Hauwa bayan mun rabu da Munnira ta ke min mgana wai kar na damu da mganganunsu ni ko sai na ce yau a ka fara? ai sun daɗe suna fadin haka ban taɓa nuna na damu ba, ita kuma Gimbiya ta na hura hamci ta na iyayi ita matar arziƙi ni ko na ce in ma tsiyar ce to Yallaɓai ne ya shafa min tun da ni kam da arziƙina ya aure ni ya tsiyata ni yanzu da ya samu duniya sai suka manta. Yanayin rayuwa ya sa na daina ma damuwa da wasu manganganun saboda ai jiya ba yau ba ne.  Kuma girma ya ƙara kamani da ya sa lamarin ya zame min jiki ba komai in na ji ko na gani na ke mgana ba amma tabbas an kusa kai ni bango akan lamarin Khalipa na zura ido na yi kara na yi kawaicin duk a banza ko ƴaƴana suna tasawa na ke daina kwana da su ballantana ɗan kishiya. A raina na ji ko me zai faru sai dai ya faru amma sai na yi ma Yallaɓai mgana.

****

Tiolet na shiga na kama ruwa sannan na fita falo. Jidda ce kawai ke gida ba ta jin daɗi Baby kuma ta tafi Tahfeez. Falon su Khalipa duk ya kama kaca kaca da shi ya watso min fillows ɗin kujera a ƙasa. Jidda na falon ta na karatu a ipad ɗinta tun da Abbansu ya ce a wannan shekaran za ta yi jarabawar fita da Jamb.

"Jidda kina zaune Khalipa ya hautsina min falo haka?

Sai ta ɗago ta na kallona kafin ta yatsina fuska ta na faɗin" Na gaji da gyarawa ne Umma da na gyara sai ya ƙara watso su."
Hararanta na yi kafin na ce" To ni ne kike so na kwashe? Ina mgana na ji ina taka ruwa na fara mata faɗan ta bari ya jiƙa min gida sai ta ce wai ita ba ta sani ba.

"To ke za ki yi min gyara gidan  ko yarinya."

Na faɗa ina shiga falon Yallaɓai nan ko sai da na kusa kuka ya watsa duka kujerun dining sannan na iske shi ya na feshe kujeru da ruwan bindigarsa ai saboda takaici ban san lokacin da na masa tsawa ba, kuma ga shi ba shi da tsoro, ke gizau Jidda na ƙwalama kira ta na zuwa na ce ta natsar da shi kuma ta gyara min gidana ko ranta ya ɓaci.

"Umma wallahi na hana shi ya ƙi bari ne."

Na wuce ina mai jan tsaki kafin na ce" Wannan ke ya shafa. Ni dai na fito na ga gidana ya yi tsab ya na tashin ƙamshi."
Kitchen na shiga na haɗa tea daman akwai ruwa a fulas na dawo falon na zauna. Ina jin su ta na gyarawa ya na ƙara ɓatawa ita kuma ga shi ba ta da zafi shi ya sa ya ke ba ta wahala da Baby ce da yanzu an fara kokuwa. Da na ga ba zai bari ba sai na fito da bulalata na na nusa masa na ce ko ya natsu ko na zane shi, bai ko natsun ba sai da na chau la masa biyu sannan ya fara kuka daga nan sai barci shi ne fa Jidda ta samu ta yi min gyaran gidan. Ita ba ruwanta ta na son aiki ga wacce sai na yi da gaske ta ke aiki nan Baby in na yi magana sai Yallaɓai ya ce ai gado ta yi kuma daman an ce magaji ai mafiyi ina jin haka zan yi shuru. Allah sarki Saude ita na ke tunawa in su Jidda na makaranta aiki ya yi min yawa. Tuni an yi mata aure shekara ɗaya kenan a jigawa yanzu haka tsohon ciki gare ta. Duka masu zuwa su tayani aiki yanzu suma sun kama ɗaku nan kansu. Jidda dai ke ƙoƙari domin in dai ta na gida ba na aiki girki kam ba abin da ban koya mata ba.

Yau Yallaɓai a gidana ya ke amma gobe zai koma gidan Gimbiya. Sai dare ya shigo gidan ya ce min ya ɗan tsaya a Gwammaja ne, da ya ke Nene yanzu ta samu lafiya sai dai ɗan ciwon kafa da ke matsa mata lokaci bayan lokaci haka. Ko da ya dawo Khalipa ya yi barci amma kamar ana masa wahayi da ya ji muryan ubab zai tashi nan fa ya maƙale masa har cikin gaurancinsa ya ke faɗa ma uban wai na dake shi, shi kuma ya ce ka yi ma Umma laifi kenan ko?

"Ɓarna ya yi min bayan na saka Jidda na gyarawa ya ƙi barin ta ta yi aiki shi ne na yi masa bulala biyu."

"Kai sarkin rigima ba za ka daina yi ma Umma ɓarna ba ko?

Ya faɗa ya na shafa kumatunsa. Kallon Yallaɓai kawai na ke yi in ya na wani abun, faɗa ya ke yi itama Gimbiya haka ta ke fama da shi. A raina na ce muna fama dai ni fa sai dai na bar Yallaɓai da Khalipa domin a daran ma wasa suka fara yaron na bin shi da bindiga shi kuma ya na ɓoyewa shi da Baby saboda ita ce mai son wasa. Jidda kam ba ruwanta da wannan shanshanci shi ya sa na ke sonta ta na da aji sosai.

Ɗaki na koma na yi kwanciya ta ban ma san shigowarsa ba, sai cikin dare na farka na gan shi maƙale da Khalipa wani abu ya kawo min wuya amma ban yi wani abu ba, ji na yi kamar na koma ɗayan ɗakin na kwana amma sai na fasa. Da safe muna karyawa bayan yara sun tafi makaranta. Yallaɓai ya siya sabuwar mota wata bakar benz tsohuwar tashi kuma ta na hannun salisu shi ke kai yara makaranta a ciki sai cefane.

"Daughter ta ce a saka Khalipa a makaranta na ce laa ba yanzu baa"

Kallon shi na yi lokacin ina tura dankalin a bakina. Ko a yanzun ma Khalipan na kan jikin shi ya na bashi dankalin a baki, ko fa fita Yallabai zai yi in ba da shi zai fita sai da dubara in kuma ya duba bai gan shi ba haka zai ta rigima to ya riga ya sabar masa.

"Gaskiya kam a saka shi a Baby cllas ba."

Na faɗa ina haɗiye abin da ke bakina.
Amma sai Yallaɓai ya ce ba yanzu ba sai ya shekara biyar.

"To me ya sa? Na ga dai  da bakin shi ko?
Kuma ko Baby ta na da shekara huɗu ka saka ta a makaranta."

"Da  Khalipa da Baby ba ɗaya suke ba. Shi fa ya shaƙu da ni kina tunanin zai zauna a makaranta?

Wani kallo na wurga masa kafin na ce" Tabbas ba ɗaya suke ba na ga alama."
Daga haka ban ƙara kula sa ba har ya gama mganganun sa. Tare suka fita da Khalipa ya ce zai kai shi gida a raina na ce a gayas daman na gaji ina so na kwanta. Bayan kwana biyu da ya dawo gidana bai zo da Khalipa fa a cewarsa uwar ce ta ce ba zai biyo shi ba.

"Ta ce wai ana takura miki. Ni kuma na ce mata duk ɗaya ne da nan ɗin da can duk in da Khalipa ya ke so zai zauna."

Kallon musulunci ma bai samu ba ya gama gyaran zencen sa ya yi shuru. Da safe kuma again muna ƙaryawa ya fara isa ta da labarin shagon Gimbiya na yi masa kasaƙe kawai ina jin sa kuma ina kallon shi.

"Shagon ma fa ta ce ya yi kaɗan kaya ba sa wata suke ƙarewa yanzu fa har jiran oder ta ke yi "

"Uhm Allah ya sa albarka."

Na faɗa ina son kauda mganar amma ina shi a dole sai ya faɗa min.

"Ina gaya miki ana siya kayan ta sosai duk abokaina da abokan kasuwancina wajenta suke ma matan su siyayya."

"Ka kyauta Marketing manager."

Na watsa masa mgana amma sai na ga ya yi dariya kafin ya ce" Haka Daugther ta ce ta naɗa ni markerting manager a shagon ta na iya talla."
Kamar wani shashasha ya na ta dariya ji na yi kamar ina make sa da kofin hannuna amma sai na basar gani na yi ya dameni abu kaɗan ya ce Daugther daman ni sunan nan wallahi ya daɗe ya na ba ni haushi kawai yau na ce bari na yi masa mgana.

"Yallaɓai kana da abin mamaki."

"Na me fa?

Ya tambaya ya na kallona.

"Ka auri mace har ka yi mata ciki ta haihu sau biyu amma ka na ta wani kiranta da sunan Daugther don Allah miye ma'anar wannan sunan? Ƴa? To kai yarka daman ka aura ka ke yi ma ciki tana haihuwa?

"Ban gane ba"

Ya faɗa bayan ya rage fara'aran fuskar shi.

"Ka duk gane abin da na ke nufi."

"To sunan Daugther ɗin ke kuma ya tsaya miki a rai?
Kike kishi da sunan?

Ya faɗa ya na kallona kafin in samu zarafin mgana a fusace ya cigaba da faɗin" Kin ba ni mamaki me ya sa yanzu kwata kwata ba ki tauna mgana in za ki faɗa min ne? Ai kin san matsayin ta a wajena da matsayin sunan tun kafim mu yi aure haka na ke kiranta kuma ya kama bakina. Sai a ka ce kuma haramun ne don ta na matata kar na ce mata Daugther?

"Ba haka na ke nufi ba."

Na faɗa ina ƙoƙarin kare kaina ganin ya taso min

"Haka kike nufi mana. Sai an yi magana ki ce ke kin girma kaza da kaza, kin girman ne kike yin abin da kike yi? Sunan mai sai kin yi masa wata fassaran? Ashe ita Allah ya jiƙanta ba domin ta mutu ba da sai ta haɗiye zuciya ta mutu. Wani irin suna ne ban kira ki da shi a gaban ta ba? Wallahi ba ta taɓa mgana ko ta nuna rashin jin daɗin ba, ban taɓa kiran ta da sunan soyayya ba ke fa! Ba sunan ƙaunar da ban kiraki da shi ba karshen ta dai to ke ɗin ce na ke kira abar ƙaunata a gaban ta, ba ta taɓa mgana ba sai ke? Don ina kiran ta Daugther? Ba ki son ji ne? To sai dai ki toshe kunnuwanki domin ba zan iya daina kiran ta da wannan sunan ba."

  "Ka yi haƙuri."

Na samu kaina da furtawa a cikin raina ina mai nadaman fara yi masa mganar. Daga mgana sai kawai cibi ya zama ƙari.

"Ba maganar haƙuri ba ce. Ki gyara a matsayin ki na babba kar ki yi abin da za ta ji ko ta gani girman ki ya zube a wajen ta."

Ya na gama faɗin haka ya miƙe a fusace ya shige ciki sai ga shi ya dawo da key ɗin mota daman a shirye ya ke ya fice ya na faɗin.

"Sai na dawo."

"A dawo lafiyan"

Ko amsa ni bai yi ba ina jin tashin motarsa da ya dawo ma zai rufe get ɗin da ƙarfi ya tura shi har sai da ina daga falo na ji wani garam! Na riƙe baki ina faɗin ikon Allah!

*Janafty*
*TKG020C20c*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX


Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

Sama da mintina goma da fitar Yallaɓai amma na kasa ko da motsa ɗan yatsa na saboda da al'ajabi daga mgana sai cibi ya zama ƙari.? Har ya na min wani gorin ya na kirana Abar ƙaunarsa ni na saka shi? Ban da ma gulma yaushe ne ya fara kirana da wannan sunan? Ba sai da ya yo min kishiya ba ne ya fara min sanaben kirana da sunaye kala kala. Sannan in zai kirani da wannan sunan sai in zai min yaudaran su na maza ko ya na so ya raina min wayau amma shi ne har ya na yi min

45 / 48