Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   19 / 48

54K to 57K   out of 141.5K words

ɗauko Qur'ani mu yi karatu. Ni ce fa har wajen bakwai na safe a ɗakin yaran sai da na yi musu karatu gabaɗaya har Marwa sannan muka shiga kitchen tun da ta ce min yau za ta je asibiti, ta re da saude mu uku muka ɗan gyara kitchen din sannan na ce su fere doya a soya sai kunu da za a dama a yi ƙosai Rahila ce ta fara tasowa ita ta karɓe ni  daman kunin Saude na gyaran wake Marwa na fere doya.

  Daga baya har Sameena da Farida sun fito sai aka kama gabaɗaya aikin, kafin lokaci an gama tunda hannun da yawa. Mai son shan kuni ya sha in tea ne ga shi nan in ƙosai ne ga shi nan, in kuma doya ne duk dai ga shi nan bayan an gama karyawa sai suka gyara min gidan su Rahila kenan yara kuma Saude ta yi musu wanka su Jidda kuma da suke manya suka yi ma kansu. Ni kaina tun safe na yi wanka na saka cikin sabbin atamfofina, zuwa azahar kowa ya yi wanka ya shirya har na fara kewa aka ce baƙo raba duk yau ɗin za su ta fi su bar ni  ni kaɗai daɗin abin ma yara sun samu hutun makaranta kaɗaicin ba zai yi min yawa ba.

Da rana Tuwo aka yi miyar agushi ina da sauran manshanu sai aka juye shi sai ƙashin naman ragon ragowan na jiya aka yi amfani da shi, akwai ma ragowan waina da safe Rahila ta ɗumama ta saka masa siga ta sha da kuni da safe, alele daman ragowan balaraba na kwashe ma sauran da za ta wuce gida na ce ta kaima yara ban bari abinci ya kwanan min a gida ba. Sai da aka ci abincin rana sannan Farida ta yi shirin tafiya tun da ta ce Tariq ya kira ta ya ce ta je Gwammaja daga can za su wuce Sameena ma can Gwamnajan za ta je shi ya sa suka shirya za su tafi tare. Na yi musu godiya ƙwarai da karamci na yi musu rakiya har haraba gidan muka rumgume juna ɗaya bayan ɗaya.

"Na gode sosai. Allah ya mai da ku gidajen ku lafiya."

"Haba. Bakomai a yi ta dai hakuri a kauda kai Allah ya zaunar da ku lafiya ya kaɗe fitina."

Farida ke faɗin haka ni kuma ina amsawa da Amin Amin, Sameena kuma hannuwana ta rike kafin ta ce" Matar Baba ni fa ba na jin ki, sannan Baba ma ya na sonki zuwan wata ba zai rage ki da komai ba in sha Allahu." Sai na yi mata mirmishi kafin na gyaɗa kai ina faɗin in sha Allahu.
Ga su dai suna na kusa da Gimbiya amma ni sun nuna min ƙauna ƙwarai kuma na yi ta musu godiya na kuma yaba da karamcin su.

Sun tafi ba daɗewa sai ga Hauwa da Munnira suka ce suma daga Gwammaja su ke, suka leƙo ni kafin su wuce gida har ina musu tsiyan ko daga gidan Amarya suke?
Munnira na tabe baki ta ce min" Wani gidan Amaryan! Allah ya kyauta. Mu ba ma mu ce za mu je ba, masu zuwa dai sun je tun jiya yau ma da na ji wasu na mganar komawa Anty Bahijja ta hana ta ce a bar Amarya da ango su huta kar wanda ya je domin ya dame su."

Cikin mamaki na ce" Topha. To su waye daman ke son zuwa?
"Can dai ahalinsu na Rano ne. Naja ce kawai aka ce za ta je itama sako za ta kai mata. Wai kar a dame su ki ji fa."
Munnira ta faɗa ta na kallona, muna zaune daman a falon yara ne sai kawai na jinjina kai kafin na ce" Ba shakka." Hauwa dai na gefe sai ta muskuta kafin ta ce" Su Ayshe tun safe suka koma ɗazu da muka yi waya ta ce min tun jiya Anty Bahijja ta ce duk wanda ke son ganin gidan Amarya ya je a jiya domin in Ango ya shiga ɗaki ba mai yi musu sintiri a dame su. Na ce kamar wata budurwa? Anty Bahijja akwai kambama abu wallahi."

Ina ta dai kallonsu amma ban yi magana ba, Munnira ta ja tsaki kafin ta ce" Ita ce uwar Gimbiyar ba ki ga alama ba? Gani na yi hiran ta su za ta iya dawo min da damuwar zuciyata ya sa na katse hiran su da tambayan ko a zubo abinci? Sai suka ce sun ƙoshi amma ƙila kafin su tafi su ɗan taba tunda tuwo ne, muna tare da su har Yamma, suna ma gidan Ya Muntari ya zo ɗaukan Rahila da yara. Na matsa masa sai da ya shigo har falon Yallaɓai muka gaisa na kawo masa ruwa ya sha har su Jidda suka zo wajen sa suna masa hira ya na biye musu, shi daman akwai son yara in dai yara ne haka za ka gan shi da su ya na biye musu ba ruwan shi.

"Ashe kuma kin samu abokiyar zama?

Ya faɗa ya na kallona, kaina na ƙasa sai na gyaɗa masa kai.
"To sai haƙuri Allah ya zaunar da ku lafiya ban da dai ɗaukan zuga."
Na ce in sha Allahu, har ya na min tsiya wai Allah ya ƙara min haƙuri domin ya san halina ba ni da haƙuri.

"Kai Ya Muntari."

Na faɗa ina ƴar dariya, shima dariyan ya ke shi da Rahila ya na ce min ai ya san halina, kamar kar Rahila ta tafi amma ina ji ina gani ta wuce gida ita da yara ni da Amina har waje muka raka su, da Amina ta so ta je Ɗorayi ta kwana yau na marairaice na ce ta bari gobe da safe don Allah sannan ta yarda ta zauna na ce sai ma ta tafi tare da Saude kawai. Su ma su Hauwa suna yin sallar mangariba suka yi min sallama suka wuce mun rabu akan zan bi su  har gida na yi musu bangajiya sai gida ya rage daga ni sai Amina sai Saude sai yara.

Nima sallar mangariban na yi sannan na natsu a ɗaki wayata tun safe ta na saman gado ban bi ta kanta ba sai da na gama azkar sannan na tube hijabin jikina na yi zaune gefen gado sannan na jawo wayar ina ganin an kirani, da ya ke a silent na saka wayar kuma ban bi ta kanta ba. 7 missed calls aka yi min Yallaɓai huɗu ya yi min sai Anty Zabba da ta yi min guda biyu sai wata lamba da ban san ko ta wacece ba sannan ga sako na an turamin tun kafin na buɗe jikina ya ba ni Yallaɓai ne shi ya sa ban yi ma rawan jikin buɗewa ba, sai da na kira Anty Zabba muka yi magana ita ke faɗa min ta ga hotunammu ni da Yallaɓai su Suwaiba sun ɗora a waya mun sha kyau.

"Sadiya gaskiya kin burgeni ba domin kar a ce na so ki na ƙi amarya ba. Da na ce ko da ranar auranta ne amma kin fita kyau."

Ina ta dariya na ce" Kin ko so ni Anty Zabba. Amma ina ni na fita kyau?
"Allah da gaske na ke yi. Kun yi kyau sossi dukkan ku. Allah ya ba ku zaman lafiya da hakuri da juna."
Ba mu jima muna mgana ba muka yi sallama, ni ban ma da hotunan ban ko hau online ɗin ba ballatana in gani, ba na ma som hawa domin na san sun ta ɗora na Gimbiya da Yallabai ni kuma ba na son ganin abin da zai ɓata min rai shi ya sa na haƙura da kunna data sai ƙura ta lafa.

Sai da na kira lambar da aka kirani na ga ba a ɗauka ba sannan na duba saƙon Yallaɓai, saƙon har guda biyu ɗaya da safe ne ya turomin wajajen goma na safe ɗayan kuma da yamma nan ne, kamar yadda kiran na shi suke a jere. Biyu da safe biyu nan kuma da yamma nan ne ya sake kira.

"Good morning My Darling Wife! Kun ta shi lafiya? Ina kewar ku. Ki gaida mini da Jidda da Baby."

Sai Ɗayan kuma cewa ya yi.

"Sadiya ta kuna lafiya ko? Gobe in zo na duba ku? Na kira ba ki ɗauka ba ko har yanzu akwai baƙi ne a gidan?

Hmm! Kawai na ce a ƙasan maƙogwaaro na saboda na kasa ma mgana. Wai My Darling Wife Yallaɓai ne har da sauya min suna mai daɗi haka, wai munafunci irin na ɗa Namiji ya kwana da wata macen amma yana ce min wai ya yi kewar mu. Sannan tambayarsa ya zo ya duba mu sai da na ja mata tsaƙi, to yaushe namiji yaushe ya fara neman izinin in zai yi wani abu? Lokacin da ya yi auran ai bai gaya min ba. Sai na zuwa duba mu ne zai turo min wani munafunci, da na so na yi banza da saƙonni ne sai na fasa na rubuta masa gajeren saƙo ina yi ina hararan wayar kamar shi ne a cikin ta.

"Muna nan lafiya. A'a ka yi zaman ka kawai ba gobe ba."

Na yi mamakin yadda daga tura saƙo ko mintina goma ba a yi ba sai ga amsar shi kamar wayar ta na hannun shi ne.

"To sai yaushe?

Haka kawai ya ce, sai kawai na ga kamar so ya ke yi ya yi wasa da hankalina. Nan take na saka wayata a filght mode na dankwafar da wayar ina girgiza kafa, har da su kaɗa harshe takaici ya isheni ni kaɗai. Ina cikin wannan halin Amina ta shigo sai na ɗan saki, kamar ta san in na zauna ni kaɗai tunani zai iya yi mun kutse zaman ta a kusa da ni ya sa sai na maida hankalina kanta muna ta ɗan taɓa hira a kan dai yan gidanmu ne.

"Ya Sadiya Ma'u ta ba ni mamaki. Ni fa in kika ce munafuka ce in yi ta mamakinta."

Mirmishin takaici na yi kafin na ce" Uhm ai wanda bai san halinta ba zai taɓa yarda munafuka ba ce. Ta iya kissa fuska biyu gare ta shi ya sa."

Amina ta jinjina kai kafin ta ce" Na gani kuwa. Ai da Ya Aina ta mata mgana sai ta fara kuka ta na cewa ita ba da wata manufa ta je Gwammaja ba. "
Ina dariya na ce" To ko da wata manufar ne za ta nuna ne? Makira ce fa Ma'u ina faɗa muku ba ku yarda. Uhm! Shi ya sa ni ban taɓa son Ma'u ba halayyanta ba su da kyau sam"

Sai Amina ta ja numfashi kafin ta ce" Uhm ai na gani yanzu. Ni dai fatana kar ta je ta rika bin Amaryan Yallaɓai ta rikita muku zama tunda ta shige ma yayar ta sa."
"Za ta iya aikata komai domin ta ga ni na yi ƙasa. Amma kuma komai za ta yi na fi karfinta ni Allah na ce ita kuma tunda makirci ta saka ma gaba sai dai ya ƙare a kanta."

"Amin wallahi kuwa ah."

Amina ta faɗa har ta na riƙe baki ita fa Ma'u ce ke ba ta mamaki, ni ko na ce ta ma daina mamaki Ma'u ta wuce tunanin su wallahi nan na ke faɗa mata wasu sirrukan nawa ita ke faɗa ma Anty Bahijja in muka haɗu ta rika zagina ta yada min mgana na ƙarishe da cewa" Ina da ta cewa ne Amina? Ƴar'uwata ce ta ba da ni fa, shi ya sa na ke addu'an Allah ya shiga tsakanina da Ma'u duk mugun nufin ta ya koma kanta."

"Amin in sha Allahu."

Amina ta faɗa lokaci ɗaya ta na cigaba da faɗin" Ita fa abin da ya faru na rashin auran Ya Hamza ne ta riƙe a ranta shi ya sa ta ke jin haushin ki Ya Sadiya."
"Sai dai ko ta mutu amma Ya Hamza ya yi mata nisa. Kuma wallahi tallahi ba na nadaman abin da na yi har nan da gaban Abada Amina"
Na faɗa ina mai jadadda mganata sannan na ƙara da cewa" Ba ki lura ƙawarta Shema na ta ya ta ba. Ita kuma shegiya ta ki auru ai duk wanda ya ce tunkunyar wani ba za ta tafasa ba ina mai tabbatar miki da na shi ko ɗumi ba za ta yi ba. Kuma ko alaqarsu da Ma'u hali ne ya zo ɗaya amma in kin lura Ma'u ta fita wayau ita kuma har da kwaɗayi gani ta ke yi Ma'un na ba ta duniya ita kuma saboda mijinta na da kuɗi sai ta riƙa yi ma Shema'un abu kamar ita ce uwarta."

Na ƙarishe faɗa ina mai kallon Amina wacce ta jinjina kai kafin ta ce" Kwarai kuwa. Kamar raƙumi da alaqarsa haka Ma'u ke jan Shema."
Ƙwafa na yi kafin na ce" Gungun munafukai ai sai munafuncin su ya ci su in sha Allahu." Nan muka cigaba da hira har muka gangaro kan Ya Murja na ce ai ita wannan na daɗe da sanin yadda ta ɗauki Ma'u ba haka ta ɗauke mu ba, sannan kuma da ƙwaɗayin itama, wani cewa halina ne ba ta so duk mgana ce amma jiya ta ɗan samu muhallin afuwa acikin zuciyata a karon farko da ta gano Ma'u ba ta kyauta ba.

Sannan Ya Abubakar ma sai a hankali. Shima raƙumin ne sai abin da ya ga an karkata acan ya ke. Har neman fitan hayyacinsa ya ke yi in dai akan lamarin Ma'u ne.
Amina ta bushe da dariya kafin ta ce" Tsohuwar zuma ce Ya Sadiya "
Nima ina taya ta dariyan na ce" Shi ya sa wani lokacin na ke yi masa uzuri."
Mun daɗe muna hira har aka kira sallar isha'i sannan ta fita ta ce min za ta je falo ta yi kallo nima na ce in na idar da sallah zan fito.

Una ko idarwa na fito na iske suna kallon wani indian Movie a Bolloywood Kuchi kuchi hota hae. Ina son film ɗin tuni na zauna muna kallo har da Saude da Jidda Baby ta kwanta ita da Sultana ɗiyar Amina ƙarama, muna cikin kallon Amina ta je ta ɗumamo mana Tuwo muna ci muna ƙona hannu sannan muna kallo bayan mun gama muka kora da lemu da ruwa, mune har 11pm har sai da aka gama film ɗin nan sannan muka tashi har Jidda ba ta yi barci ba sai da a ka gama sannan muka kora su ɗaki, ni na tsaya na rage hasken duka ɗakunan na duba ko'ina sannan na je na kwanta na iske Amina ta yi shirin barci ta na kwance suna waya da mijinta sai na ba su waje na shiga Tiolet na kama ruwa na yi brush, ko da na fito sun gama wayar sai nima na yi shirin kwanciya na saka kayan barci muka kwanta, mun ɗan fara hira ba daɗe barci ya ɗaukeni ban ƙara sanin kaina ba sai huɗun asuba sannan na tashi na ɗauro alwala na yi nafilfilu, sai da a ka fara kiran sallar farko sanman na fita na ta da su Jidda. Dakyar na idar da sallar asuba saboda barci na cin idona na haye gado ba ni na tashi ba sai tara na safe.

Na iske gida ƙal an gyara ko'ina ya na tashin kamshi har sun karyawa Amina ta shirya sai tafiya Ɗorayi ita da Saude. Ina zama a saman kujera a falon su Jidda na ce" Ke Amina da sassafen nan? Kamar ana koran ki?
Amina na gyara ɗaurin ɗankwalinta ta ce" Yau fa zan koma kaduna Ya Sadiya gwara na je na gaida su Alhaji na ɗan zauna zuwa azahar haka."

"To tare da Dattin za ku koma?

Sai ta gyaɗa min kai, ya na iya duk da ba na son tafiyarta haka nan na yi shuru ina laifi an yi min kwana uku. Ni da yara sai rakiya har bakin get muna ɗaga musu Hannu Saude dai gobe ma za ta dawo. Sai ga shi mun dawo cikin gida mun yi tsuru ni da su. Zama kawai na yi a falo ina nazarin rayuwa. Yanzu yau kwanan Yallaɓai biyu ya na cikin garin nan amma ba ya tare da mu sai na ji kwalla sun kawo min amma na yi saurin mayarwa. Tea na ce Jidda ta haɗo min na ci da Dankalin da Amina ta soya da safe. Su daman sum yi wankansu ni ce bayan na gama na tashi na yo wanka yau ma ɗin sabuwat atamfa ta na saka, ban zauna a ɗaki ba fito wajen su Jidda saboda su ɗeɓe min kewa. Baby ta ɗauke mana hankali da rawan drama ɗin da suka yi a makaranta ni da Jidda muna ta dariya.

Haka muka yinin mu kaɗai a gida sai can bayan La'asar Musbahu ya zo ya ce min Yallaɓai ne ya ce ya zo ya duba mu ina mirmiahi na ce" To me zai same mu? Ai dole ma mu saba tunda haka tafiyar za ta miƙa."
Ban tambaye shi ba da bakinsa ya ke faɗa min Yallaɓai bai fito Office ba kwana  biyu a raina na ce ya fito ya na can ya na cin amarcin sa, ya ɗan daɗe tunda har sai da ya tsaya ya ci abincin da na yi. Da zai tafi Baby sai ta fara rigiman wai ita sai ya kaita wajen Abba da Anty Gimbiya tun jiya ta fara min riginan Ina Abba na ce mata ya na gidan Anty Gimbiya ta ce sai ta je na ce ba yanzu ba, to jiyan ban biye mata ba sai yau ne bayan Tafiyan Musbahu yarinyar nan ta kafa min kuka da rigiman ita sai an kaita wajen Abba da Anty Gimbiya.

Yarinyar nan har da zan shiga salla sai da na yi ma ta jan ido akan ta tashi a saman cafet ɗin ta je ta yi salla amma ba ta ji ba. Har na idar da sallah na fito ta na wajen ta na min kukan banza ba tare da na yi mata mgana ba na koma ɗaki na ɗauko bulalar injin ce wacce na ke dukansu ne, ƙarama ce ma wannan ɗayar babban Yallaɓai ya dauke ta wai ba ta dukan mutane ba ne kamar zan doke dabbobi.

Ta na kwancen nan ta na rigima sai dai ta ji saukan bulala tuni ta

19 / 48