Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   35 / 48

102K to 105K   out of 141.5K words

ce kawai mu haɗu a can. Musamman na yi dambun shinkafa da zogale sanin Nene na so ya sa na diɓa na tafin mata da shi na je Ɗakin Nene cike da su Anty Bahijja kaf da ƴaƴanta Anty Maimuna Halima, Su Suwaiba ina gidan Hauwa ta ƙariso daman na iske Munnira.

Na shiga har ɗaki na gaida Nene na kuma kai mata Dambun da na zo da shi, ta karɓa ta yi godiya
Bayan na fito na shiga ɗakin da Gimbiya ke ciki, su Anty Bahijja na ciki da na yi sallama ba wacce ta amsa har ita Gimbiya sannan suna ganina suka yi shuru. Na gaishe su suka amsa min a daƙile, Gimbiya ina cewa ya jiki ko kallona ba ta yi ba a laɓanta ta amsa da.

"Da sauƙi."

"Allah ya ƙara lafiya."

"Amin."

Ta faɗa kamar ba ta so, sai jikina ya yi sanyi wulaƙanci ƙiri ƙiri suka yi min a ciki sai na fito na koma falo wajen su Hauwa ina ƙirkiran mirmishi ban nuna musu ma wani abu ya faru ba. muna zaune Anty Bahijja ta zo ta wuce ɗakin Nene ba jimawa sai ga shi ta fito da kulan Dambun da na kawo ma Nene muna ji Nene na ƙwala mata kira har sai da ta fito da kanta.

"Bahijja magana fa na ke yi miki."

"Nene ba za ki ci dambun nan ba fa Kawai ke ma ta saka miki mgani ta kashe mana ke kamar yadda ta so kashe abin da ke cikin Gimbiya. Tun da daman ita ɗin dangin asiri ne an saba shige shige."

"Bahijja ba na ce ki bar mganar nan ba ne?

Har ta na wani jijiyan wuya wajen faɗin" Nene to sai a ƙyaleta bayan kowa ya san gaskiya?
Ta faɗa ta na hararana ni fa da farko ban ma gane in da ta dosa ba ne sai da na ga ta na kallona sannan na fara dawo da abin da ya faru tun shigowata gidan nan, ban san lokacin da na miƙe ba haka ma su Hauwa saboda sai yanzu na gane in da Anty Bahijja ta dosa.

"Ban ga ne ba? A kan wa kike mgana?

Na faɗa ina kallonta sai kawai a gabana ta ɗaga kulan dambun ta sake shi ta a ƙasa murfin ya buɗe dambun ya Zube ƙasa idanuwana har sun ƙanƙance saboda ɓacin rai.

"Me kenan kika yi?

"Abin da idanuwanki suka gane miki."

Ta faɗa ta na kallona ai sai na ƙarisa gabanta Hauwa na riƙe min hannu na fizge ita kuma Munnira na faɗin"Subhanallah zubar da abinci me ya yi zafi Anty Bahijja?
Sai gabaɗaya har su Gimbiyar suka fffito Nene kuma faɗi ta ke yi" Sadiya ƙyaleta kin ji."

"Ke dai za ki faɗa min abin da kike nufi da zubar da abinci da na kawo. Sannan da mganganun da kike a kaina?waye zai kashe muku uwa? Sannan waye ya so kashe abin da ke cikin gimbiya? Sannan waye dangin asiri? Kar dai ki ce da ni ki ke ?

Na faɗa ina kallonta domin har duhu duhu na fara gani, ni za a yi ma tijara a bainar na si, ni za a ƙulla ma sheri a ci mutumcina da mutumcin dangina

"Na ce ina fatan ba da ni kike ba ko?

"Da ke ake ko kina da mgana ne?

Sai kawai na ƙura mata ido ina kallonta.

"Kika ce da ni kike? Ni ce mai yin asirin?

"Ke ce mana. Kin so zubar da cikin Gimbiya Allah ya fiki. Ai duk mun san komai. Mun san cewa Yayar mamanki asiri ta yi ma abokiyar zamanta kaikayi ya koma kan masheƙiya ta mutu cikin hauka, kowa ya san wannan labarin saboda asirinta ya tonu."

Mamaki ya hana ni mgana, idanuwana sun kawo ruwa cikin rawam murya na ce" A ina kika ji wannan labarin?

"A bakin da ba zai yi min ƙarya ba. Ma'u ce ta faɗa min ko za ta yi miki ƙarya ne?

"Ma'u."

Na maaimata sunan a saman laɓɓana.
Na kasa ma yin wani motai bakina na rawa na kasa mgana jikina ba in da baya rawa zuciyata ina jin kamar za ta faso ƙirjina ta fito saboda halin da na ke ciki.

"Ma'u fa?

Ma'u ƴar uwata da muka taso tare ita ce za ta zo dangin mijina ta yi min ƙazafi. Daman na san wannan bini binin na ta ba na lafiya ba ne. Sai ta ga na tozarta sannan hankalinta zai kwanta. Lalle ko akwai yaƙin duniya na uku tsakanina da Ma'u da duk wanda ke da hannu wajen yi min wannan mummunan ƙazafin.


*Janafty*
*TKG017*

"Bahijja kina mata wani sanyi sanyi ke Sadiya har mganin asirin suke kawo miki har gida. Gimbiya ta gan ki lokacin da ƙanwar mamanki ta kawo miki su har gida ko shima za ki ƙarya ta ne?

Kalaman Anty Maimuna suka buga min kai kamar an dake ni da ƙarfe sai da na ji kaina ya yi dum na ɗago ina kallonta ba bakina ba har idanuwana suna rawa ne a lokacin.

"Haba Anty Maimuna me ya sa haka?

Hauwa ta faɗa kamar ta yi kuka Munnira kuma sai ta hau tafa hannu ta na faɗin" Yanzu me Sadiya ta yi muku da za ku yi mata wannan mummunan ƙazafin?

Ni kuma Gimbiya na ke kallo cikin mamakinta ina so na tabbatar da gaske ita ce ta faɗi ta ga ƙanwar Mamana ta kawo min asiri? sai na ga ta kauda kaita alamun kenan da gaske ne. Sai kawai na ji na fara jijjiga ni kaɗai saboda ɓacin rai ranar da Inna Mariya ta zo kawo min mganin na dawo min a cikin idanuwa. Oh shi ya sa daman ta ce min ta ga ta na ta kallon mu? Kenan zargin ta kawo min asiri ta ke yi min tun da gashi har ta kawo labarin gaba. Kuma tunda ina shige shige kuma ina baƙin ciki da cikin da ke jikinta tun da ni ban taɓa haihuwa ba shi ya sa na ba ta mgani ta ci a abinci cikinta ya zube sai Allah ya fini asirina ya tonu cikin bai zube ba. Shi ne aka zauna aka tattauna gwara a turke ni a ci min mutumci, duk a lokaci ɗaya na gama hango abin da ya faru shi ya sa ban san na yi wata dariya ba sai da na ga ina yin ta cikin mamaki suke kallona Anty Bahijja na nuna da yatsa na ina faɗin.

"Ba a haifi wani ɗa namijin da zan kauce ma Allah saboda shi ba Bahijja"

"Kuma kika kaucen?

"Tunda kin yarda na kauce kuma na yi asirin tun da kin ce ni yar na gada ce, sannan ma ai an ce an ga tabbaci me kike jira Bahijja?
Na kira sunanta cikin tsawa kafin ta samu zarafin magana na zare mayafin jikina na ɗaure a kuguna ina faɗin

"Na ce tunda kin samu tabbaci me kike jira? Ba sai ki ɗau mataki ba Bahijja?

Na faɗa ina nuna ta da yatsa, Itama ta so min tana faɗin zan ko ga matakin da za ta ɗauka Hauwa da Munnira na rike ni ina fizgewa, ita ma Bahijja su Maimuna na riƙe ta Nene ma ta mgana ba wanda ya ji ta, Hayaniya ya sa har su Hajiya Iya da Maman farko sai da suka shigo lokacin Anty Bahijja na faɗin zan ga abin da zai faru.

"Ba abin da zan gani sai alheri me zan gani? Ya wuce ki saka ƙanin ki ya sake ni? To sai me? Kaina farau zawarci ke in ba ki saka shi ya yi min saki uku ba tabbas ke Bahijja ba ki haufu cikin uwarki da uban ki ba."

"Ke Sadiya ki yi shuru"

In ji Maman farko Suwaiba na ja na ita da su Hauwa ta na faɗin" Sadiya mu je mu je Sadiya."

"Ni kike zagi don uban ki Sadiya. Ni sa'ar ki ce?

"An zage ki ɗin ke uwata ce da ba za ki zagu ba? Har ni za ki yi ma kazafi na so zubar da ciki? To ni na zubar da cikin gimbiya na ci riban me? Ko haihuwa ce ban taɓa yi ba da za ta zame min baƙuwa? Amma ba laifin ki ba ne, laifin wacce ta faɗa miki ne. Amma ina so ki sani da ke da wacce ta faɗa miki na rantse da wanda raina ke hannun shi sai na yi ƙaran ku a wajen hukuma."

Daƙyar su Suwaiba suka fita da ni daga ɗakin Nene tana zagina ina zaginta. Itama ana riƙe ta tana cewa a sake ta, ta doke ni "Na ce ku sake ta mana ta zo ta ga in zan bugun mata ko wanda na ke aure bai isa ya doke ba ballantana ke banza a banza."

Itama ana riƙe ta tana fizgewa faɗi ta ke yi wai ai ba ƙarya aka yi min ba. Ina shige shige na wanke gaba na ba ma Tafida ya sha da ba ya ganin laifina, na shanye musu ɗan'uwa ko auran shi ma da Gimbiya Allah ne ya fi ƙarfina shi ya sa aka yi auren.

Ni ko na ce ita mijinta da yan'uwansa da ta shanye su sai abin da ta ce itama kenan gaban na na ta ta wanke ta ba shi ya sha kenan.?

Sai ta fara haƙilon faɗin" Ai mu kowa ya san zuru'ar mu ba mu da tambarin bin bokaye kuma ba a ji labarin wata cikin ahalin ta mutu cikin hauka ba."
Har ta na cewa na yi shige shige na na haɗa Kawu Abba da ɗiyar yayata saboda shima a shanye shi sai yadda aka ga dama dashi to na rubuta na ijiye ko ta ce bokan mu ya yi ƙarya Abba ba zai auri dangin masu asiri ba har ta na faɗin me aurena ya tsinana ma Tafida? Ni kuma na ce in ba ta saka ya sake ni ba, to ba ta haifu ba.

"Kuma dangin asirin su Kawu Abba ya gani ya ce ya na so in Allah ya haɗa ki raba in kin isa "

"Mata kin bi kwazzaba ma rayuwata a gidan aurene? Me na tsare miki? Zaman ki na ke yi! Ke da kika miƙe kafa a gidan na ki mijin wa ya takura miki? Ko kema shige shigen kike yi? Ke ki ce kina son ki ji daɗi a gidan wani da zuru'an wani amma kuma ke ce wata ba za ta zo na ku zuru'an ta ji daɗi ba? Ashe haka kike da son kan ki? To wallahi kin kure ni akan matakin da ba zan ɗauka ba tun da kin fito ta haka to nima zan fito miki ta bangaren da kika fito min ni da ke shege ka fasa Bahijja"

"Sadiya ba ki da kunya? Bahijja ba yayar mijin ki ba ce?

Anty Maimuna ke tare ni da faɗin haka har ta na shan gaba na, idanuwana sun rufe yadda bacin rai ke sarrafa zuciyata a wajen ko mari na ta yi sai na rama.

"Au ni ce ma ba ni da kunya daga ƙarshe kenan!? Ke ba ki ji duk mganganun da ta ke faɗa min ba ne! Me na yi mata? Kamar ta na jira. Ai ita ba ta kama girmanta na yayar mijina ba. Shi ya sa nima na bi girman nata na tattaka ni da ita wallahi sai mun cire renin da ke tsakanin juna."

Nene hankalinta ya tashi ta yi ta yi Bahijja ta yi shuru ba ta yi ba sai ta Umarci Maman farko da ta ja ni zuwa ɗakin ta tun da ita ma Bahijjan ta ƙi sauraranta har da Halima a masu jan Anty Bahijja amma ta na wani zillo ai nima na haukace musu ta na zagina ina zaginta itama.

Suwaiba da Maman farko da su Hauwa suka yi ta ja na Dakyar suka shiga dani ɗakin Maman farko na zame musu kamar mai aljanu sai da suka haɗa da rufe ƙofa Maman farko fadi ta ke yi" Innalillahi Sadiya ki yi shuru mana."

"Ku kira Tafida mana."

"Bari na kira shi"
Cewar Suwaiba ta na wucewa cikin uwar ɗaki."

"Ki yi hakuri Sadiya."

In ji Munnira ta na kuka ganin na zaune saman cafet ɗin tsakar ɗakin Hajiya iya na rushe da kuka kamar wata yarinya.

"Kazafin fa suka yi min? Sun ci mutumcina ni da zuru'ata?

"Ki yi haƙuri amma tabbas an ci zarafin ki."

In ji Maman farko Hauwa kuma faɗi ta ke yi" To daga ina wannan mganar ta fara fitowa?

"Ko da ga ina ne ko waye wallahi ba zan bar wannan mganar ba sai hukuma ta ƙwatomin haƙƙin ƙazafin da suka yi min."

Na faɗa ina jin ƙuna a ƙasan raina lokaci ya yi da zan tauna tsakuwa domin a ya ta ji tsoro.
Ba Ma'u ba ko Baaba ce sai na yi kararta ba Bahijja ba ko Nene ce ta yi min wannan ƙazafin sai na ji dalilinta wallahi. Ina kuka zuciya ta na wani irin zafi ina ma jin turarin zafin daga maƙoshina. Duk alherin da na yi ma Gimbiya ni ce za ta saka ma da sharri. Lalle na yarda da maganar hausawa da suka ce mai kishiya ba ya mutuwar Allah. To an kawo gabar da komai zai ƙare, zan yi abin da hankalin kowa zai koma jikinsa.

Jikina ba in da ba ya rawa kawai hasko kaina na ke yi na kama Ma'u na yi mata shaƙan da sai ta kusa zuwa lahira. Kawai sai gani na na yi na mike Munnira da Hauwa da suke ta jajanta lamarin suka mike suma, ganin na nufi hanyar barin falon na Maman farko ya sa Munnira ta ce.

"Sadiya ina za ki je?

Maganarta ya dawo da hankalin Maman farko a kan mu saboda itama wayarta ce a hannu ta na dannawa kamar neman wani ta ke yi a wayar.
Kuma daga ma nan dakin muna jiyo hargagin Anty Bahijja da zage zagen da ta ke yi.

"Ina kuma za ki je?

Suwaiba ta faɗa ta na fitowa daga ciki.

"Jakata zan ɗauko da mayafina "

Na faɗa muryata a shaƙe sai Maman farko ta ce ba zan fita ba Hauwa ta je ta ɗauko min,sai na yi shuru amma ban zauna ba ina tsaye ina karkaɗa jikina in ba sumar da Ma'u a yau ba, ina jin ba zan huce haushina ba kafin na haɗa da jami'an tsaro sai na bar mata taɓon da za ta kiyaye ni har gaban abada. Ko raba ɗayan biyu ba zan yi ba Ya Murja ta faɗa ma Ma'u maganar Marwa da Kawu ita kuma ta zo ta fesa ma uwarta ai kuma komai ya zo karshe daga yau zan kawo karshen makircinta a kaina.

Hauwa ta buɗe falon ta fita dai-dai lokacin da Maman farko ke faɗin" Kin samu Tafidan?

"E ya ce ga shi nan a kan hanya. Ya ma ce Halima ta kira shi ta faɗa masa ba ki ji yadda hankalin shi ya tashi ba na ce ya taho a hankali Sadiya ta na ɗakin ki mun rufe ta."

"Wayyo bawan Allah."

Maman farko ta faɗa cikin wani yanayi ni dai ina tsaye kiƙam na kasa zama. Sai ga Hauwa da Hajiya jiya sun shigo, jakata kawai Hauwa ta dauko min da sauri na karɓa wayata na ciki da kuɗi lokacin biyu na rana har ta gota daman sai da na yi azahar na fito daga gida.

"Sadiya ki yi hakuri. Kai wannan lamarin bai yi daɗi ba"

In ji Hajiya Iya, Mama ko faɗi ta ke yi" Ni Bahijjan ce ta ba ni mamaki ko gaya mata abu aka yi ta yarda ba ta da shaida?
Suwaiba ta karɓe da faɗin" Ita ko ke da shaida ba ku ji suna faɗin Gimbiya ta ce ta ga ƙanwar Maman Sadiya ta kawon mata magani ba! Itama ai ta haɗa fitina ita da wacce ta tari Bahijja da mganar wani tarihin wata ta mutu da hauka."

"Ma'u ce tare suka tashi da Sadiya. Da babansu da ita mahaiyar Ma'u uban su ɗaya uwar su ɗaya'

Hauwa ta faɗa sannan ta kora musu jawabin ta in da suka haɗu da Anty Bahijja.
Hajiya iya na salati Maman farko na yi, Suwaiba ta ce" Na gane ta wata yar fara haka. Amma ko ta yi asara wallahi."
Hankalinsu ya ɗauke da hiran su ba su san na zari mayafin da na gani a saman kujeran hanyar fita ba, na buɗe kofa na fice ko takalmi babu a kafata sai wani da na gani a ƙofar ɗakin na saka. Karan rufe kofa ta suka ji sannan suka far ga ga na fita sai suka biyo ni da gudu suna kiran sunana sun ɗauka ɗakin Nene zan koma sai su ka ga na fara sauka daga Bene Suwaiba da su Hauwa suka biyo bayana suna kiran sunana amma kamar wata hajijiya haka na rika sauri kamar zan kifa a haraba na ci karo da Mimisco ta iso itama ina ga kiranta aka yi. Har ta na tsayawa ta ɗauka zan yi mata mgana ne sai ta ga na wuce ta fuu kamar zan kifa.

"Sadiya tsaya. Ki tsaya na ce Sadiya."

Ko sauraranta ban yi ba mayafi a saman kafaɗa ina rike da ƙaramar jakata na fice da sauri kamar zan faɗi. Ba san ni ba ko sun biyo ni ni dai ina fita na fara sauri ina haɗa hanya har da gudu gudu ina hango bakin titi kawai na ga Motar Yallaɓai ta sha wo kwanar, yadda na dumfari in da zuciyata ke son zuwa ko waye ya tsaida ni ba zan tsaya ba ko da Alhajin mu ne kuwa.

Ya wuce ni, ni ma na wuce shi da sauri sai ga shi ya na dawowa da baya da baya a motar ya na kiran sunana bayan ya sauke gilashi ko jin sa ban yi ba ganin ya tsaya da motar yasa na saka gudu ina zuwa bakin titi na saka hannu mai adaidaita na zuwa ba kowa a ciki ya tsaya na shiga ciki da sauri na ce.

"Mu je Rijiyar zaki. Ka yi gudu da ni sosai."

Haka na faɗa ina haki, sai na juya baya ina ganin Yallaɓai ya koma mota ya yi riverse kenan ni zai biyo ni kuma ina azalzal ma mai adaidata da cewa ya yi sauri kawai hango kaina na ke yi a gaban Ma'u yadda zan makure ta sai ta kusa mutuwa ji na ke yi kamar zan iya yin bindiga ni kaɗai tsabar halin da na ke ciki na bakin ciki da ɓacin rai, kafin na fara kai su ƙara

35 / 48