Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   36 / 48

105K to 108K   out of 141.5K words

sai na ci uban Ma'u saboda in hukuma ta shiga ciki da farko ba zan samu damar cin uban ta dakyau ba gwara na fara nuna mata ina nan a Sadiyar da ta sani ban sauya ba kuma wallahi ni da zumunci da Ma'u har abada. Bahijja da sauran masu ta ya ta a kaina Yallaɓai zai shiga tsakanina da su, da ita kanta matarsa munafuka mai maida alheri da alheri sai an tuhuman min ita a gidan uban wa ta ga Inna Mariya ta kawo min asiri? Wallahi ko sama da ƙasa ne za ta haɗe ba zan bar maganar nan ba. Wato maganin nan da Inna Mariya ta kawo min ranar shi ne ta ke magana akai kenan lalle kar ka raina mutum duk wannan abubuwan da suka faru Ma'u ce sila ita ta ba ma Anty Bahijja daman cin zarafina. Shin wai da aka je asibiti an ce ne magani Gimbiyar ta sha? Ba ɗaya fa kawai ta tsane ne shi ya sa ta ke neman hanyar ci min mutumci, ban da haka ai ta san Gimbiyar na ta matsalan raunin mahaifa ko acan Abuja ma ta yi ɓari kuma ni da bakin Anty Bahijja na ji lokacin rasuwar mijin Gimbiyar ta na faɗin ai an nema mata maganin gargajiya na matsalan ciwon maran da ta ke fama da shi ke sa ta yi ɓari in ta samu ciki, amma yanzu sun manta Ma'u ta zo ta ɓata ni su kuma daman kamar su na jira sun far min da cin mutumci to komai ya zo ƙarshe daga wannan ba za a ƙara ba.

Muna tafe duk irin gudun da mai adaidaitan nan ya ke yi ni ba na gani, ji na ke yi kamar na karɓi tuƙin ƙila na isa in da na ke so a kan lokaci domin ji na ke yi kamar na yi tsuntsuwa na ganni a gaban Ma'u. Sai faman kiran wayata da ke cikin jaka ake yi amma ban bi ta kai ba, alokacin ni kaina ban san a yanayin da na ke ciki ba amma zan iya cewa tun da uwata ta haife ni ban taɓa jin irin ɓacin ran da na ke ji a yanzu ba. Ban taɓa jin nauyin ƙirji da na zuciya irin na wannan ranar ba, ban taɓa tsintar kaina a yayin fusata da fushi mai tsanani irin na yau ba. Abu ɗaya ke ƙara tafasa min zuciya in na tuna yau duk cin mutumcin da Anty Bahijja ta yi min ba kowa ya ba ta dama ba sai Ma'u. Ma'u fa ƴar'uwata ce da za ta iya tsaya min da jikinta da aljihunta in ta ga wani zai cutar da ni wani ko zai ci zarafina, amma sai gashi yau ita da kanta ta ba da damar da aka taru aka ci zarafina a ka zagi dangin mahaifiyata da ta ke ƙasa ba ta san ma abin da ke faruwa ba.

Ban san ina hawaye ba sai da na ji ɗigan su a saman hannuwana. Ban san ina kuka ba sai da na ji zuciyata na wani irin zafi, zafin kuma sosai kamar sheɗata za ta ɗauke min sai da na fara numfashi sama sama saboda halin da na ke ciki. Ina tuna labarin da ta je ta ba ma Anty Bahijja wani tsohon labari ne da mu muna yara ƙanana ma aka yi, da girman mu labari muka ji daga baya. Yayar Mama Inna Mandiya Allah ya jiƙanta mijinta ya auro wata bafullatana an yi auren ba daɗewa ta fara rashin lafiya aka yi ta yawon mgani anan ne aka ce wai asiri aka yi mata. Daga nan magana ta shiga gari aka yi ta cewa Inna Mandiya ce ta yi mata asiri ta kwanta jinya. Ƙwatsam kuma sai ta rasu bayan kuma mutuwarta ba daɗewa itama Inna Mandiya ta fara rashin lafiya na aljanu a yadda Mama ta faɗa ma na ana tunanin Gamo ta yi shi ne da wannan rashin lafiyan ta koma ga Allah. Magana ta za ga gari cewa ƙaiƙayi ne ya koma kan masheƙewa sama da shekaru amma mutane ba su bar maganar ba, an daɗe ana kiran gidan su Mama da gidan yan asiri, daga baya da mutane suka ga ji suka daina ni kaina na manta da labarin abin da ya faru sama da shekaru ashirin amma da ya ke ita Ma'u munafuka ce ta na tune da labarin shi ne ta zaunar da Anty Bahijja ta faɗa mata domin ni ta tozarta ni.

Ban san ma na buɗe muryata ina kuka ba sai da mai Adaidaitan da na ke ciki ya juyo ya na faɗin" Hajiya lafiya?
Na kalle shi amma na ƙasa mgana sai danne laɓena na ƙasa na ke yi kar na fashe da kuka tsabar yadda na ke ji na a rikice kamar na fita daga hayyacina. Wannan abin da aka yi min shi ne abu mafi munin da ya taɓa ɓata min rai tun aurena da Yusuf duk da an yi wasu a baya amma bai kai wanda ni za a tozarta ni sannan a yi min mummunan ƙazafi ba.

"Ko rasuwa aka yi miki Hajiya? Sai haƙuri Allah ya jiƙan musulmi."

Shi ya yi kiɗan shi ya yi rawan shi amma ni kallo bai ishe ni ba, ni kaɗai na san yanayin da na ke ciki. Ma'u daman suna farko farkon Rijiyar zaki ne gidanta na bakin titi da kin shiga layi kaɗan haka, gani na yi ma in na tsaya sai ya shiga dani zan ɓata lokaci ya sa na sauka a bakin titi na buɗe jakata na ɗauko masa 1k na bashi ya na mgana ban ji sa ba domin tuni na yi gaba. Hango kaina kawai na ke yi a gaban Ma'u na maƙureta ina dukanta ko zan ji kaɗan daga abin da ke taso min a ƙasan zuciyata ya ragu. Gudu gudu sauri sauri ina tafe a hanya na ga wani ƙaton dutse na ɗauka na riƙe a hannuna ina zuwa bakin get ɗin ban jira komai na saka dutsen nan na riƙa buga kofar da shi ina jin megadin gidan na tambayan waye na yi banza da shi, ya na buɗe get ɗin ta ƙaramar ƙofa bakin sa ya buɗe da shirin mgana na tura shi baya da ƙarfi na shigo gidan.

Da idanuwana na ke kallon haraban gidan Allah ya ba ni sa'a na hango Ma'u tsaye a jikin mota da shirinta tsab na fita ta dukar da kai ta na duba wayarta. Ban jira komai ba da sassarfa na fara takawa zuwa gare ta megadi ya biyo ni ya na faɗin" Baiwar Allah lafiya?
Bai sanni ba domin rabo na da gidan Ma'u tun haihuwan Alhaji ƙarami..

Hayaniyar Megadi ya sa hankalin Ma'u ya dawo kan mu yadda ta ke kallona na san ta yi mamakin ganina ne. Na dumfare ta da sauri dai dai ina fuskarta ƙofar shiga falonta. A kuma lokacin mijinta Alhaji Mustapha ya fito ya na saɓa babban riga da alama tare za su fita da Ma'u. Kafin ya ƙariso ni na riga shi ƙarisawa gaban Ma'u na saki jakar hannuna da mayafina lokacin da bakin ta ke motsi na ji ta ambaci sunana.

"Sadiy.."

Ban bari ta ƙarisa ba, saboda lokacin da na ganta ga ta a gabana sai na ji ɓacin ran da na yi kafin na zo gidanta ya ninka sama da sau saba'in ba tare da jira ba kawai na ɗaga hannuna da karfi na kwashe ta da wani mahaukacin mari ta bangaren damanta wanda sai da ta gicjiya gefe cikin razana da firgici. Adai dai lokacin da mijinta ya ƙariso ya na faɗin.

"Sadiya ke ce ta fe? Ah Subhanallah."

Sai maganarsa ta ƙare da kiran sunan Allah ganin na yi sauke ma matarsa marin diɓan mahaukaciya. Ganin ya na ƙokarin karisowa ya sa ta na ɗagowa cikin mamaki dafe da kunci na ƙara dagewa na sauke mata wani marin a bangaren dama da sai da wayar hannunta ta suɓuce a ƙasa ta ba da sautin ƙara kafin kuma ta yi wani motsi na saka hannuwana duka biyu na ɗago kafaɗunta na yo gaba da ita sai kuma da karfi na mai da ta baya gam! Na buga kanta da jikin motan da ta ke tsaye a gefenta, na ƙara ɗagota na ƙara maida ta gam sannan na saka duka hannuwana na shaƙe mata wuya kamar zan kasheta idanuwanta sun firfito waje ta na rike hannuwana domin ceton ranta amma a lokacin ni ba na ji ba na gani burina kawai na yi ma Ma'u dukan mutuwan da gaba ko sunana aka ambata sai ta razana.

Alhaji Mustapha ya yo kaina cikin tashin hankali.
"Ke ke Sadiya me ye haka?
Ya ke faɗa ya na neman ɓambare hannayena daga wuyan Ma'u amma ina ya kasa domin sai na ji wani karfi na shiga ta, hankaɗe shi na yi gefe ya ta ga taga taga kamar zai faɗi. Sakin mata wuya na yi na jawo mayafin da ke jikinta na matse mata wuya da shi, na ƙara jawo ta ta dawo na sake maida ta ta ƙara buguwa da jikin mota gam! Ban tsaya ba na saka duka hannuwana dama da hauni na riƙa yarfa mata maruka kamar Allah ya aiko ni . Sai ga Alhaji Mustapha ya yo kaina shi da megadin shi suna neman raba ni da Ma'u.

"Ke mahaukaciya ce! Yar'uwan ki ce fa?

Ya faɗa lokacin da suka ƙwaci Ma'u daga hannuna ta na bayan shi duƙe ta na maida numfashi, Megadi na gefe ya na salati shi kuma Alhaji Mustpha ni ya ke kallo ganin yadda na ke huci kamar zakin da ya daɗe a dawa bai samu abinci ba.

"Me ya same ki? Me ta yi miki za ki zo har cikin gidan ta kina dukan ta? Kin san me kika yi?

Na yi tsaye ban yi masa mgana ba sai ya juya ya na duba Ma'u ya na yi mata sannu ya mikar da ita tsaye fuskarta ta yi ja da shatin hannayena idanuwanta sun yi ja sai kuka ni kuma ina kallonta ta na kuka ina ji a raina ba ta daku ba so na yi na yi mata dukan da ba za ta iya ma mgana ba.

"Sadiya me na yi miki!l? Ni ce fa Ma'u yar'uwan ki?

Sai na ji kamar ta jona min shoking a jikina a fusace na nuna ta da yatsa ina faɗin" Ke dai Ma'u ke dai Ma'u wallahi ke tsinanniya ce."
Gabaɗayansu suka zuba min ido, ita ko sai ta fashe da kuka ta na nuna kanta.

"Ni kike kira da tsinanniya Sadiya?

"Kin wuce tsinanniya. Ke sheɗaniya ce."

"Ya ishe ka haka fa Sadiya ina ganin girman ki"

A fusace na ce" Ka daina gani daga yau. Ba ruwan ka a wannan mganar ka matsa gefe ba dai kai na ke yi ba."

"Matata ce Asma'u ba ki da hurumin da za ki zo gidana kina tsine mata"

Sai na kalleta ta na ta kuka kamar mutuniyar ƙwarai kafin na nuna da yatsa ina faɗin" Ma'u Allah ya tsine miki albarka munafuka mai fuska biyu."

"Yar'uwan ki ce fa kike tsine mawa?

Ya faɗa ya na mai daka min tsawa, ni ma a fusacen a tsawacen na ce" Ni ba yar'uwta ba ce domin na raba jinin da ke tsakanina da ita har abada. Domin abin da ta yi min jinina ba zai taɓa yi shi ba. Kuma ki sani wallahi sai hukuma ta shiga tsakanina da ke Ma'u."

Sai ya kasa mgana ya tsaya ya na kallona.

"Me ya faru?

"Ka tamnayi annamimiyar matar ka. Wacce ba ta ramin ta sai dai ramin wani."

Sai kawai ya fara lalubo waya daga cikin aljihun rigan shi lokaci ɗaya ya na faɗin" Ni dai ban san me ya faru ba amma ba ri na kira Injiniya."
Megadi kuma megidan ya ce ya tafi abin shi amma ya daga can gefe ya na kallon abin da ke faruwa hankalin shi ya tafi ga kiran waya na shammace shi na ƙara yin kan Ma'u wannan karon ta so kare kanta sai muka fara ƙoƙowa amma duk da haka sai da cire mata ɗankwalin kanta na damƙi shegen gashinta mai kama da hammatan ɗan iska na fara ja sai ta fara ihu da gudu ya rugo ya shiga tsakaninmu burina kawai na bar ma Ma'u taɓon da duk lokacin da ta kalle shi sai na faɗo mata a rai shi ya sa na riƙa waige waige ina neman dutse ko sanda na rotsa mata kai dashi ta haka ne ya samu damar saka ta cikin mota ya rufe na ɗauko dutse da na gan shi a can gefen na rika bugun gilashin motar da shi, shi kuma ba ya son riƙe ni sai dai ya na ƙare wa kuma ya na kiran sunana da faɗin na shiga hankalina.

Ita kuma ta na cikin mota ta na kukan munafunci amma na ga lokacin da ta yi min wannan mirmishin nata ita a tunaninta ta yi nasara ne. Ƙarya ta ke yi ba ta yi nasara ba sai ma faɗuwa.

"Wallahi yau dubin ki ya cika Ma'u daga yau karshen ki ya zo domin sai na tabbatar da kowa ya san wacece ke. "

"Haƙuri koma me ya faru a zauna a tattauna?

Na kalle shi da jajayen idanuwana kafin na ce" Shari'a ce za ta shiga tsakanina da matarka."
Ina mgana ya na kiran waya sai ji na yi ya na cewa injiniya ga matarka a gida ta zo ta na jan Asma'u da faɗa ban san me ya ce masa ba na ji dai ya ce sai ya zo, ni kuma na kasa na tsare na ce ko ya fito da Ma'u ko na fasa gilashin motar ni na fito da ita.

"Haba Sadiya ki natsu mana "

"Yadda ta haifar min da rashin natsuwa. Nima wallahi sai na haifar mata da fiye da abin da ta yi min."

Shi dai ya babbage bakin mota ya na ta ba ni haƙuri domin ya ga yadda na ke a rikice zan iya aikata duk abin da na ga dama. Ɗamara na ci da mayafin jikina ina girgiza kamar zan yi bi iska shi fa ya tsorata ya ɗauka ina da aljanu ne har Ma'u ma ta tsorata kuma ta bugu domin har fuskarta ta kumbura, da dai na tuna in Yallabai ya zo zai hana ni ƙarisawa ofishin yan sanda ya sa na karɓi jakata da Alhaji Mustpha ke miƙamin tun ɗazu ban karɓa ba. Sai da na karɓa sannan na ce.

"Mu haɗu a gaban hukuma."

Ya biyo ni ya na ce min injiniya na hanya na yi banza ds shi megadi tun kafin na ƙarisobya buɗe min kofa ina fita sai ga motar Yallaɓai na karisowa ina ganin shi sai na juya na nufi bangaren yamma shi kuma da sauri har da gudu ya fito ya taka ya na bina lokaci ɗaya ya na kiran sunana Allah ya sa layin ma ba jama'a da mun zama ƴan kallo.

"Sadiya."

"Sadiya magana fa na ke yi miki. Ki tsaya don Allah."

Ban saurare shi ba sai da ya yi gudu ya sha gaba na, na kauce masa zan wuce ya riƙo ni da ƙarfi ya na kiran sunana.

"Ka ba ni hanya na wuce ko?

Na faɗa ina masa wani kallo da jajayen idanuwana da ina da tabbacin yanayin da ya ganni ya daɗe bai ganni a cikin sa ba.

"Ina za ki je? Kin ga yadda kike kuwa?

Sai da ya faɗa na kalli kaina da ɗamara. Kamar wata yar dambe sai na warware mayafin na yafa a kaina amma Yallaɓai ya ƙi sakina.

"Ka sake ni na ce ko?

Na faɗa a fusace ina kuma ƙokarin kwace kaina amma riƙon Yallaɓai ba na wasa ba ne na kasa.

"In na sake ki ina za ki je?

"Offishin yan sanda."

Na bashi amsa ina huci kafin na cigaba da faɗin"Wallahi ba zan ƙyale duk wanda ya nemi ya tozartani ba. Sai hukuma ta bi min kadin kazafin da suka yi min ni da zuru'ata."
Na karishe faɗa ina fashewa da kuka sai ya rike ni a jikinsa amma ina ta fizgewa ina faɗin ya sake ni domin ni ba zan bar wannan mganar ba.

"Na ji nima ai ban ce ki barta ba. Mu je ki shiga mota sai mu je police station ɗin tare da ke."

Sai na kalle shi sai ya gyaɗa min kai ya na ƙara rike duka hannuwana ya na jinjina min kai, ban san me ya sa na yarda da shi ba na bi shi zalau zalau har bakin mota ya buɗe ya sakani a ciki ya rufe sannan ya taka ya isa bakin get ɗin gidan Alhaji Mustapha bai shiga ba amma shi ya leƙo sun yi mgana ba daɗewa ya dawo ya buɗe mota ya shiga ya ta da ita ya yi riverse muka bar layin tun da muka fara tafiya na ke kuka kuma da karfi ina yi har da jiniya bai kuma hana ni kukan ba.

"Ni Ma'u za ta tozarta? Ni yayarka za ta kalli idanuwana ta ce dangin uwata dangin asiri ne?

"Ki yi hakuri"

Yallabai ya faɗa a marairaice, ga shi sai kiran wayarsa ake yi bai ɗauka ba.

"Yusuf lokacin da ka ce min matarka za ta zo ta zauna da mu me na faɗa maka? Ba sai da na ce ina tsoron wani abu kar ya faru daga baya ba!
To yau ni matarka ta saka ma da sharri sakamakon alherin da na yi mata. Ita wai ta ce ta na gidan kanwar mamana ta kawo min asiri. Ita ce fa ta faɗi haka Yallaɓai"

Na ƙarishe faɗa ina kallon shi ina kuka har da majina.

"Ita Saudatun ne ta ce haka?

Ya tambaya cikin mamaki.

"Abin da ya fi min ciwo Anty Bahijja ta zubar da abincin da na kawo ma Nene ta ce ba zan kashe muku uwa kamar yadda na so na zubar ma da Gimbiya cikin jikinta? Yusuf a zama na da kai na taɓa kwatanta wani abu na cutarwa gareka ko yan'uwan ka?

"Ba ki taɓa ba Sadiya"

"Na taɓa zagin su! Na taba musu wani abu na rashin ɗa'a? Tsakaninmu sai girmamawa amma yau duk alherin zaman shekarun aurena da kai ya koma na sharri da ƙazafi?

"Ki daina kuka don Allah Sadiya raina na ƙara ɓaci."

Ya faɗa cikin wani yanayi ya na kuma gudu a mota sosai daga gani ran shi ya na

36 / 48