Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   24 / 48

69K to 72K   out of 141.5K words

na yi saurin ɗagowa ina kallon shi kafin na ce" Ni? Me na yi maka kuma?
"Kin sani fa Sadiya."
"Ban sani ba fa."
Na faɗa cikin shagwaɓa har ina kai masa duka a ƙirji, sai ya riƙe min hannu ya na kallona kafin ya ce.

"Kin tsara za ki fara kasuwanci amma ba ki faɗa min ba har aka kawo kaya na yi miki mgana sai ce min kika yi wai kin bar ni na gama cin amarcina ne? Wannan mgana ne? Tsakaninki da Allah duk wani abu da zan yi ko za ki yi mun saba zama mu tattauna a tsakanimmu, amma sai ga shi yanzu kin sauya kin fara yin abubuwa kai tsaye ba tare da kin faɗa min ba ko dai ba zan ba da komai a kallah dai na saka albarka na ba da shawara ko?

Ashe ya ji haushi, sai na ji daɗi ai ni haushin na ke son ya ji.

"Kin kuma san na ji haushi amma ki ka share ni."

Sai na yi mirmishi, kafin na ce" Afuwan Yallaɓai. Allah ya huci zuciyar Tafidan Rano."
Kawai sai ya jinjina kai kafin ya ce" Na yi haƙuri fa. Kawai dai na faɗa miki ne domin kin san na ji haushin ki."

"To a yi haƙuri Megida."

Na faɗa ina shafa sajen shi zuwa gefen masa.

"Laa la. Yallaɓai tafiya ta tafi. Furfura ka fara fa."

Na faɗa ina masa dariya, ɗankwalin kaina ya cire ya na faɗin"Ke ma ai kin tafi. Ina dubawa zan ga ta ki furfuran."
Ina dariya na kwaçe kaina ina faɗin" Ni yar yarinta? Yanzu na ke fa kai dai tsufa ya kama."

"To ke kika tsufar da ni. Saurayi ɗan ƙwalisa kika aura amma ji yadda yanzu na dawo."

Ya faɗa ya na wani kallon kanshi kafin ya ce" Sadiya ko yanzu na so zan auro biyu yan mata ƙwarara."
Sai na balla masa harara kafin na ce" Kai yanzu a zuciyarka akwai wajen wata mace?
"Ai ba ni na samar musu wajen ba Ubangiji ne."
Sai na kasa mgana na tsaya ina kallinsa shi kuma ya na min dariya sai kawai na miƙe tsaya na ja hannun shi ina faɗin" Sai anjuma Yallaɓai."

Ƙin tafiya ya yi sai da na riƙa tura shi sannan ya tafi ya na min dariya a raina na ce ni yanzu har wani aure za ka ƙara da zai ɗaga min hankali, ai sai dai Gimbiya itama ta ji yadda a ke ji na zafin kishi, yadda na samu na zazzage ma Yallaɓai abin da ke cikina sai na samu salama, kuma shima ai ya san bai kyauta ba shi ya sa ya ba da haƙuri.
Tuni Gimbiya ta warware. Yallaɓai ya san na yi masa tsiya tsiya sai ga shi ya zo ya na faɗa min Jidda ta na so ta dawo gida amma ya ce ta ɗan zauna ta ƙara kwana biyu na ce bakomai. Ni daman saboda tahfez ɗin ta ya yi rauni ne amma acewarsa ita Gimbiyar na yi ma Jiddan karatu a can.

Ko sati ba a yi da zuwana duba Gimbiya ba Nene ta faɗi a gida sai asibiti ana zuwa aka ba su gado. Jininta ya hau sosai ta samu jin jiri kuma ta ƙi mgana shi ne ranar kawai da safe ta faɗi Allah ne ma ya kyautata da ta samu shanyewar jiki, amma ko yanzu ɗin hannunta na dama da kafarta sun ɗan tabu bangaren hagu sun fi lafiya. Hankula sun tashi matuƙa ko ni na damu da ciwon Nene musamman saboda Yallaɓai ba ya son ganin ta cikin ciwo yanzu shina sai ya susuce. Shi ma ko in ba shi da lafiya ba ta da sukuni sai ta ji labarin ya samu lafiya shima ba ta yarda sai ta gan shi ya tako da kafafun shi ya zo duba ta.

A wani asibitin kuɗi ne na cikin gari in da Mimisco ke kaita ta na ganin likita ne aka kwantar da Nene. Gabaɗayanmu can muke yini da ni da Hauwa da har da Munnira da su Halima,Hajiya iya da Maman farko, su Anty Bahijja daman suna gaba gaba su masu uwa. Gimbiya kuma ta bar bangaren surukai ita ta koma bangaren ɗiya. Ita ta ke kwana da Nene Hajiya iya aka ce ta riƙa kwana da ita Gimbiya ta yi tsaye ta ce ita za ta riƙa kwana da ita su Anty Bahijja kuma suka amsa, da ita Mimisco ta ce gwara Hajiya Iyan ita babba ce sannan ita Gimbiya ga jikinta ba daɗi amma ta yi tsaye ta ce ta warke Yallaɓai ma ya amince ta riƙa kwana da safe sai ta je gida ta yi wanka ta huta ta kuma dawo.

An ga tururuwa har mutanen Rano duk sun zo, yan nesa kuma sun ta kiran waya. Kwana uku Nene jiki ya yi sauki ta na mgana ta na kuma motsa hannunta kaɗan kaɗan dai. Hajiya Tafida ma ta zo ta kwana ɗaya ta koma. Su Kawu Abba kuma kullum sai sun zo nima na kira Gida na faɗa Gwaggo sun zo ita da Alhajinmu da Ya Abubakar sannan su Rahila ma Ya Aina ta haɗo su gabaɗaya sun zo har asibiti sun duba Nene Ma'u kuma daman anan suka iske ta ma, ni fa har mamakinta na ke yi ko Nene ta haifi Alhaji mustapha sai haka shima ya na zuwa kuma ba sa zuwa hannu rabbana, kamar yadda muke dafo abinci ni da Hauwa haka itama ta ke zuwa da shi.
Za mu haɗu da Gimbiya kullum amma tsakanina da ita gaisuwa ce, Jidda kuma ta koma gida saboda Gimbiya na asibiti, Yallaɓai kuma daman barci kawai ke kai shi gida da safe kafin ya wuce wajen aiki zai biya haka da yamma in ya dawo, wata rana har sai na fara gangyaɗi  ya ke cewa na tashi mu tafi gida yara fa Ɗorayi Salisu ke kai su in sun tashi makaranta sai za mu koma gida mu biya mu ɗauko su.

  Kwanan Nene goma a asibiti sannan aka sallame ta ta dawo gida. Kuma ban taɓa fashin zuwa asibiti ba kullm safiyar Allah duk da zirga zirga ya sa duk na ji jikina na ciwo ga shi ina fama da ciwon mara kwana biyu nan ga ciwon kai da daddare na dai sha mgani amma ko Yallaɓai ban faɗa mawa ba. Da Nene ta koma gida Gimbiya ma can ta tare, ta na kula da ita kowa kuma yabon ta ya ke yi da ƙoƙarinta ni kaina na yaba mata ni kuma da ba a yabe nin ba na yaba ma kaina domin ni don Allah na yi. A baya kafin Gimbiyar ta yi ni na yi ko a yanzu ɗin ma ina iya bakin ƙoƙarina.




*Janafty*
*TKG*

12.

FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622

Gidana duk ya yi ƙura to ba na samun zama. Shi ya sa da aka sallami Nene sai na ɗan ɗaga kafa da zuwa Gwammaja in yau na je gobe ba zan je ba. Yallaɓai shima ya samu natsuwa tun da har Kaduna ya shiga ya kwana biyu. A ranar da zai dawo daga kadunan na je can Gwammaja da ya ke Jumma'a ne tare da su Jidda na ne tunda sai da na jira suka dawo muka taho tare. Na yo ma Nene ferfesun kayan ciki saboda na son ta na so, amma ina kawowa sai na ga Gimbiya ta yi mata amma duk da haka Nene ta karɓa ta ce za ta ci ko zuwa Gobe ne.

A gabana Anty Bahijja ta ɗanɗana ferfesun kai tsaye ta ce wai Nene ba za ta ci ba na cika ya ji kuma ya yi gishiri. Kuma ni dai har ga Allah na ci kafin mu fito komai lafiya na kuma san laluranta me ya sa zan cika mata gishiri da ya ji? Duk da haka ban nuna wani abu na danne a gabana ta ce wanda Gimbiya ta yi mata za ta ci shi ne ba zai mata wani abun ba.

"Wannan ko in kika ci sa ina ga sai kin koma Asibiti Nene."

Sai Nenen ta ce to su ci mana, irin dai kar na ji ba daɗi. Ko a fuska ban nuna ba illa Nene da na kallah na ce" Ban san gishirin ya yi yawa haka ba Nene ki yi hakuri."
Sai ta ce min haba bakomai ta gode da kyautatawa.
Falo na koma ranar Hauwa ba ta zo ba, Munnira ma haka ba ni da abokin hira, ina gidan Naja'atu ta zo da Anty Maimuna Nene ta sha magani ta kwanta sai suka baro ciki suka dawo falo suna hira suna shewa ina zaune kamar da gayya suna jefa min mgana.

Wai Naja'atu ke faɗin Gimbiya kar ta tsaya wasa ba wasa suka kaita ta yi ba. Haihuwa suke so. Ko kunya ta ma ba su ji ba kuma sun ganni domin har ita Naja'atun ma mun gaisa da ita.

"Ahto faɗa mata dai. Ni fa ciwon da ta yi kwanaki har na buga murnan mun samu ƙaruwa ashe ba cikin ba ne."

Ita kuma ta na mirmishi ta ce" Haka shima fa ya yi ta cewa ko ciki ne Daugther sai da muka je asibiti aka ce ba ciki ba ne sai da ya ba ni tausayi yadda na ga ya nuna damuwarsa."

"Allah sarki bawan Allah. Hauhiwa ya ke so amma an katse mishi ita a gidan shi da karfi da ya ji."

"To ai shi ya sa da Allah ya bashi dama ya mallaki gida biyu. Can ɗin da aka katse mishi nan kuma ba sai a buɗa masa ba."

Anty Bahijja ta faɗa har suna tafawa da Anty Maimuna. Ni ko sai na yi kamar ban ji su ba wayata na ke latsawa amma a ƙasan raina baƙin ciki ne ya cika ni, nan suka ta yada min mgana amma ban tanka su ba shi ya sa tun kafin mangariba na yi shirin tafiya na shiga na yi ma Nene sallama.

"Na gode Sadiya Allah ya saka da alheri."

Na amsa mata da Amin na tasa kan Jidda da Baby, ko jiran Yallaɓai ma ban yi ba duk da na san in ya dawo nan zai biyo amma baƙin ciki ba zai bar ni na zauna. Ban kuma ƙi yi musu sallama ba na ce musu zan tafi har ita gimbiyan.

"Ba za ki jira shi ya dawo ba?

Gimbiyar ta ce min ni kuma sai na ce mata a'a ban san lokacin da zai dawo ba gwara na tafi kawai.

"E ki tafi kawai shi in ya dawo ma ya na da wata matar a nan za ta kula dashi kafin ya ƙariso."

Sai na yi mirmishi kafin na ce" Ai hakan ne ya kamata."
Saboda kamar haka ɗin ne in ya zo sai wajen sha ɗaya ya ke komawa gida sannan ba duka ranakun ba ne in ya koma ya ke cin abincin da na dafa in na kawo masa sai ya ce ya ci abinci a Gwammaja. Shi ya sa abin da ta faɗa bai zame min wani baƙo ba

Muna tafe a cikin adaidaita ina sharan ƙwalla saboda baƙin ciki, da Jidda ta gani ta yi magana sai na ce wani ƙwaro ne ya faɗa min a ido, haka na koma gida na ƙule a ɗaki na sha kukana na ƙoshi kuma da Yallaɓai ya dawo Gwammja ya sauka sai sha biyu saura ya shigo gidan nan ina zaune idanuwana biyu ban yi barci ba na yi masa sannu da zuwa ya amsa.

"A haɗa abinci?

Na faɗa lokacin da na ga ya na tuɓe shaddar da ke jikinsa.

"No. Na ci abinci a gida"

Haka kawai ya ce min ya tura kofa ya fice ina zaune na ji ƙaran buɗe ƙofa ya shiga tiolet sai na kaɗa kaina na koma na kwanta wasu hawaye masu zafi suka zubomin ban iya saka hannu na tare su ba. Domin saukar su ɗin wani ni'ima a cikin zuciyata. Ina kwancen na ji shigowarsa har kuma ya gama shirin kwanciya ya zo ya kwanta ina jin sa amma ban yi wani motsin da zai gane idanuwana biyu ba.

Kwanciyarsa ba daɗewa na ji an kira wayarsa yanayin yadda ya ɗauki wayar ne da maganar sa ya sa na gane Gimbiya ce. A kan gadon aurena ina kwance daga gefe Yusuf ke faɗa ma wata macen ya na sonta. Har ya na ƙasa ƙasa da murya wajen furta mata. I LOVE U TOO DAUGHTER." Kukan zuciya na ke yi amma hawaye suna zuba daga saman ƙuncina a baya in aka ce hakan za ta faru sai na ƙaryata a tunanina Yallaɓai ba zai iya son wata mace sama da yadda ya so ni ba, amma tun daga lokacin da ya yi auren nan na fahimci cewa duk ƙarya ce, yarda da aminci da na ba ma Yallaɓai tuni na fahimci cewa na yi kuskure Namiji ne shi kuma zai iya sauya launi duk lokacin da ya so kamar yadda ya fara sauya min lokaci bayan lokaci.

Ban san adadin lukutan da na ɗaukan barci bai iya ɗauka ta ba, na yi kuka kukan baƙin ciki wannan ƙololin abin da ya yi min sauƙi daga ƙasan zuciyata na ji ya na ta so min, ina ma kukan ne amma ina jin kamar ma ƙaruwa ya ke yi ba ya raguwa. Yallaɓai ko barci har da minshari na juya ina kallon shi ina jin wani kuka na ƙara taso min, yaushe a ka yi daren ballatana har garin ya waye? Har Yallaɓai na neman ya yi min nisa. Nisan da har abada ba zan iya dawo dashi kusa da ni ba, ganin kamar ya motsa ne ya sa ni kuma na tashi na faɗa tiolet a ciki na zauna na sha kukana sannan na tashi na kama ruwa nufina na ɗauro alwala amma sai na ga period ɗina ya zo. A lissafi daga watan jiya zuwa watan nan al'adan nawa ya ɗan dai dai ta sai dai ina fama da matsanacin ciwon mara ne a lokacin na kira Dr. Aisha ba ta ɗauka ba amma na bar mata saƙo ta wsop da niyyar in ta gani sai ta sanar da ni yadda zan yi.

Ganin haka ya sa kawai sai na ɗauro alwala sai da na fito ne na duba lokaci a wayata na ga 2 saura ne na dare. Sai kawai na ɗau casbaha ta na koma na kwanta. A kwancen ina ta hailala da salatin Annabi a hankali a hankali kuma sai na samu sauƙin zuciya har barci ya kwashe ni ban sani ba. Kuma mai nauyi ne domin har sai da Yallaɓai ya tashe ni da asuba bayan ya dawo masallaci ya ga ban tashi ba, ban ce masa ina hutu ba sai kawai na tashi na shiga tiolet. Da safen nan da na gaishe shi a daƙune ya amsa kamar na yi masa wani abun nima ko ina ganin haka na kama kaina. Ina ma fama da kaina marata kamar za ta cire saboda yadda ta yi min nauyi sosai.

Daƙyar na yi ma su Jidda breakfast suka tafi makaranta. Shima dai tea kawai ya sha ya yi wanka ya fita ya bar ni ina ta mutsu mutsun ciwon mara sai da Saude ta zo ne na saka ta dafa min ruwan zafi da Hulba na ɗan sha sai maran ya ɗan yi min sauƙi. Sake kiran Dr. Aisha na yi shima ɗin ba ta ɗauka ba, sai na yi mata uzuri tunda ita likita ce mai harka da jama'a ba lalle ta na da lokaci ba sai kawai na yi tunanin ya kamata gobe na shirya na je asibitin matsalan ba lalle ne ma in na je a goben na samu ganin Dr. Aishan ba.

Haka na yini a gida kwance ban da lafiya. Ban kuma kira kowa ba yadda Yallaɓai ya fita bai iya tambayata me ke damuna ba saboda ai ya ganni sukuku shi ya sa nima ban neme na faɗa masa ba. Kuma tunda ya fita bai kirani ba nima ban kira shi ba, girki ma Saude na saka ta dafa kafin ta tafi ni a ɗaki na yini ina shan ruwan zafi domin na gasa marata. Sai can da yamma na ga saƙon Dr Asha ta ce bakomai na cigaba da shan mgani kaɗan kaɗan komai zai dai daita ciwon maran kuma da na ke yi sakamakon na kan ɗan daɗe ban yi al'ada ba ne kuma cuta ne a acikin jinin da ya ke fita shi ya sa zan ɗan riƙa fuskantan ciwon mara a farko farko amma ta ba ni tabbacin in na cigaba da yi duk wata zuwa nan gaba kaɗan ba zan riƙa fuskantan haka ba. Itama ta ce na riƙa shan ruwan zafi a kai a kai in sha Allahu zan samu sauƙi kuma na samu ɗin Alhamdulillah tunda har na samu na yi wanka a daren na sauya kaya sai dai fuskata duk ta kumbura har da ma kafafuna sai da na ɗan shafa mata man zafi.

Yau ma Yallaɓai sai around 11 na dare ya shigo gidan. Yara har sun yi barci nima na fara barcin marata ne ya ƙulle sai na tashi na shiga tiiolet a lokacin ya shigo gidan. Yadda na iske shi zaune ya na duba wayarsa fuskar ba alamun rahama ya sa ban neme shi da wata mgana ba bayan sannu da zuwa.

"Yauwa."

Haka ya amsamin kamar na yaɓa masa wata mgana mara daɗi. Sai na yi shuru ina ƙoƙarin danne zuciyata.

"Abinci fa?

Bai kalleni ba hankalinshi na kan wayarsa ya ce" No am ok."
Sai kawai na wuce na koma na kwanta na rufe ƙafafuwana zuwa cikina da bargo na juya masa baya ina ƙoƙarin danne tasowan wani ƙunci daga ƙasan zuciyata.

"Ba ki je Gwamnaja ba yau?

Ya tambayeni, ina daga kwancen na amsa masa da cewa E ban je ba.
Sai na ji shuru sai ni ce na juya ina faɗin" Ai na ga Nenen ta ji sauƙi sosai."
"Ta ji sauƙi Alhamdulillah."
"Allah ya ƙara mata lafiya."
Ya amsa min da Amin Amin daga nan ya tashi ya fice nima na juya na gyara kwanciyata ina ƙoƙarin danne komai na nuna komai ba komai ba

24 / 48