Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   38 / 48

111K to 114K   out of 141.5K words

ma Yayar mijin Sadiya shi ne ta ke ce ma Sadiya yadda ta shanye Yusuf shi ne za ta haɗa shi da ɗiyar yayarta domin shima a shanye shi tun da mu yan dangin asiri ne."

"La'ila. Ya Aina"

Rahila ta faɗa ta na tafa hannuwana cikin al'ajabi da mamaki.

"Gaskiya Ma'u ta yi asara. Ta zama jaka tunda ta iya zaɓan bare a kan jininta. Na ji ta fita daga zuciyata sam"

"Wallahi nima. Ta fita daga raina kwata kwata. Ji wani tsohon labari da ko mu da aka yi shi muna da wayau, mun manta amma ita da ta ji labari ta iya riƙe shi a ranta har ta na kai shi gaba. Tir da ita. Tir da mai hali irin na ta."

Haka suka haɗu suna ta tattaunawa ni dai ina gefe ina jin su su sai yau suka san Ma'u? Ai ni na daɗe da sanin hallayarta mara sa kyau.

"Gwara da kika je gidanta kika yi mata hauka tun da ba ta da mutumcina."

In ji Rahila.

"Nima haka na ce."

Ya Aina ta maida mata martani. Rahila ta daɗe sai gabda mangariba ta tafi, ni kuma ina gidan Yallaɓai bai kirani ba nima ban kira shi ba. Yau ko su Jidda ban tuna da su ba, sai na ji komai ma ni ya fita daga kaina, ba na son komai kuma ba na jin daɗin komai, har dare da Babansu Marwa ya dawo ya ganni a gidan Ya Aina ba ta buɗa masa ba sai dai ta ce yar matsala ce muka samu da Yallaɓai. Nan fa ya zauna ya na min nasihan haƙuri da rayuwa jin sa kawai na ke yi domin duk abin da zan faɗa masa ba zai yarda ba gwara kawai na yi masa shuru.

Can dare Ya Auwal ya kira Ya Aina ya ce Ya Hamza duk ya yi masa bayani kuma jibi shima ya na ta fe. Har Gwaggo sai da ta kira Ya Aina ta ce labari ba daɗi suka ji Alhaji ma duk ya shiga damuwa. Ita ta yi mata ma wasu bayanan, Gwaggo sai salati ta ke ɗaukowa ta na direwa.

"Asma'u ta ba ni kunyam ban taɓa tunanin sakara ba ce sai yau."

Gwaggo ta ce min bayan ta ce a bani wayar ta yi ta lallashina ta ce Alhaji zai yi adalci kuma Ma'u ba ta kyauta ba kuma za a gaya mata. A kallah dai yanzu sun yarda da cewa Ma'u munafuka ce kuma fuska biyu gare ta.

Gidan Ya Aina na kwana akan gadon ta ni da Marwa. Ita kuma a turakan megidan ta kwana tun da asuba Kawu Abba ya kira wayata lokacin ma ina zaune kan darduma ina azkar ne bayan mun gaisa ya ce min.

"Sadiya na ji duk abubuwan da suka faru. Ban ji daɗi ba. Amma ina so ki sani Tafida ba zai ƙyale wannan mganar ba. Yanzu haka ya kira su Kawu Sa'adu yau muna tafe za a yi zama a gidan Nene ki yi haƙuri duk wanda ya haɗa maganar nan domin ya tozartaki sai dai shi ya tozarta ta in sha Allahu."

"Allah ya sa."

Na faɗa cikin sanyin murya.
Ba mu wani daɗe muna mgana ba har ya na ce min ina gidan su Marwanatu ko? Na kuma san ita Marwan ta faɗa masa ina gidan su tun da ai na ji ta ƙasa ƙasa da daddare suna waya.

Da safiyar jumma'a na wayi gari a gidan Ya Aina duk breakfast ɗin da ta haɗa min ban iya cin komai ba sai Tea kawai da na sha. Yara duk sun tafi makaranta Marwa ce kuma aikin rana gare ta yau, Ya Aina ta saka min ruwan zafi na yi wanka ta ba ni kayanta na saka tunda yawancin jikin mu duk ɗaya ne sai dai ma ta dan fi ni kiɓa.

Munnira ta kirani a waya ta na faɗa min suma an kira su gidan Nene ita da Hauwa.

"Ni ba wanda ya kirani ko Yallaɓan ma tun jiya da ya sauke ni gidan Ya Aina ban ƙara jin sa ba."

Munnira ta ce" Hmm jiya bayan tafiyarki an yi abubuwa Sadiya. Daman ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne. Sadiya Allah ya wanke ki. Tafida ya tsaya miki jiya har ita Gimbiya sai da ta raina kanta."

"Me ya faru?

Na faɗa cikin sanyin murya.

"Bayan fitan ki Mimisco ta zo itama ta yi ta faɗa da Anty Bahijja. Da ita kanta Gimbiya Nene kuma ta ce tunda Anty Bahijja ba ta jin maganarta ta je tun da ta isar da abin da ta so. Da ko Tafida ya dira a gidan sai da ya haukace musu. Shi da Anty Bahijja suka yi kaca kaca Mimisco kuma ta da su Maman farko suka goya masa baya. Har da Nene da ya ce ba zai ƙyale maganar ba ta ce itama ba ta ce ya ƙyale ba. Ita kuma Gimbiya a gaban mu ya kalleta ya ce" Ke kuma  kin ban mamaki Saudatu! Sadiyar ce za ki bari masu zuga ki zuga ki ki yi mata ƙazafi? Shin kin ji lokacin da likita ya ce wani mganin zubar da ciki ki ka sha? Da har za a zo a yi mgana ki amince har kina maida zencen! Kin ban kumya. Ta yi miki alheri kin saka mata da sharri. Ina so ki sani ba zan ƙyale ki ba ke ma sai kin maimaita abin da kika faɗa a gaban hukuma."
Nan fa hankalinta ya tashi ta fara kuka ta na ba da haƙuri da cewa Anty Bahijja ce ta ce yar uwan Sadiya ta ce ta na shiga malamai ƙilama ta so zubar mata da ciki shi ne ta ce ai ta taɓa ganin ƙanwar mamaki ta kawo miki mgani ta na rantsuwan ita abin da ta faɗa kenan kawai."

"Munafuka."

Na faɗa ina jin zafin daga ƙasan zuciyata.

"Wallahi ai duk kukanta Tafida bai saurareta ba. Kowa fa ya ba su rashin gaskiya shi ne a ka ce yau za a yi zamacda gabaɗaya waɗanda abin ya faru suna nan."

"Allah ya kyauta."

Na faɗa ina cije baki, na ce mata ina gidan Ya Aina anan na kwana.

"Su Jidda fa?

"Muna gidan har dare amma ba su zo ba."

"Ina ga suna gida tare da Baban su."

Da haka muka yi sallama. Ya Balki ta zo gidan itama da safe ashe Ya Aina ce ta kira ta ta faɗa mata, itama ta yi ta gunduma ma Ma'u ashar ta na faɗin" Yar asara kawai. sai ta je ga ta ga mutanen duniyan nan."

Tana ma gidan Yallaɓai ya kirani ya ce ya na kofar gida na fito. Ina fita fuskarsa ba fara'a  ina gaishe shi ya amsa ya na kallona kafin ya ce.

"Kin tashi lafiya.?

Bai jira amsawata ba ya ce" Shigo mota mu je."
"Ina?
"Gwammaja."
Sai na ce bari na koma na ɗauko jakata da wayata.

Ina komawa cikin gida na faɗa ma su Ya Aina ya ce mu je can gidansu yanzu.

"Gwara ku je kan a yi ma lamarin tufkar hanci."

Na tafi da cewa duk yadda ake ciki zan kira Ya Aina a waya. Ya Balki ta rakani da cewa" Shi ya gama na shi mu ma za mu yi namu Allah sai mun taru mun ci uban Ma'u ƙila za ta shiga taitayinta daga yanzu."

Ni dai na fice na bar su, tunda na shiga motar nan Yallaɓai bai ce min ba nima ban ce masa ba sai da na ji ya na waya ya na faɗin ga shi nan ya ɗauko ni.
Sai da na bari ya gama wayar sannan na kalle shi ina faɗin.

"Ina so na fara zuwa gida."

"Me za ki ɗauka?

"Wani abu ne."

Sai ya kalleni amma bai yi magana ba.
Gida ya maida ni, na shiga ciki shi kuma yana cikin mota.
Kaya na sauya da hijabi sannan na sauya takalmi, na shiga kitchen na ɗibo magungunar da Inna Mariya ta kawo min na tusa a jaka ta, a yanayin kitchen ɗin na gane a gida yara suka kwana Yallaɓai ya yi musu girki shi ya sa na ga kitchen ɗin a hautsine.

Ko kafin na fito sai da ya kira waya na lokacin ma ina bakin get, sai na fito na rufe get ɗin da makulli, ina komawa motar ya juya muka nufi Gwammaja. Tare da shi muka jera har falon Nene sai na ga ashe ma kowa ya hallara mu kaɗai ake jira.
Ga Kawu Sa'adu da Kawu Abba sai Hajiyar Tafida da Nene a saman kujera sauran duk suna ƙasa hatta ko da Mimisco har da su Hauwa duk suna falon. Duk da zarafina da a ka ci jiya a gidan bai sa na fasa zuwa gaban Nene da Hajiya na gaishe su ba suka amsa min kamar ba abin da ya faru.

Sai na koma can kusa da su Hauwa na zauna sannan na gaida su Kawu Sa'adu da Mimisco. Anty Bahijja da Anty Maimuna kallo ba su isheni ba, ballatana wata Gimbiya can.

"Ma sha Allah. Tun da su sun iso. Ku yi ma su Maman Farko mgana su shigo."
In ji Kawu Abba.

Halima ce ta tashi ta je ta kira su sai ga shi sun shigo tare. Su kan na gaishe su tun da su kam ba su yi min komai ba,  suka amsa min suma kamar ba abin da ya faru. Yallaɓai dai kusa da Kawu Abba ya zauna a saman kujera.

Mimisco ta buɗe taron da addu'a sannan Kawu Sa'adu ya fara jawabi.

"Kowa anan wajen ya san dalilin taruwar mu a wannan falon jiya da yamma Tafida ya kira ni cikin damuwa ya na ba ni wani labari da ya ɗaga min hankali. Da cewa ke Bahijja kin ci zarafin mai ɗakin sa da yi mata kazafin ta na son zubar ma da ita amaryansa Saudatu juna biyu! Sannan har kina ikararin ita yar asiri ce kina ba da wani labarin da ba wanda ya san da ingancinsa. Abin na ki bai tsaya nan ba sai da kika bita da baƙaken maganganu mara sa daɗi waɗanda suka yi dai-dai da kin ci mata mutumci. Ta ce za ta kai hukuma shi ya hana ta da cewa shi ya kamata ya ɗau mataki shi kuma ya ga ya na da manya shi ya sa ya kira ni ya sanar da ni, ni kuma na taka na je na samu Hajiya na ce ta shirya mu je tare a yi komai a gabanta."

Sai ya ɗan dakata falon ya yi shuru sai saukan numfashin mutane.

"Ko ba haka a ka yi ba ke Bahijja?

Ya faɗa ya na kallonta sai ta dago kanta ina kallonta ban ga alamun nadama a cikin idanuwanta ba.

"Haka ne. Amma ai nima ba a ji zagina da.."

"Ban tambaye ki ba."

Ya daka mata tsawa sai ta yi shuru.
Ni ya kallah kafin ya koma ya na kallon ita Anty Bahijjan ɗin

"Ina jin ki yanzu ki faɗa min farkon abin da ya faru."

Jin haka yasa ta gyara zama ta na rattabowa har da ƙarya wai na zazzageta. A cewarta mganar asiri ba ita ta faɗa ba yar'uwa Ma'u ce da ta zo gai da Gimbiya a asibiti ta ce sai an bi a sannu saboda zan iya zubar da cikin gimbiya.

"A cewarta daman halin Sadiya ne shige shige. Tun da dangi mamanta su har shaidan bin bokaye aka yi musu. Ban san da labari ba sai ga shi ta na faɗa min ni kuma na ga yar'uwanta ne tare suka tashi ta fi kowa sanin Sadiya shi ya sa na yarda. Sannan da na zo ina mgana sai Gimbiya ta ce ai taɓa ganin Innarta ta kawo mata wasu maganguna ta na tunanin na asirin ne. Ni me na faɗa? Duk abin da ya faru ne na faɗa sai a ga laifina?

Ta faɗa ta na hararata ni ko kallonta kawai na ke yi amma na kasa mgana saboda tsabar mamakinta.

"Shi likitan ne ya ce wani abu ne ita Saudatun ta ci da cikin ya kusa zubewa?

Ya katse mata mganarta sai ta fara kame kame.

"Bai ce ba amma ya ce ta ci wani abu da cikin ta bai  karɓa ba."

"Sai kuma ke kika ce  ita Sadiya ce ta yi sanadin hakan?

"To Kawu a gidan ta take. Kuma ita ta dafa abincin da Gimbiya ta ci na ƙarshe ko kai ne Kawu wa za ka zarga?

"shi ne hujjar ki?

Sai ta yi shuru ta kasa mgana sai ya dawo da kallon shi kaina ya kira sunana na amsa cikin ladabi.

"Kamar yadda Bahijja ta yi mana bayanin abin da ya faru kema za ki iya yi mana bayanin farkon abin da ya faru?

"In sha Allahu Kawu."

"Bismallah."

Nima ko na gyara zama na fara mai da abin da ya faru tun zuwana gidan a jiya da zubar da abincin har zage zagen da muka yi ban ɓoye ba na faɗa na ƙarishe da faɗin" Kawu ni babban abin da ya fi ɓata min rai ƙazafin da suka yi min. Amma ta wani fannin ba ta da laifi tunda yar uwata ce ta ba da ni,   sai dai itama ba zan ƙyaleta ba mgana ta kai gaba za a ɗauki mataki. Saboda haka suma ina so a yi min adalci a bi min haƙƙin kazafin da suka yi min domin ba zan yafe ba "

Na karishe faɗa ina mai rufe fuskata saboda kukan da ya ta so min

"Kina da gaskiya. Tabbas wannan cim zarafi ne."

In ji Kawu Sa'adu."

"Ke Bahijja ni sa'an wasanki ne da za ki shiga gona ta don uban ki?
Kawu Abba ya faɗa bayan ya daka mata tsaawa a fusace saboda har da mganganun da ta faɗa akan Marwa sai da na faɗa.

Ai sai Anty Bahijja ta fara rantsuwa sharri na ƙulla mata ita ba ta ce  haka ba.
"Kuma ko mganar Kawu Abba ɗin iita ƴar uwan Sadiya ta faɗa min."
Ta faɗa ta na wani tura baki saboda Kawu ya zage ta.

"To ina ruwan ki da Sha'anina! Ko uwarki gata nan zaune ba ta isa ta hana ni abin da na yi niyya ba. Sai dai ta ba ni shawara ballatana ke karan kaɗa miya? Kuma kina duniya zan auri ɗiyar yayar Sadiya sai dai ki mutu saboda baƙin ciki"

"Kawu ni.."

"Ba na son ji wata magana. Ke daman ina da labarinki kin cika saka ido. Ke wa ya je gidan mijin ki ya takura miki? Ok to ke da kike zaune lafiya ke ma asirin kike yi kenan ko?

Kawu Abba ya ƙarishe faɗa a fusace, da ga ganin yadda ya ke mgana ran shi a ɓace ya ke.
Tafida dai ƙala bai ce ba daga shi har Nene da Hajiyar Tafida.

Sai Anty Bahijja ta fara kuka. Kawu Abba ya ce ta rufe ma mutane baki, kuma fa bai girmeta ba amma matsayin shi na Kawunta sannan kuma daman shi ba shi da wasa.

"Kin takura mata ita da mijinta amma ke kina can kina zaune lafiya a gidan auran ki? Wanzami daman ai ba ya son jarfa ke ko an faɗa miki wata mgana ya kamata ki zo ki saki maganar kai tsaye? Shekaran Sadiya nawa tare da ku duk ba ki san haka ba sai yanzu?

"Ni kaina sai da na ce ta bar mganar da ta faɗa min amma ba ta ji magana ta ba "

Nene ta faɗa cikin bayyana ɓacin ranta.

"Ni fa ba laifin kowa na ke gani ba sai na wannan yar'uwan Sadiyan duk ita ta ɓata komai. Ya kamata itama ta na wajen nan"
Hajiyar Tafida ta faɗa itama.

"Ba ruwammu da ita. Can tsakaninsu ne da Sadiya amma tabbas alaqar tun da ba ta alheri ba ce rabuwar shi ya fi."
Kawu Sa'adu ya ce haka sai Anty Maimuna ta fara faɗin ai Ma'u ta na auran yaron yayar mijin Anty Bahijja ne.

"To sai me? Za mu raba alaqar ko da ta fi karfin haka ballantana ba ta yi wani karfi ba."

"Sosai. Tunda daga ita Bahijjan har ita dayan ba alheri a zukatan  su."

In ji Mimisco da daman ita yar gaskiya da gaskiya ce.
Duk kuma mganar da aka faɗa sai Anty Bahijja ta karyata Allah ya sa ga shaidu suka maida yadda na faɗa daki daki.

Gimbiya ta sha kunya domin kai tsaye Kawu ya kalleta ya na faɗin" Ke Saudatu  ke ma kin ƙara hura fitina ke da kika zauna gidan Sadiya ta dafa abinci ta ba ki kina kwance sai ki saka mata da sharri? Kuma ke fa kika aure mata miji ita ba ta biki da sharri ba sai ke?
Sai ta fara kuka tana faɗin a yi haƙuri kuskure ne ba za ta ƙara ba.

"Ba tarbiyan da na yi ma Saudatu ba kenan ni kaina ta ba ni kunya."

In ji Hajiyar Tafida. Ita kuma Nene sai ta ce koma me ya faru Anty Bahijja ce ta ja shi. Sai ta ƙara saka kuka ta na faɗin shike nan duk an maida laifi a kanta ba a duba nima cin mutumcin da na yi mata ba.

"Ke kika fara ci mata mutumci. Kuma ta yi min dai-dai da ta rama kwatankwacin yadda kika yi mata."

Tafida ya faɗa cikin fusata Kawu Abba ya taya shi da cewa" Kuma daman in babba bai ji kunyar hawa jaki ba. To shima jaki ba zai ci kunyar ka da shi ba. Ke kika zubar da girman ki, ban ga laifin duk wanda ya taka ki ba. Me ya sa ita Zuwaira ba a yi mata ba? Saboda ta kama kanta ba ta kuma zama ji da jiyarwan da kika zama ba."
Sai ta ƙara fashewa da kuka ta kasa mgana ita da Gimbiya sai kunya.

"Ba kuka za ki yi ba haƙuri zaki juya ki ba ta ki kuma janye kalaman da kika yi a kanta. In ba haka ba zan bar Tafida ya ɗau matakin da ya dace."
Kawu Sa'adu ya faɗi haka Anty Bahijja da ta san akwai ranar da za ta zo ta ba ni haƙuri da ba ta aikata ba abin da aikata ba. Kowa kuma ita ya ba ma rashin gaskiya har su Maman farko dole ta juya ta ba ni haƙuri na ƙi mgana.

"Sadiya ki yi hakuri kin ji ko? In sha Allahu ba za ta ƙara ba."

In ji Nene sai na ga girmama maganar Nene shi ya sa na ce na yafe mata amma sai dai na ce"kin ci darajan Yusuf da Nene shi ya sa na yafe miki."
Gimbiya ma aka ce ta ba ni haƙuri ta ba ni haƙuri Hajiyar Tafida ma ta ba ni haƙuri na yi shuru ban yi

38 / 48