Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   13 / 48

36K to 39K   out of 141.5K words

Yallaɓai a waya sannan na ga duba lokaci goman dare har ya gota.

Yallaɓai na min ƴar murya wai ya siyo min tsire ko kaza? Ni ko na ce muna da sauran nama.

"To ko fura ba za ki sha ba?

Kar ya ga na ture ƙoƙarinsa sai kawai na ce ya siya min kawai furan, ba su shigo gidan ba sai goma da rabi na yi mamakin ganin har Baby ba ta yi barci ba na ɗauka acan ma za su fara barci,sai dai suna dawowa ta ce min Umma ina jin barci na ce ta shiga ciki mana ta kwanta. Jidda kuma na ce ta ta ya Baby ta cire kayan jikinta ta saka na barci, ni kuma da na yi ma kaina tsiya domin furan da Yallaɓai ya siyo min ita na sha na kwanta kuma na ji daɗin furan bakina ya yi min daɗi sosai.

Kafin mu kwanta ya ce ina abin da ya ce na rubuta sai na nuna masa a wayata.

"Kin tabbata su kenan muke buƙata?

Ya faɗa ya na kallona lokacin dukkanmu muna saman gado amma ba mu kai ga kwanciya ba.

"E yanzu dai su kenan gaskiya."

"Bari da safe sai na tura can singer. Na ku kuma zan saka miki kuɗin in sha Allahu."

Na amsa masa da Allah ya kaimu amin, har na juya zan kwanta na ji ya kira sunana.

"Sadiya."

Sai na juyo ina kallon shi kafin na amsa masa.

"Na'am."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Yau Nene ta yi min mganar tariya. Ta ce in son samu ne zuwa karshen watan nan."
Gabana ya faɗi amma ban nuna masa ba.
Sai kawai na kalle shi kafin na ce" Allah ya nuna mana."

"Amin. Ita ma Daughter na yi mgana da ita yau. Ta ce ba ta da matsala ko yaushe ne."

Ya na mgana ne ina kallon shi kawai ina ganin kamar almara. Wai yau ni Yallaɓai ke maganar watar matar tasa da ni turƙashi!

"Shi ne na ce a bari na zo gida na ji na ki tsarin? Lokacin ya yi miki?

Sai kawai na yi mirmishin, mirmishin da iyakarsa saman leɓena.

"Ni miye na wa a ciki? Tun da Nene ta amince da ita kanta Gimbiya ni me zan ce? Allah ya nuna mana."

"Akwai na ki a ciki mana Sadiya."

Ya katse ni, sai kawai na ƙura masa ido ba tare da na yi magana ba.

"Saboda ke matata ce kuma kina da haƙƙin na sanar da ke abin ke faruwa kuma na ji ra'ayin ki"

"Oh! Haka ne?

Na faɗa ina kallonsa in zai lura kallon kar ka raina ma kanka wayau na yi masa ban sanin masa in ya gane.

"E. "

Ya faɗa ya na kallona saboda ba na son maganar ta yi tsayi ya sa na gyaɗa kaina kafin na ce" To na ce komai ya yi. Allah ya nuna mana."
Ya amsa da Amin amma a sanyaye, juya masa baya na yi ina gyara kwanciyata.

"Zuwa da safe za mu ƙarishe maganar."

"Allah ya kaimu."

Na amsa masa mganar, da ace bai matso kusa da ni ba, ko ta kanshi ba zan yi ba amma sai na ga ya rarrafo ya matso kusa da ni muka kwanta a jikin juna duk da ba mu yi komai ba amma mun kwanta tare mun kuma tashi tare, da sassafe ya  ta fi kaduna tea kawai ma ya iya tsayawa ya sha ko yara yau ba su riga shi fita ba. Tafiyar ta sa ba ta kwana ba ce amma da yamma ya kira ni ya ce ya yi dare kuma akwai abin da zai tsaya ya yi a goben shi ya sa zai kwana sai ranar asabar zai dawo na ce Allah ya kaimu.
Ranar asabar ɗin ma sai yamma ya dawo ya na can kadunan aka kawo kayan abinci ni ma ya turamin kuɗi na abubuwwn da na ce masa ba mu da shi, ban je kasuwa ba ni dai na kira Aisha lame na siya lotion da shower gel, Marwa na kira ta zo na ba ta sauran saƙon bayan na rubuta mata, haka kurum na ji ba na son fita ko nan da kofar gida saboda ji na ke yi kamar ba ni ba.

Duk yadda Yallaɓai ya so mu zauna mu yi mgana na ƙi ba shi fuskar hakan, cikin haka ne ma na faɗa masa maganar tafiyar mu Yashe biki bai hana ni ba daman na san ba zai hana ni ba, ranar lahadi da daddare na faɗa masa tafiyar na kuma ce talata ya ce Allah ya tsare sai washegari litini bayan yara sun tafi makaranta ya na tashi daga barci kamar da ni ya tashi a ranshi ina kitchen ya leƙo ya kirani sai na wanke hannuwana daman ina fere doya ne, itama ta ƙare jiya Yallaɓai ya aiko Musbahu da ita tare da dankalin turawa da na hausa.

  Hannuna ya kama ina bin sa a baya har cikin bedroom ɗin mu ya zaunar da ni a kan gado shi kuma ya ja kujeren madubi ya zauna a gaba na ya na kallona.

"Me ya faru?

Na tambaye shi ina kallon shi cikin mamaki.

"Me ya sa ki ke gujema mganar da na ce za mu yi?

Ajiyar zuciya na sauke domin ya riga ya ritsani ba ni da mafita sai kawai na amshi laifina.

"Ka yi haƙuri."

"Na yi. Na yi Sadiya ta."

Ya faɗa ya na min mirmishi.

"Ina jin ka. Me zamu tattauna?

Gabana na ta faɗi, saboda karshen wata saura kwanaki ne kaɗan. Sati biyu ma ba wani abu, ina tsoron na ji wata mganar da za ta tada min hankalina.

"Kan mganar tariyan Daugther ne daman."

Daugther. Daughter ƙaniya. Ai wani daughter da Daddy duk ta ƙare yanzu tun da an ɗaura auren.

"Maganar gidan da za ta zauna ne daman."

Ras! Haka na ji, fargaba na taso min sai kawai na kalle shi ban yi magana ba.

"Na saka a nema min haya gida. Jiya dai an kirani an samu wani a can anguwan Taurani sai wani a sharaɗa yau na ke so mu je da ita ta ga gidan"

Na ɗago ido ina kallon shi sai ma rasa me zan ce masa?
To wai me ya rage ne? Ni fa duk wannan ga ya min fa Yallaɓai ya ke yi bai burgeni ba da ya sani da ma ya yi shuru da bakinsa ni a wajena da ya fi. Ko kaɗan ban ganin kirkinsa ta wannan fannin
Amma dai na samu salama, tunda dai ba tare za mu zauna ba. Daɗin abin ma ta na can wata anguwar mai nisa da in da na ke, gwara hakan domin gwara kazantar da ba ka gani ba akan kazantar da agaban idanuwanka ya ke faruwa hausawa dai sun ce ƙazantar da ba ka gani ba sunanta Tsafta.



*Janafty*
*TKG*

07.

Kamar a zahiri kallonsa na ke yi amma a baɗini ba shi na ke kallo ba. Hankalina da tunani ya yi nisan kiwo. Jikina gabaɗaya ya saki sai na ke jin kamar ba zan iya ba, kamar za'a ga gazawata in tafiya ta yi nisa.

"Kin yi shuru ba ki ce komai ba Sadiya."

Shi ya katse min tunani da ya sa na dawo hayyacina. Ajiyar zuciya na sauke kafin na maida hankalina zuwa ga kallon ƙasan cafet ɗin da ke gefen gadon. Ina so na yi magana amma sai na ji kamar an ɗaure min baki zuciyata ta yi wani irin nauyi sannan numfashina sai na ji kamar ya na sarƙewa sai na buɗe baki da niyyar magana sai na kasa sai da na ƙara sauke ajiyar zuciya na fitar da iska daga bakina sannan na fara jin ina dawowa cikin hayyacina.

"Are u ok?

Wani kallo na yi masa, tsabar ma Yallaɓai ya raina min wayau ya zaunar da ni yana min labarin kishiyan da ya yi min shi ne kuma ya ke tambayata ko ina lafiya? Kaɗan rage ban ce masa ban sani ba amma sai na danne zuciyata kamar yadda na saba amma ni kaina na san ina yi ma zuciyata gaddama sannan ina faɗin saɓanin abin da ta kitsa min.

"To me zan ce?

Haka na faɗa ina kallon sa, sai ya ƙure ni da ido, ni kuma sai na maida kaina ƙasa sai ma na kama wasa da zoben zurfan da ke hannuna. Ba tsammani kawai na ji ya riƙo hannayena cikin tafukan hannayensa sai na ɗago ina mai sake kallonsa a cikin kwarmin idanuwana akwai alamun taruwan ruwa, amma duk ƙoƙarina domin na hana su bayyana ne a gaban Yallaɓai a karo na biyu ne shi ya sa na ke ta ɗagagga ido na sama ina ƙokarin maida kukan da ke ƙoƙarin taso min.

"Me za ki ce haka Sadiya ta? Ke ko ke da abin cewa?

"Ko?

Sai ya gyaɗa min kai ya na mai ƙara damke hannayena cikin na shi.

"Saboda me?

Haka na tambaye sa saboda sai na ga kamar Yallaɓai so ya ke ya kureni to in ba ƙurewa ba, ina ruwana da labarin hayan gidan da zai kama tun da ba ni zan zauna a gidan ba, abin da ya shafe shi, shi da Gimbiya ne.

"Na faɗa miki ki daina cewa saboda mene Sadiya. Kar ki manta ke fa matata ce. Kuma uwar ƴaƴa na."

"Sai me?

Haka na faɗa, lokaci ɗaya ina ƙwace hannayena daga cikin na shi, sai ma na miƙe tsaye lokaci ɗaya ina faɗin" Don ina matarka sai me? Me ka ke so na ce? Duk abin da zan ce ai na gama cewa tun a baya Yallaɓai."
Na ƙarishe faɗa ina mai kallon shi. Ya na shirin sake magana na yi saurin ƙara tare shi da cewa"Allah ya sanya alheri."

"Amin"

Na ji Yallaɓai ya faɗa, har na juya zan fita daga bedroom ɗin jin abin da ya ce ne, ya sa na juya ina yi masa wani irin kallo, ganin irin kallon da na ke yi masa ya sa wajen ya kwaso maganar da za ta kare sa sai ya ƙara yaɓa ma kansa ɗanyen kashi.

"To ko za ki zo mu je Tare ne?

"Mu je ina?

Na faɗa a zabure saboda sai na ji kamar Yallaɓai na shirin dukana da bulalan kalamanshi ne.

"Duba gidan mana."

Ya faɗa ko kunya, sai na ƙara jin kamar ya watsa min ruwan sanyi sai da tsikar jikina suka ta shi yam! Kallon Yallaɓai na ke yi da dukkan zuciya wai daman wanna ne cin mutumcin irin na mazan irin sun ƙara aure! Wato ni tun kafin ma tafiya ta yi nisa Yallaɓai ya fara ƙokarin nuna min na shi halin, wata irin zuciya ce ta yunkuro min kawai sai na dawo gabansa na tsaya ina kallonsa ido cikin ido kafin na buɗe baki da na ke jin tsabar zafin da ke cikin zuciyata ina jin hucin sa daga cikin bakina.

"Me ka ce?

Sai ya yi shuru ya kasa maimaitawa ganin yadda na yi, mirmishi ya yi ya na ƙokarin ya mai da maganar ta sa wasa.

"E. Ki shirya mu je mu duba gidajen tare ai ba wani abu ba ne ko?

Ban san na ɗaga hannuna ba sai da na ga ina nuna sa da yatsa manuniya. Cikin kakkausan muryan da Yallaɓai ya ke daɗewa bai ji ni na yi masa magana da ita ba na buɗe baki na kira sunan shi.

"Yusuf."

Haka na faɗa ina masa gargaɗi da ido, shima jikinsa ya yi sanyi domin ya san duk ranar da na kira shi da sunan Yusuf ya san ba zaman lafiya a tsakanina da shi. Miƙewa tsaye ya yi cikin kwaso maganarsa.

"Tsaya ki ji. Ni fa ba da wata manuf.."

"Yusuf ko dai ni ce zan tashi daga wannan gidan Amaryanka ta zauna, ni kuma gidan hayan da za ka kama shi ne nawa?

Na faɗa ina mai tsare shi da ido, ƙokarim riƙe ni ya ke na yi baya ina mai ɗaga masa hannu, faɗi ya ke yi cikin rawan murya wai shi ba haka ya ke nufi ba a fusace na ce" To in ba haka ka ke nufi ba! Me ka ke nufi da na shirya mu je duba gida tare? Ina ruwana da maaganar duba gida? Ko ya shafe ni ne?

Na ƙarishe faɗa cikin tsawa ina mai zazzaro masa ido. Sai kawai ya sarke hannayensa duka biyu a saman ƙirjinsa ya na faɗin" Ba ki fahimce ni ba ne Sadiya. Ni fa ba da wata munafa na faɗi haka ba, saboda kar ki ji ba daɗi ne ya sa na ce haka amma tun da ranki ya ɓaci ki yi hakuri."

Ya faɗa cikin ƙasa da murya shi kan shi jikinsa ya yi sanyi, sai da na yi masa mirmishin jin haushi sannan na yi baya ina mai riƙe kuguna kafin na ce" Ni na zama a bar zolayan ka ne Yusuf? Ko bashi daman mgana ban yi ba na cigaba da faɗin" Ina ruwana da abin da ya shafe ka kai da amaryan ka. Ni abin da ya shafe ka ne ya zame min dole na ji ba wanda ya shafeta ba, in ka na so mu zauna lafiya a gidan nan ni da kai to ka cire ni cikin wannan lissafin na ka. Mgana in ta shafe ka ba ni da yadda zan yi amma in ta shafi amaryaanka ne ka cire ni a ciki saboda babu ruwana a ciki na faɗa maka."

Na faɗa ina mai sake nuna masa yatsa cikin gargaɗi.
"Laifi ne domin na faɗa miki! ? Ba na so ki ji labari a waje ba za ki ji daɗi ba."

"Na ji a wajen mana Sai me?

Na tare shi cikin tsawa kafin na cigaba da faɗin" Sai me don na ƙarishe jin sauran labarin daga waje? Auran ma ai shi kanshi daga wajen na ji to saboda haka ma wannan ka daina zaunar da ni ka na ɓata min lokaci ka na gaya min, ka bar na ji daga wajen ya fi min da ka zaunar da ni kana tattauna abin bai shafe ni da ni ba."

"Ni  al'amarina bai shafe ki ba Sadiya.?

"Na ka ne ya shafe ni, amma na ta bai shafe ni ba. Saboda haka ka koya ma kanka ɗaura kowa a mizanin matsayin shi in har kana son zaman lafiya."

Kallona ya ke yi, ni ma shi na ke, domin a lokacin ina jiran ya ƙara cewa tak ne a kan mganar Gimbiya ya ga hauka amma sai na ga kawai ya koma ya zauna lokaci ɗaya ya na faɗin" To shi kenan ki yi hakuri ba zan ƙara ba."

"Better."

Na faɗa ina mai juyawa zan bar masa bedroom ɗin, har na riƙe handle ɗin kofar sai na tuna da wani abu da sauri na juyo ina kallon shi, shi ma ni ya ke kallo sai kawai ya ga na dawo gabansa na tsaya kafin na kira sunan shi.

"Yusuf"

Kallona kawai ya ke ba tare da ya yi mgana ba.

"Abin da ka ke yi ba shi zai goge taɓon ka yi min kishiya ban sani ba. Sannan ba shi zai goge taɓon ka yi min kishiya a lokacin da ban yi tsammani ba, ba kuma shi zai goge wannan taɓon da ka yi min a cikin zuciya ta ba. Ni dai na yi ma kaina alƙwarin ba za a ji  wani abu daga bangarena ba, amma ka sani duk abin da za ka yi ba zai taɓa goge taɓon ka shammace ni shammatan da ban taɓa tsammani daga gare ka ba, gwara ka yi harkan gaban ka kamar yadda ka saba, kar wajen ƙokarin kare kanka ka ɓata komai Yallaɓai. Gwara kawai mu tsaya a hakan ba na son wannan jaye jayen maganar naka domin ni ba burgeni ka ke yi ba sai ma haushin ka da na ke ji, gwara tun kafin rayuwankan mu su kai ga ɓaci gwara mu kiyaye ma juna."

Na faɗa ina mai kallonsa cikin ido, ajiyar zuciya kafin ya ce" In sha Allahu."
Ban tsaya bi ta kansa ba na fice har ina bango masa kofa kitchen na koma ina aikina ina masifa ni kaɗai ba ta yuyu kawai na zauna Yallaɓai na raina min hankali gwara na yi ma abin tufkan hanci ko zai gane duk kallonsa kawai na ke yi, ban kara komawa Bedroom ɗin nan ba har sai da ya yi wanka ya fita, na yi masa ta yi abin karyawa ya ce min ba zai ci ba, ko ta kan shi ban bi ba ya ce min zai fita ana jiran sa na ce Allah ya tsare.

Sai da ya fita na koma bedroom ɗin na gyara sannan na wanke kaina saboda ina so na yi kitso sannan na yi wanka. Ban ko faɗa masa gobe ne tafiyarmu Yashe ni da Rahila ba sai in  ya dawo, sai yanzu ma na ƙara jin tafiyata ma ta zama dole ni ba zan zauna Yallaɓai na neman kashe ni da baƙin ciki da kalamansa ba.
Mai kitsona na kira a waya na ce mata ta zo anjuma ta yi min kitso, su Jidda ko wancan satin ni na yi musu saboda na kira wayarta ban samu ba yau ɗin ma ta ce min ta na da yan kitso amma in za ta samu zuwa za ta gaya min.

Mun yi waya da Rahila ni na kira ta kan tafiyar mu ta ce min goben za mu tafi, saboda Ya Aina ta shiga kasuwa yau da kuɗin da muka haɗa gabaɗaya za a ɗan tsinta kayan kitchen sai zanin gado da labulanya in kuɗin sun ragu sai a ƙara mata da wani abu sannan ta na faɗa min ɗinkunan Amaryan ma nan Kano aka kawo mata suma in an gama tare da su za mu wuce na ji daɗin haka domin ba na so ma a ɗaga tafiyar nan ta mu kamar fa a kan ƙaya na ka haka na ke jin kaina a gidan gabaɗaya.

Na buɗe data ne na shiga group ɗin gidanmu na ga Ya Aina ta yi godiya ga kowa saboda kuɗin da a ka haɗa ba ta dai faɗi a dadi ba, ta ce ta je ta faɗa ma Alhajinmu ya na ta saka mana albarka anan ne na ji Ya Murja na maganar yan tafiya na ji ta na ceewa har da Ma'u a cikin masu zuwa ita da ta ce ba za ta samu zuwa ba amma Ma'u ta ce ta shirya ta na tunanin direba ne zai kai su, duk ina gani ban yi magana ba sannan an yi maganar cikin matar Ya Hamza ko ta Ya Auwal

13 / 48