Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   41 / 48

120K to 123K   out of 141.5K words

Babba. Ki yi juya ki nemi gafaran Dubu in kuma ta ce ba za ta yafe miki ta yi dai-dai ba zan matsa mata ba, na san ba zan ce ta cigaba da zumumci da ke ba, amma zan faɗa mata kar ta zama mai yanke zumumci da ke, ta yi miki kara sabo da ni da Mahaifiyarki. Amma tabbas ba ki kyauta ba ni kaina ban ji daɗin abin da kika aikata ba, ina jin kunyar kaina da waɗansu mganganun da aka ce daga bakin ki a ka ji su."

Ta na kuka ta na faɗin za ta roƙe ni gafara ba ni ba dukkanmu za ta roƙi gafarammu. Ta fara da roƙon Gwaggo da cewa ta yafe mata ba za ta ƙara ba.
"Bakomai Asma'u na yafe miki amma don Allah ki kiyaye. Dadiya fa ƴaruwanki ce bai kamata ki bari sheɗan ya yi tasiri a kanki saboda ita ba."
Da ta je gaban Ya Aina ta na kuka ta na cewa ta yafe mata kai ta kauda kafin ta ce" Bakomai amma dai kin ba ni mamaki sannan ki yi haƙuri ina ji a raina ba zan ƙara yarda da ke ba."

Ya Balki kam sai da ta kalleta ta ce" Kin dai ɓata wayon ki Ma'u ban zaci haka daga gare ki ba. Ki gyara domin ko a nan gaba ba munafunci da gulma ba shi da amfani."
Ya Murja ba ta ce komai ta dai ce Allah ya yafe mana gabaɗaya amma ita kanta ai ta sha mamakin Ma'u.
Ya Auwal ma yace shi in dai na yafe shima ya yafe. Yallaɓai ko da ta isa gaban shi tun kafin ta yi magana ya dakatar da ita da cewa.

"Abin da kika aikata kin san bai chanchanci yafiya ba ko? Saboda kin haɗa fitina fitinar ba domin Allah ya taƙaita ba da yanzu lamarin ya wuce tunanin kowa. Sadiya matatace da muka yi aure tsawon shekaru goma sha biyar amma ni na san abin da za ta aikata da wanda ba za ta aikata ba, abu ɗaya zan faɗa miki shi ne ki daina biye ma zuciyarki ki kuma yi yaƙi da sheɗan da kika ce shi ya rinjaye ki. Mgana ta karshe shi ne alaaqar dake tsakanin ki da Yayata don Allah ta tsaya haka nan.  Ina son na zauna lafiya da matana da ƴan'uwana."
Sai ta kasa mgana Ya Hamza ya ce daman alaqa in ba alheri a cikin ta rabuwan shi ya fi.
Har Ya Abubakar da ya ke ɗan amshin shata sai da ya ce mata ba ta kyauta ba.

"Ba Sadiya kika tozarta ba mu kika tozarta. Kuma ba zan ƙi faɗa miki kin ba ni kunya ba. Allah ban taɓa tunanin haka daga gare ki ba."
Shi ko Ya Hamza gyara zama ya yi ya na faɗin" Ke yanzu in Sadiya ta haɗa kai da abokiyar zaman ki ta ci duduniyarki za ki ji daɗi? Ta girgiza kanta sai ya cigaba da faɗin" To me ya sa kin san ba daɗi kika aikata abin da kika aikata?
Sai ta ba shi amsa da sharrin sheɗan ne kamar zai deke ta ya ce" Ke ce sheɗaniyar kenan kuma in ba ki yaƙi da sheɗancin da ke tare da ke ba, ba za ki zauna lafiya ba. In wannan karom mun yi miki afuwa wallahi tallahi kika sake aikata makamacin haka sai dai ki je can gaban hukuma ki fitar da kan ki."

Y Muntari kuwa hadisi ya jawo mata ya ce addini ya hore mu da mu so ma junanmu abin da muke so ma kan mu. Sannan ta shiga hankalinta kar ta koma ga Allah haƙƙin zumumci ya bibiyeta."
Mijinta ko cewa ya yi ya yafe mata domin ya san sharrin sheɗan ne ba halinta ba ne har ya na share mata hawaye.
Ni ce ta ƙarshe Ma'u ba ta ji kunya ba wai ta kalleni tana cewa na yafe mata sharrin sheɗan ne.

"Ni da ke mun san gaskiya. Ba wani sheɗan daman kin shirya ma hakan. Ma'u abin da kika yi min mai zafi ne. Ina so ki sani ko na yafe miki ba zan iya cigaba da zumunci dake ba"

Na faɗa kai tsaye saboda ba zan yi ƙarya ba zan yanke alaqata da Ma'u  domin ko ban yanke ba, ba na jin zan iya cigaba da mu'amala da ita.
Sai kawai Baaba ta ce ai ni ce na ke da kafiya tunda ta roƙe ni gafara me zai saka ba zan yafe mata ba.

"Na ce na yafe mata. Amma ba zan iya cigaba da zumumci da ita ba. Nan ɗin da ya haɗamu dole in mun haɗu mu gaisa domin  ni ba zan yi gaba da ita ba. Amma duk wani abu daya dangance ni na cire ta a ciki shi ne mgana."
Kuma kowa ya goyo bayana har Alhajinmu wannan karon bai yi magana ba.
Abu ɗaya ya ce min shi ne" Ki yi mata kara Dubu. Ki yi mata kara ko saboda ni. Ba yanzu ba in zuciyarki ta huce ki sada zumumci da Asma'u domin har abada ita ɗin jinin ki ce."

Saboda Alhajinmu da kuma karan da ya ce in yi masa. Shi ya sa na gyaɗa masa kai ina mai faɗin" To Alhaji in sha Allahu zan yi yadda ka ce"

"Na gode miki Dubu. In na faɗa kina ji, in na kuma ba ki unarni nan ta ke kike yi ba tare da jinkiri ba. Allah ya yi miki albarka."

"Amin Alhajinmu."

Sai ya kalleni kafin ya ce" In na ce kin yi kuskure a lokacin kike aminta da cewa kin yi kukure sannan ki ce za ki gyara. To yau ma zan ce kin yi wani kuskure guda ɗaya kacal Dubu."

Ba ni kaɗai ba. Kowa da ke falon sai da ya kalli Alhajinmu cikin mamakin kalaman shi.

"E kin yi kuskure guda ɗaya. Kuskure kuma shi ne me ya sa kika ta ka zuwa gidan Asma'u ki ka ja ta da faɗa? Me ya sa kika yi haka?

"Raina ne ya ɓaci Alhaji. Raina ya ɓaci na ji baƙin cikin da ban taɓa ji ba, shi ya sa sai zuciyata ta ɗebeni har na je gidan ta amma ka yi haƙuri tun da na yi kuskure."

"Na haƙura tun da kin ce na yi haƙuri. Kin amince ba ki kyauta ba?

Sai na gyaɗa masa kai lokaci ɗaya ina mai dukar da kaina ina mai kallon adon cafet ɗin falon.

"To tun da kin amince ba ki kyauta ki juya ki ba ma Asma'u haƙuri."

"Shi ne adalci kam"

In ji Baaba.

Ba domin Alhajinmu ba ne da ba wanda ya isa ya sa ni ba ma Ma'u haƙuri amma Alhajinmu ne shi isar kowa ne anan falon gabaɗaya.

"Ki yi haƙuri."

"Ba komai."

Ma'u ta faɗa lokaci ɗaya ni da ita muna kallon juna. Kafin kuma kowa ya kauda kanshi gefe amma ni na gani sai da ta yi wannan shegen mirmishin na ta, a raina na ce wannan mirmishin yau na faɗuwa ba na nasararki ba ce Ma'u.

Da haka taron ya tashi Ma'u ba ta yi gigin zama ba saboda ba ta ga fuska ta bi mijinta zuwa gida nima Yallaɓai na bi muka koma gida. Ya Murja ce ta kusa sakani dariya da ta na ce ma Ya Aina ta yarda da Ma'u ta ci amanarta da ka gaya mata mgana ta je ta kai shi gaba, sai dai ta ga haka ya faru ne ta ke faɗin Ma'u ta na da daman halin an ce ka ce musamman daman a kaina ta yi ta cewa na yi mata kaza na yi mata kaza. Ban yi magana ba amma dai na yi dariya, saboda da ko da  na yi mgana sai a ce ni ce mai fitina yanzu ai sun ga gaskiya Baaba dai duk baki ya mutu. Kuma ita ta so haka ta san gaskiya amma sai idanuwanta suka rufe daga  ƙarshe sai ta ji kunya gaban surukai.

Ranar a gida muka yini ni da Yallaɓai bai fita ba. Muna tare ya na ɗan jana da hira har na saki jikina kaɗan. Tun daga ranar ban ƙara komawa ɗorayi ba, ballantana Gwammaja da na ji ma gidan ya fita daga kaina kwata kwata. Nene dai bayan lokaci ina kiran ta mu gaisa. Anty Bahijja kuma ban ƙara ganin ta ba, Gimbiyar ma haka tana can gidan Nene tun da an sake ba ta bedrest na sati biyar kuma ba a son zirga zirga. Harkan gabana kawai na ke yi tun da suka sha ni na warke shi kenan na koma tsoron duniya an fi sati biyu ban dawo dai-dai ba, har Tariq sai da ya kirani a waya ya na ba ni haƙuri haka ma Farida. Kawu Abba ko har gida ya dawo ya yi ta ba ni haƙuri na ce komai ya wuce. Mganar Marwa ko ya ce ba fashi manya ma suna shirin shiga cikin maganar tun da ba ya so shekara ta ƙare ba a yi auren ba.

Maganar gaskiya na fi wata ban iya mantawa da abin da ya faru ba. Ni gabaɗaya ma kowa sai ya koma ba ni tsoro. Ba dangin nawa ba na Yallaɓai ba har Amina sai daga baya ta ji labari ta yi ta ashar ta na zage zage. Sai ga Ma'u ta na min mgana a chart na ban hakuri na yi block ɗinta har ta test massages ta ke turomin, amma na share ta. Ai an gama har abada ba zan ƙara yarda da ita ba. Nesa nesa kallon kura a tsakanina da ita shi ne zaman lafiyata

Yallaɓai kuwa shi a ƙoƙarinsa na manta komai na sake rumgumar Yayarsa da Matarsa kamar baya. Ni ko na faɗa masa har abada. Za dai kawai a yi sha'ani, ni matar tashi ma ta fi ba ni mamaki yadda na sakankance da ita ta cutar da ni, itama ta turomin test mai tsawo na ban haƙuri ko karantawa ban yi ba na goge saboda ni gabaɗaya sun fita daga zuciyata ba na jin ko nan da shekara ɗaya ne zan iya sake sakin jiki da su. Ina ganin har abada ni da su.

*Janafty*
*TKG02020AA*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX


*BAYAN WATANNI UKU*

Watanni uku sun zo sun shuɗe kamar ƙiftawan ido. A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah da haka muke ta cinye kwanakin mu ba tare da mun farga ba.  A cikin watanni ukun da suka gabata, ba ƙoƙarin da ban yi domin na manta da abin da ya faru tsakanina da Gimbiya da su Anty Bahijja ba amma na kasa.  Duk lokacin da na tuna sai na ji gabaɗaya rayuwata ta yi ƙunci. Sai na ji zuciyata ta chunƙushe ga shi dai har a zuciyata na yafe musu amma kuma na kasa mantawa da abin da suka yi min. Barin ma in na ga ɗaya daga cikin su sai abin ya zo min shar a cikin raina.

Bayan faruwan lamarin na daɗe ba na zuwa ko'ina ina gidana. Har sai da Nene ta kirani a waya ta na faɗin saboda Anty Bahijja itama na yi mata ya ji, dalilin haka ne ya sa na je Gwamnaja na gaishe da Nene Allah kuma ya taimake ni Gimbiya ba ta nan ta je ganin likita har kuma na baro gidan ba su dawo ba, Nene sai da ta ba ni tausayi yadda ta riƙa bani haƙuri kamar ita ta yi min laifi. Saboda ita na ji a raina wataƙila in muka haɗu da Anty Bahijja na iya gaisheta. Amma ba saboda darajan ta ba sai domin ta ci darajan Nene da Yallabai su ne kawai za su saka in muka haɗu na iya buɗe baki na gaisheta. Amma a cikin idanuwana ba na kallon ta da ƙima da girman da can baya na saba ganinta dashi.

  Ilai ko mun haɗu da ita a gidan Nasara lokacin da ta haihu ranar suna. Sai ga ni ga Anty Bahijja da Anty Maimuna. Daƙyar na iya daurema zuciyata na gaishe su. Suka amsa suma cikin irin yanayin da na gaishe su. Kuma har na bar gidan sunan nan bamu ƙara mgana ba, ni ina tare da su Hauwa su kuma suna ciki tare da su Suwaiba. Gimbiya ba ta zo ba, ta na can Gwammaja ba ta fita tun da ta na ƙarƙashin dokan likita ne a bakin mijinta na ke jin kwanakin cikinta ya ɗan dawo baya, saboda raunin da ya samu amma ya tarkato ta ya kawo min ita har sau biyu gida na da sunan ta ƙara ba ni haƙuri amma bayan gaisuwa ban sake yarda wata mgana ta haɗamu ba sai ma na bar mata falon ita da yara da mijin gabaɗaya.

A zuwan ta na farko bai yi magana ba sai da suka ƙara dawowa shi ɗin ma daddare ne ya ɗaukota ya sake kawo min ita da cewarsa ta ƙara sake ba ni haƙuri
"Yallaɓai ka daina sa ta wahala ni fa na riga na ce na yafe tun a wancan lokacin"
Haka na faɗa masa amma sai ya dake da cewa in na ce na yafe me ya sa ba zan saki jiki da ita mu dawo kamar da ba.

"Yallaɓai da kamar wuya mu dawo kamar baya. Kawai ka bar ni tun da na ce komai ya wuce a bar shi a komai ya wucen mana."

Ya ƙara nacewa da cewa wai ai shima ya na yi min laifi nima ina yi masa mu yi faɗa sosai daga baya kuma mu manta komai mu zo mu shirya me ya sa yanzu ba zan manta ba.

"Kai Mijina ne. Kuma Ubangiji ne kaɗai ya san falalan da ke cikin aure. Wataƙila laifukan junanmu Allah ne ke umartan mala'iku suna shafe su daga cikin zukatan mu saboda martaba da daraja irin ta aure. Ita kuma matarka ce ita ɗin ba dole na ba ce, gaba ne ba zan yi da ita ba in muka haɗu za mu gaisa amma ka yi haƙuri ba zan ƙara sakin jikin da na yi a baya ba. Hausawa suka ce ruwa cikin cokali ya isa mai hankali wanka."

Amsar da na bashi kenan a lokacin na samu ya shafa min lafiya da kawo matarsa tare da min magiya na saki jiki a koma kamar baya sai ka ce ba ni da tunani ko ban san ciwon kaina ba. Ma'u ma mun haɗe sau biyu da ita bayan abin da ya faru, na farko mun haɗu a Ɗorayi da Baaba Aminu ya zo Gwaggo ta kikkiramu ta ce mu zo mu gaishe shi. Ban fara yi mata magana ba ita ce ta gaishe ni na amsa kuma bayan nan har na koma gida magana ba ta ƙara haɗamu ba, amma su Ya Aina kam har sun manta sun sake sakin mata ni dai kan an gama sha ni kuma na warke. In aka yi maka laifi ka nuna an yi maka haka ma Annabi(SWA) Ya ce. In kuma a ka ba ka haƙuri to ka haƙura amma kar ka manta domin rashin mantawar shi ne zai ba ma mutum daman kar ya ƙara sakankacewa a sake cutar da shi.

  Sai haɗuwa ta biyu a gidan Ya Balki da Firdausin ta ta yi sauka Qur'ani muka je walima a gidan ma ita ta fara min mgana muka gaisa shima kuma har muka rabu ba wanda ya ƙara tanka ɗan'uwansa ni fa da gaske na ke yi da na ce na yanke alaqa da ita. Kuma na ji daɗin yadda har Alhajinmu wannan karon bai tsamamin bq. Amma a raina na ce itama ba zan yi gaba da ita ba amma zumunci kamar ba ya ne dole ya ja baya a tsakaninmu. Dalilin haka ne ya sa har munafukan ƙawarta shema na daina ganin ta na ma na zarya a gida in wani abu ya faru. Ido ai da kunya ita kanta Ma'u ba ta san kunya ba ne shi ya sa ta iya gagicewa ta na shiga cikin jama'a bayan duk tsiyar da ta tafka.

Maganar Marwa da Kawu Abba manya har sun shiga ciki amma ba'a saka rana ba. Cikin watan da zamu shiga Yallaɓai ya ce za a je a saka rana ita ma Marwa alokacin za ta koma makaranta ta ƙarishe semester ɗin ta. Koma da wani abu a zukatan su Anty Bahijja maganar da Kawu Abba ya yi ta rufe bakin kowa. Yan'uwan shi ko murna suke yi domin abin da suka daɗe suna jira ne sai yanzu ya tabbata. Shi ya sa ko kaɗan ba su damu ba su dai fatan alheri suke yi da fatan Allah ya sa albarka. Ta bakin Nene ta ce abin da muka daɗe muna jira ne mu dai ya furta ya na son wata zai aure ta kuma tun da har ya gani kuma ya na so za a nema masa kuma a aura masa. A cewar wasu ƴan'uwa daga can Rano wai Marwa ɗin an ce yarinya ce ta yi masa ƙanƙanta shi kuma ya ce tun da ita ba ta ce ya yi mata girma ba shima ko bai ga ƙanƙantarta ba.
Da Yallaɓai ke faɗa min abin da ke faruwa sai da na yi dariya a fili na ce Marwa ai ta wuce yarinya shekarata ta ashirin da uku ta ke ba, waɗanda ma ba su kaita ba an yi musu aure sun zauna ballatana ita? Yallaɓai ya ce shima haka ya gani amma shi sai ya danganta haka da cewa haushi ne bai nemi ƴaƴan su na nan Rano ba ya tsallake sun kuma rasa abin kushe shi ya sa suka ɓullo da haka. Ba su san Abba na dai-dai da su ba. Muna ta dariya ni da shi ni kaina ina jinjina masa ya na da dakiya sannan kaifi ɗaya ne in ya ce A to ko ruwa da iska ba su isa su saka shi ya sauya ra'ayi ba. Shi ya sa na sha faɗa ma Ya Aina da Marwa za su yi alfahari da wannan auran watan wata rana in sha Allahu.

Tuni na daina shan mganin asibiti. Na hannuna na ƙarewa na daina sha, ban kuma sake komawa asibitin ba. Gani na yi na daɗe ina amfani da na asibiti ba a samun abin da ake so ba sai dai sauƙi kam. Tun da al'adata na samu ya dai-dai ta. Sai kawai

41 / 48