sai itama ta ce.
"Daman ko ba ka kirani ba Ya Sule ni zan kira ka. Kana da labarin Sadiya ta je har gida ta daki Ma'u? Me ta yi mata? Ko na ce me Ma'u ta tsareta mata da ta tsane har haka?
Ni da Ya Hamza muka kalli juna cikin mamaki. Ni fa ban yi wani mamaki ba domin yadda na san yunwar cikina a haka na san wacece Ma'u kuma ina da tabbacin ta san Ƙwanta ne ya fashe ya yi wari shi ne ta kira Baaba ta shirya mata mgana yadda in aka taso da maganar za ta samu mai tsaya mata.
"Na samu labari. Kuma akan haka ne na ce ki zo."
"To ai dai ya fi. Gwara ga Sadiya ga Ma'u sai na ji abin da ta yi mata da ta bi ta har gida ta dake ta"
Ta na ta faɗa fa, ta na nuna daman ai tun zuwan Ma'u gidanmu ba ƙiyayyar da ban nuna mata ba, yanzu ma ta yi auren ban ƙyaleta ba to itama ta daina yin shuru wannan karon sai ta ji dalili.
"Baaba ma ta na ƙara ɗaure ma yarinyar nan kugun yin wasu abubuwan"
Ya Hamza ya faɗa cikin mamakin mganganun Baaba a waya.
"Daman ai Hasiya ba ta son laifin Ma'u. Shi ya sa ta ke goyon bayan duk abin da ta faɗa mata."
Ni dai mirmishi kawai na yi, to ko na yi mgana ban san me zan ce ba. In faɗa musu saboda Ma'u Baaba ta tsane ni ko na ce daman tun can ba ta so uwata ba shi ya sa nima ba ta sona. Ko na faɗi haka za a iya ƙaryatawa amma a cikin raina na kudiri niyyar gobe in aka zo zama wallahi ba zan raga mata ba, tunda ni ba ni da uwar da za ta kare laifina ai ina da bakin da ni zan iya ƙwatan kaina.
"Bakomai. Allah ya kaimu goben zan kira Asma'u ta zo da megidanta kema goben ki taho tare da Yusufan kin ji?
Alhajinmu ya faɗa ya na kallona sai na amsa da in sha Allahu. Ban daɗe ba bayan azahar na koma gida saboda na bar gidan ba shara. Bayan na tuɓe na share gidan na yi mopping na saka turaren wuta gidan ya ɗau kamshi.
Mganin da Inna Mariya ta kawo min ko a raina ban ji ba na so na yi amfani da shi ba. Daman na asibitin sauran kaɗan na adana shi da cewa na asibitin na ƙarewa zan fara amfani da shi in gani ko za a dace. Duk da ko na asibitin ma ya yi min sosai. Ya dai-daita min lokacin al'adata kwanakin nan yanzu lafiya lau na ke yi na gama sannan ba wannan azababben ciwon maran sai ɗan abin da ba rasa ba.
Sai shidda su Jidda suka dawo daga hadda. Allah ya sa na gama abinci da wuri jalop ɗin kuskus na yi musu mai kayan lambu da hanta abinci ni kaina na san ya yi daɗi. Haka Jidda da Baby suka rika santi suna faɗin" Umma girkin ki ya yi daɗi sosai."
Ina dariya na ce ko na saka musu waigi ne suna santi ne. Daman sun dawo a jigace tea kawai da buredi suka tafi dashi makaranta to daman ina tea zai riƙe su tun safe har yamma dole su ji kunya. Maimakon su dafa ko indomie ne, ko da ya ke na rasa me ya sa ba su son tafiya da indomie makaranta, barin ma Jidda sai ta ce wai indomie na yara ne, in dai ba ni ce na tashi na dafa musu taliya ko shinkafa suka tafi da shi ba ta gwammace su ɗura tea a goran su da buredi su tafi dashi akan su dafa indomie.
Yallaɓai sai wajen tara na dare ya dawo ya zo da yara da rake mai yawa ya ce Nene ce ta ba shi ya kawo mana ni da yara. Na karɓa na ce mun gode daman ko bai faɗa ba na san zai biya ta can tun da matarsa na ca. Jidda ce ma ta tambaye shi ina Anty Gimbiya? Ya ce ta na gidan Nene ta na gaishe su amma ni ko sunanta na ji an ambata sai raina ya ɓaci kuma a saman fuskata ma rashin jin daɗin ya na bayyana. Tun a daran na faɗa masa Alhajinmu na neman mu ni da shi a gida gobe, bai tamnbayi dalili ba ya ce Allah ya kaimu.
Shi ya sa tun safe na tashi na dafa ma su Jidda Macaroni da Miya suka tafi da shi makaranta. Indomie kuma suka ci kafin su tafi, sai da na yi wanke wanke na gyara kitchen sannan na yi wanka shara daman na ce na gaji gaskiya sai gobe ina dalili har bayana na ciwo. Saude duk ta sangartani, mu kan mu da indomie da ƙwai muka karya sannan muka fita, muna hanya Ya Aina ta kira wayara wajen goma na safe tace kowa ya zo ni kaɗai ake jira na ce gamu nan a kan hanya.
Ko da muka isa falon Alhajinmu cike, har Baaba ta iso matar nan ina gaisheta ba ta amsa ba, ni ko ban ƙara ba na wuce wajen Gwaggo na duka ina gaisheta ita da Alhajinmu. Shi kuma Yallaɓai ya fara gaisawa da Mazan har Ya Auwal na gani shi jiya da yamma ya sauka garin. Sai Ya Muntari da Ya Abubakar sai Alhaji Mustapha, matan kuma daga ni sai Ma'u sai Ya Aina sai Ya Balki sai kuma Ya Murja sai Gwaggo da Baaba.
Dukkansu na yi musu magana ban da Ma'u. Saboda sai da na ganta na sake jin wani ƙuna ya taso min daga ƙasan zuciyata ta kalle ni nima na kalleta amma ba mu yi ma juna mgana ba. Sai dai na ɗan ji sanyi da na ga fuskarta gefe da gefe duk sun kumbura.
A gefen Ya Aina na samu waje na zauna shi kuma Yallaɓai sai ya zauna a gefen da Ya Hamza ya ke zaune a ƙasan cafet ɗin da ke malale a falon Alhajinmu.
Ya Muntari Alhajinmu ya umarta shi ya buɗe mana taro da addu'a. Sannan ya ce dangane da sanin dalilin taruwarmu wasu sun sani wasu kuma ba su sani ba. Amma yanzu zan ƙara mamaita dalilin taruwarmu anan wajen yanzu nan kuma.
Kiran sunana Alhajinmu ya yi na amsa sai ya ce na faɗi duk abin da ya faru daga farko har ƙarshe. Na ko gyara zama na fara maida zence kafin na gama Ma'u ta fara kukan makirci Baaba ko ina dire maganata ta nuna ni da yatsa kafin ta ce" Ƙarya kike masharranciya. Asma'un ne za ta faɗi haka? Ai ko ba ta san in da kika fito ba Sadiya Asma'u ba ta da wannan halin ki dai canza wata ƙarya wannan ba ta hau ba."
"In karya ake yi mata ai ga ta nan sai ta ƙarya ta ko?
Ya Hamza ya katse ta itama sai ta kalleshi kafin ta sake wata mgama ya kalli Ma'u ya na faɗin" Ba ga ta nan ba. Ta buɗe ta ce duk abin da aka faɗa sharri ne ba gaskiya ba."
Sai Baaba ta kalli Ma'u ta na faɗin" Bar kuka buɗe baki ki karyata ta a gaban kowa da kowa"
Na san daman Ma'u za ta iya karyata ni shi ya sa ma da ta buɗe ba ki ta ce ƙarya ne ita ba ta faɗa ba ban yi mamaki ba.
"To kun ji dai ko? Ina fatan yanzu za ku yarda Sadiya na bin Asma'u da bi ta da ƙulli. Kuma magana kan dangin bokaye ba Mau ce ta faɗe shi ba tun tale tale haka ake kiran gidan su Ruƙayya da shi, su kan su ai ba su isa su hana ba. Wataƙila itama yayar mijin na Sadiya a can a gari ta ji labarin shi ne saboda kin tsani Asma'u za ƙi kulla mata sharrin ita ta faɗa ko?
Ta ƙarishe faɗa ta na kallona sai ma na kasa mgana, ina tattaro abin da ya kamata na maida mata kar ace na yi rashin kunya.
"Baban Jidda ko za ka taimaka ki kirana mana ita yayar naka? Kamar muna bukatar ta anan wajen"
Ya Hamza ya faɗa fuskarshi a ɗaure. Shi ko Yallaɓai ya fito da waya a cikin aljihun ya na faɗin" Ba zai gagara ba, bari na kirata na ce ta taho yanzu."
"Yauwa mun gode. Ke kuma yanzu ita wacce kika faɗa ma mganar za ta zo. A cikin su za mu gano mai son ya yi wasa da hankalim mu"
Ya faɗa ya na mai kallon Ma'u Gwaggo na gefe ta ce gwara haka domin kar ma a ja mganar da nisa. Alhajinmu kuma na zaune amma bai yi mgana ba.
Ina ga Ma'u ta ɗauka wasa ne ba za a kira Anty Bahijja ba. Sai da ta ga Yallaɓai ya kira wayarta ya kuma saka a speaker sai ta rage kukan makircinta ta na ƙifta idanuwana kamar wacce ta yi ƙarya. Allah na tuba ai ƙaryan ma ta yi.
Ta na ɗaukan wayan da sallama Yallaɓai bai ma tsaya amsawa ba ya ce" Ina gidansu Sadiya. Ana maida mgana Ma'u ta ce ita ƙarya ake yi mata mganganin da kika ce ita ta faɗa ta ce ba ta ita ba ce.
"In ji ita Ma'un?
Anty Bahijja ta tambaya cikin mamaki.
"E. Shi ne aka ce ko za ki iya zuwa nan gidan su Sadiyan?
"Me zai hana? Ai sai na zo. Kuma in ba Ma'un ta ke faɗa min ba ina na ke jin wasu labaran? Ita ta san ita ta zo asibiti duba Gimbiya ta faɗa min mu yi hankali da Sadiya za ta iya sanadin cikin Gimbiya tunda sun yi gadon shiga bokaye ko a gabanta zan iya maimaita haka sai ta ƙaryatani na gani"
"To shike nan in da buƙatar zuwan na ki zan sake kiran ki"
Daga haka Yallaɓai ya katse kiran gabaɗaya sai kowa ya maida hankalin shi kan Ma'u da ta yi wani iri da ka ganta ba ta da gaskiya. Shi kan shi mijin na ta a cikin mamaki ya ke kallonta.
"Da sake. Wannan sharri ne ban yarda da mganaganunsu ba."
Baaba ta faɗa a fusace itama fa ta san gaakiya amma ta na neman take gaskiyan.
"Za ki faɗa mana gaskiya ko sai ranki ya ɓaci?
Ya Hamza ya faɗa cikin tsawa. Da ya sa Ma'u ta tsorata daman ko a baya ta na son shi amma kuma ta na shakkar shi. Sai kawai ta fara ɓarin jiki amma ta kasa mgana.
"In faɗa ko ba ki faɗa ba?
Ya sake maimaita tambayarsa cikin hargagi da ba ta san lokacin da ta ce e ita ta faɗa, Masu ƙoƙarin kare ta ma duk sai suka yi shuru jikinsu ya yi sanyi kuma ta ce ita ta faɗa amma ta koma ta na ta faman kuka.
Ya Hamza sai sake mgana Alhajinmu ya ɗaga masa hannu.
"Ƙyaleta Hamza. Yi mata a hankali mana."
Ya faɗa cikin yanayinsa kafin ya mai da kallonsa kan Ma'u da ke kukan munafumci.
"Asma'u"
Ya kira sunanta ta amsa cikin kuka in ka ganta sai ka rantse da Allah an yi mata wani abu ne ko wani nata ne wani abu ya same shi ko an yi mata mutuwa.
"Me ya sa kika aikata abin da kika aikata Asma'u? Me ya sa kika zaɓi ki tozarta yar'uwamki da ahalinta a idon duniya? Me ya sa kika aikata haka? Me ya sa kika zama haka? Ina ganin ki da girma a cikin idanuwana amma aikata abin da ban yi zato ba ya sa girmanki da ƙimarki da na ke gani ya ragu a cikin idanuwanan tabbas Asma'u kin yi ɓarna. Ɓarnan ma mai tarin yawan da kafin a yafe miki sai an ɗau lokaci. Kin ci amanar zumunci, kuma ba Dubu kika tozarta ba, ni kika tozarta kamar yadda itama in ta yi miki wani abu na tozarrci to itama ba ke ta yi ma wa ba. Ni ta yi mawa"
Ya ƙarishe faɗa cikin kaushin murya ka na ji za ka san ran shi ya gama ɓaci. Ma'u sai kuka ba mgana saboda ba ta da tacewa.
"Ina jin ki. Ki bar kuka ki faɗamin dalilin ki na yi ma zuru'an ki wannan tozarcin Asma'u. Ni fa da kaina na kira ki na kira Dubu na kira mazajenku na tara ku na yi muku sulhu. Na san Dubu da na fitina da riƙo amma ba ta tsallake mganata tun da na ce ta yi zumumci da ke ta ce za ta yi na san za ta yi ne. Kuma zan iya ba da shaidar ta ba ma ita ba kaf ɗin su ba za su yi miki ƙwataƙwacin abin da kika yi ba, sannan in suka ga wanda zai ci mutumcin ki sai in da ƙarfin su ya ƙare. Amma abin tir sai ga ki da kan ki kike zuwa kina cin zarafin yar'uwanki domin ki ɓata mata suna ki kuma haddasa mata fitina a gidan aurenta? Shin me kika aikata? Kin san sunan abin da kika aikata! To sheɗanci ne. Kin zama sheɗaniya tun da kin zama silan haɗa fitina da dama. Kin ba ni kunya, ban taɓa zaton haka daga bangaren ki ba Asma'u."
Ma'u sai kuka ba mgana, kowa jikinsa ya yi sanyi amma ban da ni domin ni na san wace ce Ma'u a kukanta ma ba Saduda a cikin shi. Alhajinmu ko a yadda ya ke mgana ranshi ya riga ya gama ɓaci, Baaba ce ganin Ma'un ta ƙi mgana sai kuka sai ta tare mganar da cewa.
"Yaya Sule ba fa gaskiya ba ne Ma'u ba za ta yi ma Sadiya haka ba. Sai ma ita Sadiyar ce in aka ce ta yi hakan ba zan yi musu ba, saboda tun tuni ba ta ƙaunar Asma'u kowa kuma ya san haka. Shi ya sa na ce a yi.."
"Ba ke na ke tambaya ba Hasiya. Ki bari Asma'u ta ba ni
Amsa."
Alhajinmu ya dakatar da ita a fusace da ya sa dole ta yi shuru ita kanta ta ji kunya ba za ta nuna ba ne, to ga suruki a wajen kuma ya gano munafuncin yarki dole kunya ta kamata amma da ya ke ba ta san kunya ba, ta na ƙoƙarin nuna a yi adalci yarta ce mai gaskiya ni ce mara gaskiya.
"Muna sauraran ki. Ki faɗa mana dalilin ki na aikata abin da kika aikata."
Alhajinmu ya sake tambayarta da ya sa cikin shessheƙan murya ta ce" Ban da wani dalili Alhaji sharri sheɗan ne don Allah ka yi haƙuri."
Ta faɗa ta na kuka kamar za ta shiɗe Ya Hamza ya fara masifan ai mutum ba ya aikata laifi kuma ya ce ba dalili ita dai ta san dalilinta na aikata abin da ta aikata.
"Wallahi ba ni da wani dalili kawai dai sharrin sheɗan ne"
Ta sake faɗa ta na gunjin kuka. Sai kowa ya yi shuru ya ba sauraranta.
"Alhajinmu ka yi haƙuri ka yafe min. Kuma zan karɓi duk hukuncin da ka yanke min"
Ta sake faɗa tana kuka, sai na zama yar kallo kawai domin film kawai Ma'u ke yi ta na zuba acting. Kukan da ta ke yi domin a ji tausayinta ne amma ni na san wallahi ba kukan nadama ba ne.
"To in sharrin sheɗan ne me ya sa shi sheɗan ɗin bai faɗa kan kowa ba sai kan Sadiya? Ki dai faɗi manufarki kawai."
In ji Ya Auwalu Ya Hamza kuma ya karɓe da cewa" Nima shi na gani ba rami ba abin da zai kawo maganar rami."
Karar Baaba ta karɓe da cewa" Ba ya wuce yar tsaman dake tsakanin su. Tunda kuma ta ba da haƙuri ai shikenan ko?
"Ba shiken ba Baaba."
Na faɗa a fusace saboda na ga tana son ture laifin yarta.
"Ba shike nan ba, zarafina ta ci, ta yi min ƙazafi yau ko ƙararta na kai wallahi sai min yi sharia da ita."
Baaba sai ta kasa mgana ni kuma sai na cigaba da faɗin"Me ya sa duk a cikin gidan nan ba ta son ganin bayan kowa sai ni? Me na yi mata? Abin tambayan kenan ni kuma na san abu ɗaya ne na yi mata tun a baya da na faɗi cewa Ya Abubakar na sonta har aka fasa auranta da Ya Hamza. Daman tun a baya ta faɗa min zan gani yadda na hana ta abin da ta ke so nima sai ta yi barazana da farinciki na ga shi kuma ta ɗau hanya kuna gani."
Na faɗa ina kallonta ta tsorata ba ta ɗauka zan kawo wannan mganar ba sai ta daburce tun da ga mijinta a wajen ta fara rantsuwan ba haka ba ne.
"To in ba haka ba me na yi miki? Miji ɗaya muke aure ko facaloli ne mu da za ki bi ki addabi rayuwata?
"Wallahi ba ki yi min komai ba Sadiya ko a baya da na faɗi haka yarinta ne. Amma tunda na auri Alhaji na cire komai a raina domin ya zame min garkuwan da na ke jjingina dai-dai da rana ɗaya ban taɓa nadaman auran shi ba."
Sai ta ɗan dakata ta na kuka shi ta ke kallo, duk makircinta na fahimta ba ta so mganganuna su yi tasiri a zuciyarsa shi ya sa ta tsiro da wasu maganganu.
Shi ta ke kallo ta na faɗin" Alhaji shin dai-dai da rana ɗaya ka taɓa ganin wani chanji daga wajena a kan ka?
Sai ya girgiza kai kafin ya ce" Babu Ma'uta. Kuma kin ban labarin daman cewa Yayanki Hamza aka so ki aura sai Allah bai yi ba. Ni tsakanina da ke sai godiya da tarin alheri Asma'u."
"Alhamdulillah ka gama mgana"
Baaba ta faɗa da ƙarfi,kawai sai na ga Ma'u ta rarrafa zuwa gaban Alhaji ta faɗi ta na faɗin" Ka yi min gafara Alhaji in ba ka yafe min ba ina za ni Ba ni da wani uba kamar ka Sannan ba ni da wani gata sai gatan ka da gatan ƴan'uwana Don Allah ka yi haƙuri ka yafe min sharrin sheɗan ne ba zan ƙara ba."
Bai ce komai ba sai ta cigaba da kuka ta na masa magiya sai ya saka hannu ya ɗaga ta zaune ya na cewa ta share hawayenta.
"Na yafe miki Asma'u. Uba ba zai taɓa riƙon yarsa a zuciyarsa ba. Sai dai ba shi zai hana ban faɗa miki cewa ba ki kyauta ba kin yi kuskure