Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   20 / 48

57K to 60K   out of 141.5K words

fara ihu tun tana kiran Abba sai ta koma Umma ki yi hakuri Ya Jidda Ya jidda. Ta na kuka ta na majina karshenta dai Jiddan ta ƙwace ta, ta na ba ni hakuri.

"Don Allah Umma ki yi haƙuri."

Kwafa na yi kafin na ce"ka ji min yarinya mara mutumci kawai da mangariban nan ki ɗaga min hankali! A'a ba gidan Anty Gimbiya ba saura gidan Sarki."
Raina a bace na koma ɗaki ina magana ni kaɗai.
"Mata duk ta bi ta gama min da ƴaƴa. Ina dalili."
Wayata da ta kwana ma a kashe ban san ko uban na su ma yau ya tuna da su ya neme ni ba. Sai ga shi can ajuma na koma na ganta har ta yi barci a raina na ce ashe ma iskanci ne irin na yara, Jidda ma da wuri ta kwanta ranar amma ni na ɗan dade ina kallo saboda ma kar na kwana ni kaɗai na yi tunani na ce Jidda ta zo ɗakina mu kwana ni kuma na ɗauki Baby na kaita bedroom ɗina na kwantar.

Ranar tare da yara muka yi barcin mu har da su makara domin sai shidda na safe muka farka. Qur'ani na riƙe shi kuma ya kawo min salama da kwanciyar hankali a kwanakin da Yallaɓai ya yi a gidan wata mace ko na ce wata matar ta sa bayan ni, sai a ranar na kunna wayata na kikkira mutane na yi musu ban gajiya Amina ma ta ce jiyan da suka isa gida ta yi ta kirana a kashe haka ma Farida ta ce itama ni dai na ce su yi hakuri wayar ce ta mutu ba chaji ban sani ba.

Ina lissafe da yau kwanan Yallaɓai uku kenan a gidan Gimbiya na ɗan ji ba daɗi da na kunna wayata ban ga saƙon shi ba amma dai ina ji a jikina ya kira ni wayar ce bai samu ba. Ko bai sanar da ni ba na san kwanakin bazawara kwana uku ne yau Yallaɓai zai dawo gidana shi ya sa da yamma na dumama sauran kazar da na siya wajen Hajiya Surayya Halin yau, na ci tare da tsumi karfe bakwai da wani abu na yamma Yallaɓai ya kira ni lokacin ma ina kan darduma ina lazimi ne bayan na idar da sallar mangariba.

Ban ɗauka a lokacin ba sai da ta katse sannan ba daɗewa ya ƙara kira sannan na ɗauka cikin sanyin murya lokaci ɗaya da sallama a bakina.
Sai ya amsa min daga can bangaren shima a sanyayen, tambayar ya kuke? Ya yara na ce lafiya lau daga nan shuru muka yi dukkanmu na wani lokaci.

"Me ya faru jiya da yau wayarki a kashe."

"Ta mutu ba chaji ne ban sani ba."

Domin kar ma ya kawo tambayar ba wuta ne? Shi ya sa na ce ban san ta mutun ba.

"Ok. Yanzu ba daɗewa za mu taho nan gida tare da Daugther"

Haka na ji ya faɗa sai da na dan yi jim kafin na samu damar magana ya cigaba da faɗin" ina so zan yi magana da ku gabaɗaya."

Sai da sauke ajiyar zuciya sanna na amsa masa da cewa.

"Shike nan sai kun ƙariso."

Da ga haka muka yi sallama ban tashi ba sai da na gama lazimina na yi salatin Annabi na shafa sannan na miƙe na ninke darduman na ɗora saman gado daman na yi wanka na saka riga da wando. Ban kuma jin zan iya sauya shigata turaren wuta na ɗauka na fita falo na  saka Jidda ta kunna Burner gidan ya dan yi kamshi Baby kuma na baje a falo ta ba je littafinta na drowing ta na ta zane zane kuma ta na bin shi da kala a baya in na gani sai na hana ta Yallabai ya ce na kyaleta na sani ko ita ce za ta ga je shi? Tun daga lokacin na saka mata ido daga karshe ma katon drawing ya siya mata mai kama da littafi da pensira na zane da clours ya na zane ni, in akwai makaranta ban barin ta yi amma yanzu da suka samu hutu ba na hana ta.

Muna zaune a falon gabaɗayan mu mu ka ji shigowar Motar Yallabai gidan da ƙaran rufe get, tun da karfe ne dole in an buɗe ko an rufe sai mun ji kara. Jidda ta daka tsalle ta mike ta na faɗin" Baby Abba ne."
Daga ita har Baby a guje suka fice baby ta yi falati da kayan zanen ta suka fice da gudu suna kiran oyoyo Abba, na ji buɗe kofar falon da yadda yaran suka naɗe shi da muryan shi ya na faɗin.

"Oyoyo My princess. I miss u."

Ina zaune a in da na ke na kasa tashi. Haka kurum sai na ji gabana na faɗuwa ras! Kamar kuma sai na ji kamar wani tsoro tsoro na shiga ta.
Yau ne fa zan hada ido da kishiya? Kishiyar da mijina ya kwana da ita har uku. Ƙilama akwanakin nan ta samu ciki.

"Auzubillahi minal sheɗanir rajim"

Haka na faɗa da sauri domin koran sheɗan ɗin da ya ziyarce ni.


*Janafty*
*TKG*

*Assalamu alaikum!*
*Ina muku gaisuwa irinta addinin musulunci da fatan masoya labarin ƳAR KARUWA suna cikin ƙoshin lafiya,baya ga haka ina muku albishir da cewa free pages na labarin ya ƙare mun shiga asalin labarin wanda ya kasance shine part 2 na labarin.*
*Karku manta bamu ce komi ba a free page's na labarin domin kuwa yanzu nema za a fara wasan,don haka karku bari ayi tafiyar babu ku masoya.Ku hanzarta ku shigo cikin tafiyar ARCH.AMMAR CHIROMA TARE DA HAFSAT KABEER CHIROMA,Tabbas a cikin wannan tafiyar akwai tarin faɗakarwa,zazzafar soyayya,ƙiyayya mai zafi da kuma halacci.*
*Paid page's sun fara sauka a manhajar whatsapp da kuma Telegram,masu biyiyar arewabook tuni labarin part 2 ya fara nisa a can,sai ku garzaya domin Shan karatu.*

*Ku biya kuɗinku ta wannan asusun Kamar haka👇🏻*

For VIP on Telegram Pay 1k for Whatsapp group Pay 500 in to this account 👇🏻
7087809778
Aisha Dansabo Ibrahim Opay,evidence of payment to 08167768704.

*Masu buƙatar free pages na labarin ku tuntuɓeni ta wannan line ɗin 08167768704.*

10.

Ina zaune ne amma na kasa tashi domin sai na ke jin gabaɗaya ilahirin jikina na rawa. To in ma na tashi wa zan je tarowa? Kishiya ko miji? Kawai sai na yi zama na amma fa zuciyata bugawa ta ke yi da sauri da sauri cikin lokaci ƙalilan hankalina ya tashi ina neman fita hayyacina saboda wani iri abu na ke ji yana ta so min daga ƙasan zuciyata.
Kishi masifa ne, zai iya haifar ma da mata lalura mai karfin da nan ta ke za a iya kai su emergency a yi tunanin ciwon ya daɗe a jikinsu ne ba a sani ba alhalin kishi mai saka ma zuciya ciwo nan take ba tare da mutum ya sani ba.

Idanuwana suna kallon ƙofar falon suka shigo, shi ya buɗe mata kofar ta fara shigowa hannunta na riƙe da na hannun Baby.  Sai shi ya biyo bayan su, shima hannunsa na riƙe da na Jidda. Gimbiya fara ce sosai doguwa domin har ta ɗan fini tsawo sannan tana da jikin murjewa kyakyawa ce domin hancin ta har baka. Sanye ta ke da atamfa mai kalan orange shi ya sa mayafin da ke jikinta ma kalan shi kenan, shi kuma Yallaɓai an cakare cikin ƙananun kaya har da zanzaro. Dukkansu fuskarsu tana fitar da wani annuri ne. Annurin da ka na ganin shi za ka san na farinciki ne wanda zuciya ke samu ta hanyar gangan jiki.

Duk ina zaune ne na ƙare musu kallo, ina ganin za mu haɗa ido da su na yi saurin ɗauke kaina ina jin zuciyata na ƙara tsananta bugawa. Ina jinjina ma matan da ake yi musu kishiya sannan a haɗa su zama da su a gida ɗaya. Wallahi in ni ce ba zan iya ba, domin na tabbata wata rana zan iya haɗiyan zuciya na mutu saboda baƙin ciki.  Da na so na tashi na tarbe ta amma daga baya kawai sai na fasa sai ma gyara zaman da na yi daga in da na ke zaune na ce.

"Sannun ku da zuwa."

Na faɗa ina ƙara gayyato mirmishi a saman fuskata.
Ita ta amsa amma a hankali shi ne na ji amsar ta shi da ƙarfi yaran na maƙale da su, shi ya nuna ma Gimbiya kujeran da za ta zauna na zaman mutum biyu, ta isa ta zauna Baby ta haye jikinta shi kuma sai ya durkusa a gabana lokaci ɗaya ya na mai riƙe duka hannayena cikin tafukan hannunsa so ya ke mu haɗa ido, ni kuma na ki bashi damar haka sai ma Juyawa da na yi ina kallon Jidda da ta zauna gefen Gimbiya sai mirmishi suke yi daga ita har Baby umh yara ai ba ku san dawan garin ba.

"Jidda kawo ma Antyn ta ku ruwa da lemu mana."

"To Umma."

Ta faɗa da saurin ta sannan ta ta shi ta nufi kitchen ɗin.

"Kalle ni mana Sadiya ta."

Ya faɗa ya na leƙa fuskata sai na yi fuska ma maze na kalle shi ta ƙasan idanuwana. Haushi fa ya ke ba ni, hannayena ma da ya riƙe ji na ke yi kamar na ƙwace, domin haskowa na ke yi da waɗanan hannayen na shi fa ya riƙe Gimbiya da su, shi ne nima zai dawo ya na taɓa ni tuni na ji gabaɗaya hannayensa sun zame min kamar lantarki mai ja a cikin hannayena sai ƙokarin kwacewa na ke yi ya na ƙara riƙe ni, ita kuma Gimbiya ba ta kallon mu tana ta hiran ta ita da yara.

"Yallaɓai. Ka bari mana."
.

Na faɗa bayan na ƙwace hannayena lokaci ɗaya ina kallon shi.

"Ba ki yi mini sannu da zuwa ba."

Ya sake faɗa yana mai ƙure ni da ido.

"Shi wanda na yi maka fa?

Kawai sai ya buɗe mini hannuwansa yana faɗin" Ba wannan ba irin wannan."
Kaɗan ya rage ban danno masa na katsinawa ba amma dai na daure ban yi ba, sai ma hararan shi da na yi na matsa gefe ina kallon Gimbiya.

"Ki sha ruwan mana."

Ta na kallona ta ce" Zan sha."

Muka yi shuru ni da ita, shi kuma sai ya zagayo ya zauna kusa da ni har kafaɗan shi na gogan nawa, a hankali na ƙara matsawa sai na ga ya ƙara matsoni, ina kuma ɗaga kaina sai na ga ta na kallon mu shi ya sa na barsa ban ƙara matsawa ba.

"Na yi kewar ki sosai Sadiya ta."

Haka ya yi min raɗa a kunne ya faɗa mini, ko kallon shi ban yi ba domin sai na ga kamar rawan jikin Yallaɓai ya ƙaru ne saboda a gaban matar shi ne, ni zai faɗa ma burauba a gaban matarsa. Kallo ma ni bai ishe ni ba sai ma na juya masa ƙeya ina ce ma Gimbiya ta sha ruwa mana.

"Zan sha "

Ta sake faɗa a hankali tana wasa da yatsun hannun Baby.

"Anty Gimbiya ina ta kuka ina so na je wajen ku ke da Abba."

Baby ta faɗa cikin shagwaɓa ita kuma sai ta shafa kanta ta na faɗin" Ban sani ba da kin kirani da gudu zan zo na tafi da ke My Baby."
Sai Baby ta fara murna, ni ko gani zaune ina yaƙe ban yi mgana ba.

"To ko Baby za ta ture gwamatin Jidda ne kawai sai ki tafi da ita ta ta ya ki kwana."

Sai ta yi mirmishi ta na kallon shi kafin ta ce" Sai abin da ka ce Daddy"
"Duk ɗaya ne ko Baby ko Jidda Daugther. Gwara Jidda ma ba za ta yi rigima ba amma Baby ba za ta yarda ki ta fi da Jidda ita ki bar ta ba."
"Sai na tafi da su gabaɗaya mana Daddy."
Ta faɗa cikin shagwaɓa ta na yi masa wani kallo. Kawai sai na ga ya yi wani mirmishi, mirnishin da na ɗauka bayan ni Yallaɓai ba zai sake yi ma wata mace irin shi ba sai gashi a gaba na a gaban yara Yallaɓai ke hira da wata mace ta na masa shagwaɓa ya na jin daɗi.

"Daughter.."

Ya faɗa ya na yar dariya sai kuma ya kwantar da kansa jikin kujera ya na faɗin" Ke ma kin cika rigima. Su biyu ai sun yi miki yawa. Ita Madam sai a bar ta ita kaɗai ko su je kawai ni kaɗai na ishe ki ko Sadiya ta?
Ya ƙarishe zencensa ya na kallona, ban ko kalle shi ba amma a cikin raina ina jinjina karfin halin irin na Yallaɓai wato ma har ya raba mini yayan nawa amma ni ban da darajan da zai faɗa min, ni fa a baya ne na ke da bakin cikawa a kan Yallaɓai amma a yanzu na shaida munafuki ne na gidi ma, ni fa yanzu ba duka ma mganganunsa ne abin yarda a wajena ba, na tabbata tunda ya ƙara aure zai kulla alaqa da ƙarya da munafunci.

"Ya baƙun ta?

Na katse shurun namu da mganata. Cikin wani karya murya ta ce" Baƙunta ya fara bin jiki."
Ta faɗa ta na ƴar dariya, ni kuma sai na yi mirmishi ba tare da na sake yin magana ba amma da za a tona zuciyata baƙinƙirin ta ke, kiran sunan Allah kawai na ke yi domin saura kiris na fallasa a sirin zuciyata. Mun zauna shuru har na tsawom mintina ashirin ita dai sai hira ta ke yi da su Jidda Yallaɓai kuma ya na ta faman latsa waya ni kuma ina zaune abin tausayi E mana abar tausayi ni da gidana amma na kasa sakewa, sai satan kallon Gimbiya na ke yi sai da na ƙara lura dakyau na ga har da kwalliya ma ta yi, to wai ta manta yau mijin ma ya fita ɗakin ta ne? Sai da na lura sosai sai na ga jefi jefi suna kallon juna ita da Yallaɓai suna sakar ma juna mirmishi, ji na yi kamar na tashi na bar musu falon amma na ƙara dai haƙuri na zauna, ina so na duba lokaci amma wayata na baro ta a ɗaki kuma gashi ba na so na tambayi Yallaɓai kawai sai na yi shuru kamar in yi tagumi in fashe da kuka haka na ji, ban yi hakan ba amma acikin zuciyata Allah ya saka min kawai na ke faɗa domin Yallaɓai ya gama cutata.

Kiran sa a ka yi a waya sai ya tashi ya koma falon shi, ba daɗewa ya dawo yadda ya bar mu haka ya dawo ya tadda mu, ita dai ta na ta hira da Baby mai shegen surutu in ta fara ba ta son ta tsayawa gwara Jidda ta fita Aji shi ya sa na ke son ta ba ta cika surutu haka barkatai ba. sai balla mata harara na ke yi ta gefe amma yarinyar nan ba ta ji ba sai zuba ta ke yi kamar ƴaƴan kanya.

"Kun yi shuru abin ku."

Ya faɗa yana mai sake zama gefena sai a lokacin na saci kallon Yallaɓai kwata kwata bai yi min kyau ba a raina ma faɗi na ke yi Yallaɓai an yi girman banza ka rufe arba'in kana wani cin zanzaro. A baya ne in yi ta masa nacin saka ƙananun kaya ya yi ta kuma cewa shi ba ya son sakawa amma sai ga shi yanzu ya saka har da zanzaro saboda ya burge wata tir! Tsaki na ja a hankali amma kuma sautin ya fita tun da shi ya ji har kuma sai ya kalleni na basar na haɗe rai kamar ba ni ba shi ya sa bai samu damar yi min wata mgana ba.

"Jidda kama hannun Baby ku je falona ku kunna Tv ku yi kallo kafin na gama mgana da Ummomin na ku."

Haka ya faɗa ya na kallon Jidda sai ta amsa masa da to. Amma Baby har da ƙin tashi ta makale ma Gimbiya. Shi ya tsaya ya na lallashinta shi da Gimbiyar ni ko tsawa na daka mata kafin na ce" Za ki tashi ko sai na zo nan na tattaka ki ?
Na faɗa ina mata wani kallo ai kafin ma na yi wani matsi ta sauko daga jikin Gimbiyar ta na neman yi min kuka.

"Kina ɓare min baki yanzu jikin ki zai gaya miki."

Na faɗa ina kallonta jin haka yasa ta koma bayan Jidda ta raɓe, shi kuma Yallabai ni ya kallah kafin ya ce" Haba! Sai ki da ke ta?
"Ta yi kukan sai ka gani."
Na bashi amsa a takaice sai na ga kawai ya tsaya ya na kallona ni kuma na ɗaure fuska ina kallon jidda kafin na ce" Kama ta ku je mana."
Sai ta riƙe hannun Baby suka wuce wacce ta yi narai narai kamar za ta yi kuka ga shi ba hali kuka Gimbiya na ɗaga mata hannu da alamun ta na nan ba tafiya za ta yi ba.

Sai da suka shige da mintina sannan Yallaɓai ya gyara zama gyara murya ya yi irin na juyo na kalle shi sai ma na ƙara yamma da fuskata.
"Wannan hijabin fa? Ki cire shi ki sha iska mana."
Ya faɗa ya na kama gefen Hijabin kamar da gayya ya yi maganar ni zai ma mutumci gaban matarsa. Daman hijabin da na yi salla dashi ne ban cire ba, kawai sai na fizge hijabin daga hannun shi kafin na ce.

"Ka bar min kayana. Tun da kuma ba zafi ake yi ba."

Na faɗa ina jin kamar na rufe shi da duka ni fa na kosa ya gama maganarsa na shige ciki zuciyata ta kusa daina ɗaukan munafuncin Yallaɓai kar ta kai mu ga in ya faɗa na maida masa mara daɗi.

"Halima."

Ya kira sunana amsawa kawai na yi ban kalle shi ba saboda ni dai yanzu in Yallaɓai ya kirani da Halima ban wani rawan jiki saboda na san na yaudara ne shi ya sa na daina ma rawan jiki.

"Daughter."

"Na'am. Daddy".

Ta amsa cikin sanyin sauti. Ina zaune ne amma ji na ke yi kamar ina yawo a sararin samaniya saboda hazo hazo na fara gani saboda wulaƙancin Yallaɓai, ni ya kira sunana sunan da ko ubana da ya yankamin rago ba ya kirana da wannan sunan ya na sakayawa saboda girmamawa haka sauran ahalina Sadiya suke kirana amma shi yau sabida cin mutumci ni ya kira ni da Halima ita kuma tunda sunan Nene gare ta ba zai iya kiran ta da sunanta na yanka ma sai ya sakaya kamar yadda ya

20 / 48