ta ce"Ikon Allah. Ni ban ma san shi ba. Amma ya faɗa ma Babanta tarihin shi ya ce an taɓa saka masa rana yarinyar ta rasu tun daga ranar bai ƙara neman wata ba sai yanzu akan Marwa. Sannan ya ce ya na noma ya na kiwo."
Na karɓe da faɗin" Kwarai an yi masa tallar mata ba adadi ya ce ba ya so. Ke ce ba za ki san shi ba amma Rahila ta san su shi da Tariq tun Yallaɓai na neman aurena sun sha zuwa tare. Ya Aina gidan gona gare shi a Rano wai kin ga gidan da ya gina a can ne? Ba wai ina nuna ya na da kuɗi ba ne amma ina mai faɗa miki ya na da rufin asiri mata da yawa suna rubibin shi saboda in ba ya faɗa ba sai a ce saurayi ɗan shekaru talatin ne ba arba'in. Ke Ya Aina har Shema ƙawar Ma'u ta yaba da shi ya ce ba ya so, kin tuna na taɓa mata mgana har ya so ya zama faɗa kika ce na yi shuru?
Ya Aina cikin mamaki ta ce" Na ko tuna ikon Allah."
Ina dariya na ce" To kin ji fa. Ai mu sai godiya mun yi suruki ni uwar Amarya kuma surukar ango."
Ya Aina ma dariyan ta ke yi kafin ta ce" Kin sani kika yi min shuru ko Sadiya.?
"To ai na yi shuri ina ta addu'a kar na zo na faɗa kuma a ji shuru."
"Haka ne kuma to Allah ya sa alheri. Yanzu a sanar da su Murja ko mu jira zuwa gaba kaɗan?
Sai na ce" A'a su ba yanzu ba amma ki sanar da Alhajimmu da Gwaggo."
Da haka muka yi sallama duk Yallaɓai na jin mu muna gama wayar na yi masa gwalo ina faɗin" Labarin ka ya yi kwantai Yallaɓai "
Ya na dariya ya ce" Na ji bakomai. Kema ai kwantan kika samu"
Nima na ji bakomai tun da bai faɗa min ba ya riƙe labarin shi, sai daga baya ya ke faɗa min yadda aka yi ya ce min na sanar da Marwa domin Kawu ya na so ya fara mgana da ita.
Ina dariya na ce" To Kawu fa da gaske ya ke yi "
"Ai Kawu ya susuce. In ba gani ya yi an yi auren ba to Kawu zai iya ba da mu."
Ina ta dariya muna ma cikin mganar Ya Aina ta sake kirana ta ce ta manta ba ta ce na zaunar da Marwa na faɗa mata in ji Babanta na ce kar su damu zan sanar da ita. Yallabai bai fita da wuri ba sai azahar ya ce zai je Rano ya ɗauko Gimbiya na ce sai ya dawo nima ranar ban fita ba ina gida amma na yi waya da su Ya Hamza suma duk sun ɗau hanya domin komawa gida saboda aiki Amina ma ta bi Ya Auwal za su sauke ta a kaduna sai fatan Allah ya kai su lafiya.
Ni na zaunar da Marwa na yi mata bayani ta na jin kunya ta rufe fuska ta na faɗin" Umma abokin Kawu fa kika ce? Ina dariya na ce" E to mi ye a ciki? Zan yi matukar farinciki in haka ta faru ina tunanin gobe ko jibi zai zo ya ganki. Marwa Kawu Abba ba shi da matsala ki ba shi dama kin ji ko?
Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" To Umma in sha Allahu."
Na ma ɗauka a ranar zai zo amma sai bai zo ba mun yi waya da Yallaɓai ya ɗauko Gimbiya sun dawo gida ya ce min ba ta da lafiya ta na fama da ciwon mara da safe za su je asibiti na ce Allah ya sauwaƙe.
Washegari Kawu Abba da kanshi ya kirani ya ce zai zo. Marwan na gidana ne? Na ce ta na gidana da yau za ta koma gida amma tunda ya na tafe sai gobe a lokacin da muka yi wayar na faɗa masa ba ta nan ta je asibiti ta na da aikin safe sai biyu na rana za ta dawo sai ya ce min zai shigo da yamma in sha Allahu. Mun gama wayar da shi kenan Yallaɓai ya kirani.
"Sadiya Albishirin ki "
Ina ɗauka abin da ya fara ce min kenan duk da ban sani ba amma a raina na san abin da zai faɗa min ba na raba ɗayan biyu tun da na ji Yallaɓai farincikinsa ya ƙasa ɓoyuwa.
"Goro fari ƙal. Me ya faru?
"Daughter tana da ciki. Wata biyu Sadiya."
Sai na danne abin da ke taso min na washe baki ina faɗin" Alhamdulillah Ma sha Allah barka da arziƙi Yallaɓai Allah ya raba su lafiya."
Ya amsa min da Amin Amin sannan ya ce ni ya fara kira ya sanar ma wa, sai na ji daɗin haka ko bakomai ya karramani kuma na ji daɗi na yaba. Jin haka yasa na ce ya ba ni Gimbiyar na yi mata sannu sai ya ce ta na ciki tare da likita ya fito ne daman ya kirani sai na ce shikenan in sun koma gida zan kira shi sai ya ba ni ita na yi mata sannu.
Duk yadda zuciyata ke son kaɗaicewa ta yi damuwa ban ba ta damar haka ba. Na taya Yallaɓai murna kwarai kusan shekaru bakwai ne ba a sake yi masa haihuwa ba dole ya yi farinciki amma na yi hawaye tare da fatan nima Allah ya sake ba ni ba domin ban gode masa ba a'a na gode masa ina kuma fatan ya ƙara min.
Marwa ta na dawowa na faɗa mata ta shirya Kawu zai zo duk sai ta daburce daga karshe ni ce na taya ta shiryawa bayan na saka ta yi masa girki jalop ɗin shinkafa mai karas da gabeji. Ana idar da sallar la'asar sai ga shi ya iso ni na fara fita muka gaisa su Kawu an sha kwalliya za a burge Marwatu ta bakin Yallaɓai ba.
"Yallaɓan kuma ba ya nan Kawu Abba."
"E mun yi waya. Ya na can baki ya ƙi rufuwa Saudatu ta na da juna biyu."
"E wallahi."
"To Allah ya raba su lafiya. Mun yi mgana ya ce zai shigo kafin na tafi "
Sai na amsa masa da toh na kuma ciki na turo Marwatu da farantin ruwa na ce in sun gama gaisawa ta koma ta ɗauko abinci Jidda dama ba sa nan yau suka koma makaranta sai shidda saura za su dawo gida.
Bederoom na koma na ɗau wayata na kunna data. Ai na ga ruwan status. Anty Bahijja ta saka Ni'imar haihuwa za ta ƙara sauka a gidan Tafidan Nene Ubangiji Allah ya riƙa musu ya tsole idon maƙiya saboda na shaka mata haushi na tagging ɗin status ɗin na shiga na ce" Amin ya rabb mun gode. Ai ni Yallaɓai ya fara kira a wayar ya sanar min da cewa mun samu ƙaruwa."
Ta gani amma ba ta yi mini mgana ba Anty Maimuna kuma har da saka hoton Gimbiya ta na cewa" A karon farko Hajiyar Tafida da Nene za su samu jika na farko da tsatson ahalinsu. Congratulatin Mutanen Rano da kewayenta gabaɗaya."
Itama na shiga na ce mata Amin na ga har Naja'atu ta saka yadda kika san su Jidda ba ƴaƴa ba ne a bola aka tsinto su gajiya na yi da ganin takaici na kashe data ko na ce kiran Yallaɓai ya katse ni. Bayan mun gaisa sai ya haɗa ni da Gimbiya na yi mata sannu sun dawo gida kuma na ji hayaniya kenan gidan na cike da su Anty Bahijja domin ni na san ko kowa bai je ba ita sai ta je, mun yi sallama ya ce min zai shigo gidan anjuma.
"Su Kawu ana can ana yaɗa manufa ko?
Ina dariya na ce" Ban sani ba."
"Su kaɗai kika bari a falo Sadiya? Kawu fa Tuzuru ne kin sani."
Ina ƙara yin wata dariyar na ce" Ka zo sai ka saka ido "
Ya ko ce ga shi nan zuwa sannan muka sallama ba daɗewa sai ga shi, sai da ya gama yi ma Kawu tsiya a falo sannan ya ƙariso ciki yunwa ya ke ji na saka mai abinci ya na ci ya na faɗa min tun shayin safe bai ci abinci ba a raina na ce na ga alama kam domin ya ci abinci sosai.
"Ya mai jiki?
"Ta ji sauƙi sun ce ta samu hutu ne. Shi ne na ke tunanin wa zai zauna da ita Jidda kin ga akwai makaranta."
Sai na jinjina kai kafin na ce" Gaskiya ne. To kai ka koma can da kwana mana har ta ɗan samu ƙwarin jiki"
"Ni kuma?
Sai ya kalleni ya na mai nuna kan shi sai na gyaɗa masa kai lokaci ɗaya ina faɗin" E. Ka je bakomai ai lalura ce."
Sai ga shi a gabana ya rumgumeni ya na faɗin" Na gode. Allah ya iya miki Sadiya ta." Na amsa da Amin sai hira ta buɗe ya na faɗa min yau duk abin da ta ci sai da ta amayar da shi sai da Anty Bahijja ta zo mata da kunin tsamiya daga gidanta shi ta sha ya zauna mata. Ya na ma faɗa min ta na can gidan ya baro ta shi ne ya samu sararin zuwa nan ni dai ina ta bin sa ne ka nuna wani abu a ce kana baƙin ciki.
Yana gidan har mangariba suka fita tare da Kawu. Marwa ta dawo min da fara'an ta ta na gaya min ya ce ta ba shi lambarta ta ce wayarta ta lalace ya ce to zai kawo mata waya.
"Umma to Baba zai bari na karɓa?
Ina dariya na ce" Me zai hana! Ai ya je ya ga Baba. Kuma baban ne ya bashi izini Marwanatu."
Sai ta dukar da kai ta na jin kunya ni kuma na daki kafaɗanta ina fadin" To ya ya a ke ciki? Kin san an ce ƙaramar uwa abokiyar shawara."
Kanta na ƙasa ta ce" Ya na da ban dariya Umma."
"To ina ruwan kawu. Balle ke da ya ke so ai za ki sha hira da barkwanci."
Sai ta rufe fuska ni kuma na leƙa ina faɗin" To wai ya ya ne! A tsaida shi ko a sallame shi?
Sai ta ki mgana sai ma tashi da ta yi za ta gudu na ko ce to shikenan tun da ba ta son shi zan faɗa masa.
"Umma ni fa ban ce ba na so ba."
"To kina so kenan?
Sai ta gyɗa min kai kafin ta zura da gudu zuwa ɗakin su Jidda, har suna cin karo ma da Jiddan da ta fito ta na ce min" Umma me ya samu Ya Marwa?
Ina dariya na ce" To Jidda ni me zan ce? Ki tambaye ta."
Na faɗa ina dariya ita Jidda irin yaran nan ne marasa damuwa kawai sai ta wuce kitchen ta bar ni nan ina ta annuri.
Washegari Marwa ta koma gida na faɗa mata zan tura ma Kawu lambar wayar Ya Aina zai riƙa samun ta ta can kafin ta tafi ta ke gaya min suna gama pratical suka koma makaranta semester ɗaya za su yi sai jarabawa ashe Diploma ce Kawu zai ji daɗin jin wannan labarin domin ya ce min ba ya so a ɗau lokaci sannan kuma ya ce shi bai faɗa ma kowa ba sai Innayi sai mu da muka sani ya na so ko maaganar za ta fita sai manya sun shiga ciiki shi ya sa na yi gum da bakina.
Na je har gida na duba Gimbiya gaskiya ta na shan laulayi, duk ta rame sai ido ta ƙara fari kamar ba ta da jini Sulaihat ɗin Anty Bahijja kan je ta yinin mata suma kuma suna zuwa sannan kuma ga Yallaɓai. Sai dai ya yi kusan kwana goma a gidan Gimbiya sannan ya dawo nan lokacin ta ji sauƙi sosai ta na cin abinci kuma ta ɗan ayyukanta sai ɗan abin da ba a rasa ba.
A washegarin ranar da ya dawo gidana karfe huɗu na asuba wayar Gimbiya ta tashe mu ta na kuka wiwi da cewa cikinta a firgice Yallaɓai ya dau mota ya tafi can gida ni kuma ya bar ni a gida amma duk na damu ni na ma kira shi wajen shiddan safe na ji yadda ake ciki sai ya ce min ciwon mara ne ya turƙeta an ba ta gado kuma likita ya ce za a ba ta bed rest saboda cikin jikinta ya samu rauni zai iya zubewa a kowani lokaci yadda na ga hankalin Yallaɓai ya tashi ne ya sa na ɗan kwantar masa da hankali. Nima yara na tafiya makaranta na taho asibitin duk da dai ita Gimbiyar ba za ta ci komai ba yanzu amma na je da kayan tea da ruwan zafi ko da na je na iske Anty Bahijja da Maman farko a asibitin.
*Janafty*
*TKG015*
Maman Farko ce kawai ta sakar min fuska to sai Yallaɓan amma Anty Bahijja ina gaishe ta ma kamar ina faɗa mata cuta a daƙune ta amsa ni. Na zo na iske an kai Gimbiya ɗakin hutu an yi mata kuma alluran barci amma ba su fara ba da izinin a shiga a ganta ba.
Muna asibitin Anty Bahijja ta kira mutane ba adadi ta na faɗa musu Gimbiya na asibiti ina ga ko suna tambayan ta cikin ne? Sai ta ɗaga murya ta na faɗin.
"Ciwon mara ne ya turƙeta. Cikin na nan ba abin da ya same shi amma sun ce za su ba ta bedrest ta huta sosai."
Ni dai ina gefe zaune kusa da Maman farko Yallaɓai ya tafi gida ya je ya yi wanka ya dawo. Ita Nene da Maman farko suka yi waya ta na faɗa mata halin da ake ciki, bayan sun gama ne ta kalle ni zaune da kwandon da na sako kayan tea da ruwan zafi a gabana kamar wata marainiya sai ta kira sunana na ɗago ina amsawa.
"Sannu da ƙokari Sadiya."
Sai na amsa ina jinjina mata kai. Ai dole ta gaisheni na zo asibiti na yi zaman dabas saboda kishiya amma sai na duba Yallaɓai da ita kanta Gimbiya sai na saka a raina zan yi domin Allah domin kirkinta saboda ana ganin ban zo ba kafin kowa ya yi magana Anty Bahijja za ta fara yi da ni. Kafin kace kwabo an cika asibitin nan ni dai bayan azahar na koma gida tun da har lokacin ba ta farka ba kawai sai na yi musu sallama na koma gida Yallaɓai kuma ya dawo asibitin amma ya sake fita ya ce akwai mutane a office suna jiran shi sai da ya dawo da daddare ya ke faɗa min Gimbiya ta farka jikinta da sauƙi.
"Allah ya ƙara mata lafiya."
"Amin Amin."
Sai na kalle shi ganin ya yi wani shuru haka ya na cin abinci sannu sannu.
"To wa zai kwana da ita?
"Maman farko aka bari da ita."
Sai na jinjina kai ban yi magana ba amma a raina sai na ɗauka ai Anty Bahijja ce za ta tsaya ta kwana yadda ta ke nuna kamar ita ce ta haifi Gimbiyar ma. Washegari ma da safe yara na tafiya makaranta tare muka tafi asibitin da Yallaɓai ni na kai ma Maman farko abin karyawa har muka iske Gimbiyar ta na kwance amma idanunta biyu.
"Sannu ya karfin jikin?
Ta na ɗan mirmishi ta ce" Da sauƙi Madam ina su Jidda? Sai na ce suna makaranta amma sun ce a gaisheta ta amsa ta ɗan yamutsa fuska. Ni da Maman Farko waje muka fita muka ba su waje muna ta ma hira da ita. Ta ce min ai ta ji sauƙi matsalan ba ta son cin abincin Tea kawai ta sha jiya kuma a jiyan ta amayar dashi.
"Topha. Subhanallah to yanzu me ta ke son ta ci?
"Ban sani ba. komai a ka ce sai ta ce ba ta ci. Laulayin ta mai zafi ne sai dai fatan Allah ya sa a rabu lafiya."
Na amsa da Amin Amin ban wani daɗe ba. Amma dai anan Yallaɓai ya bar ni ya tafi office ni kuma zuwan Anty Maimuna ya sa na yi musu sallama na koma gida da daddare ma na yi girki na ce Yallabai ya ɗauka ya kai ma Maman farko bayan ya je ya dawo shima ƙorafin da ya ke yi min kenan na rashin cin abincin Gimbiya sai na bashi shawaran ya samu likita da mganar. Ɗayan washegarin da safe ban koma ba shi kaɗai ya tafi da abin karyawa bayan ya dawo ne ya ce likitan ya ce masa ya tambayeta ko akwai wani abin da ta ke so ne in ta faɗa sai a dafo mata shi a kawo mata, ya na faɗa min ta ce ita faten tsaki ta ke so mai yakuwa.
"Ikon Allah.."
Na faɗa ina kallon shi.
"Wallahi wai fanten yakuwa."
Ina ƴar dariya na ce" Ina ko da bushasshiyar yakuwa da mai kitsona ta kawo min tsaki ma kamar ina dashi."
Sai ya kalleni nima shi na kallah ban yi magana ba saboda na ga kamar ya na so ya yi magana.
"Yallaɓai."
"Uhm"
Ya amsa a ƙasan maƙoshi ya na zaune a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ni kuma zaune na ke a hannun kujeran.
"Mene ne? Ko kana son wani abu ne?
Domin sai na ga kamar ya na so ya yi magana amma kuma ya kasa furta abin da ke zuciyarsa.
"In roƙe ki alfarma?
Sai na gyaɗa masa kai kafin na ce" Ba alfarma tsakaninmu Yallaɓai sai dai mutumtatawa da martabawa. Ka yi umarni kawai zan yi maka duk abin da kake so in dai bai saɓa ma shari'a ba."
Kai ya jinjina kafin ya ce" Ina so in ce ki taimaka ki yi ma Daugther faten don Allah sai kuma na ji kamar ina jin kunyar ki "
Ya faɗa ya na kallona nima shi na kallah amma ban yi magana ba.
"Don Allah Sadiya ta."
Sai na basar ina ƴar dariya kafin na ce" Haba miye na wani don Allah? Zan yi mata in sha Allahu."
"Na gode. Allah ya yi miki albarka Abar ƙaunata."
Na amsa da Amin shi kuma sai ya ja hannuna ya na sumbatata. Bai jima ba ya yi min sallama ya fita har a cikin zuciya ban ji kishi ko wani abu ba da zuciyata ɗaya na yi ma Gimbiya faten nan da yamma yara suna dawowa makaranta na ce su shirya tare da su za mu je asibitin su gaishe da Antyn