Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   22 / 48

63K to 66K   out of 141.5K words

Wannan rawan jikin kam ya na yi mata a gaba na kuma sai ya riƙa nuna ni ya ke yi ma rawan jiki, wai ni Yallaɓai zai maida ƙaramar yarinya Allah na tuba wani dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa.

****

20January 2016.

Tuni na koma asibiti na ga Dr. Aisha Alhandulillah abin farincikina duka na tsallake matakin gwaje gwajen su kuma ta ba ni tabbacin ba wata matsala mai girma. Sai dai kawai side effect ya taɓa ni sannan kuma hormones ɗina sun ɗan yi rauni ne amma ta rubutamin manganganun da za su dai dai tamin al'ada da wanda za su ƙara taimaka min wajen samun ciki suna da tsada domin da na je phamarcy ma kuɗin da Yallaɓai ya ba ni ba su isa ba, na yi ta kiran wayar shi ban samu ba sai na kira na Musbahu shi ya faɗa masa sai shi kuma ya taho asibitin ya same ni, bayan ya biya kuɗin magunguna ya ɗauke ni ya maida ni gida. Duk da ina da kuɗi a cikin acct da gangan na ƙi taɓa su ni fa yanzu na fara jin ƙyashi yin hidimar da nawa ba, ba kamar da ba da shi kan shi ya san wani abun ma ba na jiran shi.
Kan jiki kan karfi na dage na fara shan magunguna na saboda fata na da burina ni ma Allah ya sake ba ni wani cikin ko ɗaya ne na sake haifa.

Kwana biyu tsakani na je gidan Hauwa daga can ni da ita muka je gidan Munnira muka haɗu muna ta hira. Sun tambayeni ya yanayin zaman na ce lafiya lau. To me zan ce? Zaman da yanzu aka fara ai sai tafiya ta tafi sannan halin kowa ma zai bayyana. Hauwa ita dai faɗi ta ke yi Yallaɓai ɗan halas ne, ni ko a raina na ce ai ba a yabon ɗan kuturu sai ya shekara da yatsa a hannun shi.
Sai yamma muka rabu Hauwa ta hau adaidaita anguwarsu nima na hau ta anguwarmu na koma gida. Ina komawa ma na iske Marwa ta zo daga asibiti ta biyo ba na gida, daman Saude na bari a gida tare da su Jidda sai da dawo suka tafi gabaɗaya.

Tun bayan tariyan Gimbiya sau ɗaya na je Gwammaja na gaishe da Alhajinmu daga nan na ɗauke kafa ina gida mai son ganina ya san in da na ke, iyakata in ina son mgana da mutun na yi masa waya. Ni yanzu ba ma Yallaɓai da Amaryansa ba ne a gabana sauran kudaɗen hannuna na ke son zama na yi tunanin sana'ar da zan fara, kar ma su ƙare a banza ban yi komai da su ba, tun dai na fahinci Yallaɓai zuma kawai ya ke lasamin a baƙi burina da ya ce zai zama sillar cikarsa na cire rai da su. Hankalina ya koma kan wani busineess ɗin da zan fara da zan dogara da kaina har Khaleesat na kira mun yi mgana saboda na ce ko nafara gwada hijabai ne? Sai ta ce wata Akwai ƙanwarta na siyarwa za ta tambaya min ta ji harkan in akwai fita sai ta haɗani da masu ɗinkin Hijaban anan sabon garin Zaria in muka saba ma ba sai na je ba ma. Kololin kawai zan faɗa su za su riƙa siya suna dinka min sai dai kawai a saka a mota a kawo min nan da nan na ce ta yi min ƙokari ko Yallaɓai ban faɗa mawa ba da Amina kawai muka yi mgana ta ce wallahi na fara itama yanzu turaruka ta ke saidawa har ta ba ni shawaran na saro mayukan gyaran gashi tunda ina son bangaren na fara saidawa na ce shima zai zo daga baya mu fara da wannan ɗin dai mu gani.

Ko a raina ban ji zan faɗa ma Yallaɓai ba sai dai in ya gani ya tambaya na amsa masa. Shima yanzu ai hankalinsa kashi biyu ne. Da ni kaina da ita amaryansa, ga su Jidda sun koma makaranta ta shiga Jss2 Ita kuma Baby primary 3, ya biya musu kuɗin makaranta daga nan na san Yallaɓai kuɗi gare shi, ba zan zage shi a yanzu ba  tunda iya adalci yana kwatantawa. Sai ɗan abin da ba a rasa ba na halin Ɗan adam. Zama ya yi zama an kwarari wata biyu da tariyan su sannan na fara lura da wani abu.

Duk da Jidda ta koma makaranta ranar da ba ya gidan Gimbiya sai ya kaita. Ita kuma da safe sai in za ta wuce wajen aiki tunda ta na da mota sai ta kai Jidda makaranta in sun tashi ta je ta ɗaukota. Nan kuma Baby ita kaɗai Salisu kai kaiwa sai dai in har Yallaɓai na wajen Gimbiya ne ta ke gida duk da na ga ana ta min gantali da yarinya ban yi magana ba saboda ina ganin akwai sauran lokaci. Sai da na ga in dai zai zo gidan nan ranar da zai bar gidanta sai ta rako shi, kuma tana da mota amma a tashi za su zo bayan nan kuma shi zai maida ta gida ya ɓata lokaci kafin ya dawo duk na kauda kaina ban yi magana ba, sai abu na biyi in dai yana gidana to ta rika kiran waya kenan kamar wani ɗan kasuwan da ya ci mata bashi. Ni ko ba alfahari ba bana kiran shi in na san ya na gidanta. Sai dai in ma ya zama dole na yi masa saƙo in ya gani ya kira amma ita ba haka ba ne a wajenta in abu ne ta nema ba ta gani ba sai ta kira shi ta tambaye shi tun ina ba ta lokaci har dai na fahimci da gangan ta ke yi, ranar dai na ga abin na ta ya isheni da daddare har mun kwanta ta kira shi wai ta kasa kulle ƙofa, ina jin sa ya na faɗa mata key ɗin ne ya lalace gobe da safe zai saka Musbahu ya je da mai gyara sai a sauya key ɗin gabaɗaya.

"Wai shekarun Gimbiya na wa ne?

Sai ya kalleni kafin ya ce" 33 to 34 ina jin ko za ki girmeta da kaɗan ne"

Sai na jinjina kai ban yi magana saboda na gama fahimtar renin wayau ne kawai kamar wata jaririya.

"Me ya sa kika tambaya."

"Na ga ta na yin abubuwa kamar Jidda ne"

Ido ya zuramin alamun ƙarin bayani ni ko ina gyara gashina da tun da na yi tsifa ban kitse shi ba a gaban madubi na yi masa kamar bangane ba.

"Me ya sa kika ce haka?

Sai da na gama abin da na ke yi sannan na zo na kwanta lokaci ɗaya ina faɗin" Ka fi ni sanin dalilin."
Da ga haka na yi kwanciyata na juya masa baya. Na san ya yi ta kallona ya kuma kasa mgana saboda ya san abin da na ke nufi. Mata kawai daga zuwanta za ta zo min da makirci a cikin gidana to ba ta isa ba zan taka ma ta burki daga ita har me biye mata.



*Janafty*
*TKG*

11.

FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622

Yanzu Gimbiya tana cikin wata biyu ne da tarewa. Zaman su ya fara miƙawa tun ina ganin lamarin kamar wasa har dai daga karshe na saka a raina gaskiya ne sannan zan saba ɗabi'ar haka ta zame min jiki ko domin samun zaman lafiya ta.
In na buɗe wardrope ɗina na ga cikin kayan Yallaɓai kashi uku babu kashi ɗaya a hankali a hankali ya na ta rage su, suna can gidan Gimbiya, bayan kaya ma hatta ma'ajiyar takalman mu sun yi rauni, wajen gudu huɗu duk babu su a wajen suna gidan Gimbiya bangaren unders ma sannu sannu dai suma ɗin suna ta raguwa, a raina na ce shi kenan duk ikon da na ke dashi a kan Yallaɓai da duk abin da ya mallaka yanzu wannan ikon ya fita daga hannuna saboda ba ni kaɗai ke da shi ba ya na da wata matar kuma itama ta na da iko akan shi da duk abin da ya mallaka.

Iya kauda kai ina yi, saboda ni ce babba kuma na riƙe girmana duk da na san ina saurin fushi da zafin zuciya amma na danne ban bari kishi ya saka ni na yi abin da ba dai dai ba ne. Kwanaki na je na gaida Nene ta ƙara yi min nasiha da ƙara tunasar da ni girman da ake cewa ina da shi kar na ɗauka wani ne ya ba ni. Na saka a raina girma ne da Ubangiji ya ba ni. Na ji kuma na yi kamar ban ji ba sannan na gani na yi kamar ban gani ba. Duk da Gimbiyar ɗiya ta ke a wajenta ni Nene ba ta ƙi ni ba kuma ina ganin girmanta shi ya sa duk abin da ta faɗa min zan ji sannan ina ƙoƙarin yin amfani da shawarwarinta.
Saboda haka ne ma na saka ma Yallaɓai ido ya gama mararin amarcinsa da rawan kafansa ƙala ban taɓa ce masa ba.

  Na yi ta ƙoƙarin kauda kaina a kan al'amarin sa da Amaryansa shima kuma tun kafin auren nan da muka yi mganar ya daina mini labarinta ya tsaya iya matsayin shi. Iyakata dashi abin da ya shafe ni ko ya shafe shi ko ƴaƴana ni ma kuma bana tsallake hurumin da ba nawa ba domin samar ma kaina zaman lafiya da kwanciyar hankali.

  Ko na sana'ar sai da Hijabai da aka kawo min daga Zariya guda Hamsin sai da  ɗan nuna rashin jin daɗin sa saboda ni dai ban faɗa masa sai dai kawai ya zo ya ga an kawo hijabai. Da farko ma ya ɗauka ko na saƙo ne bai tambaya ba sai da ya ji ina waya da Khaleesat anan ne ya fahimci nawa ne zan fara saida wa.
Sai da ya bari har mun yi shirin kwanciya sannan ya yi min mgana.

"Kasuwanci kika fara ban sani ba Sadiya?

Sai na kalleshi kafin na ce" E. Ban fara ba zan dai fara in sha Allahu."

Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Shi ne ba ki faɗa min? Yaushe kika fara yin wani abu ba tare da na sani ba?

Sai ya ba ni mamaki ji karfin hali ɓarawo da sallama.

"Ina ka samu lokacin zama ballatana na faɗa maka?

"Ban gane ina na samu lokaci ba?  Ba nan na ke kwana ba in ban kwana ba, ba na zuwa da safe? Ban kiran ki a waya?

Kai tsaye na ce" Ba wannan ba kai da ka ke cin amarci? Amma ina da niyyar in faɗa maka daman."

Sai kawai ya kasa yi min mgana. Nima daga nan ban ƙara jan sa da wata mgana ba amma washegari na yi masa talla na ce ya siya ma yara tunda akwai na yara sai ya ce na ɗaukan musu guda biyu. Ba tare da ya sani ba na cire ma Nene da Gwaggo ɗaya ɗaya na saka albarka sai kuma bayan ya fita ya kirani a waya ya ce ya faɗa ma Gimbiya ta ce ta na so za ta zo ta duba nima na duba na ɗauka zai biya sannan na duba ma Nene itama. Ban ce masa na ɗaukan mata ba na yi masa godiya. Haka ko aka yi a daren ya kawo ta ta duba guda biyu ta ɗauka nima sai na ɗau biyun nan kuma ta ke ya turamin kuɗina Nene kuma biyu na ɗaukan mata sai na haɗa da na wajen nawa ya zama uku, ba shi ya kai mata ba Musbahu na kira ya zo ya karɓa ya kai mata daga baya na kira ta a waya na yi mata bayani ta ji daɗi ta yi ta saka min albarka.

Kuma an ta siyan Hijaban duk da na ɗan yi kyattuka da wasu. Na ɗaukan ma Saude da Marwa. Sauran kuma na tallata ma su Ya Aina da su Ya Hamza kuma duk sun siya ma matansu. Sannan har group ɗin makarantarmu na shiga na yi musu talla har mutum uku sun aiko da kuɗi sun siya sun kuma aiko har gida an karɓan musu. Duk da mun ɗan samu saɓani da Anty Bahijja amma tuni na yi mata na ƴan duniya da kaina na kira ta na yi mata tallar Hijaban sai ta fara min faɗa wai na gama yi mata rashin kunya zan  neme ta yanzu. Ina dariya na wayance da cewa.

"Haba Babbar Yaya. Wace ni Sadiya ai ban isa ba. Rashin fahimta ce. Ke ce ba ki fahimce ni ba."

Sai kawai ta ce min" Ni Yar mijin ki ce ba ƙanwarsa ba Sadiya ya kamata ki riƙa tuna haka."
Nan dai na samu na basar da mganar na tura mata tallar Hijabai kuma sai da ta siya ma ƴaƴanta haka itama Anty Maimuna ita sai gashi ta na gaya min Nene ma ta nuna mata wanda na bata da wanda Tafida ya siya mata. Itama ta siya ma kanta da yaranta, Mimisco babban harka ta yi min tambaya na kawai ta yi guda nawa suka rage? Na ce 15 suka rage na manya goma na yara guda biyar kawai ta ce na saka mata acct ɗina da farashin za ta saka min kuɗi sannan za ta aiko direba ya karɓa.  Da ina mata godiya sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce.

"Haba Sadiya ku fa namu ne. Dole mu zama masu ƙarfafa muku gwiwa."

"Na gode Mimisco Allah ya ƙara ma rayuwa albarka."

Ta amsa min da Amin Amin sannan muka yi sallama kuma ba daɗewa Ina tura mata acct ɗin sai ga kuɗina ya shigo na daka tsalle ina murna. Tuni na kira Khaleesat na faɗa mata sai ta ce za ta tura min lambar ƙanwar na ta mu yi magana ita za ta haɗa ni da mai saida yadiddikan hijaban kawai da shi zan dinga magana da na siya kawai aiko min da shi direct ta hannuna kawai zai yi, sai na ce hakan ma ya yi. Ina ta murna na siyar da Hijabai na kuma ina fatan wannan sana'ar da na fara Allah ya sa ta ɗaure min ta kuma ta riƙe ni, na yi ma kowa talla amma ban da Ma'u domin ni ban ma faɗa mata ba, ba kuma na saka wani abu a raina ba ne a'a kawai dai ban faɗa mata ba ne amma a raina na saka cewa in aka ƙara saro wasu zan yi mata talla bakomai in ma ta na da wani aniya a cikin ranta ne Allah ya mayar mata da sharrinta.

Khaleesat na tura min lambar ƙanwarta Madina na kira ta muka yi mgana ita ta haɗa ni da shamsu mai yadin hijabai na sabon garin zariya. Shi kuma ya haɗa ni da mai ɗinkin Hijaban anan kasuwar ya iya sosai domin shi ma ya ɗinka min na farko na biyun ma bayan duk na tura masa kololin da kuma adadin yadinka ya ce za a ɗinka nan da kwanaki biyu za su iso hannuna. Amina ma mun yi waya ta ce za ta tallata min in ana so anan Kaduna za ta yi min mgama sai na riƙa aiko mata da shi ta na siyar min aiko na ji daɗi har a cikin raina tuni na fara jin gwara na manta da rayuwar Yallaɓai da Amaryansa na kama sana'ata domin shi ne alherina.

****

Alhamdulillah kawai zan ce domin har Hijaban da aka sake kawowa sun ƙare. Gimbiya ta sake min ciniki guda huɗu ta siya sannan ta ƙara siya ma su Jidda. Kuma ta yi min talla a can wajen aikinsu kusan ma rabin Hijaban daga ɓarayinta suka ƙare. Nima saboda jin daɗin haka har kyauta Hijabi na ba ta guda ɗaya na yi kuma mata godiya ta ce bakomai an zama ɗaya shima Yallaɓan na faɗa masa da cewa ya ta ya ni yi mata godiya sai jin daɗi ya ke yi an yabi Amaryansa tun ina mamakin Yallaɓai ni fa yanzu har ya zame min jiki ma.

  Duk da ba wani sakar mata na ke yi ba. Ni dai ban taɓa takawa gidan ta ba amma ni tana yawan zuwa za mu gaisa a zauna ana hira sama sama na ke saka baki, saboda ni na kama girmana ban zaƙe ba ban kuma tusa kaina ina daga gefe gefe dai. Amma ita da yara kam ban isa na shiga tsakaninsu ba tun kafin auran ta da Yallaɓai daman ta shaƙu da su sannan komai ta samu su ne tun a baya ballatana yanzu da ta ke auren uban su. Komai ta samu su ne kuma na yarda ya na siyan mata daraja da ƙima a wajen Yallaɓai ya kuma saka ya ƙara sonta domin in dai ta kawo min wani ko ni ko yara haka zai ta washe baki, wani lokacin ma saƙon shi ya ke kawowa ya na faɗi ya na nuna farincikinsa.

Ba ta zuwa hannu rabbana. Ko ta yo girki ko ta soyo nama ko kaza ko kayan fulawa haka dai. Su kuma su Jidda wani riborn da kayan kwalliya duk ta ɗauke min duk ita ke siya musu. Ni ban taɓa cewa komai ba sai godiya kayan wasa kam har suna yi musu yawa ta siya musu yan kanti ta kuma ɗinka musu duka dai, yadda ta ke kyautatamin da ƴaƴana in na fara wata mgana sai a ce baƙin ciki ne ko ba ni da haƙuri shi ya sa na koma gefe na yi bakam kawai ina lura da komai, in suka zo tare haka za ta yi ta wannan karera yan ita wai mai miji, ta na wani maƙale murya tana kiran Daddy shima ya na wani kiranta Daugther tun ina mamakin su har na koma na daina kawai ni dai sai ido domin ni ba wani munafuncin namiji da ban sani ba, sannan makircin mata ma ai mun gan shi kala kala so daga ita har shi ni sai dai kawai na kalle su.

***

Yau Asabar Yallaɓai a gidana ya ke bayan ya dawo

22 / 48