halin da gangan jikina da zuciyata ke ciki, amma ban bari na shagala ba, sai na fara kiran sunan Allah a acikin raina domin na samu natsuwa.
Haka kawai na ji ba na son komawa cikin bedroom ɗin mu, tun da Yallaɓai a yanzu na san ya fito wanka ya na shiryawa. Tun da aka faro wannan al'amarin ban bari Yallaɓai ya ga gazawata ba. In ko na bari ya gani yanzu kamar na yi faɗuwar baƙar tasa ne, shi ya sa da na koma na gan shi raina ya sosa hankalina ya tashi gwara na yi zama na a nan cikin ƴan'uwana a ƙalla dai ko ba na da natsuwar fahimtar hiran su ina kallon fuskokinsu za su iya zame min garkuwa daga bayyana raunina a wannan daren.
Ina nan zaune shuru sai ga Sameena ta fito daga ɗaki har sannu da su Amina suka yi ta mata wallahi ni ban ma ji ba, sai da ta zo kusa da ni ta na taɓa kafaɗata sannan na dawo duniyar da suke, kallona ta yi sai ta ga kamar ina firgice ne, sai ta zagayo kusa da ni ta zauna ta na faɗin" Matar Baba lafiya?
"Ya jikin ki! Sannu"
Na katse wancan tambayan na ta, sai ta amsa min da ta ji sauƙi, daga ni har ita sai muka rasa abin cewa, ni kam ba na rasa ba ne yanayin da na ke ciki ne ya sa kalaman bakina suka ƙare, Faridan Tariq daman ta na ɗakin su Jidda ta je kwantar da su Hassan sai ga ta fito ta na faɗin ga su Tariq can a waje ya ce suna kiran wayar Tafida ba ta shiga suna jiran shi a ƙofar gida.
Lokacin da ta faɗi haka sai gabaɗaya jikina ya fara rawa har Sameena da ke gefena sai da ta fahimci haka, da sauri ta saka hannu ta riƙe hannuna guda ɗaya sai na juya ina kallonta da idanuwana da na ji kamar sun juye, kai ta girgiza min kawai sai na bi ta da kallo domin kamar wata yarinya sai na kasa fahimtar ta, bakina na ji ya bushe na kasa ma haɗiye miyau, maƙogaro na kuma na wani irin zafi kamar wani abu ya karce ni ban sani ba.
"Sadiya ki faɗa ma Yallaɓai suna jiran shi a ƙofar gida."
Farida ta faɗa ta na kallona sai kawai na bi ta da kallo itama kamar irin ban fahimta ba, kuma dukkansu sai suka kasa gane yanayin da na ke ciki, illa Sameena da ke gefena da ta yi saurin cewa" Ta shi Matar Baba."
Ta faɗa ta na kallona, lokaci ɗaya ta na ɗan bubbuga hannuna alamun lallashi da ban baki, ina ƙokarin ƙwato numfashina ne na ji muryan Yallaɓai ta korido ya na kiran sunana.
"Sadiya."
"Sadiya.."
"To ai ga Yallaɓan ma can ya na kiran ki Ya Sadiya."
Amina ta faɗa ta na kallona kamar an ja ni tsaye sai ganina na yi na miƙe kan kafafuna duk yadda na so na yi musu mirmishi na kasa illa kaina da na kaɗa ina faɗin" Ba. ba ri na yi masa mgana."
Ina gama faɗin haka na juya zan wuce ban ko kallon gabana sai gashi na ci tuntuɓe da cafet na kusa faɗuwa gabaɗaya suka haɗa baki wajen faɗin" Subhanallah."
Na kusa kaiwa kasa na samu na riƙe kujera ban riga na kai ƙasan ba, jikina ba in da ba ya rawa sai kawai na wuce ina tafiya ina ji kamar ina jin sanyi zazzaɓi zai kamani domin ina ta matse jikina a waje ɗaya, da kallo suka bi ni, saboda sai a lokacin dukkansu suka kula da yanayina sai kuma jikinsu ya yi sanyi ina jin Farida daga bayana ta na faɗin" Ki yi a hankali Sadiya kar ki faɗi." Cikin muryan sanyi kamar na tausayi haka na ji a cikin maganarta.
Ina gama shigewa koridon Sameena ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Allah ya ƙara ma Matar Baba haƙuri da juriya." Faridan Tariq sai ta koma ta zauna a gefen kujera ta na faɗin"Amin. Amma lamarin ba daɗi."
Rahila dai da Amina ba su yi magana ba, amma jikin su duk ya yi sanyi sai falon ya koma ya yi shuru hiran ma sai ta tsaya kowa da tunanin da ya ke yi shi da zuciyarsa.
Ni kuma ina fita daga koridon na buɗe kofa na tsaya a ƙofar bedroom ɗin na kasa shiga, dafe kirjina na yi jin kamar zuciya ta za ta faso ta fito saboda yanayin da na ke ciki, duƙawa na yi ina maida numfashi sama sama kamar wacce ta yi gudun tsere ji na ke yi kamar sheɗata na neman ɗaukewa na ma kasa iya dai daita yanayina ballatana har na tura ƙofa na shiga ɗakin, ina duƙen ban sani ba sai kawai na ji an buɗe kofa Yallaɓai ya bayyana a gabana. Kaina na dago ina duke kan gwiwoyiyina na ɗago ina kallon shi, na ga lokacin da ya ɗan buɗe ido cikin mamakin ganina a wajen, ni kuma kayan jikinsa na ke kallo wata shadda ce sabuwa ce mai ruwan sararin samaniya ɗinkin zamani ne, har saman kaina na ke jin ƙamshin turaran Yallaɓai har kafarsa sabon takalmi ne domin ni ban ma san ya siya takalmi sabo ba, kamar wani cuta ina ganin Yallaɓai sai na ji kawai ina haƙi, daga tsuggune kamar ina ganin hajijiya ne ma.
"Sadiya lafiya? Me kike yi anan?
Ya faɗa yana kallona yana ƙokarin shima ya duka shima da sauri na yi ƙoƙarin na miƙe kawai sai na ji juwwa ta ɗauke ni na yi baya zan faɗi da hanzari Yallaɓai ya taro ni, nima sai gani na ƙamƙame hannayensa ina cigaba da haki kamar mai cutar Asthma saboda na ɗauka zan faɗi ne, ni fa gabaɗaya ji na ke yi kamar wata cuta ta kamani, kuma irin cutar da ban taɓa samun kaina a cikin sa ba, ina tunanin cutar yau ce ta kamani.
"Ba ki da lafiya ne?
"Subhanallah."
Na ji yo Yallaɓai na faɗa Sama sama ni dai ban dawo hayyacina ba sai da na ganni zaune a gefen gado, kitchen ya koma ya ɗauko min ruwa mai ɗan sanyi ya buɗe min ya kuma kafa min a baki ya ce na sha. Na ɗauka ban ji ƙishi sai ga shi na ɗaga roban ruwa na dire bakomai a ciki shi kan shi Yallaɓai da mamaki ya ke kallona Allah ya taimake ni sai na fara dawowa hayyacina na ji numfashina na daidaita sannan na daina hakin nan, kuma bakina bai bushe ba yanzu sannan ina jin maƙogwarona ya daina kartamin ɗin da ya ke yi ɗazu.
"Sadiya."
Yallaɓai ya faɗa yana durƙushe a gabana lokaci ɗaya kuma ya na kallona sai na ɗago ina kallon shi, yadda kuka san na gaji haka na ke jin duk jikina ya yi sanyi kamar an yi min dukan tsiya. Fuskata ya saka hannu ya na shafawa har ya na ɗan tapping ɗin shi da hannun shi sai na ƙara buɗe idanuwana ina kallon shi amma ban yi magana ba.
"Me ke damun ki?
Haka ya faɗa cikin kulawa, a cikin zuciyata na ke maimaita Hasbunallahi wa'imal wakel. Sai kuma na ji nauyin jikina ya ragu sannan bakina ya saki numfashina ya dai daita, Yallaɓai ya tashi tsaye ya saka hannunsa guda biyu ya ɗago duka kafaɗuna tsaye lokaci ɗaya ya sakani a jikinsa ya rumgumeni ƙamƙam a cikin jikinsa nima ban san lokacin da na miƙa hannuwana na zagaye bayan shi na shige jikinsa sosai kamar zan tsaga jikinsa na koma ciki, shi kan shi ya ji yanayin riƙon da na yi masa duk yadda na so kar kuka ya zo min duk yadda na so kada yau ɗin nan na raunana sai da raunin zuciyata ya rinjayeni sai kawai ji na yi ina kuka har da shessheƙa, hawayena suna sauka a saman kafaɗan shi, ko bai faɗa min ba ni na san jikin Yallaɓai ya yi sanyi, domin kansa na saman kafaɗata kawai ya na riƙe da ni amma ya kasa iya mgana ni kuma ina ta kuka yi yi har da kamar zan shiɗe, kuma in za a kashe ne ba zan iya cewa ga dalilin kukana ba kawai ni dai a raina ji na ke yi kamar na fi kowa na duniya nan shiga matsala, kuma ina ji kamar Yallaɓai zai yi min nisan da tun da muka yi aure bai taɓa min irin shi ba.
Bai hana ni kuka ba sai da muka yi kusan mintina goma a haka, daga ni har shi muna ji ana ta kiran wayarsa da ke saman side drower ɗin gadonmu. Amma bai sake ni ba har sai da na gaji da kukana na yi shuru ni ce ma na sake shi tuna cewa ana can ana jiran shi a waje sannan ita kanta Gimbiyar ta na can ta na jiran sa. Ban kalle shi ba da sauri na juya baya murya ta shaƙe ina faɗin.
"Su Tariq na waje suna jiran ka."
Na faɗa lokaci ɗaya ina goge hawayena da hannuna guda ɗaya. Ƙaramar jakarsa na gani a saman gado alamun ya gama haɗa kayan shi da zai bukata acan ina kallon jakar sai ga hawaye sharr, amma ina ƙokarin tare su, ya na ƙokarim sake riƙe ni na yi saurin kaucewa ina faɗin.
" Yallaɓai ka je kawai sai da safe."
Na faɗa ina ƙokarin maida kukana da ya taso min amma zuciyata sai da ta rinjayene na fashe masa da kuka na ma kasa iya kallon shi, sai kawai na juya da sauri zan fita amma bai bar ni ba da sauri ya riƙo ni amma ina ƙokarin zamewa daga riƙon shi cikin kuka kamar ina masa magiya na ke faɗin
"Don Allah."
Ina kuka maganar ta tsaya mini na kasa cigaba da magana sai ya sassauta riƙon da ya yi min ya na kallona wai ni Yallaɓai ke yi ma kallon tausayi saboda ya san ɗin abar tausayi ce.
"Don Allah ka ƙyaleni."
"Don Allah."
Na faɗa ina masa magiya kuka na ke yi kamar raina zai fita, sai kawai ya sake ni na juya zan fita daga ɗakin sai ya kira sunana.
"Sadiya."
Sai na dakata amma ban juyo ba, sai dai na saka hanuna guda ɗaya na dafe bakina har sautin kukana ya fito.
"Ki yi hakuri."
"Kin ji."
Wai haƙuri ya ke ba ni? In na ce ban hakura ba zai fasa tafiya ne? Ko kuwa zai iya maida hannun agogo baya ne, ko juyawa ban yi ba na buɗe kofa na fice sai na rasa ina zani kawai sai na buɗe kofar tiolet na shige na rufe ƙofar da sakata na sulale sai ga ni na yi zaman dirshan a saman tayels ɗin Tiolet ina mai fashewa da kuka da karfin gaske, suya zuciyata ke yi, har hancina na ke jin ya na fitar da wani yaji yaji, idanuwana sun yi min mugun nauyin da na kasa iya juyawasu, kaina na wani irin saramin da ƙarfin gaske, kaina na kasa a cikin gwiyoyina ina cigaba da kukana mai sauti, roƙon da na yi masa ne ya sa ya ƙyaleni na ji fitowarsa daga bedroom sannan jikina ya ba ni ya daɗe a ƙofar tiolet ɗin kafin ya buɗe kofar korido ya fice, ba jimawa na ji buɗe get din sa tunda shima window ɗin makewayin na ta haraban gidan ne, ban san ko shi ya faɗa musu ga in da na ke ba domin can ba jimawa sai ga Farida ta zo har ƙofar tiolet ɗin ta na kiran sunana ban amsa ba, sai ga Sameena Amina da Rahila kar su yi tunanin wani abu ya sa daga ciki na yi musu gyaran murya.
Ban san suna tsaye a ƙofar Tiolet ɗin ba, har sai da na wanke fuskata ina fitowa na gansu tsatsaye cikin damuwa sai kawai na yi mirmishi na fito ina rufe ƙofar Tiolet ɗin lokaci ɗaya ina faɗin" Lafiya ta kalau fa kar ku ɗaga hankalin ku."
Na faɗa ina raɓawa ta gefen Rahila na buɗe kofar Bedroom ɗin mu na shiga sai na juyo ina rike da kofar ganin duk sun bi ni da kallon Tausayi sai na ƙara yin mirmishi da kumbararrun idanuwana kafin na ce.
"Da gaske na ke yi lafiya ta ƙalau. Sai da safe ina so na zauna ni kaɗai ne."
"Kin tabbata?
In Farida ita kuma Amina sai cewa ta yi" Ko na zo na taya ki kwana ne Ya Sadiya?
Sai na gyaɗa mata kai alamun toh, sai Sameena ta ce hakan ma ya yi, na juya na shiga cikin ɗakin Farida ce kaɗai ta biyo bayana sauran kuma suka koma a gefen gado na zauna ina yarfe ruwan fuskata.
Ta na tsayen ba ta zauna ba ta ce" Ki yi ta kiran sunan Allah, in natsuwar ba ta samu ba ki kunna karatun Qur'ani in sha Allahu za ki samu salama da Aminci."
Sai na amsa mata da toh, bayan na ce ta ɗauko mini wayar a can falo, sai ga shi ta fita ta kawo mini ta kuma fice bayan ta yi mini sai da safe, kayan jikina na sauya domin sun jiƙe, na saka riga da wando na barci da hula sai kuma na saka wani ƙaramin hijabi domin ina jin sanyi, sai da na kwanta na rufe kafafuna da bargo sannan na ɗauki wayar tawa sai na ga Yallaɓai ya tura mini saƙo yanzu ba daɗewa.
"Ki yi haƙuri Sadiya ta. Ki sani auran da na ƙara ba shi ne zai cire ƙaunar da na ke yi miki a cikin zuciyata ba. Ki sani ke ce Yusuf haka Yusuf ne Sadiya mun zama Hanta da jini ɗaya ba zai iya rayuwa ba ɗaya ba. Kar ki ji a ranki cewa matsayin ki ya sauya ke ce a jiya kuma har da gobe ma ke ɗin ce.
Ina ƙaunarki Sadiya ta ƙauna mara yankewa. Na gode da dukkan sadaukarwarki gare ni, na gode da karamci da mutumtawa, na gode da yaƙana da martabawa ba, na yi miki alƙwarin adalci mai yawan da zan kwantata a tsakanin ki da Saudatu.
Ki yi barci cikin salama Amintattaciya ta."
In a baya ne Yallaɓai ya turo mini waɗanan kalaman yini zan yi ko kwana cikin farinciki amma yau sam sai na ji ba su yi mini tasiri ba, ban goge saƙon ba amma na yi saurin fita daga kan sunan shi, domin sai na ji kamar zuciyata na zugani da na rubuta masa cewa in har ya na sona kuma adalci zai yi mini to ya saki Gimbiya ya dawo gareni, abin da ba zai taɓa faruwa ba kenan shi ya sa na yi saurin fita daga wajen na shiga cikin wayata na lalubo karatun Qur'ani baƙara na kunna na ɗan rage ƙara na saita shi dai dai kunnuwana sannan na koma na kwanta ga casbaha a hannuna ina ja, daman na rage hasken ɗakin sai duhu, ina kwance ina ta hailala da salati lokaci ɗaya karatun na shiga kaina duk yadda sheɗan ya so ya fassara tunanina na kasa barcin ayoyin Allah sun fattake shi, haka na ji iskar natsuwa na shiga jikina da zuciyata sai ga ni na yi luf a kwance ina lumshe ido barci na son kamani barcin da ban taɓa tunanin zai iya ɗaukata a wannan daren ba.
Sai ga shi kuma ya ɗauke ni, ba ni na farka ba sai uku na dare har lokacin karatun Qur'anin ya na ta yi, sai da na juya sai na ga Amina a gefena ta na barci da waya ta daman na duba lokaci uku ta gota sai kawai na sauko daga kan gadon na yaye bargo karatun na kashe sannan na yi amfani da wayar na haska tunda na ga sun ɗauke wuta Tiolet na shiga na ɗauro alwala na dawo ɗaki na shimfiɗa sallaya sannan na saka dogon hijabina na kabbarta salla sai da na yi raka'a takwas sannan na rufe da shafa'i da wuturi, bayan na idar na tashi na ɗauko Qur'ani na fara karatu daga suratul Tauba, a hankali na ke yi karatun saboda kar na ta da Amina, ba ni na tsaya da karatu ba sai da aka fara kiran salla na biyu daga msallatan kusa damu sannan na dakata na ɗaga hannayena sama na roƙi Ubangiji juriya da hakuri sannan na roƙe shi da ya iya yi min a dukkan lamarin da ni ba zan iya ba ya cire min kishi da kyashi ya ba ma zuciyata aminci da salama na daɗe ina kai ma Allah kukana sanman na shafa, na kuma koma ina neman gafaran Allah da casbahan hannuna lalle Ubangiji shi ne ke saukar da duk waraka sai ga ni zuciyata wasai sai ma wani iskar da na ke ji ya na shigata na salama da aminci.
Ni na ta da Amina na ce lokacin sallah ya yi sai kawai ta juya ta ce min ba ta yi, fita na yi zuwa ɗakin kusa da ni sai na ga har sun ta shi ma Sameena ce kaɗai cikin bargo Farida ta ce min ta na hutu, na san da ga ita har Rahila sun yi mamakin ganina kamar ba ni ba, Farida ta kalleni lokacin da na ce ba ri na je na ta da su Marwa har na juya sai ta kira sunana na juyo ina kallonta.
"Ina ta jiyo karatun ki ɗazu."
Sai na mirmishi kafin na ce" Wai har kin jiyo?
Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" Nima da na kasa barci, fitan ki na ji ya sa bayan kin fito da ga tiolet ɗin nima na tashi na shiga na ɗauro alwala na yi nafiloli."
Sai na jinjina mata kai ban yi mgana ba itama kuma sai ta ta da salla, Rahila daman sallar ta ke yi lokacin da na shigo. Fita na yi zuwa ɗakin su Jidda suma sun ta shi manyan sai yaran ne ke ta barci ni na ta da Baby ta na mutsike ido na ce ta shiga tiolet ta wanke ido ta yo alwala, na fita da cewa in na idar da salla zan dawo mu yi azkar, haka ko aka yi ina idar da salla na koma ɗakin yaran na tattara su gabaɗaya baƙi da yan gida har da su Saude, na ce mu fara karanta azkar da karfi a tare, bayan mun gama na ce kowacce ta