na watsar da na asibitin na fara shan wanda Inna Mariya ta kawo min kuma ina jin daɗin shi, ya na wanke mara kuma in na yi fitsari ko bayan gida ina ganin abin da na ke fitarwa da datti daga cikina. Na farko har ya ƙare na sake yi ma Inna Mariya mgana ta sake karɓo min har kuma a lokacin ban bari ta ji labarin abin da ya faru sanadin mganin ba, ko ba komai bai kamata ta ji ba, domin yadda zuciyata ta yi ɗaci na ta zuciyar sai ta fi tawa yin ɗaci shi ya sa ko da wasa ban taɓa gigin faɗa mata ba. Kuma na gargaɗi Amina itama na ce kar ta je wajen surutun ta ta kwashe ta faɗa mata ga abin da ya faru. Shi ya sa har lokacin ba ta sani ba kuma ba na fatan ta sani ɗin har abada.
****
*Saturday*
29May. 2016.
Yau asabar ɗin karshen maƙo ne. Jidda da Baby sun tafi Tahfez. Ni kaɗai ce a gida Yallaɓai ba anan ya kwana ba jiya ya na gidan Gimbiya tun da ta koma gidanta satin da ya kamata. A bakin mijinta na ke jin cikinta wata biyar har ya na faɗa min ya yi girma tun da har ya fito, ni in Yallaɓai na surutansa ba na biye masa iyaka kawai na kalle shi in abin Allah ya sauwaƙe ne na ce in kuma na Allah ya kyauta na ce na kama kaina. Tun da na fahimci ya na jin daɗin yin hiran matar da ni sai ka ce ni ina da matsala da hakan ne.
Yau akwai ranar iyaye daga makarantar su Jidda. Kuma Yallaɓai ya sani an aiko da takarda kuma head teacher na class ɗin su Jidda ta kira sa ta faɗa masa, kuma an tura a group na makaranta tun da ya na ciki. Nima clasa teacher ɗin su Baby ta faɗa min tun da ina da lambarta muna mgana in wani abu ya taso ta yi min mgana na ce za mu taho ni da Yallaɓai. Tun da duk shekara suna yi domin tattaunawa cigaban makaranta da yaranmu.
Yallaɓai ya fi zuwa ni duka duka bai fi sau biyu na taɓa ba, ko a jiya da ya zo yi mana sallama yaran sun tuna masa nima na yi masa mgana ya ce daga can zai shirya sai ya biyo mu tafi tare. Amma Yallaɓai tun 10 na safe na shirya na zauna ina zaman jiran shi har Saude ta zo sha ɗaya da wani abu na rana Yallaɓai bai zo ba kuma in na kira shi sai ya ce min ga shi nan a saman hanya.
Raina ya ɓaci na ga dai ba office ya je ba ya na gida amma kuma ya na ta raina min wayau. Ko daga Zaria ne a awa biyun da Yallaɓai ya kwashe ai kamata a ce ya sauka, har na yi zuciya na ɗauko jakata zan tafi saboda taron goma da rabi ne ga shi har an ci rabin lokaci kawai ina fita haraba gidan sai ga shi ya shigo ya na maiƙon wata farar shadda har da babban riga ta angon cin shi ce shi da Gimbiya. Baki na saki ina kallon shi domin ganin shi na yi ya na wani annuri kamar wanda aka yi ma albishir da kujeran makka sai da ya matso kusa da ni sannan na ji ƙamshin mai daɗi da sanyi dake tashi daga jikin shi. Ban ma san na saki baki ina kallon shi ba sai da na ji ya na faɗin.
"Na yi miki kyau ne Madam?
Ya faɗa ya na rufe min baki. Hannunsa na kaɓe daga fuskata ina jifansa da wata uwar harara.
"Afuwan Abar ƙaunata."
Ya faɗa har ya na ɗaga hannuwa sama.
Kanar in yi tsaki sai kuma na fasa na wuce kawai na bar shi nan tsaye sai ya biyo bayana yana faɗin" Ba mu makara ba ki daina damuwa"
"Haba Yallaɓai in ka san lokaci za ka ɓata me ya sa ba ka ce mu haɗu a can ba?
"Mu haɗu can abin ai ya yi wani iri kuma? Gwara mu je tare zai fi ko?
Ya faɗa ya na kallona lokaci ɗaya ya na ƴar dariya. Ni ko na sake maka masa wata harara na fice daga gidan, motarsa a waje ya barta ce min ya ke yi ba zan rufe gida ba ne sai na ce Saude na ciki sai kawai ya jawo kofar. Yallaɓai bai faɗa min ya ɗauko Amaryansa ba na je da ƙarfina na buɗe gidan gaba da niyar shiga kawai sai na gan ta a zaune ta kame ta ci uban gayu gyale a kafaɗa har da saka wani glass baƙi a fuskarta. Sannan kamar yadda mijinta ya faɗa ne ga cikinta ko har ya fito ta cikin doguwar rigar da ke jikinta kamar ma ado ta ke yi da cikin. Tiƙashi.
Sai gani tsaye galala ina kallon ikon Allah. Ita ko da ta ganni ko a jikimta sai ma gilashin fuskarta da ta cire ta na faɗin" ina kwana Madam"
Na kasa amsawa sai Yallaɓai da na kalla lokacin da ya ƙariso yanayin kallon da na ke yi masa ne ya sa ya yi saurin cewa.
"Tare zamu je saboda da ga can zan sauke ta gidan Naja"
Kuma ya na gama faɗin haka ya buɗe bangaren direba ya shiga ni kuma ina tsaye kamar wata sakara. Dakyar na iya fusko numfashina sannan na iya matsawa baya ina matsawa ta saka hannu ta rufo ƙofar gaban da na buɗe. Duk sai na ji na muzanta har zan buɗe ƙofar gidan baya in shiga sai wata zuciyar ta hana ni. Wato su suna gidan gaba suna shan soyayya ni kuma ina gidan baya kamar almajira sai kawai na juya na zagaya ta can bangaren Yallaɓai ina zuwa sai ya sauke gilas ya na faɗin.
"Ki shiga mana ba ke kike ta faɗan mum makara ba?
Da idanuwana da suka kusa fallasa asirin da ke zuciyata na ce amma na danne ina faɗin" Ku je kawai"
"Ban gane mu je kawai ba "
Ya faɗa cikin mamaki.
"To ai na ga ba sai mun je mu biyu ba tun da ga Gimbiya ku je kawai ni ba sai na je ba."
Na ɗauka Yallaɓai zai matsa min sai na je amma ga mamakina sai kawai ya rausayar da kai ya na faɗin.
"Kin tabbata mu tafi bakomai?
Sai na gyada masa kai cikin ƙarin mamakin sa.
"Ku je kawai. Itama kamar uwa ce a wajen su Jidda."
"Gaskiya ne to mun gode da kara Maman Jidda."
Ya faɗa ya na kallon matarsa har ya na kashe mata ido. Ni ko kaina na kauda ina faɗin" Sai kun dawo"
Ina jin ta ta na faɗin" Allah ya sa" daga haka na wuce ko waigensu ban yi ba jakata na laluba na saka key na buɗe get ɗin domin in na na tsaya bugawa ɓata lokaci ne Saude na cikin gida kafin ta ji sai na daɗe. Haka na koma gida ina ƙara mamakin Yallaɓai ashe daman ni ya shanya ni ya na can ya na cin soyayyarsa bayan sun gama kuma ya tsaya jiranta ta shirya ni kuma ga ni shegiya ina ta zaman jiran shi kuma tsabar wulakancin namiji bai faɗa min tare suke ba sai dai kawai na je na ganta kuma ya na faɗin wani wuri za su wuce daga nan kenan sai dai na hau adaidaita na dawo gida. To ai Yallaɓai bai isa ya wulaƙantani ba in ma ya shirya na shiga gidan baya ne su suna gaba suna soyayyarsu sai dai duk abin da ya shirya ya koma masa. Tsabar ma daman ɗaukonin da za su yi kamar cikas ne gare su ina cewa su tafi gabaɗaya suka yi murna kamar daman ni ɗin lalura ce a wajen su.
Yini na yi a gida ina kunci ni kaɗai. Da su Jidda suka dawo daga makaranta suna tambayan ko mun je makarantar su? Na ce Abban su ne ya je ni ban samu zuwa ba, shi kuma Abban na su sai dare ya zo gidan. Ƙala ban ce masa ba nima bai yi min mgana ba yaran dai suka zagaye shi ya na faɗa musu yadda malaman su suka yaba musu sosai. Baby dai ya ce teacher ɗin ta, ta ce ta fara saka wasa record ɗin ta ya fara ɗan jan baya.
"Ki daina wasa kin ji ko My Baby?
Ha faɗa ya na shafa kanta sai ta gyaɗa masa kai. Kwanto da da ita ya yi a saman jikinsa ya na faɗin" Anty Gimbiya ta ce ki ƙara dakewa za ta siya miki ipad na karatu."
Baby na jin haka ta fara tsalle Yallaɓai ne fa ya yi zaune ya na faɗa musu tare da Antynsu Gimbiya su ka je makarantan na su, suna ta murna ni dai yadda bai ce Sadiya ji ba, nima ko ban nuna na ji ba. Bai jima ba ya yi musu sallama ya wuce ni ina ganin ma zai tafi sai na shige tiolet domin na gaji da ganin yaudaran Yallaɓai ya na ƙara ɓata min rai matuƙa.
Washegari lahadi gidana Yallaɓai zai dawo da yamma. Bayan jiya sun yini tare yau ma tare suka yinin kawai da ya tashi dawowa sai ga shi ya ɗauko min matarsa ta sha gayu cikin wata doguwar rigar yadi mai baza a ƙasa. Ta yi rolling mayafi a saman kanta fuskar nan har tana maiƙo saboda hoda. Bakin nan ya na sheƙi saboda ƙyalin jan baki. Ta kawo ma yara cake ne da donut amma ni na san ba haka ya kawo ta ba, ta rako shi ne ko kuma shi ya ce ta rako shi ba su gaji da ganin juna ba.
Tun kafin mangariba suka shigo gidan har ya fita salla ya bar mu. Ɗakin yara na bar ta tana salla nima na shiga ɗakina na yi, tuwon miyar allayu na yi mana. Har bayan isha'i tana gidan tare muka yi dinner har mamakin yadda Yallaɓai ke kafa kafa da ita na ke yi, ita ko sai wani iyayi ta ke wai ita mai ciki. Duk na gani na nuna ban gani ba, bayan mun gama cin abinci na ga dai Yallabai ya ce zai mai da ta gida har na ka ba shi da niyyar haka sai ma yara da ya kora falon su mu kuma sai ya kunna mana ya zauna saman kujera mai zaman mutum biyu ita kuma Gimbiyar ta na zaune a gefen shi ya na ba ta labarin wani American film da suke haskawa a MbAction.
Ni ko ina kan kujeran Dining ban ta so ba ina kallon ikon Allah kamar ma fa ya manta da ni ne, sai can ne da ya juyo ya ganni sai ya ce" Kika zauna acan?
Sai kawai sa ya sake juyawa ya na ce ma Gimbiya.
"Kin san ita ba ta damu da kallo ba."
Tsabar takaici sai kawai na miƙe ina tattara abubuwan da muka ɓata zuwa kitchen daga can ban dawo ba, falon su Jidda na tsaya na ce su kashe kallon in suna da sauran aikin makaramtan da ba su yi ba su ɗauko su duba gobe akwai makaranta suka ce min to. Daga nan na yi wuceta ɗaki domin ba dole aka yi min da sai na zauna ina kallon wulaƙanci da Yallaɓai ya shirya min a falona ba.
Kai tsaye na shiga tiolet na kama ruwa na dawo na yi shirin kwanciya. Na kwanta kenan sai ga shi ya shigo.
"Kin kwanta ne kuma?
Dago kaina na yi ina kallon shi amma ban yi magana ba.
Amma kaɗan ya rage ban amsa mishi da cewa" To kar na kwanta na zauna ina muku gadi."
"Kin bar Daughter ita kaɗai ko?
Kamar na yi masa tsaki sai na fasa kawai sai na mai da kaina saman filo ina faɗin" Ba ga ka ba?
Sai ya yi dariya kafin ya ce" Haka ne. To zan mai da ta gida ko za ki zo ku yi sallama ne?
"A'a na riga na kwanta. Ka faɗa mata mun gode mu kwana lafiya."
Kamar zai yi magana sai ya fasa ya dai ce Amin ya fice. Ina jin fitar shi da mota wallahi sama da awa ɗaya sannan Yallaɓai ya dawo gidan kuma don ba shi da kunya ya dawo ya na ƙwaƙwumata sai ko na yi masa barcin ƙarya dole ya ƙyaleni, abin da ke ba ni mamaki matar nan ta na da mota amma duk in da za ta je shi zai kaita na rasa gane ita motarta amfanin da ta ke yi da ita. Ko aikinta da ta koma wata rana shi ya ke kaita kuma ya koma ya ɗaukota ranar dai na gaji na yi masa mganar ita motarta ba ta fita ba ce ta ado ce?
"No kawai kin san yanayin da ta ke ciki ni na ce ta daina driving in dai ina kusa zan riƙa kai ta duk in da za ta je."
"Ba shakka."
Na bashi amsa cikin renin wayau ina taɓe baki amma sai ya basar da cewa.
"E mana. Ke da ita kun maida ni direban ku da ƙarfi da ya ji."
Kamar na ce ita dai ka ke yi ma aikin direban ci, ba ni ba sai kuma na fasa ban bashi amsa ba amma Allah na tuba tun ina amarya Yallabai da ko keke bai da shi adaidaita na rika yawo da ƙafata. Duka duka yaushe ya yi motar? Bayan tarewaan mu gidan nan ne fa, kuma ni dai a sananin ba ko'ina Yallaɓai ke samun damar kai ni ba, yawamci na fi yawo a cikin adaidaita. Duka kuma cikin Jidda da cikin Baby haka na riƙa zaryan asibiti a cikin adaidaita, duk bai duba condtion ɗina alokacin ba sai yanzu tun da yar gwal ta yi ciki ai ba zai bar ta ta riƙa tuƙi ba. Tsabar haushi ma ban ƙara tanka ma maganarsa ba na dai ɗauka da ya cigaba da maganganun sa zai kuma gangaro kan cewa nima ya na jigila da ni a motar shi a baya ni ko na yi masa wankin babban bargo don na lura bai san ina masa kawaici ba.
Yallaɓai bai daina kwaso mini matarsa duk ranar girkina ya na kawo min ba. Alhalin ranar girkinta ba na ganin shi sai dare in ya ta so daga wajen aiki ya biyo mu gaisa amma ita in ya na gidana tare suke yini. Na yi musu bakam ina auna tunaninsu na ga daga shi har ita sun maida ni shashasha. Ranar ko na yi niyyar taka musu burki ranar da aka kai sadakin Marwa da kayan saka rana aka saka wata takwas lokacin ta kamallah makaranta ta dawo gida. Ranar daman ya na gidan ta ne, da yamma zai dawo gidana kuma daman tare da Yallaɓai aka je aka yi komai tare da su Kawu Sa'adu.
Bayan sun dawo ne shi ya tsaya gidan Gimbiya ya yi wanka kuma kawai ya ɗaukota suka taho tare. Ni daman ina gida amma suna tafiya Ya Aina ta kirani ta faɗa min an saka rana na riƙe hanci na rangaɗa guɗan farinciki ni kuma na shiga group ɗin gidanmu na sanar da su. Duk farincikin da na ke ciki da na ga Yallaɓai tare da Amaryansa sai da na ji raina ya ɓaci muna zaune afalon bayan ya dawo daga sallar isha'i har da yara gabaɗaya
"Sai kika ji yau dai Finally Kawu ya fara taka matsayin girma."
Yaƙe kawai na yi masa kafin na ce" Wallahi fa yanzu Ya Aina ta kirani ta na faɗa min."
Ita ko ƴar iya sai buɗe baki ta yi ta na faɗin" Ma sha Allah. Allah ya sanya alheri."
Ya amsa mata da Amin kafin ya ce" Lkacin kin haihu za a yi bikin ko?
Ya faɗa ya na yi mata wani kallo sai ta kauda kai ta rufe fuska ta na yarfa masa hannu kafin ta ce"
"Kunya na ke ji Daddy"
Ta faɗa cikin shagwaɓa kawai sai Yallaɓai ya kalleni ya na faɗin" Sadiya kin ji ƙanwarki wai kunya ta ke ji in na yi maganar haihuwa."
Kamar na ɗura ma shege ashar haka na ji, haka kurum Yallaɓai na neman ƙure haƙurina. Ai ban san lokacin da na basu amsa dai-dai da kalamansu ba, da ga shi har ita sai da suka kalleni. Amma sai da na ce Jidda da Baby su koma falon su suna ficewa na kalle su ina faɗin.
"Kunyar me? Cikin? Ita ko ba ta ji kunyar yadda ta samu cikin ba ne sai fitowar cikin ne ta ke ji ma kunya?
Sun kalle ni dukkansu kuma daga nan ba su ƙara mgana ba yan jakar uba ai sai ya sauya hira. Kan dai auran Kawu da Marwa ne ya na cewa kowa sai mamaki ya ke yi in ya ji an saka rana ana faɗin ashe dai Abba dai da gaske ya ke yi, tun ina amsa shi har na gaji na yi masa banza na bar ma ta hira saboda na ga sai tsoma baki ta ke yi cikin yanga da iyayi.
Agogon bangon falon na kai ma duba tara har ta gota kawai sai na tashi ina faɗin.
"Zo ka ji mana Yallaɓai."
Ya ɗauka wata maganar arziƙi ne ya miƙe ya biyo bayana ya na faɗin" Mu je ta samu ne Sadiya ta? A raina na ce za ka ga samuwa har ɗakin barcin mu na kai shi na rufe ƙofa na tsaya ina kallon shi.
"Me ya faru?
Domin na san ya sha jinin jikin shi ya san mgana ce a bakina.
"Yallaɓai ban ga ne sabon salon da matarka ta fito dashi ba. Ko na ce sabon salon da kai ka fito da shi ba."
"Wani irin sabon salo? Ban ga ne ba?
Ganin ya na neman raina min wayau ya sa na gyara tsayuwa ina faɗin" Duk ranar da za ka dawo gidana sai ka kwasomin matarka ta zo ta raba min dare a gida ina so na sake da mijina ta bi ta kankame ta hanani sakewa. Sannan bayan duk haka bai ishe ta ba sai ta ƙara jan ka ka je mai da ta gida nan ma ka ƙara ɓata lokaci kafim ka dawo! Shin wai me hakan ke nufi ne? Ko wani tsari ne ka fito da shi ni ban sani ba? Tsabar ma shiga haƙki ko ƴaƴana ka ga ina tura mata ranar da kake