Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   33 / 48

96K to 99K   out of 141.5K words

iya wannan ashar ɗin ba."

"Abin ne na ji kamar ma na yi zage zage"
"Me ye a ciki? To ai ta aure shi to gida kuma don ta zauna ai duk abu ɗaya ne Munnira. Ni dai fata na mu rabu lafiya kawai "
Duk yadda ta so ta nuna min kar na yarda ta zauna ba ta aiki kuma ina bata miji ban nuna na gane ba, ni yanzu me zai dame ni? Abin da na ke ma gudu da kishi tuni ya faru to me ya yi saura? Ciki gare ta fa kuma cikin ba na kowa ba sai na Yallaɓai to me ya yi saura? Babu saboda haka mganar gida ko kwana ƙaramin abu ne a waje na tunda na iya hakuri na bari muka raba mijin da ita ai kuma an gama mgana.

Daman ni a raina na yi niyyar na ce Yallaɓai ya yi sati a ɗakin Gimbiya ban dai riga na furta masa ba amma ina da niyyar haka har a cikin raina. Ranar da ya cika kwana uku a ɗakin Gimbiya ina shirin sai ya dawo da daddare na ce masa kawai ya yi mata sati kafin ya dawo wajena amma sai na ga da safiyar Allah Yallaɓai ya fito min da munafuci wai ni Yallabai zai mayar ƙaramar yarinya muna karyawa a saman dining ni da shi yara sun tafi makaranta. Gimbiya kuma ta na ciki ba ta tashi ba tukunna. Sai ya kalleni ya na min duniyan cin da ya koya tun da ya yi aure nan.

"Abar ƙaunata."

Sai na kalle shi amma ban yi magana ba.

"Na gode."

"Wannan godiyar fa?

"Ta ki ce, ki karɓa da martabawa."

Sai na yi mirmishii kafin na ce" To shike nan na karɓa."
Tun da na ga yanayin shi na san cewa tabbas wani abu ya ke so, shi ya sa sai wani kashe murya ya ke yi ya na wani ja na da hira, sai faɗa min ya ke yi yanzu kwangila biyu ne a kan tuburin shi akwai na gina wani ƙaramin ma'aikata sannan akwai ma na Kaduna again faɗa min ya ke yi wattanin nan ya na ta samun aiki sai godiya.

"Ma sha Allah. Allah ya sa albarka ya kuma ba da sa'a."

Ya amsa min da Amin ya na faɗa min zuwa gaba in komai ya dai dai ta, ya na so shima ya gina kamfanin shi ko ƙarami ne kafin zuwa gaba, ni kuma sai na ce ai hakan ya yi saboda komai na son cigaba, kuma babbar cigaba ne a gare shi tun da ya na samun manyan kwangiloli mun daɗe muna tattauna abin da ya shafi aiki sannan muka ganganro kan maganar Gimbiya wai ni Yallaɓai zai zaunar ya na kallo na ya na min bariki da munafuncin su na maza.

"Ina faɗa miki jiya fa Daugther sai ciwon ciki cikin dare."

"Subhanallah me ya faru?

"Ni ma ban sani ba, ta ɗan yi kukan cikin ne amma ina ba ta mganinta sai kuma ya lafa sannan ta yi barci."

"Allah ya ƙara lafiya. Ko dai za ku je asibiti ne?

Sai ya girgiza min kai kafin ya ce" Na ce mu je asibiti ta ce min wai cikin ya bari."
Sai na kalle shi amma ban yi mgana ba sai na ji ya cigaba da cewa" Ni tunani ma dare Sadiya. Amma dai na ce ga waya nan tun da muna tare in wani abu ya faru kawai sai ta kira ni ko?
Ƙura masa ido na yi ina kallon shi sai ya ƙara cewa" Ko? Na ce ai ga waya ma da ta ji wani abu ta kirani ko ta kira ki."

Har Yallaɓai ya gama lissafin kwanakin shi ya ƙare a ɗakin Gimbiya ba ya so ya ce min zai riƙa kwana a can saboda kar cikin dare wani abu ya faru kai tsaye shi ne zai shiryamin alaye kamar ni ɗin ƙaramar yarinya ce.

"Ba ki ce komai ba?

Ya faɗa ya na goge bakin shi da Tissue, sai na yi masa wani irin kallo kafin na yi mirmishi.
"Me zan ce! Ai ba sai ta kai ga haka ba. Daman ina shirin na faɗa maka cewa ka yi zaman ka a ɗakin Gimbiya har ta samu lafiya ta koma gidan ta."
"Saboda mene?
Ya faɗa ya na kallona irin me ya sa kika min haka ɗin nan.
"Saboda cikin dare mana? Ba fata mu ke yi ba in wani abu ya faru kiran waya zai yi wahala gwara dai ka na kusa ɗin zai fi."

"Ban gane ba."

Ya faɗa ya na kallona ni kuma sai na miƙe ina tattara kwanakun da muka yi amfani da su lokaci ɗaya ina faɗin" Shi ne na ce ka cigaba kawai da kwana tare da ita har ta samu lafiya ta koma gidan ta."
Ina gama faɗin haka na kwashi kayan hannuna na bar masa falon, ni sai ma ya ba ni dariya daman wai Yallaɓai ya iya alayen magana haka? Ai ban taɓa sani ba sai yau ƙwalla suka cika min ƙwarmin idanuwana yau har an yi lokacin da Yallaɓai ba ya son kwana dani sai da wata macen. Har an zo gabar da zai ji gwara ya riƙa kwana da mataras sama da ni. Ni ce fa Sadiya. Sadiyar shi da ban taɓa tunanin wata rana da za ta so Yallaɓai ya ririta wata mace bayan ni ba, sai ga shi ya na faruwa a lokacin kusan ma da ban yi tunani ba.

Ina kitchen din ya biyo ni ya na borin kunya. To borin kunya mana Yallaɓai ya kalli tsabar idanuwana ya na faɗin" ban gane na koma wajen ta gabaɗaya ba? Da wa kika yi shawara kafin ki yanke hukunci?
Ni ko na ce ai maganar ba ta bukatar shawara shi ya sa ban faɗa masa ba. Sai ya fara kunyata kan shi ya na faɗin" To ni ban amince ba. Ki ma bar wannan mganar."

Shuru na yi masa kawai saboda ba na so maganar ta yi nisa. Ya zo ya rumgumeni ya sumbace ni a goshi ya na faɗin" Sai na dawo." Na yi masa fatan dawowa lafiya ina ganin shi sai da ya shiga ciki ya duba Gimbiya sannan ya fice, ina aiki ina danne abin da ke ta so min a ƙasan raina ina ƙara karfafama kaina gwiwan da komai ma zai wuce in sha Allahu, duk rashin son aikina yanzu na zage Saude na makaranta sai al'hamis zuwa lahadi ta ke zuwa. Ko kafin Gimbiya ta tashi barci na gama duka aikina har na yi wanka sai da na fita falo na ganta zaune muka gaisa cikin faram faram ɗin da muka saba. Maaganar abin da za ta karya na yi mata sai ta ce.

"Madam in da zan samu kunu da na so."

"Ina da sauran garin kunun ai bai ƙare ba sai na dama miki."

"Na gode Allah ya saka da alheri."

"Amin. Bakomai."

Na faɗa ina kallonta, sai na ga ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa sai na dawo ina faɗin" Na manta ya jikin? Yallaɓai ɗazu ya ke faɗa min jiya cikin dare ciwon ciki ya taso miki.?
Sai ta kalleni kafin ta yi mirmishi ta na faɗin" Laa ba fa wani abu ba ne, wai sai da ya faɗa miki?
Sai na gyaɗa kaina kafin na ce" Allah ya ƙara lafiya. Ina fatan dai ba matsala?
"Babu matsala, kawai cikina ne ya ɗan lalace amma ba matsala "

"Ayya sannu. Allah ya ƙara lafiya"

Ta amsa da Amin sai na ce ta kunna Tv mana zaman shuru ba daɗi sai ta ce ba ta son hayaniya. Sai na ƙyaleta na tafi kitchen na ɗora mata ruwan zafin sannan na ɗauko garin kunin na dama, tsamiyar tawa ma kaɗan ta rage ita kenan na yi mata amfani da shi har garin kunin ma ya ƙare daman Maman Saude ce na aika ma gero ta daka min dole itama zan ƙara yi ma mgana ta sake daka min tun da Gimbiya kokon ta ke sha ai saboda ita ne gero har tiya goma Yallaɓai ya siyo ya ijemin ni dai ya san ban cika shan kuni ba in dai ba azumi ba, zai yi wahala na sha kuni sai dai kuma in ba ni da lafiya Yallaɓai ma sai irin shekara bayan shekara gaskiya tun da na ga an kawo gero na san saboda wacce aka kawo shi.

Bayan na dama mata ban saka mata siga ba saboda ba ta so na kuma kawo mata har falo, ta karɓa ta na ta min godiya. Mun ɗan zauna ni da ita muna ɗan taɓa hira sama sama kafin ta gama shan kokon ta ce min za ta je ta sha mgani ta ɗan kwanta na ce mata to. Tun da ta shige ciki sai ni kaɗai a gida sai can da rana sai ga Naja'atu ta zo itama muna gaisawa ta shige ciki, daman haka suke yi da sun zo domin ita daman suka zo za su shige ciki.
Ni daman muna ta waya da mai hijabai za a kawo min wasu sannan na saka a ɗinka ma Amina domin ta ce ta yi talla ana so. To shi ne za a aika mata kaduna ni ma za'a aiko min dashi, da daddare tuwon shinkafa na yi miyar ganye Naja'atu sai mangariba Direba ya zo ɗaukanta ashe ƙasar za su bari ita da mijinta shi ya sa ta zo yi ma ƙawar ta ta sallama nima da suka fito ne Gimbiyar ta rako ta ta ke faɗa min na ce Allah ya tsare hanya.

Yallaɓai ya ɗauka na bar maganar sai ga shi ya na dawowa, bayan ya shiga ɗaki na ya yi wanka ya fito falo ya ni da shi da yara har da Gimbiyar muna cin abinci ita kaɗan ta ci tuwon miyan ne ta ɗan sha da yawa. Ni da Yallaɓai ne muke hira ita kuma daman yara ne abokan maganarta, ban sanin musu ba amma ba ta sakin jiki ta yi hira da shi in dai ina wajen gwara shi ma ya na ɗan janta da mgana ita ce za ka ga ta na wani sunne kai, amma na san in sun shiga ciki ba za su rasa yin hiran su ba.

Ni da Yallaɓai mun daɗe a falo muna kallo daman in dai ya ga ana Horror film sai ya ja ni ya ce mu kalla tare. Yara tuni sun shige ciki Gimbiya ma ana fara ta tashi ta ce ba ta kallon fina finan tsoro har ya na zolayanta da cewa" Ke ba Jaruma ba ce Daugther amma zan koya miki kallo kamar yadda na koyar da Sadiya ta."
Banza da shi ta yi ta shige ciki ta na yi min sai da safe ta bar ni da shi ya na ta takalata da hira ni ma da na gaji sai na fara yi masa hammar ƙarya, na kuma ce masa ina jin barci zan je na kwanta har na miƙe sai na kalle shi kafin na ce.

"Sai da safe."

"Sai na shigo dai ko?

Ya faɗa hankalin shi na wajen kallo.

"Ka manta! Ai a ɗakin Gimbiya za ka kwana."

Sai ya ɗago ya na kallona kafin ya ce" Ba na ce a bar mganar ba."
"Ba za a barta ba. Domin da gaske na ke yi."
Kallona ya yi ni kuma sai na juya ina ƙara faɗin" Mu kwana lafiya."
Na yi wuceta ciki Tiolet na shiga na kama ruwa sannan na koma ɗaki na sauya kaya zuwa na barci ina shirin kwanciya sai ga shi ya shigo sai na kalle shi kafin na ce" Ba mun yi sallama ba?

Karisa shigowa ɗakin ya yi ya na faɗin" Sadiya me ya sa kika yi hakan?
"Saboda hakan ne ya kamata. Ba ta da lafiya gwara ka riƙa kwana a kusa da ita."
Sai ya yi shuru bai yi mgana ni kuma sai na zauna a gefen gado ina faɗin" Kar ka damu ba matsala ni na ce ai ka je."

"Kin tabbata ba matsala?

Sai na kalleshi ina jin takaici in Yallaɓai ya yi min tambayar nan daman zai yi min kishiya ne ya ce min kuma ba matsala. Ban nuna masa ba illa ƴar dariya da na yi kafin na ce" Na ce ba matsala ka je kawai."
"Na je bakomai?
Sai na gyaɗa masa kai sai na ga ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Na gode. Allah ya tashe mu lafiya."
"Amin."

Takowa ya yi zuwa gaba na ya duƙa ya na sumbatar goshina.

"Sadiya."

Ya kira sunana na ɗago ina kallon shi kafin na yi mgana ya ce.

"Sai da safe."

"Sai da safe."

Na mayar masa da martanin mganarsa har ya juya zai tafi sai gashi ya ƙara juyowa ya na kallona kafin ya ce" Ko za ki ɗauko yara ne?
"Bar su kawai yau ni kaɗai zan kwana."
Sai na ga ya kalleni ni wannam makircin na Yallaɓai ya fara ba ni dariya wai yau ya saba tafiya ya bar ni? Da ya ke barin gidan ma gabaɗaya fa? Duk bai yi haka ba sai yau.

"Ka je kawai Yallaɓai bakomai"

"Kin tabbata?

Sai kawai na kwashe da dariya kafin na ce" To ko da wani abun akwai abin da za a fasa ne?
Sai ya ware min ido ya na kallona ni kuma sai na cigaba da faɗin" Ba abin da zai canza Yallaɓai, mene ne a cikin kwana? Tun da na yi sharing ɗin ka da ita an gama mgana. Kwana a ɗakin ta ba zai rage ni ba kuma ba zai kare ni ba saboda haka ka je kawai sai da safe."

Ina gama faɗin haka na koma na kwanta ina mai rufe kafafuwana da bargo har ina lumshe ido, shima ganin haka ya sa ya ja siraran kafafun shi ya fice na bi shi da kallo daga wutsiyar ido na sai da ya fice ya jawo min kofa sannan na sauke ajiyar zuciya ina mai ƙara jinjina halin Maza in suka ƙara aure. Na daɗe ban yi barci ba sai can kuma barcin ya ɗauke ni har sai da na makara domin sai bayan da Yallaɓai ya dawo sallar asuba sannan ya tashe ni a cewarsa ya ɗauka na tashi ne.
Da safen ne bayan Gimbiya ta fito mun gaisa sai take ce min wai Yallaɓai ya ce na ce ya riƙa kwana a wajenta har ta koma na ce haka ne, sai ta kalle ni kafin ta ce

" Ba komai ai na ji sauƙi wallahi."

"Duk da haka dai gwara ya na kusa da ke."

Ina kallonta ta na ta mirmishi amma ba ta ce komai ba a raina na ce munafukai to daga ita har shi ɗin suna ji da munafuci da gulma. Ranar an yi baki daga Rano, Yayarta Mardiya da wasu ƙannen Hajiyar Tafida suka zo duba ta, ni na yi musu girki suna ta min godiya Yayar tata har ɗaki ta same ni ta yi min godiya a kan yadda na ke kula da Gimbiya na ce bakomai ai an zama ɗaya sai La'asar suka bar nan zuwa gidan Nene. Ranar asabar kuma Anty Maimuna ce ta zo da yaran ta nan suka yini a ɗakin Gimbiya ni dai iyakata na girki na ba su shi ne aiki na sun ƙule a cikin ɗaki ana hira ana shewa saboda can da Yamma ma Anty Bahijja ta zo gidan. Ranar lahadi ma an yi baƙi ƙawayen Gimbiyar su biyu sun zo duba ta suna ta min taɓe taben fuska ni kuma ban ba su fuskar da za su rena ni ba ni da gidan mijina ba matar da ta isa. Suma ciki suka bi ta ranar ma Dambu na yi kuma sun ci sai la'asar suka tafi a daran ranar aka kawo min hijabai na Amina ma mun yi waya a ranar aka tura mata na ta.

Washegari litini kuma ina da komawa asibiti kuma magunguna sun kare shi ya sa na shirya na ce ma Yallaɓai zan koma asibiti amsar da ya ba ni lokacin ta ƙara sakani mamakinsa.

"To dole sai kin koma yau ɗin ne?

"E zan koma saboda magunguna sun ƙare gabaɗaya."

Sai na ga ya yi jim bai ce komai ba sai na gyara tsayuwa ina faɗin" Me ya faru?
Lokacin ma wanka na ke shirin shiga shi kuma ya na zaune a saman gado ya na aiki a system ɗin shi.

"Ina tunanin in kika tafi wa zai zauna da Daugther?

Sai na buɗe ido ina kallon shi, daman ai a rina an saci zanin mahaukaciya. Kamar ya ɗauke ni aiki na kula masa da mata har da cewa ya na tunanin in na fita wa zai zauna da ita? Kamar wata jaririya mata ta ji sauƙi in ta yi baƙi ta na dariya da shewa in a waya ne haka zan ji ta na ta rera hira rai rei amma ya na faɗa min in na tafi wa zai zauna da ita.

"Ko za ki ɗaga tafiyar ne zuwa Next week?

Kallon shi na yi irin kallon ba ka da adalci, wato na fasa zuwa asibiti na zauna a gida saboda matarsa da na ciki. Kawai sai na juya na hau tuɓe kaya ƙala ban ce ba, shima bai yi mgana ba na jawo towel ɗina na saka na fice na bar masa ɗakin, ina wanka ina jin takaicin Yallaɓai. Gaskiya wasu mazan ba su da adalci, haka kurum na fa sa zuwa ganin likita saboda matarsa? Duk mutumcin da na yi masa baya gani. To lalle ko yau zai sha mamakina daman da safen nan bayan ya dawo kai yara makaranta Salisu ya yi tafiya shi ne ya shigo ɗaki na ya zauna da na yi magana sai ya ce wai ta kwanta barci ne ba ya so ya dame ta, ni kuma tun da likita bai ba ni hutu ba sai ya zo ni ya dame ni shi ya sa na haɗe raina ban sakin masa fuska ba sai da na yi masa mganar zuwa asibiti shi ne zai tare ni da mganar banza.

Ko da na fito wanka baya ɗakin na yi tsaki a raina na ce shirme kawai. Agurguje na shirya na saka hijabina sabo dogo har ƙasa, na ɗauki jakata a hannu da takalmina ina fiowa sai ga shi ya fito daga ɗakin Gimbiya sai muka haɗe.

"Sai ina kuma?

Ya faɗa ya na kallona nima ko ina kallon shi na ce" In da na ce maka zan je"
"Asibitin?
Sai na ɗaga masa kai, na duƙa ina saka takalmi kafata na saka safa gajera na zamani

33 / 48